Showing 81001 words to 84000 words out of 126208 words
Chapter 28 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
fika,ba zaka taba samun nasara a kaina ba,nuradden kuma idan Allah yaga
dama kai baka isa ka rabani dashi ba"itama ta fada cikin tunzura fushi da bacin rai
"kome zaki fada dai dai ne,duk yadda kika fassara lamarin a ranki ko a bakinki kisa a ranki haka
ne,any ways ma ni nasan na taimaki rayuwarki ne,ko kina tunanin wancan wawan idan yaji
wace ke a baya zaici gaba da haukan da yake a kanki?,kinga 'yammata....koki sawa ranki sauqi
ko kar kisa duk uwar ubansu daya" kai take gyadawa bacin rai na cinta,idanunta fes cikin
nashi,ji take kaman ta shaqe anwar din,a yanzu babu halittar data ji ta tsana sama dashi
"Zan saka salamar duk da bakayimin fatanta ko burin samunta,amma ka sani....tsugune bata
qare ba,don babu abinda zanyi da masoyi irinka nawar!,ka shirya tarbar duk wani abu da zai
tunkaroka!" Tayi lafazin da alama wani abu ya motsa ranta qwarai,duk da murta na a raunane
amma amma fuskarta da qwayar idanunta na bayyana jarumtarta,wani malalacin murmushi ya
saki ya sake matsowa inda take,wannan karon har qamshin turarensan nan data sanshi dashi
yana busowa zuwa hancinta,ya kafeta da idanunsa,muryarsa can qasa kamar mai shirin furta
kalaman soyayya a gareta yace
"A shirye nake,kece zan gayawa ki shirya zama dani idanma ba'a shirye kike ba,yaushe kikeso
wasan ya fara?" Ya fadi cikin halin ko in kula,ganin kallon da yake mata bacin rai ya sanya ta
fashewa da kuka sosai ta zube saman kujerar tana rufe fuskarta da tafin hannunta,saiya tabe
baki yana isa inda hularsa take yasa hannu ya dauka yana cewa "Ashe raguwa ce ta gaske,tun yanzu?,wasan namu kuwa zaiyi iri qarkon da nakeso?" Ya dora
hularshi saman kansa sanda ya qarashe maganar,saiya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya ciro
kudade sabbabi masu dan yawa ya aje hannun kujerar da take kai yana cewa
"Ga kudin zance nan,kuma bance a sayi abunda za'a bugu da kudina na,idan aka siya Allah ya
isa na" sosai maganar ta doketa,tana niyyar daga kai ta dubeshi ta fuskanci ya juya zai fita
ne,har yakai bakin qofa sai yasake cewa
"Ammmm..." Yana dawowa da baya,kanta yazo ya tsaya hannunsa daya a aljihun wandonsa
dayan kuma yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa
"Karki manta da sadakina akanki,shaidu kawai za'a tara a daura,ban lamince ki kula kowanne
dan iska ba,ciki harda wannan looser din,idan kuma kikayi hakan shima Allah ya isa ban yafe
ba" saiya sassauta murya ya sauko da kansa qasa qasa gab da ita
"Ina fata har yanzu wasu daga halayen anwar basu bace miki ba daga kanki,mutum ne mai
kishi,ina da kishi kan mace koba wadda ban biya sadakinta ba bare wadda na cire halalina sa
nasha wahalar nema zafi da sanyi nabiya" a fusace ta bude fuskarta saboda yadda
maganganunshi suka isheta,saita ganshi dab da fuskarta,cikin bacin rai da muryar kuka take
cewa
"Sadakinka din banza da wofi,idan kana son nunan kudinka wata tsiya ce kaje ka karbi
sadakinka idan har ka isa cikakken namiji" tsaf ya karanci bacin ran dake kwance muraran
saman fuskarta,saidai yadda yake jin quna yana tunanin bata jin haka,duk sanda zai kalli
fuskarta yana tuna sanda aka sauketa ne a gabanshi,cikin maye,cikin jini,pant dinta a gabanshi
aka cilloshi,wani ya riqe zuwa jikinsa gaban idanunsa,saiya runtse idanunsa kana ya bata baya
ya soma takawa
"Idan kin isa ke kije ki karbo kin kiga idan ban amsa ba,dama taimako nayi kuma na fuskanci ke
bakiga hakan ba" daga haka ya qarasa ficewa daga dakin,sake rushewa da kuka tayi,ta tsani
kalmar taimakon nan,wannan wanne irin cutace?,ita zai taimaka.
