Showing 78001 words to 81000 words out of 126208 words

Chapter 27 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf


"Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran saurayina qafa
da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya aurar da jikokinta,wai basai
ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini kawai yace masa ya wadatar Allah ya
sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta
mata dakyau ma data amshi kudin aure,amma gwara hasina da ita sau dubu
"Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida
"Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da nasan
waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya dace dani"
idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu suka jiyo maganar daada
daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin "Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne yaja
bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana ta tabe baki
"Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da shahida
cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga bandaki tayi fitsari
sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin nata.

Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta wayarta ta dauki
tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba tasan ya iso ne,gabanta
taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada data qarawa fura da nono ruwa take
sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta
biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen ta gaya mata abinda ke faruwa
"Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi akan bar arha,bari na
gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga shiga falon yaro ya tamfatsa
sallama yana rangada fadin wai ana sallama da shahida,daada dake zaune a rumfarta tayi
katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana cikinsu,shuru sukayi ba wadda ta amsa,sai daadan ta
kira yaron ya qaraso bakin rumfar
"Waye yake sallama da ita?"
"Wani ne,wai nuradden daga kano"
"Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan tace
"Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da hasina gaba
daya
"Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi hasina
"Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta nuna mata
shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta dora saman nan.

Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya yanata
qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da dan uwanshi
ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa musu kadaran

kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida.

Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a kofi,kusan shi
kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana tambayarshi kano,kasancewar
ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin rasuwar babansu shahida.

Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe suke,tilas ta
rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan sayyid yace
"Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina
nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba"
"Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu
"Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta boye
maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake ciki"
"Ta fadama bata boye ba daada"
"Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai kamata
kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman aure akan
nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum kabarinsa,Allah
ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka garemu,saboda haka ina mai
yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai maka fatan samun dacewa da
wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka
dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu
murus,zufa ta dinga yanko masa tako ina
"Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan sun
ajewa daada kudi
"A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi alkhairi"
qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake zaune gefanta tana
sharbar qwalla
"Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma qofar gidan tuni
su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata don yanzu baida nutsuwar
tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin hadiye kukanta.

Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta soma magana
"Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki baki bashi
dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu warware maganar da
mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da hankalinki ki nutsu waje guda
shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga
juna,idan kinga dama kuma idan yazo din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta
juya tayi ficewarta,sai kawai shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo
mata,kuma shima saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba
tare data shiryawa hakan ba.

***** ****** ****** *****

Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai daga nan ta
koma can,hasina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin jikinta amma ta qeqashe qasa,ko
kallo bata ishi daada ba sangar gabanta kawai take,tana daga kwancen tana kallon
daada,yadda ta cika fridge dinta da fura da nono mai kyau,lemuka da kuma ruwa,tasa hasina
tayi total na kayan fulawa aka siyo komai hasina tayi dan dai dai aka adana komai,baki ta tabe
ta dauke kai bacin rai na cinta sanda daada ta fito da sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya
bata sanda ya dawo daga umara ya fesheta da turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin
soro.

Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da warwara ta
zauna gefanta
"Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake girma saboda
kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin salon tambaya
"Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya qara
zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai
"Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe ga
azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla kodon tsaftar jikinki
ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta amsa mata
"Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa
"Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya
gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan wallahi
daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina
"So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana kallonta
"Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?"
"Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu"
"Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba kenan"
kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce bai sameta ba,har
ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita saboda wani abu dake takore da
wuyanta "Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin dariya ta fice
tana cewa
"A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba".

Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta
"Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da gaske
take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga bandaki tayi
wankan.

Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka wasu riga da
skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta ta soma da nafila kafin
ta gabatar da farillar sallar la'asar.

sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal
wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba.

