Showing 93001 words to 96000 words out of 126208 words
Chapter 32 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
zauna cikinsu huda wadanda ke kallo,faruq ya kalleta
"Anty harkin fara canzawa,kaman bakeba akan dazun da kuka fita'binsa tayi da ido kawai ba
tare datace komai ba,kafin ta gama tunanin da take ta jiyo muryar huda
"anty...zamuyi kewarki,tafiya zakiyi yanzu ki barmu?"ta qarasa fada a shagwabe kaman zata
saki kuka,nan take ran shahida yaso ya sake baci da tuna hakan da tayu,anty zubaida ce ta
katse komai tana tambatar faruq me suka dafa musu,yace white rice ne bazai iya miya
ba,hararsa tayi "Daga kai har haidar din a rasa wanda zaiyi miya?" Huda na gefa na musu dariya,kai ya
langabar
"Allah ummi shi yasa nace ki samo mai aiki fa" tsaki taja sai shahida ta miqe
"Bari na hada" tafurta tana yin gaba zuwa kitchen.
Kayan miya ta diba ta soma gyarawa sannan tayi blending,dukka rabin hankalinta da
nutsuwarta nakan tunani,data hada miyar saita zauna cikin kitchen din tana duban agogo,tasan
zuwa sanda zata gama hudu tayi saita da alwala kawai gaba daya.
Miyar na soyuwa haidar ya shigo yana shaida mata tazo inji anty zubaida,saita rage wutar
can qasa yadda ba zata kama ba kafin ta dawo ta fito zuwa falon,a zaune ta sameta da tulin
kaya a gaba da alama sabbabi dinkuna ne tana dagawa tana kalla gami da ware wasu gefe
"Kije waje kinyi baqo"gabanta yadan fadi,tadan bata fuska
" waye haka da la'asar din na"
"Ban sani ba nima,idan kinje zaki gani" hakan yadan kwantar mata da hankali jin ba wanda ta
tsani ganin bane,nan kan kujera ta dauki mayafinta data dawo dazu dashi ta yafa sannan ta
fice.
Matashin saurayine mai kyau da aji tsaye jikin motarsa,sanye yake da shadda riga da
wando dinkin tazarce,hankalinsa duka nakan wayarshi a haka ta kusa cimmasa,bata sanshi ba
amma sai take ganin tasan fuskar a wani waje daban ko can da dadewa,sallama ta masa ganin
baisan da isowarta ba,ya daga kai da hanzari yana amsawa fuskarsa ta fadada da fara'a "Barkanki da yamma kin wuni lpy"
"Lafiya alhmdlh" ta amsashi a taqaice
"Ya mutanen gidan kowa da kowa lafiya?"
"Lafiya qalau" ta sake amsawa tana mamaki ina ya santa tare da zurfafa tunaninta ko zata iya
tuna a inda ta sanshi,murmushi ya saki
"Nasan baki sanni ba,ni sunana muhsin,aboki kuma aminin anwar" lokaci daya maganar ta
sauka a zuciyarta,sai yanayin fuskarta ya soma sauyawa,fuskarta ta soma tsukewa,duk da haka
tadan dake hadi da qoqarin sassautawa,shima dubanta yake yana karantar sauyawar yanayinta
lokaci kadan,bai sake cewa komai ba ya bude murfin motar da yake jingine a jiki ya zura hannu
ya ciro wata babbar envalope da qarama ya miqa mata,kallon envalope din tayi sannan ta dawo
da kallonta kanshi alamun neman ba'asi
"Katin gayyata ne na dinner ko zaki gayyaci qawayenki,wannan kuma kudine ko zaki buqaci
wani abu" kai ta girgiza tana danja baya,a fuska tana ganin mutuncinsa amma baya ga haka so
take taci masa mutunci ne shida wanda ya aikoshin,amma duk da haka ba zata kasa bashi
saqo ba "Ka maida masa dukkan kayansa,ka gaya masa aurensa baya buqatar wani shiri tunda a
shiryensa aka qulla shi,kudi kuwa baiyi kudin bani ba a yanzu har zuwa nan gaba,ka gaida na
gode" daga haka ta juya zuwa cikin gidan tana takawa a nutse,da kallo ya bita qwaqwalwarsa
cunkushe da tunani da mamaki,kullum kwanan duniya sake mamaki yake kan meye haka mai
girma daya raba kwanunansu ya tarwatsasu haka zuwa pieces suka kasa kuma daidaita tsahon
shekarun?,amsar daya kasa samunta kenan haryau daga wajen anwar duk da sanda rabuwar
ta afku shine mutum na farko daya sha wuya da anwar din kafin rayuwarshi ta daidaita,saiya
xagaya ya bude murfin motar tasa ya shiga yana tuna yadda sukayi da anwar sanda zai ya
shirya kudin da katin yace zai kaimata da sunanshi,har kusan haurawa sukayi kan koda zaikai
din yakai amma bada sunanshi ba.