Cikin gida ya qarasa,daada na rumfarta a zaune ita da hasina,saiya cire takalmansa ya
zauna saman tabarmar dake shimfide qasan inuwar bishiyar dake tsakar gidan,daadan tayi tayi
dashi ya shigo amma yace wucewa zaiyi,dole ta fito ta zauna daga gefan tabarmar itama
"Zan wuce daada,ina tunanin rana ita yau za'a kawo lefe,to bansan inda za'a kai ba,can wajen
umma,ko nan garin ko kuma gidan uncle hisham?"
"Babu damuwa akai can hidan hashimun tunda acan za'a yi duka bikin,muma can zamu tattara
ai mu tafi"
"To daada,Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" ya furta yana dan sadda kanshi qasa alamun
girmamawa
"Ina kuma ta shiga?" Daada ta tambaya,ya fuskanci shahida take magana,saiya saki
murmushin daya qwata fuskarshi duk da baikai masa qasan ranshi ba
"Tana daki tana kukan bata sona can na barota" kama baki daada tayi tana salati harta baiwa
anwar dariya,harya miqe ya aje mata kudi ma sam bata kula ba tana ta jajjabi tare da sillewa
shahidan hasina na dariya,sai daya sanya takalmansa sannan ya kalli hasina
"Taimaka kije ki fito da ita daga dakin karta rube" dariya hasina ta saki sosai,abun saiya qayatar
da ita,ya yiwa daada sallama suka fice zuwa soron gidan shida hasina.
Bakin qofar dakin ya coge ya yaye labulen bayan hasina ta shiga dakin,ta isa inda take
dunqule tana gursheqen kuka
"Saikace yau akace za'a kaiki?,taso da Allah karki tara mana jama'a" hannun hasina ta buge
tana jin takaici yana cikata,duk maganganunsu da daada tana jinsa,tamkar ma ya raina mata
wayo ne,ko yana tunanin 'yar qaramar shahida daya sani a baya ce wannan?
"Matsa hasina barta,bari na rage miki aikin na dauketa zuwa qofar soro saiki qarasa shiga da ita
ciki,da sauri ta bude fuskarta,idanunta da sukayi jawur zuwa fuskarta ta kalleshi dasu
"wallahi wallahi ka sake ka tabani sai kayi dana sani!" Ta fada a kausashe
"Meye hakane shahida?" Hasina ta tambayeta tana dubanta cikin mamakin kausasa lafazin da
tayi,dubanta yake sosai,yana son yace shine farau?,amma idanun hasina yasa ya maida
amsarsa
"Wallahi wallahi kinji nima na rantse matsawar baki tashi kin shige ba ko abinda yafi danasani
zanyi saina dangana dake har rumfar daada" saiya maida dubansa ga hasina dake tsaye tana
kallon dramer
"Ina cikin mota a qofar gida,minti biyar na bata idan ta dara hakan bata tashi ba ki fito ki
gayamin" kai ta gyada ya saki labulen ya taka a sannu ya fice daga soron.
Bata buqatar duk wani abu da zai kawo wani kusanci tsakaninta dashi,so take ya tafi yabar
gidan saboda haka ta miqe tana hada hanya,hasina ta dauki kudin dake aje inda ta tashi ta bita
dasu a baya,ko kallon dada dake tsakar gida tana mita batayi ba ta shige rumfar daadan ta
zube saman kujera,saita dora hannu aka ta fashe da ihun kuka ko zataji salamar radadin da
take ji cikin ranta,hasina kallonta take idanu a waje cikin rudewa tace
"Meyw haka ne shahida kike kamar wata 'yar shekara goma,ya zaki tara mana jama'a?" Takai
qarshan maganar sanda daada ta runtumo cikin dakin tana tambayar ba'asi
"Au ihu kike?"
"Wallahi daada bana sonshi,shima daada ba sona yake ba bazai gaya muku gaskiya bane
kawai" baki ta tabe tana mata duban sakarya
"Au Allah ko?,ashe tun farkon saninmu dashi mu muka jajibo miki shi ko?,ashe qiyayya ce ta
hadaku a baya ba soyayya ba?"
