Showing 111001 words to 114000 words out of 126208 words

Chapter 38 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

ba" ya fada yana
takowa zuwa inda take tsaye,yanajin bazai iya barinta yadda ta rikitashi taci bulus ba ba tare da
shima yau yadan taba koda fatarta ba yaji yadda akeji,baya ta soma ja tana kallonshi,bata
fahimci me yake shirin aikatawa ba saida ya kusa qureta jikin madubin dakin,idanunta cike fal
da tsoron da takeson boyewa tace
"Meye haka kakeyi?"
"Abinda kika gani" ya bata amsa bai fasa nufota ba,cikin dan tsoro tace
"Karka tabani" cak ya tsaya yana kallonta
"Tunda kwartone ni?" Ya amsa mata ta sigar tambaya,bai kuma bi ta kanta ba yaci gaba da
nufarta,don baijin zai iya haqura din shima bai d'aana ba,ko ina ta kalla ya riga daya kangeta,a
haka ya hade gap din dake tsakaninsu,ya zagaya hannunsa ta qugunta ya janyota sosai cikin
jikinsa,fuskarsa ya sauko da ita dokin wuyanta yana kai hancinsa,ta soma juye juye tana son ta
qwace daga hannunshi
"Banaso,meye haka,ka sakeni"
"Ni kuma inaso" ya fada yana fidda numfashi saboda yadda abun ya soma masa dadi,wayarsa
dake saman mudubin ta dauki haske da qara,wanda hakan yaja hankalinsu gaba dayansu,a
tare idanunsu ya sauka a tare kan screen din wayar,sunan NAFISA ya bayyana saman screen
din,dauke idanunshi yayi yaci gaba da abinda yake,hakanan taji wani abu yadan sosa mata rai
kadan,amma saita dauka yadda ya tarfata ne yake yadda yaso da ita,sosai yake shinshinar
kowanne lungu da saqo na jikinta yana fitar da numfashi,ko ina jikin shahidan rawa yake
itama,karon farko da irin hakan ya soma faruwa da ita a rayuwarta,tsoro da haushin anwar din
ya cikata ganin da gaske yake yau ba wasa bane,kaman wanda aka tsikara ya saketa da sauri
gami da turata baya shima yaja baya da hanzari yana zama gefan gado ya dafe kanshi dayaji
ya sara masa lokaci daya
"Ya Allah" ya furta yana ci gaba da dafe kan nashi,hanqota kawai yayi sanda take rungume jikin
wani,bayaso ire iren wadan nan tunanukan su dinga dawo masa kwanya,saboda haka saiya
dinga maimaita
"Hasbunallahu wani'imal wakil" tana zuge zif din rigarta tana mamakin yadda lokaci guda
yasaketa haka,yanayin da taga ya shiga din,saidai itama ba'a nutse take ba saboda haka tana
gama jan zip din nata ta soma tattaki cikin hanzari zata fice
"Dawo nan!" Ya fada cikin kakkausar murya,ba musu tadawo din ta tsaya cak saidai bata
dubeshi ba,fuskarshi a dinke take tsaf babu fara'a ta sisin kwabo
"Shiga ki hadamin ruwan wanka" jikinta a mace take takawa zuwa bandakin,ta hada mishin ta
fito ta shaida masa,saiya miqe kawai ya zari towel
"Karki tafi saina fito" ya fada yana shigewa cikin bandakin,tsayawa tayi cak,ta jingina da madubi
tanajin yadda qafafunta suka mutu,jikinta babu qwari sam,ta soma tuna yadda taji daxun da
yadda abun ya kasance,saita lumshe idanunta tana tuns komai,qamshin jikinsa daya goga mata
yana zarya cikin hancinta har zuwa qwaqwalwarta,kasala na sake saukar mata,qarar da wayar
tashi ta sakeyi ita ta katse mata duk tunaninta ta sanyata bude ido,bata tabata ba sai dubanta

data kai kan wayar,sunan nafisa ne dai again,saita ci gaba da kallon wayar harta katse,tana
shirin dauke idanun nata wani kiran ya sake shigowa.

