Showing 120001 words to 123000 words out of 126208 words
Chapter 41 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
gata masu jeren amarya zasu zo...."
"Me zanyi musu to?,meye amfanin gayamin din?,Allah ya kawosu lafiya" ta fada cikin zafi zafi
wanda ita kanta batasan ta aikata hakan ba,idanu ya zuba mata har takai aya sannan yace
"Babu abunda xaki musu,kawai inason ki kwashe kayanki xaki koma dakunan sama"
waiwayowa tayi tana dubanshi,me zataje samanshi tayi masa,dai kawai ta miqe ta soma takawa
tana cewa
"Na barwa amarya,inda nake nan ya isheni na qarasa kwanakin da suka ragemin" bai fuskanci
me kalmarta ta qarshe ke nufi ba,amma ganin zata fice sai yace da ita
"Umarni na baki ai ba shawara bace bare ki gayamin naki ra'ayin" daga haka shima ya juya
abinda shida kujerarsa,saita waiwayo tadan dubeshi kadan sannan taci gaba da takawai ta fita
daga dakin.
Tana shiga nata dakin taji kuka ya qwace mata,duk yadda taso hana kanta abun yaci
tura,batasan me yasa takejin bacin rai da damuwa ba,kuka tayi sosai kafin taji zuciyarta tayi
sanyi.
*BAYAN KWANA UKU*
Tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata doguwar riga na wani yadi me sulbi
wanda yake kama da yadin satin,hakan yasa yabi jikinta ya lafe,gajeran hannu ne dashi gami
da wuyan half shoulder wanda ya fitar da wuyanta da wani sashi na qirjinta sosai,kanta babu
dankwali kana a tsefe yake,hakan yasanya gashinta da bata kamashi da ribbom ba ya biyota
shima ya kwanta saman filon da take kai,gama wayarta kenan da ummanta tana nazarin
maganganun data gaya mata taji an murda qofar dakin,wanda hakan yaja hankalinta zuwa
kallon qofar,yana shigowa idanunshi cikin nata,mamaki ya sanyata miqewa ta zauna sosai
saman gadon,tama mance da irin dinkin da yake jikinta,idanunta fal da alamun tambaya,jingina
yayi daura da qofar ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo,sai a sannan ta tuna da
rigar jikinta,tabi kanta da kanta da kallo saita daga kai tana hade fuskarta tsaf,miqewa tayi ta
nufi wardrobe dinta ta soma lalubar mayafi,yana tsaye still yana kallonta har yanzu baice komai
ba,harta gama yafa mayafin ta dawo gefan gadonta ta zauna
"Ki shirya gobe qarfe tara na safe xamu fita tare xan saukeki gida" fuska a tattare ta bishi fa
kallo har ya fice,saita ja qaramin tsaki ta koma ta kwanta tana tunanin ina zai kaita?,kuma me
zata fita tayi.
Tara saura tana tsaka da shirinta wayarta ta shiga ruri,ta qarasa inda take aje ta daga tana
duba mai kiran,anty usaina ta gani,a ladabce ta daga suka gaisa sannan tace
"Na kasa samun layin anwar,inata kira busy,taimaka don Allah ki gaya masa idan zai fito ya fito
da wadan nan takardun"
"Toh anty" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar,qarasa shiryawa tayi sannan ta fito ta haura
saman nashi,tana shiga yana aje wayar gami da miqewa ya tura qofar toilet ya shige,bata masa
magana ba don qyashin hakan takeji,saita barshi ta samu saman kujerar mudubi inda ya tashi
ta zauna tana dakon fitowarsa.
