Showing 1 words to 3000 words out of 101191 words

Chapter 1 - JINNUL AASHIQUE BOOK COMPLETE By Yar Fillo .pdf

08 Jul 2025

3164

Compiled By Umar Dalha Funtua.




[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: JINNUL
AASHIQUE

_NA_
_HARIRA ALIYU_ ( *Yar Fillo*)


✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍

❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical
Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will
cause you no pain_❄



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


Dedicated to aisha a ibrahim

*Bissmillahirrah manirrahim*

Fatan alkhairi ga kowa inafatan za ayimin hakuri abisa ga wasu kura kuran da kila zanyi

Gaisuwa da jinjina ga GOLDEN PEN WRITTERS


AGE 1⃣


Gid'ane madai-daici dayike cike taf da jama'a idan kakalli kowa zaka fuskarsa dauke da
farinciki da annashuwa banda wacce akayi taron da gayyar dominta

Datake makwabta tare da kawayenta anayimata lalle

Kallo daya zakamata kagano tashin hankali da tsananin fargaba atare da ita

Batawuce seconni batare data duba agogon wayarta ba faduwar gabanta na dada tsananta

Babbar aminiyarta ce tafahimci halin datake ciki ta matso gab da ita tafara magana ahankali

"Rauda please kikwantar da hankalinki banaso jama a sufahimci halin dakikeciki"

Kai kawai Rauda tagyada ma salma dantasan bazata fahimci tashin hankalin datakecikibane
Hakanma bakaramin dauriya takeyi ba

Tanaji kawayenta nayaba kyan lallen amma takasa tankamusu

Wata yar makarantarsuce tashigo tana sallama
Suka amsa salma nafadin"munyi fushi saiyanzu"

Tazauna kusa da rauda tana yar dariya"nabiya kasuwane salma yanzukuma danashigo layin
dakyar na iya kutsowa
Jama a suncika layin tundaga farkonsa har karshensa"

Rauda tayi saurin tambayar jamila
"kinga umar?

Jamila ta girgiza kai"gaskiya ban lura ba kinsan mutanen dayawa"

Tajinjina kai tare da kara lalubar numbansa amma har lokacin akashe

Takara duba agogo karfe biyu saura hankalinta yakara tashi

Kallon me lallen tayi tace"dan allah kitakaita lallen haka"

"To"
Me lallen tace batafi minti biyar ba kuwa tace tagama

Mikewa tayi ganin mama tashigo suka shiga dakin matar gidan dasuke lallen

Mamar ma hankalinta atashe yike
Rauda da jikinta yagama yin sanyi ta dubi mama tanacewa
"mama wayar umar tundazu nike kira akashe kuma bana tunanin yazo gurin daurin aurannan
gashi yanzu biyu dai dai"

Mama tasauke numfashi
Dan tama kasa cewa komai

Kasa rauda tayi dakanta hawaye na gangarowa
"mama idan aka fasa aurannan awannan karon bansan yaya zanyi da raina ba"

Mama takara sauke numfashi tare dacewa cikin kwantar da hankali

"insha allahu ba abunda zefaru"

Zaunawa kawai tayi amma ita ta riga da ta sadakar

Mama tafice zuciyarta cike da damuwa

Salma tashigo dakin tazauna kusa da ita tana karemata kallo
"haba Rauda meyasa bazaki kwantar da hankalinki bane bakisan wannan damuwar zata iya
haifarmiki da wani ciwon na dabanba"

Wasu hawayenne suka kara gangarowa cikin shesshekar kuka tace

"Salma bansan yazanyi da rayuwata ba tundazu nike kiran wayar umar batashiga,gashi yanzu
biyu harta gota amma banji alamun wani nasa yazoba bare maganar daurin aure ba

Salma inason umar bantaba son wani kamar yadda nike sonsa ba,idan narasasa bansan
yazanyi da rayuwata ba......

Takarasa maganar cikin karyewar zuciya

Salma tasauke ajiyar zuciya hakika itama tagama karaya amma bataso ta nunama Raudan
bataso hankalin raudan yakara tashi

Cikin karfafa gwiwa tajanyota jikinta tanadan bubbuga bayanta

"kawata kukannan ya isa haka dan allah insha allah ba abunda zefaru"

Kuka kawai takeyi me cin zuciya

Khadija ce tashigo dakin aguje fuskarta dauke da tsananin farinciki
Salma tace
"lafiya"

Cikin sauri khadija tace
"gasu umar can sunzo da tawagarsu"

Dasauri Rauda tamike
"dagaske khadija?