Ci gaba tayi da kallon wayar har kiran ya sake katsewa,duk kiran daya shigo din kan
idanunta ya dinga shigowa yana katsewa,wanda a qalla kafin ya fito din an kira yakai sau goma
sha biyar,kuma ba'a fasa kiran ba,bata dauke idonta ba itama saida taji ya soma qoqarin bude
qofar bandakin sannan ta kauda kai tana tunanin wace wannan haka?,meye ya faru take jero
kira haka ba qaqqautawa?,bakin mudubin ya tako saita matsa gefe tana sake dauke kanta wani
sashen,towel ne daure a jikinsa iya qugu,sai wani daya ratayo wanda duka duka bai gama rufe
jikinsa ba gaba daya,wani nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,gabanta ya dunga
faduwa sosai,ta sake dauke kanta yadda ko inuwarsa ba zata gani ba,baice mata komai ba ya
daga wayar ya duba mai kiran,duka nafisan ce,cikin zuciyarsa yaja tsaki yana tambayar kanshi
me zata masa?,ya aje wayar yana cewa
"Kije ki shirya,zamuje duba anty usaina batajin dadi" waiwayowa tayi cikin faduwar gaba da
fargaba,bala'in kunya da nauyin anty usainan takeji,yanzu kuma zai kaita gidanta?,saidai a
kamatance ma bai kamata ta musa masa ba kodon karamci irin na anty usainan da qaunar da
take gwada mata.
Tana shiryawa amma kiran wayar ya tsaya mata arai,ta rasa dalili,kiran sai takega kamar
yayi yawa,a haka ta gama shiryawa tsaf cikin wani lace,ta yane kanta da yalwataccen mayafin
daya dace da shigar tata,saidata dubawa anty usainan abinda zata kai mata ta saka cikin jakar
hannunta sannan ta fito,a falon qasa suka hadu,saita tsinci kanta da satar kallonsa duk da bata
shiryawa hakan ba,anwar badai wanka ba,tunda can tun lokacin da bashi da komai mutum ne
mai tsafta da kwalliya ma gaba daya,yayi kyau cikin yadin kufta na maza,dubanta yayi sosai
wannan karon kanshi tsaye babu boye boye
"Wannan qamshin yayi yawa" yana takowa zuwa gabanta,tuna abin daxu daya mata tayi saitayi
hanzarin jaa da baya kada ya maimaita,don har yanzu jikinta a mace yake,tsayawa yayi cak
saiyayi murmushi cikin ranshi,ya gane me take gujewa,itakam ba wani turare ta saka ba bayan
na jikinta,juyawa yayi ya fice ta mara masa baya.
Zata shiga baya kamar yadda ta saba masa taji qofar taqi buduwa,haka tayita qoqarinta na
budewar amma taqi da alama lock ya saka,dole ta dawo gaba ta bude ta shiga.

Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa da anwar
din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna gab da valcony din
da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da yalolon mayafi,hada idanu
sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake
ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na
musamman da gake fitarwa,shi ya soma janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu
da shahida dake bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa
take sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba zata taba
mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta ta rufawa anwar
baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan shahidan har suka wuce,sannan

taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta
takai maqurar da bazata iya jurewa ba.

Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty usaina,gaba daya
yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare shahida ta rungumeta
"Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau"
"To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin da
maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa
"Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda yace
komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba hira da
sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty usainan?.

Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a baya har
suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka shiga da
sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota anwar ma bata biba,a
kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar antyn fitilun harabar gidan da
wasu suka mutu
"Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga shahida
wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa cikin
kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata
"Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a qasa cike da
jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray wanda ta cikashi da kayan
ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana zuba mata duk abinda ke cikin
farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya idanu a waje yadda su anty usaina
bazasujiba tace
"Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe"
"A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman"
"Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?" Tana
dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta kalleshi cikin dariya
"Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda ne,kaga
idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana satar kallon
shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty usaina don sake
kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta sa'idan bata mantuwa,ta
kammala zubawa shahida komai ta miqe tana duban anty usaina
"Na gama ummi"
"Shikenan,idan kin sauka ki shiga kitchen ki tafasa min maganin nan,ki samu botiki mai murfi ki
xuba a ciki kidan sabashi yasha iska kafin na sauko shi xansha"
"Tohm" tajuya ta dubi shahida
"Anty kici sosai don Allah ki cinye duka" murmushi kawai tayi tana dubanta,sosai yarinyar take
sonta da burgeta.

Inda shahidan ke zaune ya sauko,ya zauna sosai a gabanta,farantin dake tsakiyarsu ne
kawai ya raba tsakaninsu,idanunsu suka shiga cikin na jina,kowanne ya zare nashi idon daga

cikin na dan uwanshi yana jin yarrr cikin jikinsa saboda kusancin da sukayi da juna yayi
yawa,saiya sanya hannu ya dauki kofin gabanta yana cewa
"Tunda niba wanda yayimin tayi bari nayiwa kaina"
"A'ah..ban yarda da wannan juyin mallakar ba,aje mata,kaidin baqo ne da bazaka dauka da
kanka ba?" Murmushi ya saki yana tsaida kofin da yayi nufin kaiwa bakinsa
"To ai anty itama ba zata sha ba idan bansha ba" ya qarshe maganar yana waiwayawa ya dubi
shahidan yana kashe mata ido,sadda kanta qasa tayi saboda wani abu dataji ya saukar mata
saman zuciyarta mau nauyi,yakai bakinsa ya kurba lemon ya miqa mata suna magana da anty
usaina,qin amsa tayi har ya gama maganar ya juyo yana dubanta "Karbi mana,kosai na baki da kaina?" Harara ta cilla masa a fakaice ta saka hannu takarba
ganin yana kai kofin bakinta,ya xuba mata ido sanda takai kofin nata bakin,tana sane ta juya
daga wajen daya sha ta sauya gurbi,murmushin mugunta ya saki ya waiwaya wajen anty usaina
yana tambayarta "Me yarinyarnan tazoyi gidan nan?,na ganta sanda muke shigowa"
"Nafisa?....waitaji banji dadiba shine tazo dubani,amma tazomin da wata magana da nace
saikazo naji ta bakinka tukunna" ta fada tana dan dubam shahida,batason yin maganar a
gabanta,amma kuma tana ganin yin maganar a gabantan kamar xai bada wani alfanu game da
kawo gyara kan yanayin mu'amalarsu da anwar,don har yanzu bata gamsu da yanayin zaman
nasu ba,tana ganin yadda suke abu kaman baqin juna
"Tace na baka haquri akan kuskuren datayi a baya,tana son idan da hali ka dawo ka....." Daga
kai anty usaina tayi tana duban shahida wadda ta miqe tsaye
"A'ah,ki zamanki shahida mana?"murmushi tadan saki,don tunda aka ambaci sunan nafisa
zuciyarta ta gaya mata ba kowa bace illa wannan wadda suka gani dai sanda zasu fita,fuskar
da anwar ya aiko mata da ita cikin envalope din data baiwa suna da baqin saqo,hotunan da har
yau ta kasa rabuwa dasu dukda yadda suke qona ruhi da zuciyarta duk sanda ta tuna dasu,ko
kuma duk lokacin data kallo gefan da suke aje
"Zan saukane wajensu sa'ida"
"To shikenan,nima ganinan zuwa,ai bamu gama hirar ba"
"Toh anty" ta fada ta juya tana fice daga dakin,anty usaina ta bita da kallo farinciki na ratsa
zuciyarta,tanason karanto wani abu game da shahidan,saita maida dubanta ga anwar,wannan
karon shiya soma magana
"Don Allah anty karki shiga maganar nan,an riga da an wuce wajen tuni,na godewa Allah da
bani na soma gudunta ba bare aga butulcina,ta ruga data gayamin manufarta tun rannan,kuma
kullum kwanan duniya saita aikomin da saqo kan hakan" ajiyar zuciya anty usaina ta
saki,itakam a duniya yanzu ba abinda ya rage mata illa taga kan shahida da anwar din ya hadu
kawai,ta tabbatar idan hakan ta faru babu kuma sauran wata matsala
"Shikenan Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,nikam yanzu bani da burin daya wuce naga kanku
ya hadu yadda ya kamata kaida shahida,yarinyar tana da nagarta anwar,kayi qoqarin gyara
zamanku,gashi kuna qoqarin cinye wata na biyu amma a karatuna banga hadin kan da nake
buqata ba,ajiyar zuciya ya saki yana dan kashingida kadan,cikin zuciyarsa yana fadin antyn ba
zata gane ba,shi kadai yasan me yakeji kullum kwanan duniya,a raye yake amma zuciyarsa
matatta ce,ya gaza gano dalilin daya sanya shahidan aikata dukkan abinda ta aikata a
rayuwarta,meye sila?,meya janyo haka?.