Wayar daya aje saman mudubi wanda take dab da ita ta dauki ruri,idanunta kai kan me
kiran,nafisa ta gani,ta riga data haddace sunan,saita dauke kai saidai hankalinta ya kasa
daukuwa daga kai,tana jin sautin ringing din har cikin kanta harta katse,aka sake kira ta sake
katsewa,ba jima wani kira yasake shigowa,batasan sanda taja wani mugun tsaki ba ta finciko
wayar ta kasheta gaba daya ta dangwarar da ita awajen,tana tuna sanda ta shigo waya taga ya
gama,wala'alla ma shi yasa anty usaina ta gaza samunshi wayama yake kenan
"Ina ruwana da wayarshi" ta gayawa kanta tana sake tsuke fuska ita kadai,daidai lokacin daya
fito daga bandakin jikinsa jiqe da lema,da alama wanka yayi,fuskarta a dinke tsaf cikin kaushi
tace dashi tana miqewa
"Anty tace karka manta ka fito da takardun nan" daga haka tayi gaba,binta yayi da kallo,tana
gab da ficewa yasha gabanta,ya murza key ya rufe qofar,saita danja da baya tana
dubanshi,kuka takeson tayi amma batasonyi a gabansa,don tasha alwashin ta daina yi din yana
gani yana jin dadi "Ka budemin na fita na qarasa shiryawa" ta fada cikin sanyi,wanda ba haka taso,taso tayi
maganar ne cikin kaushi da zafi,saiya kada kai yana duban idanunta wansa hakan yaso mata
tasiri,saita zare nata idon gami da kauda kanta wani sashen daban.
_Dadai zakuyi haquri harmu cimma manufar labarin,don kowanne labari yana da manufar da
akeso a cimma,idan kuma kunason shortcut shikenan_♀️
Mai yiwuwa gobe kujini shuru,idan kuma Allah ya bada dama to.
*karku manta kuyi wekend dinku da tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,ku saurari littafanmu
ba tare da kunsha wahalar karatu ba kuna daga kwance*
*Asha weekend lafiya**Alqawarin Allah*
45
"Zuwa yanzu ya kamata ki fara koyan wasu abubuwan,saboda karta shigo ta rainaki" ya fada
yana son dawo da salon tsokanarshi.
Wani kallo ta watsa masa da idanunta sanda yake komawa zuwa bakin mudubi,wani abu ya
tokare mata wuya
"Wace zata shigo din?,bani ya kamata ka gayawa wannan maganar ba,don ni ba kallon mijina
nake maka ba" saiya waiwayo yana zare idanu
"Da gaske?,lallai kinci tuwo da yawa,wait....waima kallon me kike min?" Harara ta sake watsa
masa ganin yanason maida abun shirme kamar yadda ya saba,baisan yadda ranta ke tafasa ba
"Oho,koma meye ba damuwarka bane,ka budemin qofa kawai na wuce,abu daya na sani
shine,daga kai har ita kada wanda ya sake yashiga hurumina" baki ya kama yana kallonta,sau
tari yakanso yaga tana rashin kunya,sai dan qaramin bakinta yayita burgeshi,don a tsahon
xamansu na baya bai taba ganin tana tsiwa ba sai yanzu "Idan kuma akaqi fa?"
"Raine zai baci" ta amsashi kai tsaye,qaramar dariya ya bushe da ita
"Kinga...kawai ki fito kice kishi ne yake damunki ko?,to kiyi haquri,na miki laifi" sake hararshi
tayi,tanajin kaman ta makeshi ko zataji sauqi
"Ni na gaya maka duka wannan na damuwata bace,bama kallon miji nake maka ba bare nayi
kishinka,ka budemin na fice kawai"
"Aiko kin makaro,dakin yadda kawai da hakan yanzu zan bude miki qofar salin alin,amma tunda
kika musa to sai na gama shiryawa tsaf sannan zan bude ki mu sauka tare" tanaji tana gani yayi
funfurus yahau shiryawa a gabanta ko kunya baiji,haka ta zauna ta kallo bango harya gama ya
budeta.
Har daki yabita ta gama daukar abinda zata dauka kaman wani body guard,tana kumburi
tana komai amma bai kula ba ta fito suka fita.
Gidansu ya soma kaita,ta cika da mamaki sanda suka isa taga ya sake cikinsu sosai kaman
yadda suka saba a baya,sai taga kamar ma sunfi zumudin zuwanshi akan nata,hira suke abinsu
da umma kamar danta,baqinciki yasa ta kasa sakewa ma bare tayi hira,basu bar gidan ba sai
qarfe daya da rabi na rana bayan yaje masallacin layinsu yayi sallah sannan yace ta
taso,kaman ba zata tashin ba,don ita sam lokacin bai isheta ba,amma yadda umma ke jifanta
da harara yasa dole ta miqe tabi bayanshi.
Daga nan gidan anty zubaida sukayi,can dinma haka suka gaisa da antyn cike da
sabo,sannan ya yiwa anty zubaidan sallama kan zaije anjima zai dawo ya dauki shahidan.