Iska ya furzar daga bakinsa lokacin da muhsin ke zaune kan daya daga cikin kujerun office
din yana sake tambayarsa wanne laifi ya aikatawa shahida haka?,ya dubi envalope din daya fita
dasu ya dawo dasu kamar yadda suke,hakan na nufin bata karba ba kenan
"Bata karbi kayan daka kai din ba kenan?" Anwar ya tambayi muhsin kai tsaye yana
dubanshi,kai ya kada
"Ni duk ba wannan na tambayeka ba,inason gyara wannan barakar ne shi yafi damuna,banason
alaqar taci gaba da tafiya a haka"
"Me ta gaya maka sanda kaje?" Ya sake jeho masa tambaya ba tare daya damu da nashi
bayanan ba
"Batace komai ba" murmushin yaqe ya saki,takowa yayi kusa dashi kujerar dake fuskantarsa ya
zauna
"Ta fadi maganganu a kaina,takuma ce ba zata karba bata buqata right?" Idanunsa cikin na
muhsin ya fada,kauda idonsa muhsin yayi saboda shi kansa wasu lokutan anwar na masa
kwarjini da yawa
"Kaga malam nidai bance maka haka ba,banason tone tone" miqewa yayi yana jijjiga kai
"Ta fada,na santa kamar yunwar cikina" gaban envalope din ya qarasa,ya farke dayar ya cire
kudaden ciki ya janyo locker din office din nasa ya zubasu ciki,sannan ya janyo daya locker ya
ciro wasu ya musanyasu dasu ya maidata ya manne muhsin na kallonsa,ya kwashesu duka ya
aje masa key saman teburinsa "Idan ka gama ka rufe ko ina" daga haka ya juya yana takawa sannu sannu zai fice daga office
din
"Wait mana malam,ina zaka je?" Murmushi ya jefa masa ya fita ba tare daya amsashi ba.
Gidansa ya soma isa ya bude sashensa ya shiga,ya aje kayan hannunsa,bandaki ya shiga
ya tara ruwan wanka mai dumi ya sake wanka sannan ya nemi abinci yaci ya qoshi,wardrobe
dinsa ya bude ya zabi kayan da yaje gani sun dace da irin wannan lokacin ya sanya,ya tsaya
gaban mudubi yana taje kansa gami da kallon kansa yadda kayan suka amsheshi,tuna abinda
ya faru tsakaninta da muhsin yayi,saki yaja,wato ita mai taurin kai ko?,har yau bata kallon
laifinta sai wani take dorawa alhakin faruwar komai ba tare data duba nata laifin ba,aikawa yaso
yi direct inda dole ta karba saqon,amma hkanan yaji yana son yaje yaga hawayenta ya takaleta
ya kuma tsone zuciyarta,saiya aje cumb din yana daura agogon fata sannan ya zauna ya daura
takalmansa ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motarsa ya fito.
A hankali yake tafiyar kaman bazaije ba,karon farko da zai fara zuwa gidan anty zubaida
kenan,yadan yi nauyi a hanya hakan yasa bai isa ba sai qarfe shida mintina hamsin suka rage
kenan a yi sallar magarib.
Maigadin gidan anty zubaida ne ya iso ya bashi hannu don suyi musabaha,cikin tantama
yadanyi jim don yana ganin bai kamata suyi hannu da hannu ba
"Mu gaisa mana abokina,bakason ladar ne" da sauri ya miqa masa suka gaisa
"Inason magana da wata yarinya shahida a gidan nan ne" cikin washe baki yace
"Au,kaddai kaine angon?" Murmushi kawai yayi sannan ya sake cewa
"Idan ka shiga matar gidan zaka sanarwa zuwa na,sannan ka turomin faruqu ko haidar"
"Toh...toh" ya fada yana juyawa zuwa ciki.