Shahida na qasa suna hirarsu dasu sa'ida anty usaina ta koro anwar qasan takuma ce ya
turo mata shahidan,sanda taje kusan karatun xama da miji tayi mata sosai ba kunya ko nauyi
tsakaninsu
"Shahida...kiyi haquri da yadda rayuwar aurenku taxo muku ahagunce kuma a kaikace,farinciki
gamida walwalar gida a hannun matar gida take,tana da ikon maida gidanta aljannar duniya ko
kuma akasin haka,duk yadda namiji keda taurin kai,taurin zuciya da kuma kafiya abune mai
sauqi matarsa ta canzashi matuqar tayi karatu mai yawa akanshi da halayyarshi,kiyi haquri kiyi
qoqarin canza gidanki,ki zama mace sosai,kiyi amfani da hikima da basirarki,kaf dinmu
makusantanki dana anwar ba wanda yake fata ko burin rabuwarki dashi,kinga kenan babu ranar
da zaku rabun,tome zayasa abinda babu ranar yankewarsa maimakon ka gyarashi kaji dadinsa
ka amfaneshi saika zabi dawwama cikin karkatacciyar rayuwa maras dadi?,duk lokacin da
rayuwar auratayya ta kacame ta lalace babu wanda yafi cutuwa a ciki,yafi quntata,yafi zama
cikin wahala baqinciki da bacin rai irin MACE,namiji nada tarin hanyoyin da zai debewa kansa
kewa ya ragewa kansa baqinciki da bacin rai,ba kamar ke mace ba da taki damar qwaya
dayace wannan mijin da kike aure,kome anwar ya miki,duk da bansan girman cutarwar da yayi
miki ba abaya,ina mai qasaqantar da kaina da roqa masa alfarmar ki yafe masa,ki tashi tsaye ki
gyara gidanki,ki masa kyautatawar da girmanta zaisa yayi nadama yayi danasani,ya kuma ji
kunyar aikata miki dukkan abinda ya aikata mikin,ita mace tana da wannan power,zuciyar namiji
a wajenta ba komai bace horewa ce ta ubangiji,nasan zaki iya din ina kyautata miki wannan
zaton,ina roqar alfarma zakiyimin shahida?"cikin jin kunya da nauyi gamida gasgata kalaman
anty usaina ta gyada kai
"Xan miki anty,zanyi in sha Allahu" ajiyar zuciya ta saki tana lumshe idanu
"Na gode qwarai,amma kafin sannan,ki nutsu ki mu'amalanceshi ta yanayi da sigar da yake
mu'amalantarki gudun kadda kisha wahala,ina fatan kin fahimceni?" Kai ta gyada mata alamun
ta gane,hakan ya yiwa anty usaina dadi sosai,da kanta ta bude cupboard dinta ta ciro mata
wasu rigunan bacci masu shegen kyau da sulbi guda shida,ta hada mata da turarukan bedroom
suma guda hudu masu kyau da tsada,ta amsa tayi mata godiya sosai,saita danyi jim,anty
usainam ta fuskanci akwai maganar da takesonyi,saboda haka tace da ita ta fada kada taji
nauyi ko kunya
"Anty aron sa'ida zaki bani don Allah tayimin ko sati guda ne" baki anty usaina ta bude
"Keda zaki shiga yaqarmin tunanin dan uwa na hadaki da sa'ida ta hana ruwa gudu?" Kunya ta
sata sadda kai tana dariya
"Shikenan,amma ba zata wuce kwana uku ba"
"Don Allah anty ki barta tayi sati" daqyar ta yadda da hakan,sa'ida murna kaman me ta hada
kayanta ta bisu.