Kusan fiye da rabin hirarsu ya ranar jirwaye me kama da wanka anty zubaidan ta dinga
mata da gugar zana,ta kuma fahimceta sarai saidai tayi kaman bata gane ba,duka dai kan
zamantakewarsu ne da nafisa dake shirin shigowa gidan,wanda duka ita tana ganin wannan ba
matsalarta bace,dubanta anty zubaidan tayi sanda suke tsaye cikin kitchen tana tayata yanka
cabbage zata hada coleslow
"Ranar yaushe zaki yinin naki ne banji kince komai ba,yaufa alhamis,lahadi kuma daurin aure"
baki ta tabe bayan ta dubi anty zubaidan
"Ko nawa bikinma ban tsaya wani tsara wuni ba bare bikin wasu" ta fadi cikin qunquni,murmushi
ya subucewa anty zubaida saita kada kai,lallai yaro yaro ne,ga zallar kishi na bayyana kan
fuskarta da kalamanta amma taqi yarda da cewa kishi take
"Wancan daban wannan daban,bakyace ba zakiyi ba kodon idon mutane,kuma kema zaki
buqaci wadanda zasu tayaki karbar amarya"
"Waini zan karbeta ma?" Ta fada tana nuna kanta da wuqar hannunta
"Eh mana,haka akeyi ai" saita jijjiga kai tana ci gaba da yankanta
"Lalllai kam" anty zubaida ta fuskanci zancan ciwo yake mata ba tare datasan da hakan ba,sai
kawai ta shareta suka shiga wata maganar daban.
Bayan sunyi sallar la'asar anty zubaidan tace tazo ta rakata kitso,ba musu ya dauki
mayafinta suka fita a motarta,huda tace zata bisu antyn yace sam tayi zamanta,suna tafe a
motar antyn na nuwa shahidan wasu robobi masu dauke da gumba ta kwakwa da
dabino,wanda idan kanaci zaka xaci an hada kayan qwalamane kawai sai aiki a jiki,wadda
takan jima jikin mace bata bar jikinta ba,ta dinga mata dabara kanta dandana mata taji,haka ta
dinga ci suna hira,antyn tana tuqi a hankali har sai dataci da yawa,ta sake nuna mata wata roba
wadda ke cike da tsumi tace
"Sha kiji wannan fa"dan bata fuska shahidan tayi
"Wainikam anty wadan nan ba irin kayan nan naku bane na matan aure?" Harara ta jefa mata
"Ke matar shika ce?" Sai zancan ya bawa shahidan dariya,ta bude robar ta ta soma
sha,zaqinsa da dadinsa yasa sai data sha rabi,abun har ya baiwa anty zubaida dariya tace
"Ya haka?"
"Wannan kam yayi dadi sosai shima"
"Tsumin maman farida ne,jiya aka aikomin shi daga zariya"tana rufe robar tace
"Amma yayi dadi wlh ya tsumu" dariya ta sake baiwa antyn.
Bata gane inda sukazo ba saida anty zubaida tayi parking,wajen da aka mata gyaran jiki ne
na aure,saida suka shiga ta gane wai ita antyn ta kawo ayiwa,narke mata tayi don ita sam bata
sha'awa,hasalima tasan cewa asarar kudi kawai za'ayi
"Don Allah anty,iya qunshinma kawai ya isa" daga qarshe dai da qunshi kawai aka tsira ja da
baqi,itama antyn aka mata jaa sannan sukayo gida,zuwa lokacin har anyi sallar
magariba,saboda haka tana shiga salla kawai tayi,ko abinci bata ciba ya iso suka wuce.
Tun daga falon qasa taga gidan gaba daya kamar ba nata ba
"Sama zaki wuce" ya furta mata yana zama saman daya daga cikin kujerun,bata kulashiba ta
shige,saidai tayi tayi qofar dakin nata ya budu amma sam yaqi,haka ta dawo falon tana raba ido
zuciyarta fal qunci,da gaske kenan ya maidata saman ya saka nafisan a nata dakin?,zuwa
yanzu baya falon,haka ta gaji da zama a falon bacin rai na sake cikata,tilas ta haura saman.
Dakin da yake kallo nashi ta tura,komai na dakin sabo ne kaman yadda kayan falon saman
ma suke sabo dai dai dana qasan,abu daya yasa ta gane dakinta ne takacen kayan makeup
dake jere saman mudubinta gasunan jere saman sabon mudubinta,ta jima tana qarewa dakin
kallo yadda yatsaru yayi wani kyau,dukka colours din ciki masu kyau da kwantar da
hankaline,sai data gaji don kanta sannan ta cire kayanta tafada wanka,tana wankan tana kallon
lallenta wanda yayi kyau sosai ita kanta ya burgeta.