Sanda saqon kiran ya sameta tana daki tana shiryawa bayan ta gama mitar wankan turaren
da anty zubaida ta kafa nata dokarshi,turaren na nata dadi da qamshi amma tuna dalilin yinsa
ke qona mata rai da dagula mata lissafi,tsaki taja sanda huda ta gaya mata ana kiranta,ta shiga
mita "Wai wanne irin kirane da baqi haka tun dazu ba za'a bar mutum ya huta ba?,haka kawai kana
zaman zamanka daada ta tada zaune tsaye cak,ni wallahi na gaji da wadan nan
abubuwan,daga wannan sai wancan?" A haka ta shirya ta zari hijabi ta fito
"Baqon na waje ai" anty zubaida tace da ita sanda taga ta tsaya ta mata turus,haka ta juya ta
fita kaman zata fashe.
Faruq ta soma hangowa cikin dakin saukar baqi na gidan baki na motsi da alama hira yake
zubawa,harara ta zabga masa duk da bai ganta ba,a haka ta isa ta yaye labulen,tare idanunsu
suka sauka cikin na juna,yawun bakinta ya tsaya kowannensu na kallon dan uwanshi ba tare
daya dauke ido ba,gani yayi kamar ba ita,fatarta ta sake sauyawa kyanta kaman an matso
shi,qamshinta ya soma cika wajen,shima kwarjini taga yayi mata,shigar ta amsheshi,yayi kyau
ya sake zama cikakken mutum da hankali da ilimi suka ratsashi,ita ta soma janye
idanunta,ranta a hade tsaf ta taka zuwa ciki tana duban faruq,saiya miqe,anwar yace
"Zan nemeka kafin na wuce kada kayi nisa"
"To yaya" ya fada yana ficewa,sai da taga fitarsa sannan ta zauna hannun kujerar dake a dab
da bakin qofar fita,tanason tsareshi da ido donta karanci me ya kawoshi amma batasan me
yasa takejin rashin qwarin gwiwa ba,ta maida idanunta kan tafin hannunta tana murzawa ba
tare data ce masa uffan ba,hakan ya bashi damar kafeta da ido,ya soma kallonta tun daga
yatsan qafarta zuwa saman kanta,yana jin wasu tagwayen abubuwa na fada cikin
zuciyarsa,daya nason yaqar daya gami da rinjayarsa,inda daga qarshe dayan yayi galaba,saiya
runtse idanunsa yabar kallonta saboda wani bacin rai dakeson shaqeshi,kullum kwanan duniya
yana son sasautawa kanshi,yana son ya daina ganin baqinta da baqin abinda ta aikata,yana
son abinda idanunsa suka gane masa da hotunan daya gani su bace daga idanunsa ko zai
samu salama da rangwame amma hakan ya faskara,sai komai yayi kaman zai goge saiya sake
dawowa sabo fil a ransa.
Walwalar da yake jin kaman zata samu a ruhinsa ta dusashe,sauran faragar fuskarsa ta
bace bat.
Zaman kurame ne yaci gaba da wanzuwa tsakaninsu harna tsahon wasu mintuna,sai daya
gama zamanshi don kanshi sannan ya miqe,cikin wani taku ya isa dab da ita ya tsaya
akanta,kana ya ranqwafa gefanta har tana iya jiyo qamshin ya aje envalope din hannunshi,ba
tare daya dago ba yace mata "Baki iya gaisuwa ba saikace a gidan mashaya inda kowa yake ogan kanshi,karki tsammaci
xaki gidana da wannan dabi'ar ki tsira,ga saqon da muhsin ya kawo miki daxu kika maidashi
nina dawo dashi,idan kin isa karkiyi amfani dashi yadda ya dace kiga yadda zata kaya mana
nidake,tunda na fahimci cikin halayen da kika koyo kala daban daban harda taurin kai
ko?,good....inason wannan sabon halin naki,idan kin tashi gayyatarki karki sake ki kwaso min
tarkacen 'yan maye,ko tarkacen qazaman tsaffin samarinki" daga haka ya dago yana shirin
wucewa zuciyarta taje iya wuya,ta kasa daurewa
"Idan ba haka bafa?,me zakayi?" Ta fada a tsiwace cikin fushi da fusata,saiya sake dawowa
gabanta ya tsaya,ya dubeta na wasu mintuna sannan ya saki murmushi
"Ki aikata din sai kiga sakamakon" miqewa tsaye tana masa kallon tara saura kwata sannan
tace dashi cikin salo na masifa dake cin zuciyarta