Khadija tadaga kai
"dagaske wallahi"

yaye labulen dakin tayi dasauri wanda ke fuskantar cikin layin tafara hange hangen inda zata
hangosa

Daga can nesa tahangosa cikin abokanansa yasha wata purple din shadda abunka ga fari tas

Sai shaddar ta hausa kyawunsa yakara futowa

Kuramasa ido Rauda tayi da jikakkun idanunta

Tanajin wani sanyi da farinciki naratsa zuciyarta

Salma tadafa kafadunta tana dan murmushi
"kinga ni ba,bagashi yazo ba amma da duk kinbi kintada hankalinki nima kin tada nawa"

Kallon salma tayi tana yar dariya "karkiga laifina kawata kinsan yadda nike sonsa kuwa?

Dariya salma tayi itama sai lokacin hankalinnata yakwanta
"jibeki hawaye na zubowa kina kuma dariya, kuka da dariya alokaci daya"

Hannu tasa ta goge fuskarta dasauri tarasa

Ma mezatace saboda tsananin farinciki

"salma bazaki gane bane aure biyu anafasawa dole hankalina yatashi bare umar danike sonsa
kamar raina"

Murmushi salma tayi tana girgiza kai

"allah dai yasa yadda kike son umar shima yana sonki haka"

Rauda ta jingina tana lumshe idanuwanta
"aganina salma ayanzu dai babu wanda yakai umar sona
Saboda kullum maganarsa batawuce idan babu ni baze iya rayuwa"

Dariya salma takuma yi
"lallaikam kunason junanku dayawa,amma dai kada wannan son yasa kibada kanki da ankaiki
ehe

Kija aji kidan bashi wuya tukunna

Bude idanu rauda tayi tanayima salma wani irin kallo

"lallai salma bakida saiti,tunda nike aduniya bantaba yima umar musu ba

Ko bani da lafiya nakasa cin abinci idan yacemin inci sainaci kobadadi

Haka bacci ma kobanaji idan yace inyi dole nikeyi alokacin

Anguwa ma haka idan yace kar inje to ko inason zuwa fasawa nikeyi

Kekomai idan Umar yace inyi atake nikeyi bana bata lokaci

Bare kuma abunda ya dade yana muradi sai kawai in hanasa saboda wani ajin banza......


"Ya isa ya isa mamar soyayya"
Salma tafada tana mikewa
Sannan tacigaba dacewa

Yanzu nasan ko rijiya Umar yace kifada fadawa zakiyi wannan soyayyar taki tayi yawa wallahi

Dariya Rauda tayi
"najidai koma mezakice dan haka kigayawa wa'ancan
(sauran kawayen)
Dannaji suna zancen kwana babu wacce zata kwananmin agida"

Baki Rauda tarike
"eyyeh lallaima Rauda yazune bakinki yabude ko?

Amma dazu ko ihin kasa furtawa kikayi
To kwana ko zamuyi yazama dole"

Waro idanu Rauda tayi tanajin kamar mafarki takeyi
Yayinda taji ana sanarwa

"andaura auran umar da Rauda bisa ga sadaki naira dubu dari

Cinta,shanta,suturarta duk sunkoma kan umar

Jama a sunshaida
Fatiha

Runkunkume salma tayi tanfadin
"kinji abunda kunnuwa na sukaji salma"

Salma tadaga kai
"naji andaura auran Rauda da umar"

Durkushewa Rauda tayi,tayi sujada ga ubangiji
Tana fadin allah nagodemaka allah nagodemaka

Wayarta tafara kara tadago ahankali tana duban wayar

Salma tamikamata wayar tanufi hanyar fita tana cewa

"kinga bari naje muciga da shirye shirye tunda dai allah ya yadda"

Kallon wayar tayi ganin numban umar yasa tadauka

Cikin tattausar muryarsa mesata natsuwa aduk sanda tajita yace

"madam yadai"

Fashewa tayi da kuka wanda batasan ko namenene bane

"haba madam kukan kuma namene?
Yatambaya yana sassauta muryarsa

Cikin kukan tace
"yau tunda natashi nike kiranka amma wayarka akashe kasa hankalina yatashi...