Kallo daya zaka yiwa fuskarta ka tabbatar da cewa yau din rana ce ta musamman a
wajenta,hakanan farincikin da take ciki ayau din shima farinciki ne na musamman.
Ta kasa boye duk wani jin dadi da walwalarta,duk da cewa yadda taso ba duka haka anwar
yayi mata ba,dinner daya yaje mata a gaggauce,hatta yau da yake daurin aurensu tana da
labarin a makare ya iso wajen,bai kuma jima ba ya koma,saidai duka wannan ba damuwarta
bane,da taimakon mima tasan cewa komai zai daidaita,zata kuma samu yadda takeso.
"Qawata jimana" mima dake tsaye dankwali gaban goshi ta fada bayan ta gama yiwa duk
yarinyar dake madaidaicin falon nafisan kallon tara saura
"Kowa zaici uwasa" ta fadi a ranta,shigowarta kenan ita dinma batazo da wuri ba,ta jima tsaye
daga waje tana kallon yafda nafisa ke wani rawar kai kamar zata taka kan shege
"Gani,ta samu ne?"
"Eh kusan hakanne,amma qawata,bayan sauran event da ango baizo daurin aurenma ance a
makare yazo ko?" Tabe baki nafisa tayi da alama tadanji haushin abun
"Hmmmm,wallahi in gaya miki mima,ban sani ba ko waccar matar tashice ta tsaidashi Allahu
a'alamu"
Sake tabe baki mima tayi
"Waxai hanashin idan ba ita ba?,kinga abinda nake gaya miki aiko?" Sanyin jikin nafisa
yayi,saita zubawa mima ido kawai tana kallonta,da alamun neman mafita take,hakan yayi dai
dai da tsarin miman,saboda haka tasa hannu cikin jikirta ta fito da wani qullin baqar leda ta
soma warwareta,layune tafka tafka guda biyu wanda jikinsu yake wani iri babu kyan gani ta
nuna mata
"Wannan,ki tabbatar ayau ko gobe idan an kaiki kin maqalata gefan gadonki" ta ajeta ta dauko
wasu baqaqen garin magunguna da wani mai kama da man shafawa saidai kore sharr yake
"Wadan nan kuma kin gansu?" Tafada tana duban nafisan sosai,alamun maganar da zata gaya
mata babba ce
"Kin gansu dakyau ko?"ta sake jaddada mata,gyada kai nafisan tayi tana kallonsu tana kallon
mima
"qananu ne amma amfaninsu yawa ne dashi,wadan nan da kike gani idan kikabi doka da
tsarinsu to rayuwar gidan aurenki zata inganta ta tafi yadda kike fata,idan kika tsallake doka
daya ko sharadinsu to kuwa babu shakka kjn wargaza komai,kuma komai zai iya biyo baya"
cikin nuna zaquwa da qaguwa ta gyara tsaiwarta tana cewa "In sha Allahu ba abinda zai faru,gayamin ya amfaninsu yake" sai data daure ta miqa mata
sannan tace
"Daga randa za'a kaiki gidanki zaki jiqa kowanne kiyi tsarki dashi,mai kama da man shine na
shafawa,zakiyita amfani dasu har tsahon watanni uku cif cif,sharadinsu sune,idan kika soma
amfani dasu babu maganar kwanciyar aure harsai kin kammala,kinga kenan daga randa xaki
shiga gidanki harki kammala amfani dasu ba zaki bawa anwar kanki ba harsaikin gama amfani
dasu,ammafa daga randa kika gama amfani dasu yasanki a 'ya mace ko?" Sai tayi shuru tana
juya idanunta sannan tace
"Uhmmm.....abun ba'a magana kawai" ta furta murmushi na qwacewa fuskarta,shuru nafisa tayi
tana nazari,da alamu ta shiga damuwa,cikin zuciyarta tana jin babu dadi,ba qaramin buri ta
cuwa first night dinta ba,tayi alqawarin saita hana shahida bacci a ranar saboda tayi tayi anwar
ya kaita gidansa na alfarma data sani wanda da yake zaune a ciki amma yaqj,gidan da xai
kaitan sam yayi mata qanqanta
"Yanzu har watanni uku kenan ba wani mu'amala tsakaninmu?"
