Showing 75001 words to 78000 words out of 126208 words
Chapter 26 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
ne
koko yaya abun ya faru?abinda ya shiga tsakaninsun dama baiyi girman da zasu kasa daidaita
tsakaninsu ba amma har ya zama silar rabuwarsu na tsahon shekaru?,ya zama silar lalacewar
soyayyar da kowa yake sha'awa,duka cikin lokaci kadan ya karanci tarin tambayoyin dake yawo
a idanunta,qaramin murmushi yayi yana jin wani ciwo cikin ranshi,inama ace yadda kowa ya
kalli lamarin hakan yake
"Karki damu anty,na rage miki aikin da kiketa yunqurin yine" ya qarasa fada yana son ganin
yanayin fuskarta,ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sosai zaman dake nuna ta soma samun
nutsuwa
"Zuciyata ta kasa karbar rabuwarka da ita ne anwar,inaji a jikina bai cancanci ku rabu ba"
"Shikenan ai....yanzu dai anty abinda nakeso kici gaba da zama a yadda ta sanki har zuwa
lokacin da komai zai daidaita" sai yanayin fuskarta ya sauya
"Komai zai daidaita kamar yaya?,kana nufin baku daidaita ba ka nemi aurenta a haka?" Kai ya
gyada mata
"Eh kusan hakanne"
"Me hakan ke nufi anwar?"
"Babu komai,kema hakan kikeso mu kasance tare fa?"
Eh...amma zanso ace hakan ta faru ne a lokacin da duk wani sabani dakw tsakaninku ya zama
babu shi"
"Karki damu anty" shuru tayi tana nazari,yayin da zuciyarta taji ta mata sanyi sosao,ta dinga jin
farinciki na shigarta,tana ji babu shakka abune mawuyaci anwar ya samu soyayya irinta
shahidan,abune mai wahalar gaske yaso wata kwatankwacin nata son koda shi yana qaryata
hakan tasan wani dalili ne nashi na daban daya rufe masa idanu har yake qaryata hakan "Nafisa fa?" Ta sako mishi zancan da take ganin kamar ya manta ne
"Ba abinda ya sauya tsakanina da ita"
"Tasan da wannan maganar?"
"Zata sani anty,zata sani idan lokacin daya dace ta sani yayi"
"Shikenan,Allah ya shige gaba ya kauda dukkan abunqi"mai makon ya amsa saiya soko wani
zancan
"cikin satin nan ne tafiyata,ina ganin ki lissafa duk abinda kuke da buqata don bazan dawo ba
saina gama wata biyun gaba daya,aiki ne mai muhimmanci a gabana"
"Babu wata matsala,don bana tunanin zamu buqaci komai harka dawo din"
Ranar juma'a qarfe biyu na rana suma gama shirin tafiya katsina,ga mamakinta sai uncle
hisham ya hadasu ita da haidar da faruqu,ganin haka huda itama ta turje saita je,hakan yasa ta
hada kayanta duka suka bar gidan sai anty zubaida kawai.
Tafiyar tayi mata dadi sosai saboda su faruq,har Allah Allah ta dinga yi su isa,basu jima sosai
saman hanya ba suka isa katsina.
Sosai daada tayi farincikin ganinsu su duka,ta rasa inda zata sanyasu,kowannensu haba
haba takeyi dashi,saida suka ci suka sha suka nutsu qarfe uku na yammaci,a lokacin su faruqu
sun fita kewaya 'yan uwa dake nesa,shahida tace ta gaji ba zata iya fita ba sai gobe,jin haka
yasanya huda itama cewa bazata bisu,nan tayi kwanciyarta saman cinyar daada suna hira
abinsu.
Duban shahida daadan tayi bayan ta maida nutsuwarta sosai
"Rahama" ta kirayi ainihin sunanta,saita daga kai daga danna wayar da take ta dubi daada
"Yau kuma sunan nawa kike sha'awar kira" maimakon ta maida mata yadda suka saba sai tace
"Maida hankalinki jikinki ki aje wannan wayar" jin hakan yasa ta sauke wayar saman cinyarta
tana kallon daadan
"Abinda yasa nace a turomin ke,inason gaya miki cewa mun bada ke kuma mun karbi kudin
aurenki"
*KIYI SUBSCRIBING,KI TURA WANNAN NUMBER DON SAMUN DAMAR SHIGA GROUP
DIN SABON LITTAFINA DA ZAN SOMA RUBUTAWA BAYAN ALQAWARIN ALLAH IN SHA
ALLAH*
07038670166
SAUTIN HIKIMA
https://youtu.be/H7M7h6l6wNMhttps://youtu.be/_XVqJSBXVPI
*Alqawarin Allah*
2️⃣9️⃣
Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta tura
masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta tayi barci
ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu.
Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma shigowa,yadda
taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi ita dinne,tun a ranar
suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace sam,ya sameta kawai a can ran
alhamis din,murmushi ya saka mai sauti "Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura qiris
in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana yanke kiran,bazai
gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga motar wani ta sabbabawa rayuwarta
bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga jiki da rayuwarta gaba daya.
Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar gidan qanin
abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar
"Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki amma ki
kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun laifi?" Murmushi
shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire mayafinta ta aje gefe,iskar
fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami da shigarta tako ina sakamakon zafin
da ake zabgawa da kuma uwar rana
"Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya
shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki
"Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba da
zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai har zuci ba
shahida tayi tana cire agogon hannunta
"Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu na
takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai takanji sassauci
idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi
"Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba tare da tace
komai ba tana son jin qarin bayani
"Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran saurayina qafa
da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya aurar da jikokinta,wai basai
ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini kawai yace masa ya wadatar Allah ya
sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta
mata dakyau ma data amshi kudin aure,amma gwara hasina da ita sau dubu
"Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida
"Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da nasan
waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya dace dani"
idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu suka jiyo maganar daada
daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin "Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne yaja
bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana ta tabe baki
"Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da shahida
cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga bandaki tayi fitsari
sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin nata.
Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta wayarta ta dauki
tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba tasan ya iso ne,gabanta
taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada data qarawa fura da nono ruwa take
sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta
biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen ta gaya mata abinda ke faruwa
"Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi aka
n bar arha,bari na gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga shiga falon
yaro ya tamfatsa sallama yana rangada fadin wai ana sallama da shahida,daada dake zaune a
rumfarta tayi katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana cikinsu,shuru sukayi ba wadda ta
amsa,sai daadan ta kira yaron ya qaraso bakin rumfar "Waye yake sallama da ita?"
"Wani ne,wai nuradden daga kano"
"Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan tace
"Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da hasina gaba
daya
"Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi hasina
"Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta nuna mata
shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta dora saman nan.
Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya yanata
qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da dan uwanshi
ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa musu kadaran
kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida.
Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a kofi,kusan shi
kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana tambayarshi kano,kasancewar
ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin rasuwar babansu shahida.
Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe suke,tilas ta
rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan sayyid yace
"Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina
nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba"
"Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu
"Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta boye
maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake ciki"
"Ta fadama bata boye ba daada"
"Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai kamata
kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman aure akan
nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum kabarinsa,Allah
ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka garemu,saboda haka ina mai
yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai maka fatan samun dacewa da
wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka
dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu
murus,zufa ta dinga yanko masa tako ina
"Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan sun
ajewa daada kudi
"A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi alkhairi"
qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake zaune gefanta tana
sharbar qwalla
"Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma qofar gidan tuni
su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata don yanzu baida nutsuwar
tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin hadiye kukanta.
Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta soma magana
"Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki baki bashi
dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu warware maganar da
mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da hankalinki ki nutsu waje guda
shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga
juna,idan kinga dama kuma idan yazo din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta
juya tayi ficewarta,sai kawai shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo
mata,kuma shima saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba
tare data shiryawa hakan ba.
***** ****** ****** *****
Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai daga nan ta
koma can,ha
sina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin jikinta amma ta qeqashe qasa,ko kallo bata
ishi daada ba sangar gabanta kawai take,tana daga kwancen tana kallon daada,yadda ta cika
fridge dinta da fura da nono mai kyau,lemuka da kuma ruwa,tasa hasina tayi total na kayan
fulawa aka siyo komai hasina tayi dan dai dai aka adana komai,baki ta tabe ta dauke kai bacin
rai na cinta sanda daada ta fito da sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya bata sanda ya
dawo daga umara ya fesheta da turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin soro.
Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da warwara ta
zauna gefanta
"Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake girma saboda
kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin salon tambaya
"Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya qara
zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai
"Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe ga
azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla kodon tsaftar jikinki
ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta amsa mata
"Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa
"Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya
gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan wallahi
daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina
"So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana kallonta
"Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?"
"Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu"
"Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba kenan"
kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce bai sameta ba,har
ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita saboda wani abu dake takore da
wuyanta "Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin dariya ta fice
tana cewa
"A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba".
Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta
"Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da gaske
take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga bandaki tayi
wankan.
Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka wasu riga da
skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta ta soma da nafila kafin
ta gabatar da farillar sallar la'asar.
sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal
wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba.
*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da
buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
2️⃣9️⃣
Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta tura
masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta tayi barci
ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu.
Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma shigowa,yadda
taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi ita dinne,tun a ranar
suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace sam,ya sameta kawai a can ran
alhamis din,murmushi ya saka mai sauti "Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura qiris
in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana yanke kiran,bazai
gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga motar wani ta sabbabawa rayuwarta
bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga jiki da rayuwarta gaba daya.
Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar gidan qanin
abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar
"Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki amma ki
kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun laifi?" Murmushi
shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire mayafinta ta aje gefe,iskar
fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami da shigarta tako ina sakamakon zafin
da ake zabgawa da kuma uwar rana
"Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya
shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki
"Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba da
zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai har zuci ba
shahida tayi tana cire agogon hannunta
"Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu na
takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai takanji sassauci
idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi
"Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba tare da tace
komai ba tana son jin qarin bayani