"Baka isa ka sakani abinda banyi niyya ba,baka isa komai ba idan ma kana tunin ka isa"
murmushi ya sake saki wannan karon mai sauti,yadan buga qafarsa sannan yace
"Ko a haka aka tsaya ai inga irin tawa isar ko?,hukuncin da zan miki ba isata kawai zai nuna
miki ba,izzar aure da izzar anwar namiji"
"Namiji shine zai tsaya takara da abokan adawarshi ya kuma samu nasara,ba wanda zai wafta
koya biyo ta bayan gida ba,koya taka wani tsani don kaiwa wannan bigiren,ka daina batawa
kanka lokaci wajen kiran kanka da namiji,ba namiji bane kai saidai mata maza" idanunsa ya
qura mata qir sanda take maganar cikin dakiya da rashin nuna tsoro,hakanan bilhaqqi da
gaske,ganin takai aya saiya soma takowa inda take tsaye,ta tsaya cak don ganin iya gudun
ruwanshi,saidai harya iso gab da ita bai daina takowa ba,hakan na nufin zai hade gap din dake
tsakaninsu kenan,don haka ta soma ja baya ga zatonta zai tsaya amma ina,bai barta ba sai
daya tabbatar ya hada bayanta da bango,qafarshi dake saye da takalmi saman tata qafar
wanda yana iya jin zafi zafi na tudun takalminsa daya take mata qafa,kusancin dake tsakaninsu
yayi yawa,tana iya ganin fuskarsa tarwai wadda kyau ya cikata gamida iya gyara,idanunsa sai
suke juye mata irin na anwar dinta na wancan lokacin sak,janye qwayar idanunta tayi gabanta
na bugawa da sauri da sauri,tsoro da fargabar me zaiyi mata na shigarta,saitaga ya daga hannu
kaman yana shirin marinta,ta runtse idonta da sauri tana wassafa me zata masa ita bayan ya
gama marin nata,ji tayi yaja baya da sauri cikin kaushi yace
"Sai na saki kinyi nadamar lafazinki,tsautsayi kuma yasa bakiyi yadda nace miki ba" daga haka
ya juya da sauri sauri ya fice daga dakin,cikin hanzari ta daga murya
"Idan ka isa ka tsaya mana ka dakenin kaga yadda akeyinta" gab da zai fice ya waiwayo yace
"Aiba a gidan syrup muke ba" kalmar ta tsaya tana fassarawa,take wani abu ya cushe mata
maqoshi,cikin qanqanin lokaci hawaye ya ballewa idanunta,tana jin zafi a zuciyarta duk sanda
yayi wani lafazi dazai iya tuna mata da abinda ta aikata a baya,sulalewa tayi ta zauna a
wajen,ba shakka ba'a bari a kwashe duka,shaye shaye ashe wani tabone da tambarinsa bai
barin jikin maishi?,koda kowa ya manta ba'a rasa burbushi,ta jima a wajen tana jin ciwo kala
kala kafin ta miqe ta fice daga dakin,ko kallo envalope din basu isheta ba bare ta dauka.
A falo anty zubaida tace ta tsaya ta duba dinkunanta na biki wanda ita batasan ankai
bama,don ko kayan har yau bata kalla ba bare ta gane me takeso a ciki har tayi tunanin kaiwa
dinki?,bata cikin yanayin da zata iya zama cikinsu saboda haka tabawa anty zubaidan uzurin
kanta na ciwo zata duba zuwa safiya da haka ta wuce dakinta.
Washegari sun fito da anty zubaida zata koma gidan gyaran jiki tanata kumbure kumburenta
da mita cikin ranta na yadda aka takura mata ba gaira babu dalili faruq dake sharar dakin da
uncle hisham ya sakashi sabida zaiyi baqi ya fito da envalope din yana miqawa anty zubaida
"Anty wannan a dakin na gansu,kaman na anty shahida ne don jiya na gansu a hannun uncle
anwar" hanu tasa ta karba sannan ta waiwaya tana duban shahidan
"Me yasa kika barsu a dakin?,abinda kikayi dai dai kenan?" Saita langabe kai,ita abun goma da
ashirin,komai tayi batayi dai dai ba,saita saka hannu kawai ta amsa suka wuce,suna shiga mota
ta kasa daurewa ta saki kuka tana kife fuskarta saman cinyarta,anty zubaida batace komai ba
saidai ta dora hannunta saman bayan shahidan,saida tayi kukan na wani lokaci sannan anty
zubaida tace mata.......