"Daada baya sona yanzu bana sonshi!" Ta sake fada cikin kuka
"Eh naga alama,shi yasa bai bar kakarki ba yaci gaba dayi mata aike a boye bai bari nasan
wayeshi ba,kuma qiyayyar ce tasa ya tasl qafa da qafa ya nemi aurenki hannun iyayenki"
"Wallahi daada kinji na ra ntse miki da manufa a lamarinsa"
"Dama akwai auren da babu manufa?,shirme kenan" ganin duka taqi fahimtarta saita sauko
gwiwoyinta qasa tana kallonta
"Daada,don girman Allah ku maida masa kudinsa,ko bazaku bani nuradden ba na amince ko
zabamin ko waye a lokacin da kuka saka na bikin nawa ayi dashi" nazarinta daadan tayi na
wani dan lokaci sannan ta kamata ta miqar da ita tsaye
"Naji,zauna muyi magana" sanyi taji yana ratsa zuciyarta,ta soma jin qamshin nasara,saita miqe
din kamar yadda daada ta buqata suka koma saman kujera suka zauna.
Saidata bata 'yan mintuna ta nutsu tukunna sannan tace
"Komai da kika gani a rayuwa yana da dalili,inason ki gayamin dalilinki na duka wadan nan
maganganun da tsallen badaken qin auren mutumin da kowa ya shaida kuma yana da labarin
soyayyarku" shuru tayi kawai tana qiyasta ta yadda zata gayawa daadan komai bayan basusan
komai ba akan rayuwar data fada a baya,sannan uwa uba shi kansa anwar din ta fahimci ba
wanda ya taba gayawa ko bashi labarin komai,idan ta aikata hakan kamar ta dabawa cikinta
wuqa,kamar ta yaye mayafin asirin da Allah ya rufa mata kenan?,ganin tayi shuru sai daada tayi
tsammanin ko batason magana ne a gaban hasina,saboda haka ta korata waje
"Ki gayamin dalilinki,indai matuqar na gamsu,toba shakka a yau basai gobe ba zamu maida
masa komai nashi" tofa ga qoshi ga kwanan yunwa,ta ina zata fara ya zatayi?,batason tona
komai,batason kowa yaji komai,tana ganin kamar ba muhallin kowa bane ba hurumin kowa
bane Kai ta kada
"Daada baya sona ne,nima yanzu na daina sonshi,kinga babu amfanin aurenmu" murmushi ta
saki tana kada kai
"Banda abinki shahida ta yaya masoya haka siddan zasu daina son junansu?,ai ruwa baya
tsami banza" cikin nuna dagiya da qarfin hali tace
"Hakanan nidai daada muka daina son junanmu,don Allah karku qulla auren qiyayya" hawaye ta
siraro daga idanunta muryarta ta soma rawa,saita sake murmushi tana kallonta
"Shahida,anyi auren hadin da baki taba ganinsa ba bai taba ganinki ba sai hadi kuma an zauna
lafiya harma yafi na soyayyar qarko,kin ganni nan gani da ran Allah?,to sanda na auri kakanku
sai randa ya shiga dakina nasan shi na aura,saboda haka indai rashin soyayya ne hujjar fasa
aurenki da anwar indai kikaga an fasa to la shakka mutuwa nayi bana raye,ko bana raye zanbar
wasiyyar a tabbatar an daura,don anwar din ya cika dukkan siffa da kamalar da annabi yace a
baiwa mutum aure" daga haka sai daadan ta miqe ta qyaleta,tashin hankalin data ji a sannan
yasa taji zuciyarta ta bushe gaba daya,hawayen idanunta sun bushe tas,saita miqe itama ta
shige daki tayi rub da ciki tana sakin ajiyar zuciya ko zataji sanyin tuquqin da ranta yake.
Ta shafe a qalla minti talatin a haka kafin daga bisani ta janyo wayarta,ta lalubo number
nuradden ta kira,bugu daya tak ya daga,ajiyar zuciya ya soma saukewa da alamu hankalinsa
shima ba'a kwance yake ba,duk sai taji bacin rai ya sake shigarta,shi ya janyo komai,shine silar
komai "Ka dawo ka sake neman aurena karo na biyu nuradden,bazan iya aurensa ba" ta fada kai
tsaye ba tare da tayi sallama ba ko tace komai,kafin taji yace wani abu taji an karbe wayar,da
sauri ta daga kai don ganin waye,daada ce,bata ce komai ba ta kara wayar a kunnenta
"Nura kana jina?" Ta fadi sanda take ficewa daga dakin,saita miqe ta zauna sosai saman katifar
tana bin qofar da kallo.