Shigowar hasina dakin ya sanyata daga kai tana dubanta
"Kamar fa baqonki ya iso,ta kamata ki sauya kaya ko powder ki samu ki shafa" harara ta jefa
mata,tana ganin bata amsa ma bata lokaci ne,saita dauke kanta taci gaba da jan carbinta,dariya
hasina tayi
"Kefa bai kamata kice auren dole za'a miki ba,keda zuciyarki babu kowa ciki bare kice an mishi
over taking?"ta qarashe maganar cikin salon tsokana,kasa amsa mata tayi saboda muryar
sulaiman data karade gidan yana shaidawa daadan isowar baqon,idanunta ta lumshe tana sake
maimaita hasbunallahu ba qaqqautawa,tana kallon hasina ta juya ta fice.
Mintina aqalla goma kyawawa tana kasa kunne ko zata jiyo wani motsi ko wata magana
daga tsakar gida ko rumfar daada amma bataji komai ba,a haka aka share minti goma tana
zaune tana zaman jiran tsammani,jiran da bata da tabbas sai azabar fargaba da faduwar gaba
da suka mata rubdugu,daga labuken da akayi ya sanyata daga kai tana duban na bakin qofar.
daada ce,tana daga tsaye riqe da labulen dakin tace
"Au,zaman me kike da kika bar mutane a daki su kadai?" Duban daada tayi qwalla na cika
idanunta,wani irin fargaba tana shigarta,saita sauke idanunta qwalla nason xubowa ta miqe
tsaye ta aje carbinta kawai tana gyara zaman hijabinta a jikinta sanda daada ta saki labulen tayi
komawarta rumfarta ta zauna.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka tazo ta ratsa falon,hasina da daada suka bita da
kallo,hasina baki bude ta dubi daada saboda ganin yadda shahidan zata fita ba kwalliya babu
komai sai zabgegen hijabi,qwafa dadan ta saka sannan tace
"Rabu da ita ja'iarar kawai shashasha" sarai ta jiyo dadan,haka ta dinga takawa har zuwa dakin
soron,ta saka hannu ta yaye labulen ta shiga.

Babu kowa cikin dakin sai kayan ciye ciyen dake jere a tsare,daga saman daya daga cikin
kujerun kuma hula ce mai azabar kyau da daukar ido da alama ta baqon ce,to ina ya
shiga?,shuru dakin sai uban qamshi daya cika dakin na turaren baqon,wanda qamshin turaren
yaso daukar hankalinta,saita samu hannun daya daga cikin kujerun ta zauna tana qarewa dakin
kallo da idanu kamar yau ta soma ganinsa,ta dinga qoqarin rage faduwar gabar da takeji tana
saisaita kanta da nutsuwarta.

Kamar a mafarki kamar a wasa ta dinga jiyo murya kamar ta anwar tana doso dakin,saita
ware idanunta ta zubesu duka bakin qofar,yayin da zuciyarta ta soma qara gudu daga gudun da
take yi a dazu,a nutse ya yaye labulen yana sauke wayar dake kunnenshi,cikin sakan daya
idanunsu suka sarqafe cikin na juna,a nutse ya janye nashi idanun tamkar ba ita ya gani
ba,yayin da shahidan ta miqe zumbyr kamar wadda aka tsikarawa wani abu idanunta dukka a
waje saman fuskar anwar wanda ya jingina bayanshi da bango daura da qofar fita,tafin qafarsa
guda daya ya tokare bangon da ita ta baya dayar kuma yana tsaye a kanta.

"Ki nutsu shahida ki fuskanci komai yadda ya kamata" shawarar farko da zuciyarta ta soma
bata kenan bayan qwaqwalwarta ta dawo daga aiki bayan daukewar da tunaninta yayi na wucin
gadi.

Shuru ya ratsa dakin na tsahon minti biyu tana jira taga shin anwar dinne da kansa ko wani
ya rako?,wajenta yazo ko batan kai yayi?
"Lafiya malam me kake a gidan mutane?" Idanunta a kansa fuskarta na nuna zallar bacin rai
"Ina cewa kin fito ne don ki gana da wanda ya nemi aurenki?" Ya qarashe maganar da sigar
tambaya fuskarsa a dinke yana dage girarsa qwaya daya idanunshi cikin nata,cikin tsananin
razana da firgici ta fiddo duka idanunta waje.



_kuyi searching tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,daga qasanta zakuga an rubuta
subscribe da jan rubutu,ku danna sau daya zai koma black,sai kiyi screenshoot ku turo zuwa
number wayar da zata zo a qasa,za'a saku group na littafin da zan soma bayan na kammala
rubuta alqawarin Allah in sha Allahu_
07038670166https://youtu.be/H7M7h6l6wNM

*xafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,ga mai buqatar siya zai
tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
3️⃣0️⃣


"Kana nufin kaine mutumin daya kawo sadakina da mudin airena ba tare da sani ko yardata
ba?" Ta furta wani bala'i na cinta,maimakon ya bata amsa da baki saiya daga mata dukka
girarsa biyun yana dubanta kai tsaye ya kafeta da idanunshi,wani tashin hankali taji ya rufto
mata irin wanda bata taba jin irinsa ba tunda maganar aurenta ta bullo,tashin hankali da ba'a
saka masa rana,ko zata yarda da kowa ba zata yarda da anwar ba,ko zata amince da auren
kowa ba zata taba amincewa da auren anwar ba koda su biyu kadai suka rage a
duniyar,murmushin takaici ta saki wanda qasan zuciyarta ji take kaman zata fashe
"Kaima kasan ka dauko abinda bazai taba yiwuwa ba har abada,tamkar wanda ya mutu ya
dawo ne,kai bakaji kunya ba anwar?,kana tunanin akwai abinda yayi saura?,kana tsammani