Yakatseta"haba honey,kema kinsan hakanan dai bazan kashe wayata ba

Kinsan hidimar bikinnan jiya agajiye nakoma gida dasafe kuma mutanene suka addabeni da
kira

Shiyasa nakashe"

Numfashi tasauke

"kasani cikin fargaba da tsoro bazan iya kwatantamaka tashin hankalin dashiga ba"

Murmushi yayi wanda tajiyo sautinsa
"kiyi hakuri bama jina kadai ba yanzu gabadayana nazama naki
Mallakinki ke kadai

Murmushi ya subucemata zuciyarta har harbawa takeyi saboda tsananin farinciki

"jaana"
(sunan datake kiransa kenan)

Takira sunan ahankali sannan tacigaba dacewa
"ina sonka bazan iya kwatanta kaunar danike maka ba.....

Ya katseta
"chuchu inasonki fiye da yadda kikesona,

Inasonki fiyeda yadda nikeson kaina

Zan iya yin komai akanki zan iya yin komai dan inga nakasance
Tare dake har abada
Kece farinciki

Lumshe idanuwanta tayi wasu hawayen farinciki masu dumi suka gangaromata

Anty larai ce tashigo dakin tana salallami

"wai dama amaryan tananan ko wanka batayi ba bare tashirya?
Ga jama a saikara cika sukeyi?

Murmushi Rauda tayi,tayi kasa da muryarta tare da kara matse wayar akunnenta

"jaana bari naje nayi wanka "

Yace to afito lafiya




Yarfillo
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: JINNUL
AASHQUE


NA
HARIRA ALIYU( *Yar Fillo*)

✍✍✍✍✍✍✍

*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍

❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical
Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will
cause you no pain_❄



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


Dedicated to aisha a ibrahim



AGE 2⃣


Cikin kankanin lokaci aka tsantsara mata kwalliya

Take kyawunta yakara fitowa
Farinciki agunta kuwa baya misaltuwa bakinta yakasa rufuwa

Haka mahaifiyarta ma itama farinciki gareta baya misaltuwa

Karfe hudu suka kammala shirin zuwa reception

Motocine manya masu tsadan gaske sukazo daukansu zuwa gurin reception din

ansha shagali sosai saikarfe bakwai akatashi Harsu salma sunshigo motar datake

Abokin umar yazo yace sukoma dayar motar

Wannan motar amarya da angone zasushiga

Basuyi musu ba suka koma dayar motar

Saida motocin suka gama tafiya sannan umar yashiga motar

Tanazaune tayi shuru tana tunani batasan yashiga motarba harsaida yashafamata wuya

Tadanyi firgigit tana kallonsa

Murmushi yayi yanafadin
"matsoraciya tunanin mekikeyi?

Girgiza kai tayi
"babu komai"

Ya gyada kai
"ook fadamin wani hotel kikeso muje mukwana"

Danzaro ido tayi tana kallonsa
"hotel kuma?

Yadaga gira
"yes hotel ko da aurena zan kwana nikadaine?

Ta rausayar da kai
"dan allah kabar wasa mutafi gida"

Ya gyara zamansa yana fuskantarta
"allah dagaske nikeyi da aurena bazan kwana nikadai ba idan bazaki zabi
Hotel din dakikeso ba nizanzaba"

Ganin dagaske yikeyi yasa ta marairaice fuska

"haba jaana kaima kasan abunda bazeyuwu bane.....

"mene bazeyuwuba?

Yakatseta ya na hade fuska

Tasauke numfashi
"tayaya bamu tare ba zamutafi hotel?

"keba matata bace?
Yawurgo mata tambayar

"matarka ce mana amma......