*muna muku fatan alkhairi tare da fatan zaku gudanar da bukukuwan sallarku lafiya cikin
amincin ubangiji,Allah ya karba mana ibadunmu,ya gafarta mana zunubanmu,yaji qanmu ya
jiqan mamatanmu,yasa mu cikin 'yantattun bayinsa amin umma amin,ZAFAFA BIYAR na muku
fatan alkhairi*
*_karku manta,ku kasance da tashar SAUTIN HIKIMA TV don sauraren littattafan da zasu debe
muku kewa yayin ayyukan sallah a gida*
*kundin qaddarata*
*daurin boye*
*mutuncin mace*
Duka wadanda na rubuta
*fatan alkhairi a gareku*
#zafafa biyar
#sautin hikima tv
#team anwar
#team shahida
#team nafisa ♀️
_ma'assalam__ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsaffin litattafanmu dama
sababbi da zamu fara dorawa nan gaba kadan in sha Allah_
https://youtu.be/H7M7h6l6wNM
*Alqawarin Allah*
3️⃣1️⃣
Minti goma kyawawa daadan ta dawo,ta miqa mata wayartata tana dubanta,sannan ta miqa
mata kudin da anwar ya bata tana cewa
"Tunda kin zabi zubar mana da qima rahama mu zuba nida ke" daga haka ta juya ta fice,a
sannan ji shahidan take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu ko xata ji sanyi cikin
zuciyarta,me yasa ba zasu fahimceta su bata uzuri ba?,me yasa ba zasu haqura ba?,wai da
anwar da itama wa sukafiso ne?,waye nasu a ciki?,kira ne ya sake shigowa wayarta,ta daga ta
duba da sauri sai taga nuradden ne,muryarsa kadai ta gaya mata cewa ya karaya bashi da wani
sauran fata
"Shahida,na rasaki shahida,ta ina zan iya jurewa rashinki?,zan iya tsira daga hukunci da horon
rasaki da zuciyata zata yimin?,ki tayani addu'a bansan ya zata kayamin ba" daga haka ya yanke
kiran,me daada ta gayawa nuradden?,shikenan ta rabata dashi?,dole ta zauna da mutumin da
sam bata ra'ayinsa ne wai?,irin wannan masoyin zata rabata dashi?,kalamansa kawai sun
tabbatar da tsantsar qauna da soyayyar da yake mata,saita kifa kawai rubda ciki tana lalube da
binciken meye abunyi a qwaqwalwarta,mecece mafita?duk wata dabararta ta qare,wayonta
duka ya qure,daada ta yanke komai.
Qarfe bakwai da rabi ne na daren ranar,yana zaune a harabar gidan saman daya daga cikin
fararen kujerun roba dake wajen,shi ya zabi zama a wajen saboda yadda iskar damina mai
sanyi ke busawa gabas da yamma,hakanan qwayayen lantarkin dake harabar gidan sun haske
ko ina harda korayen tsirran dake harabar wajen,sai yake jin zuciyarsa wasai,hakanan babu
nauyi qunci ko wani abu da yakejin ya dameshi a yanzu,shaqar iskar yake sosai yana fesarwa
har cikin huhunshi qamshin iskar da sanyinta na sake sa zuciyarsa cikin wani shauqi da
walwala,fuskarsa fes take a washe.
A hankali take takowa cikin gayunta,tayi kyau don ba qaramar kwalliya ta dauka ba,don yau
din na daya daga cikin ranakunta na musamman,saboda bako da yaushe take samun dama irin
wannan ba,ace yau anwar din yazo zance takanas saboda ita,zata iya irga sau nawa hakan ya
taba faruwa a tarayyarsu,shi yasa duk ransa zaizo din ba qaramin tanadi takewa ranar ba.