3️⃣4️⃣
"Abubuwa da yawa da mukeso muke qwallafa rai a garesu ba alkhairi bane ga bawa,kiyi
qoqarin rage wannan kaifin qiyayyar kamar yadda annabi yayi umarni saboda kada ta juye miki
zuwa soyayya mai zafi daga baya,kiyita addu'a Allah yasa abinda zai faru dake ya zama shine
mafi akhairi a rayuwarki duniyarki da lahirarki" da ire iren wannan nasihar suka isa wajen gyaran
jikin.
Anty zubaidan ita ta karbi envalope din ta bude taga abunda ke ciki,saita amsa ta aje tana
jiran hasina tazo ta raba cikin 'yan uwa,don shahidan a yanzu bata da wata qawa banda
zunnurah da take sokoto,tunda abun ya faru gaba daya ta cure qawa daga tsarin
rayuwarta,saidai gaisuwa kawai ta mutunci,sabida card din bashi da wani yawa sosai,da alama
dinner ce da akayi selecting iya adadin mutanen da zasu shiga.
Gaba daya ta susuce cikin kwanakin ta fita hayyacinta,idan ka ganta saika dauka ba ita bace
ba,gashi daga mummy har abban nata ba wanda ya sake bi ta kanta koya tanka mata dangane
da hukuncin data yanke na ba zata auri anwar ba bare ta fadi abunda yake ranta ko zataji
dadi,kullum kwanan duniya kamar ibada kuwa saita kira number mima sau babu adadi amma
tana a kashe amsar kenan kullu yaumin,ko fita yanzu ba kasafai take ba,kishin anwar da sauran
kwanakin daya rage ya zama mallakin shahida su take lissafi,sanda taga kwanakin na qaratowa
kuma bata da madafa ko makoma saita soma dana sani da nadama tana tuhumar kanta anya
kuwa batayi kuskure ba?,anya bata aikata ba dai dai ba?,da wannan tunanin ne a yau daya
rage saura kwanaki hudu biki ta sake jan wayarta tana gwada lambar mima karo na wajen dari
biyu da wani abu.
Kaman a mafarki taji ta shiga,saita miqe zumbur tana kaiwa da kowawa ita kadai tana fadin
"Ki daga mima,ki daga ki daga don Allah" gab da zata katse ta daga din kuwa
"Ina kika shiga don Allah?,ina kika tafi?,don Allah duk inda kike ki dawo a yau"
"Lafiya?"
"Ba lafiya ba mima,nace na fasa auren anwar saboda zai aureni nida shahida mima kina ina,ina
buqatar taimakonki"
"Shahida kuma?" Ta tambaya cikin mamaki
"Eh ita dai" wani malalacin murmushi mima ta saki sannan tace
"To ai kinyi dai dai da kika ce kin fasa,hukuncinki shine dai dai"
"Kaman yaya mima,nifa ina qaunar anwar har yanzu ina jin soyayyarsa cikin raina,ina jin bazan
iya rabuwa dashi ba" dan bata rai mima tayi sannan tace
"Duk da haka dole kiyi haquri ai yanzu bake ba shiga gidan saikin shirya,sabida haka kici gaba
da walwalarki har zuwa sanda zan dawo karki damu komai zai gyaru yadda kikeso"
"Ina cikin damuwa mima,burina yanzu kawai shine na mallaki anwar,sai zuwa yaushe zaki
dawo"
"A'ah fa,aikina kinsan babu gaggawa sai biyan buqata,saboda haka idan gaggawa kike kawai ki
nemi wata mafitar bani ba"
"Shikenan saikin dawo"
"Yauwa...am idan ba damuwa kimin transfer mana,ina da buqatar wasu yan kudi"
"Babu damuwa,kaman nawa kike da buqatar?"
"Dubu dari uku ma sun isheni in jalauta"
"Ohk,accnt dina ya samu matsala bazaiyiwu inyi miki trasfer ba,amma zanje banki na tura miki"
"Shikenan saina jiki,karki wuce la'asar"
"Ba case" daga haka suka aje wayoyin,duk sai taji salama na shigarta tamkar matsalarta ma ta
yanke kenan tunda sukayi magana da mina,saidai kuma har yanzu zuciyarta cike take da kishin
anwar da tsanar shahida,da kuma jun babu