"Eh...indai kinanson samun yadda kikeso,idan kuma ba haka ba,kina iya bani maganina na juya
dashi,saiki shirya fuskantar duk wata rayuwa da zaki gani" da sauri ta janye maganin ganin
mima ta miqo hannu tana cewa
"A'ah,Allah na tuba don dai wata uku kawai?"
"Ah to nima shi na gani,kuma gidan nan bake kadai bace bare kice akwai matsala,idan ya
matsu ya tafi wajen dayar" harara nafisa ta watsa mata cike da kishi
"Tabdi,lallai ma,to bari kiji,nijin kaina nake ni kadai nake wallahi" dariya mima ta kwashe da ita
harda tafa hannu tana duban nafisan,yayin da nafisan ta taka tayi gaba ta koma cikin mutane
yana yiwa miman godiya,juyawa tayi mima ta fice daga gidan tana sakin murmushi don tace
mata ba zata zauna ba akwai inda zata,amma anjima da ita za'a kai amarya.
Sake dawowa yayi jikin qofar karo na babu adadi,tun kafin ya fita daurin aure take cikin
dakin kuma taqi fitowa,yayi juyin duniya amma taqi tabude mishi,ko bata fada ba koda bai sani
ba jikinsa ya bashi kuka take,dalilin daya sanyashi makara baije akan kariba kenan,bayan yaje
ya dawo kuma nanma ko reception din da aka shirya bai tsaya ba yayo gida saidai jiya
iyau,daga qarshe badon yaso ba ya yanke tilas ya kira anty xubaida ya gaya mata.
Sakin ajiyar zuciya tayi tana aje wayar bayan gama doguwar waya da sukayi da anty
zubaida da kuma zunnurah,ita kanta tanason tayi controlling kanta amma ta kasa,wani irin bacin
rai da baqin ciki ke taso mata,tadan dauki wasu mintuna a zaune a wajen sannan ta miqe ta
shiga bandaki,ta hada ruwan wanka mai dumi sosai tayi wanka,already ta riga data sauko ta
gyare gidan tun sanda taji fitarsa,shi kadai dinne kawai batason gani,amma dole ta haqura ta
dauki maganar anty zubaida da zunnurarta,donta wuce komai a wajenta.
'Yar madaidaiciyar kwalliya tayi cikin wani sabon coffe lace me adon silver pink da
golden,sosai ta dinkin ya tsaya mata,hakanan lace din yahau fatarta qwarai,ta saka awarwaro
dan kunne da sarqa duka silver ta wadata jikinta da turare.
Dai dai nan taji ana sake knocking,ta kalli qofar ta dauke kanta,sannan ta soma takowa ta
bude ba tare data tambayi waye ba,anwar dinne yana tsaye qofar dakin sanye da rigar da
wando na shadda blue ruwan sararin samaniya,fuskarsa sam babu walwala,hannunsa goye a
qirji ya zubawa qofar ido,wanda tana bude qofar idanunshi suka sauka a kanta,rabon daya
sanyata a idanunsa tun ranar dinner din nafisa data matsanta mishi sai yazo,sanda ya shirya
zai fita tana falon qasa tana kallo,abinda kusan ba dabi'arta bace,zai mata magana bata tsaya
saurarenshi ba ta tattare wayoyinta da kayanta ta haura saman ko waiwayoshi batayi ba,sai yaji
sam baiji dadi ba,tunda ba dabi'arta bane zaman falo mai yiwuwa yau tayi sha'awa ne gashi ya
bata mata yanayi,koda yaje a gurguje ya dawo,amma saiya tadda ta garqame kanta,tun ranar
rabonshi da ganinta sai yau.
Bata ankara ba har ya iso gabanta,saiki tayi ta riqe dukka hannayenta cikin lallausan tafin
hannunshi,runtse ido tayi tana son zamewa amma ya riqe gam,saita soma qoqarin ganin ta
qwace din,gaba daya ya janyota sai gata cikin jikinsa,saura kadan numfashinta ya dauke,ta
dinga qoqarin zuqoshi hadi da shaqar qamshin daddadan turarenshi "Babu dadi ko?,kiyi haquri" ya gaya mata muryasa qasa qasa,tsigar jikinta ta zuba sosai,saita
soma kokawar cire jikinta