akwai wani sauran abinda ya rage tsakanina dakai?,to bari kaji na gaya maka,ba zaka taba
samun yardata ba,ba zaka sake samun soyayyata ba,har abada aure tsakanina dakai,har
abada...." Qawataccen murmushi ya saki,da alamun kwanciyar hankali kwance kan
fuskarshi,sai daya sauke qafarsa ya sauya jinginar da daya sannan ya rungume hannunsa daya
dayan kuma yana shafar sajensa idanunshi a kanta,fara'ar fuskarshi ta bace bata
"Hajiya shahida....dukka tunaninki bai baki dai dai ba,baije inda ya kamata yaje ba" sauke
qafarsa yayi ya soma takowa inda take tsaye,sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai
sannan ya tsaya ya soke hannayensa cikin aljihun rigarsa
"Kina tunani ko tsammanin soyayya ce tasa na nemi aurenki?,ko kina tunanin neman yardarki
nake kafin na aureki?"sai ya sake takowa gab da ita kamar zai hadeta da jikinsa,ya nunata da
yatsa
"Zan aureki don na nunawa wancan wawan cewa nidin na girmi qaramin dalili babban dalili ne
ni,sannan nayi isar da zan yanke guntuwar soyayyar da yake taqama da ita,soyayyar da bai
iyata ba,bai gama saninta bama bare ya iya,baisan kanta ba baisan mece ita ba!" Ya qarasa
fada yana dan daga muryarsa gami da nuna qofa da yatsa kai kace nuradden ne ke tsaye a
wajen,saiya sauke hannun nashi yana maidashi aljihunsa kana yaja baya kadan har yanzu bai
dauke idonsa daga kanta ba
"Yana tunanin ya sanki?,yana tunanin yafi kowa saninki koya riga kowa saninki?,ya gayamin
magana yayi tunanin yaci bulus?,inaso yaji ciwo ya kuma ci gaba da jin ciwo a ransa duk sa'a
daya da zata wuce da tunanin wani mai suna anwar ya haramta masa auren wadda yake
iqirarin yanaso,wadda yake iqirarin ba wanda ya isa ya shiga tsakaninsu" yana kaiwa nan ya
juya mata baya,yana jin kamar ana yankar zuciyarsa
"Baki cancanci na qyaleki kici gashin kanki ba,baki cancanci na barki kiyi zabin da kikaga dama
ba,bayan kin cutar da zuciyar da bata cancanci sakamakon da kika bata ba,kin bata rayuwar da
alokacin ya kamata ki tattaleta kodon iyaye da qannenki,kin bada jikinki ga wani har yayi ajiya a
wajen daba muhallin......" Saiya kasa qarasawa saboda wani dunqulallen abu daya tokare masa
maqoshi,ya dinga jin wani turari tun daga zuciyarsa zuwa fuskarsa,bakinsa yaji ya dauki zafi ya
fitar da iska zazzafa,yana jin wani irin ciwo da qunci duk lokacin daya tuna da lokacin da kuma
abinda ya faru,hotunan dake wajensa da ganin da yayi kaya ido da ido sun kasa gogewa daga
qwaqwalwa da zuciyarsa,yana jin wani irin ciwo mara misaltuwa,tabbas da yana da iko daya
dawo da lokacin ya goge duk wani abu daya faru ko xai samawa zuciyarsa salama.

Tuni hawaye ya soma wanke mata fuska tana tuna lokacin da abinda ya faru alokacin daya
bayan daya,sai a sannan ta dinga tuna kaman ta ganshi,kaman a gabanshi aka sauketa,hakan
na nufin ya ganta cikin maye?,ya ganta a lokacin da jini kebin qafafunta?,yaga sanda aka cillo
mata pant dinta da kwalabenta?,amma me yasa ya zama mai qaramin tsinkaye?,mai yasa ya
zama mai gajeran nazari?,me yasa ya yanke mata wannan danyen hukunci farat daya,haka
soyayya take?,haka masoyi yakewa masoyinsa?,sai taji ya sake sireta,daya zama mai dogon
nazari da dukka abubuwan da suka faru yanzu basu faru ba
Ranta ya ninka bacin da yayi,hankalinta taji ya tashi,da qyar ta bude baki cikin muryar kuka tace
"Mugu azzalumi,ba ruwanka da kowa sai kanka,ba ruwanka da damuwar wani sai taka,ka
tanadi mugun nufi akaina kan abinda baka da cikakkiyar hujja a kai...."
"Wacce huja nake nema baya ga wanda na samu....!" Ya juyo a fusace ya fada idanunshi da

suka kada zuwa jaa suna kanta
"Ba hujjar kake nema ba,kanayin komaine don ka wulaqantani dama,ka shirya komai ne donka
tozartani,to Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login