Showing 66001 words to 69000 words out of 126208 words
Chapter 23 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
awajen sonshi na shawagi da ita,sai kuma ta tuna yau akwai partyn da zata saboda haka da
sauri ta juya zuwa cikin gida.
Qarfe biyar ta fito daga kamfanin kaman yadda qa'idar lokacin tashinsu yake,saidai gaba
daya hankalinta ba'a kwance yake ba saboda baqin hadarin daya hado yake kwance a sama
yana shirin zub da ruwa.
Kusan mutum uku ne sukayi mata tayin sauketa a gida amma ta doje don kare mutunci da
qimarta,ciki harda alhajin dake nacinta wanda ta lallaba ta fito abinta ta baroshi a office din
rayyan mai kamfanin gaba daya suna lissafin wasu sarqoqi da sukayi masa,haka ta fito cikin
ranta tana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya qalau.
Titin babu wadatar motoci sai jifa jifa,ko dama can titin bashi da wadatar wucewar ababen
hawa musamman ma na haya,yawanci saina gida,hakan ya sanya ta kusa kashe minti goma
tsaye ba tare da taga gilmawar wani abun hawa na haya ba,cikin abinda bai gaza minti biyar ba
hadarin ya taso sosai,iska ta shiga kadawa ko ina sama ta sake duhu,fargabarta ta dadu,ta
runtse ido tana jin saukar ruwan saman bisa fuskarta,Allah dai yayi saiya daketa.
A hankali yake tuqin saboda yanayin ruwan dake sauka din,uwa uba yanajin kaman yayita
shawagi saman titi ba tare daya koma gida ba,yakan kasance cikin kewa da kadaici duk sanda
ruwan sama irin haka ke zuba yana cikin gidan shi daya,yakan tuna masa wata hira da suka
tabayi da uta,duk da yadda yakeson bunne komai nata amma duk lokacin da ake ruwan sama
kaman haka sai hirar ta fado masa
"Nafison damina akan kowanne yanayi,tana saka nishadi cikin zuciya,komai yana wankewa yayi
fes,tsirrai zaka ga sunyi kyau ya anwar sunyi kore shar,kosu kasan suna farinciki da
zuwanta,qamshin qasa iska mai dadin da babu kamarta" tayi maganar ne idanunta na
alumshe,saita budesu tar cikin nashi a lokacin da ya zuba mata ido yana tayata murmushin da
takeyi na tuna yanayin da tayi
"Kasan me yaya anwar?" Ta tambayeshi wanda bata kai ga fadin abinda takeson fada din ba
kiran nafisa a sannan ya katsesu,dai dai sanda shima nashi tunanin ya katse yana hango
tsaiwar wata matashiya cikin ruwan saman da har hazo hazo yake,tsurawa wajen ido yayi yana
ci gaba da tuqin a mugun slow kai kace motar na dab da mutuwa ne,baikai ga qarasawa ba
wata farar mota ta yanko daga layin da yake kusa da ita,dab da ita ta tsaya na cikin motar ya
fito riqe da lema ya iso gabanta ya matsar da lemar zuwa kanta da alamu magana yake
mata,idanu ya runtse yana tsaida motar duk da a tsakiyar titi yake,idanunsa qur akansu,alokaci
shahida ta sake ja baya
"Ka wuce kawai,bani da damuwa nasan ko ban samu mota yanzu ba ruwan daya tsagaita zan
samu"
"Haba yallabiya,ke kuwa yau dai kawai,uzuri ne fa,kiga yadda ruwa ke dukanki ke daya atsaye
anan,uwa uba tsaiwarki a titi irin wannan lokacin hatsarine ga rayuwarki"kai ta girgixa
"ba komai Allah zai kareni"
"Duk da haka amma kiyi...." Ta gaji dajin kalaman bakinsa,saboda haka kaman adan hasale
tace
"Don qaunarka da mahaliccinka kayi tafiyarka" ya fuskanci kaman tanason hasala ne don haka
yace
"Allah ya baki haquri,naji zan tafi,amma kema don qaunarki da mahaliccinki ki karbi wannan
lemar" batason dogon zance saboda haka tasa hannu ta amsa,ya koma ya shiga motar ya
tasheta ya wuce,ajiyar zuciya ya saki ganin tafiyarsa,duk da haka saiya kasa tafiya yaci gaba da
tsaiwa kaman me gadinta.