Gabansa ta tsaya sannan tayi sallama tana kallon yadda yayi masifar kyau cikin qananun
kaya sai kace wanda ya dawo daga europe,ya daga kai yana dubanta sannan ya amsa,cikin
shagwaba shigarsa da yadda yayi kyau yana dada burgeta tace
"Ya bakaci komai ba dear?" Ta qarashe fada tana jan kujerar dake kallonsa ta zauna,duban tulin
kayan ciye ciyen dake gabanshi yayi sannan ya kalleta,shi sam a ra'ayinsa ba mutum bane mai
yawan son ciye ciye,kusan ma babu cimarshi ciki sai kadan,kafada ya daga
"Karki damu,duka basu da muhimmanci,zuwankin da ganinki ya fisu muhimmanci" wani farinciki
data jima bataji kamarsa ba ya tsirga mata,ta lumshe ido tana sakin murmushi,ta jima bata ji
kalmar data mata dadi matuqa daga anwar din ba irin wannan,sannan ta budesu idanun nata a
kanshi "Ya gida yasu momy"
"Kowa lafiya suna ma gaidaka" ta fada tana zuba masa lemo sannan ta tura masa,bai musa ba
yaja yadan kurba tana binsa da kallo,batasan wane irin qauna takewa anwar din ba,jifa jifa take
sako hura yana tayata kana ta sako masa zancan bikinsu,lissafin events da zatayi da sauran
abubuwa,yana kurba yana saurarenta sai daya shanye sannan yace mata "Next week za'a kawo lefen idan Allah ya kaimu....saidai kuma kafin sannan inason nayi wata
muhimmiyar magana dake,duk da na riga na shaidawa su momy amma naga kece yafi
cancanta ki sani,kuma ni yafi dacewa na sanar miki da kaina" dukka hankalinta ta bashi ganin
yadda ya tara shima nutsuwarshi waje guda gamida soke yatsunsa cikin na juna yana dubanta
sosai
"Uhmm,ina jinka"
"Komai da kika gani a duniya muqaddarine daga Allah,hakanan ba wanda ya isa sauya tsarin
Allah,yadda ya tsarawa bawa haka zai karba,naka kawai ka gode masa,zaka iya tsarawa
rayuwarka abu amma idan baiyi dai dai da tsarin Allah ba zai sauya maka ne da wanda yake
ganin shine daidai da rayuwarka kuma shine mafi alkhairi,to...ina tunanin ku biyu za'a daura
mana aure dasu lokaci guda,na nemi aure watanni biyu baya da suka wuce Allah ya qaddara
kuma an bani,yanzu haka cikin satin da za'a kawo naki kefen suma za'a kai,lokacin daurin
aurenma kusan daya ne,rana ce kawai aka bambanta,kinga ya kamata ace kin sani saboda
kina da haqqin ki sani din,nasan mai yiwuwa hakan zai bata miki rai saboda halin kishi irin na
mata,saboda haka ina mai baki haquri tare da shaida miki haka Allah ya qaddara dama tun
fil'azal shi yasa ya hukunta faruwar hakan,ina fata hakan bazai dameki ba don kowacce cikinku
matsayinta daban" wani irin abu taji yana mata yawo tsakiyar kaa kamar ana yamutsa
qwaqwalwarta,wannan wacce iriyar mummunar rana ce?,wanne irin mummunan labari
kunnuwanta suke dauko mata?,saita cije lebanta da kyau ga zatonta mafarki take ko zata
farka,saita fuskanci da gaske ne,wani abu ke niyyar toshe mata numfashi,ta fahimci idan bata
bari tayi kuka ba wani mummunan abu na iya faruwa da ita,saboda haka kawai ta saki hawayen
da take qoqarin tarewa suka soma zuba
"Wanne irin abu kake gayamin haka anwar?,kana gayaminne fa kishiya zaka yimin tun ban
shiga gidanka ba,anwar kana gayamin zaka hada soyayyata data wata ne fa,kana gayamin
zamu hada miji da wata,zaka raba soyayyarmu,wai shinma yaushe ka ganta harkaji kana sonta
kaji zaka iya aurenta?" "Karki damu,ba wata sabuwa bace cikin rayuwata,mun jima tare,rabuwarmu da ita qaddarar
haduwarki dani ce"
"Shahida?!" Ta fada cikin razana da kuma salo na tambaya,saiya zuba mata idanu yana kallonta
tare da mamakin kama sunanta farat daya da tayi kafin daga bisani yace
"Eh,ya akayi kika santa?" Sam batabi takan tambayarshi ba saboda ji take kamar alqiyamarta ta
tsaya,a ina ya tono shahida?,a ina ya ganta?,ya akayi suka daidaitawa?,ya akayi ta aminta zata
aureshi?,ya akayi yaci gaba da kulata?,dama soyayyarta bata mutu cikin ransa ba?,inaa,har
abada ba zata taba yarda ta hada anwar da shahida ba qarqashin inuwa daya,kuma ta kasance
a tsakiyarsu?,ashe data cika shashasha
"Kacemin kawai ka koma wajen tsohuwar masoyiyarka donka samu damar wulaqantani idan ka
aureni,har abada anwar bazan hadaka da wata ba,bazanyi zaman kishi da kowa ba,bazan
zauna da kishiya ba" ta fada tana miqewa tsaye,cikin hargagi,hannunshi ya daga mata a nutse
"Ki nutsu nafisa ki samu waje ki zauna"
"Bazan nutsu ba,bazan zauna ba,ka daina kiramin nutsuwa a wannan yanayin,saidai ka zaba
koni ko ita" furucin ya fito hade da kuka mai cike da tashin hankali
"Ba wanda zan zaba hakanan ba wanda zanqi zaba" ya amsa mata kai tsaye tana dubanta cikin
yanayin dake nuna