*11:30 pm*


Doguwar rigar bacci ce a jikinta mai sulbi wadda takai har qasa da dogon hannu,sai baby
hijab data sanya wanda iyakarsa saman kafadunta,duk motsin datayi qamshi ne yake tashi

harta iso matatattakalar qarshe wadda daga ita sai qaramar baranda da zata sadaka da falon
samanshi,cak ta tsaya tana ajiyar numfashi,shida kanshi ya mata magana kafin su shigo gidan
kanta taho samanshi saboda sa'ida kada ta karanci yanayin zamansu,baiso anty usaina ta
fahimci komai,baisan yayi sara bane kan gaba,ta riga data gama shirinta dukda ciwo da takeji a
qirjinta da nauyin alqawarin data dauka,anya zata iya saukewa?,takewa kanta wannan
tambayar,duk sanda fuskar nafisa ta gilma mata a idanu,yadda ya cillota da girman kalaman
daya sossoka mata saitaga gaba daya yayi mata baqi a ido,koren shaidan tayi sannan tayi
bismillah taci gaba da takawa ta tura qofar falon ta shiga.*Alqawarin Allah*
42

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU

Yana zaune saman kujera ya miqe qafafunsa gaba daya,sanye yake da gajeran wando iya
gwiwa da vest,hannunta riqe da wayarshi yayin da rabin hankalinsa ya tafi ga kallon labaran da
ake a VOA,bude qofar yaja hankalinsa,ya daga idonsa ya dubi qofar,hada ido sukayi da ita,ta
janye nata idon saboda nauyin ganinsa da take a haka,yayin dashi kuma yaci gaba da kallonta
har zuwa sanda ta iso inda yake,ga mamakinsa sai yaga tayi wucewarta bedroom dinshi
rungume da kaya a hannunta ta tura qofar ta shige,sai a sannan ya janye idanunsa yana
lumshesu gamida budesu duka lokaci guda hadi da zuqar qamshin turaren data wuce tabar
masa,saiya sake miqe bayansa saman kujerar,ya aje wayarshi saboda kasalar data saukar
masa,ya tattara hankalinsa duka kan tvn yaci gaba da bibiyar labaran.

Idanunta ta waro tana sarawa kanta abinda tayi na farko na wuceshin da tayi kaman
dakinta,ta kalli gadon nashi,fes dashi kaman gadon mace,ta tabbatar shike gyara abinsa,ta
bude ma'ajiyar kayan sawarshi ta aje kayan data shigo dasu a hannunta,bata kwanciya saida
ruwa,saboda haka dole ta fita ta samu ruwa,ta zare hijabin jikinta ta gyara dankwalin kanta ta
rufe gashinta sosai sannan ta soma takawa ta fito daga bedroom din.

Baiji fitowarta ba sai gilmawarta ya gani zuwa saqon da fridge dinsa ke ajiye,yaso yiwa
idonsa shamaki amma ya gaz,yana kallonta qasa qasa wanda ahaka saika tsammaci bacci
yake ta ciro ruwan gora daya ta juya ta koma zuwa ciki.

Duka addu'o'inta tayi,ta shafe jikinta da su sannan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login