Ganin ruwan yadan fara sauqi saita soma takawa don canza wani titin ko zata dace,shima
saiya tashi motar yaci gaba da binta sannu sannu,yana kallon yadda take digar ruwa har cikin
zuciyarsa,saidai bazai iya daukarta amotarsa ba,yanajin wani abu cikin zuciyarsa,kallonta na
tuna masa da ganinta da yayi,fitowarta daga motar wani,wanda ba qaramin suya yake masa a
qirjinsa ba.
*ga mai buqatar littafina da zan fara bayan gama alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching
SAUTIN HIKIMA,daga qasa zaiga an rubuta SUBSCRIBE da jan rubutu,ya danna sau daya zai
koma black,yayi screen shoot ya tiro zuwa wannan number,za'ayi adding dinsa agroup din in
sha Allah*
07038670166*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,idan kina da
buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
2️⃣3️⃣
Gab da zata tsallaka daya titin mai adaidaita ya taho,ta tsaidashi da sauri,babu kowa a ciki ta
gaya masa inda zata ya dauketa suka wuce,sai da yaga tashinsu sannan ya saki ajiyar zuciya
"Wai anwar meye damuwarka ne haka?" Wani sashe na zuciyarsa ya jeho masa tambaya,sai a
sannan ya dinga tuno abinda ke faruwa,sam duka baisan yana abinda yayin ba,kamar wani
umarni yaji ana bashi,kai ya girgiza yana jin haushin kansa,yana ganin ya tsaya ne kawai ya
bata lokacinsa,motar ya bawa wuta sosai cikin gudu ya figeta ya harba titi.
Su duka suna zaune a falon suna kallo,da sallama ta shiga,dukkansu sannu da zuwa suke
mata,anty zubaida na cewa
"Wai wai,sannu rahamatullah" murmushi tayi tana zuge lemar hannunta,huda ta tashi da
hanzari zata tarbeta ta dakatar da ita
"Tsaya huda karki jiqe,don ni da kika ganni yau jalaf nake a kaina ruwan yau ya qare" tayi
maganar sanda take aje jakarta
"Ahto...haka kawai za'a baki mota kika qi,da kinga yanzu ba ruwanki da ruwa ko rana"
"Wallahi anty to ya za'ayi....faruqu don Allah zazzagemin jakarnan ka duban wayata ka shanyan
abinda kaga ya jiqe" da sauri huda ta amshe cikin shagwaba
"Anty gani sai kice ya faruq kuma?"hararta faruq yayi
"To kishiyata" Dariya shahida tayi
"Auto auta yi haquri,gyaramin bari naje na sauya kayan jikina sanyi sanyi nakeji"
"Idan kin saukoma ga dinkunanki nan an kawo" waiwayowa tayi
"Yauwa,yaushe ya kawo?,jiya fa mukayi waya dashi yace bai gama ba"
"Dazu ya kawo"
"Ya kyauta,don kayan matar data bani aron style nakeson maida mata,kar taga rashin
hankalina...bari naje na dawo saina gani"
"Uhmmm" anty zubaida ta fada.
Sai data soma kunna qwan dakin data kashe dazun da zata fita aiki,haske ya gauraye ko
ina,ko.ina tsaf yana fitar da qamshi kaman yadda ta saba masa,ta kalli agogo,shida harda rabi
na yamma,an kusa kiran magariba kenan,kayan jikinta ta fitar ta shiga bandaki ta hada ruwa
mai dumi sosai tayi wanka hade da alwala sannan ta dawo daki ta shirya cikin wasu kaya masu
dan kauri,sai datayi sallar magariba sannan ta sake fitowa.
Yanzun ma a zaune ta samesu,saidai da alama faruqu da haidar sunje masallaci sun
dawo,anty zubaidan ma wannan karon da hijabi jikinta,huda dake duqe gaban socket ta dago
tana cewa
"Yauwa anty,yaa nuradden ne ya kiraki"
"Uhmmm" ta amsa tana dubanta,saita ciro wayar ta kawo mata ta karba tana dubawa,Allah ya
taimaketa ba abinda tayi ruwa bai tabata
"Na gode hudallahi" shahida na murmushi ta fada.
Saida sukaci abinci sannan ta duba dinkunan,sunyi masifar kyau ko ba'a fada ba tasan zasu
zauna mata a jiki,saita yanke kawai ta barsu saida bikin da zasuyi,ta ninke kayan ta kwashesu
ta haura sama dasu,don yau da wuri takeson kwanciya har yanzu kuma yayyafi ake,saboda
gobe sammakon fita zatayi akwai ayyuka da yawa.
Tana shirin jan abun rufa kiran nura ya shigo wayarta,ido ta lumshe sannan ta waresu,ba
yadda ta iya haka ta daga
"Ranki ya dade....yau an manta dani kwata kwata ko?,koda yake dama idan ban nemeki ba
saidai na shekara ina jajenki"
"Ba haka bane...ayyuka ne yau sai hamdala"
"Ina fatan dai basu gajiyarmin dake ba?"ajiyar zuciya ta sauke
"Gajiya kam akwaita,don yanzu ma shirin kwanciya bacci nake"
"Da wuri haka?,da qorafi nakira nayi,amma tunda haka ne kiyu baccinki dakyau,ki gayan
yaushe zanzo mu hadu?" Kanta ta juya daya sashen,ta danyi nazari kadan
"Kasan yanayin aikin nawa,wunin office ne,idan na dawo kuma na gaji bacci kawai nake
buqata" tsaf ya gama ramfota,haduwar tasu ne bataso,ita kuma takurawa da zancan aure da
yake a 'yan kwanakin da yadda yake marairaice mata ya sanya bata fiya son haduwar tasu
dashi ba,sakata yake kawai a corner "Duka ba damuwa bace,ni idan anmin izini saina riskeki har office din lokacin break mu tattauna
abinda zamu tattauna din,karki damu bazan jima ba zan tafi,daga nan har zuwa next week ina
jiranki" numfashi ta sauke,ya gama kamata kenan iya wuya,amma itama bari ta qure haqurinsa
"Saidai nan da sati daya rana ita yau"
"Allah ya kaimu" ya amsa hakan bisa ga mamakinta,da haka sukayi sallama ta kwanta tunani fal
ranta,tana mamakin yadda nuradden yake iya shanye duk wani hali nata,bata taba kamashi da
rashin yi mata uzuri ko hanzari ba,tanajin nuran na hawa wani mataki fiye da wanda yake kai a
baya,ya kamata ta sake bashi wata damar ko yaya take,da wannan tunanin bacci yayi awon
gaba da ita.
*BAYAN SATI DAYA*
Turare ta dauka ta fesa abu na qarshe cikin shirin fitarta office,ta kalli kanta sosai ta tabbatar
komai yayi mata,shiga mai kyau da tsari,riga da skert na swiss atampha wanda suka mata cas
da mayafi yalwatacce wanda ta dorashi saman daurin dankwalinta data dan turoshi gaban
goshi,hannunta agogo ne kaman yadda tafi son sakashi fiye da awarwaro,wuyanta sarqa ce da
dan kunnayensu masu azabar kyau qirar kamfaninsu,wanda gwaji ne akayisu aka bawa masu
manyan matsayi a kamfanin,takalmanta ta jawo rufaffe na mata wanda ya dace da shigarta,tana
zuge jakarta da zata fita da ita taji shigowar saqo a wayarta,saita dakata da abinda take ga
zatonta mudassir ne daya daga cikin abokan aikinta wanda yace zai tura mata wasu bayanai
kan lissafin da suke tayi na wasu siyayya da wani kamfani yayi na sarqoqi,ga sabanin tunaninta
saita tarad da nuradden ne
_Da fatan wannan kyakkyawar halittar ta tashi lafiya cikin amincin ubangiji,yau sati guda cif
cif,Allah yasa banyi azarbabi da yawa ba_
Kyawawan idanunta masu kyau da haske ta juya gabanta yadan fadi,sam ta manta da
zancansu wanda yace ya bata sati guda,saita sauke numfashi data tuna cewa bai taba zuwa
kamfanin nasu ba,asalima bata taba gaya masa inda yake ba,hakan na nuna baisan office dinta
ba,bazai kuma iya zuwa ba har sai ta bashi adress,tuna hakan ya mata dadi,don idan yazo din
bata jin zaya samu amsar da yake da muradi,saboda haka ya kashe wayarta ta jefa a jaka tana
murmushin nasara,ta duqa ta qarasa saka takalminta ta dago tana rataya jakarta huda ta shigo
cikin shirin makaranta itama,gaida shahidan tayi ta gaya mata sun fito
"Muje hudallah...wannan makaranta anaji da ita" dariya ta saki
"Sosaima anty,kinga randa me makarantarmu yazo,ya bamu labarin wahalar da yayi saboda
karatu,yace mu dake muyi karatu sosai muma donmu zama irinshi" yatsine fuska shahida tayi
saboda yadda zancan ya tuna mata da ranar
"Allah ya kiyaye" shahidan tayi subul da bakan fada wanda yasa buda ta juyi da sauri
"Allah ya kiyaye kuma anty?,yana da kirki fa,sannan yana da karatu,ya iya turanci da
larabci,gashi kyakkyawa,shiyyasa ranar banji dadi ba da kika koma gida baki ganshi
ba.....kinsan me?,uncle fa muke ce masa,yace duka mu yayanmu ne..."
"Hudaa....a'ah" shahida ta fada tana kallonta,itama sai ta saka ido kawai tana kallon shahidan
"Oya muje karki sa muyi late dukanmu" dariya ta saki tana tafiya sauri sauri
"Mu yanzu ai ba'a dukan late comers,uncle ya hana" goshinta ta dafe da tafin hannunta,wato
dai hudan ba zata daina mata zancan mutumin nan ba.
Tana mamakin yadda suke ganin kirkinsa haka da yawa,basu san cewa macijin sari ka noqe
bane shi?.
Agurguje kuma a tsaye ta hada tea dan kadan ta kurba,duk yadda anty zubaida tayi kan ta
tsaya tayi break sosai cewa tayi sauri take yau suna da aiki da yawa,haka ta fice bayan ta musu
sallama,aka dauki huda itama ta shiga tata adaidaitan suka wuce.
A cikin company ya ajeta kaman yadda suka saba ya juya ya fice ita kuma ta shige zuwa
cikin ainihin kamfanin,a sashen kula da baqi na musamman zata wuce cikin hanzari tajuyi
muryar mudassir
"Kin kusa makara fa" waiwayowa tayi fuskarta babu yabo ba fallasa ta dubeshi
"Wallahi,amma na gode Allah da ban makara ba,ina fatan komai ya zama ready" kafadarshi ya
daga yana dubanta,yana da muradin shahidan sosai tana burgeshi,komai nata abun sha'awa ne
amma kame kai da jan ajinta yasa ta masa wani irin kwarjini daya sanyashi ya kasa kwatanta
mata bare ya furta "Eh tuni ma" ya qarashe maganar yana miqa mata daya daga cikin file biyun dake
hannunshi,hannu ta saka tana buda shafukan farko tana dubawa sama sama,daga kai tayi sai
suka hada ido yana kallonta,hakan ya sanyata dan tsare gida
"Ka sameni a office dina muyi acan inaga zaifi" ta juya abinta ta isa bakin elevator da xata kaita
zuwa bakin ofishinta.
Da sallama ta shiga duk da cewa ya sani babu kowa ciki,a nutse ta qarewa office din kallo,ko
ina tsaf yake yana fidda sassanyar qamshin da ita ta yiwa kanta zabin kalar freshner din da
takeso wadda ta banbanta data kowa,wadda ke mata shara din ta qwarai sosai,sannan kuma
tasan aikinta,hakan yasa takejin dadin aikin da take mata,tasan ra'ayinta da tsarinta,jakar
hannunta da file din ta dora saman teburinta sannan ta taka a hankali ta isa bakin windows din
office din ta bude kowanne,iska mai dadi da sanyaya rai ta soma kunno kai,irin iskar damina
mai taushi da sanyi,tana son irin wannan iskar,sabida banu iska mai dadinta,fresh ce daga
indallahi,sai data tabbatar ta gauraye office din sannan ta rufe windows din,ta sauke labulayen
ta kunna AC,hakan ya qarawa office din wani dadi da yanayi na musamman.
Tana zama mudassir ya shigo,yaja kujera ya zauna yana qarewa office din kallo sanda take
kiciniyar futo da system dinta wadda a office din ta kwana bata je da ita gida ba jiya
"Kai masha Allah,duka kamfanin nan ba office din dake burgeni nakejin dadin shigoshi irin
wannan,komai neat masha Allah" ya qarashe maganar yana sauke idonshi a kanta,dan qaramin
murmushi ta saki sannan ta soma dai daita cumputer din gabanta,ba tare data sake bashi wata
qofar sako wani zancan ba ta soma gabatar masa da abinda ya zaunar dasu.
Tun tara da rabi suke abu daya har qarfe daya da rabi na rana kafin su kammala,ta gaji
matuqa tayi tubus,ga 'yar banzan yunwa dake damunta,kujerarta taja baya bayan ta rufe system
din tana hamma idanunta lumshewa wanda sam bata kula da yadda mudassir ya zuba mata ido
yana kallonta ba cikin burgewa,tunda suka zauna qamshinta ke burgeshi "Yadai madam?" Ya tambayeta har yanxu idanunshi na kanta,sai a sannan ta juyo ta
dubeshi,fuskarta adan hade kaman yadda ta saba idan ta fuskanci kana da shiga sharo ba
shanu
"Da akayi me?,ai mun gama ko?,sauran aikin ya rage naka da nawa,kowa yaje ya tsara abinsa
cikin system dinsa,duk randa zamu gabatarwa da boss kowa yasan me zai fada" kai ya
rausayar
"Ba haka nake nufi ba,naga kaman bakijin dadi ne" miqewa tayi tsaye tana gyara yafen
mayafinta,bandaki takeson shiga sabida fitsari ya matseta gashi yaqi fita ya bata waje
"No,ba komai gajiya ce kawai.." Ta tura kujera baya sosai yadda zata samu damar fita daga
tsakanin kujerar da teburin.
Gab da zata shige bandakin aka nemi izinin shigowa office din ta bayar,masinjarta ce cikin
girmamawa tace
"Kinyi baqo ne anty(haka take kiranta saboda yadda take ganin qimar shahidan" cikin mamaki
tace
"Baqo kuma?,custumer ne?", ta tambaya duk da tasan bashi bane,don yawanci ba'a ganinta ita
idan ba wata matsala bace akan pyment da custumer zaiyi,koda kuma zai ganta ma za'a
rakoshi ta qarqashin wani office dake kula da shige da fice da kuma siyayyar kaya a kamfanin
" a'ah,yace yana son ganinki ne personal"tayi tsammanin cikin mutanen dake takura mata
ne,abun saiya qona mata rai,batason abinda zai shafi mutuncinta a wajen aikinta,sabida haka
taja tsaki
"Jeki ce masa lokacin aiki ne yanzu,ya nemeni ta waya ko waye idan na tashi daga nan"
"Toh" ta fadi tana juya ta fice daga office din,tsaki taja ta dawo don daukar ruwa ta soma sha
tukunna
"Sai haqurifa,kinsan kowanne mutum da yadda Allah yake masa baiwar jama'a" waiwayowa tayi
ta kalleshi,shaf ta mance dashi cikin office din,saita dauke kai tana sake hade girarta ba tare
datace masa komai ba,batason a dinga zama mata cikin office tafison kuna gama aiki ka kama
gabanka,wayarta dakw cikin jakar hannunta wadda ke saman teburinta tayi qara,a nutse ta
qarasa ta zugeta ta cirota,sai taga number nuradden,fuska tadan yamutsa saboda yadda taji
gabanta yadan fadi,ta daga ta kara a kunnenta
"Allah ya baki haquri gimbiya nine fa,ko nima ba za'a samu damar ganina ba bayan alqawari
aka yimin?" Mamaki ya cikata,ta yaya akayi yasan kamfanin da take aikin,banda abinki wannan
wajen kina tunanin zai xama boyayye ne?,shahararren waje irin wannan? Wata zuciyar tace da
ita,murmushi ta qaqaro "Ayyah bansan kai bane,minti daya ina xuwa" kiran nashi ta katse ta soma neman wata number
cikin ranta fana dana sani da Allah wadai da kunna wayarta data yi,data sani tun daxun ta barta
a kashe kawai,wani sashe ta kira na kamfanin ta bada umarnin a rakoshi,daga haka ta kashe
wayar,duka sai jikinta yayi sanyi taju qafafunta kamar an bubbuge mata su,sai ta zauna saman
kujerun cushion dake gefe daya na office din.
Sanda ya turo qofar lokacin saddam ya miqe yana fadin
"Bari na samo miki wani abun,na fuskanci kaman yunwa kike ji" bata iya amsa mishi ba yayin da
sukayu clashing da nuradden sanda yake shigowa,suka kalli juna saddam ya sanya kai ya fice
nuradden ya bishi da kallo,sai daya bace masa sannan ya dauke idanunshi ya qaraso yana rufe
office din idanunshi a kanta "Waye wannan din?" Ya tambayeta kai