Yadaga mata hannu
"kinga dakata!
Banason wasu surutai marasa tushe ke matata ce ina da ikon dazanyi duk yadda naga dama
dake

Zata kuma magana yakuma katseta
"nace taredake zan kwana idan kuma tunyanzu zakifara min gardamane sai inji"


Shuru tayi tana kallonsa tarasa tayadda zatamai magana yafahimta

Ganin zetada motar yasa tarike mai hannu tana langabar dakai

"jaana please kayi hakuri kasani bazantaba iya yima musu ba amma hakan badai dai bane

Duk da nasan ba haramun bane dan na kwana tare da kai
Amma surutun mutane nike gudu

Kaga za a daukeni marar kunya

Kayi hakuri gobe iyanzu inadakinka duk abinda kaga dama saikayi amma kayimin hakurin yau
please"

Bekara cemata komai ba yatada motar ya nufi hanyar gida da ita

Kallonsa kawai takeyi tasan ransa yabaci itama saitaji zuciyarta babu dadi

kwata-kwata batason ganin bacin ransa

"jaana.....

Zatai magana yayi saurin dakatar da ita tahanyar daga mata hannu batare da ya ko dubeta ba

"inace gida kikace inkaiki?

Tadaga kai

Yacigaba da cewa"to yanzu hanyar gidan nikeyi ai dan haka banason surutu please"

Jikinta yayi sanyi takuma kai hannunta tarike nasa

"muje hotel din inhar zuwan zesaka farinciki"

Fakawa yayi agefen titi yazuba mata manyan idanuwansa masu juya mata lissafi

"bazantaba yimiki abunda bakyaso ba chuchu,danhaka kibari kawai ba fushi nayi ba kawai dai
banji dadi bane"

"amma....

Shhhhhhh yadora yatsunsa biyu akan dan karamin bakinta

"nacemiki banyi fushi bakarki damu,dayau da goben ai duk na allah ne

Kuma goben kaman yaune"

Yakarasa maganar yana sakin fuskarsa

Sai lokacin taji hankalinta yakwanta bata kaunar bacin ransa kwata

"nagode mijina dakafahimceni"

Yasakarmata murmushi tare da shafa gefen fuskarta

"bar wani jindadi gobe zaki gane kurenki ne yarinya"

dariya tayi tana kauda kanta


Washegari karfe goma nasafe sukabar kaduna zuwa garin abuja

Iyayenta sunyimata fada da nasiha sosai

Taci kuka kamar ranta zefita dan tanada kawa zuci sosai ko tafiyar kwana biyu tayi allah allah
takeyi takoma inko tayi sati to dama wajibine saitayi rashin lafiya

To bare wannan da tafiyar dun-dun-dunce saidai takaima gidansu ziyara

Saiwajen karfe shabiyu suka isa birnin tarayya

Cikin wata hadaddiyar unguwa suka shiga wani kayatacce fankacecen gida me kama da gidan
sanator

ko nawani gomna gidan yatsaru sosai gaba d'aya wadanda suka rakota sakin baki sukayi suna
kallon gidan

Wasu daga cikinsu suna fadin
"gaskiya Rauda ta dace"

Yan uwan Umar ne suka futo da ga ciki yayarsa me suna kaltum itace tazo tarungumota

Tana rangada buda

Nandanan sauran suka fara yan wake-wakensu na buzaye

Ahaka suka shiga kayataccen falon dayasha kayan alatu

Atsakiyar falon anty kaltum tazaunar da ita inda sauran suka zagayeta

Anty kaltum tayaye lullubin da ke kan rauda fuskarsa ta bayanna

"masha allah"
Sauran yan uwansa suka fara fada suna yaba kyanta

Kasa tayi dakanta dangani takeyi kaman zaginta sukeyi yadda sukeda tsananin kyau har zasu
dubeta su kirata kyakkyawa

Ba abata lokaci ba aka cika gabansu da abinci kala kala

Saiwajen karfe biyar yan kaduna suka fara shirin komawa

Fada suka kara yimata sosai sannan suka juyo

Suma yan uwan umar din fashewa sukayi yan kaduna suka juyo yan niger suka nufi
masaukinsu

Anty kaltum ce kawai tarage itama kuma tanajiran zuwan angwaye ne takama gabanta

Wanka tasa Rauda takumayi taciromata wani leshi rantsatsse tasa

Sannan tazauna tatsaramata kwalliya kasancewar ta kware afannin kwalliya

Saida akayi sallar issha sannan umar yashigo tare da babban abokinsa zayyad

Nan itama takarayimusu tata nasihar sannan tamusu sallama shima zayyad yayimusu nasa

Sannan yayimusu saida safe

Umar yarakasa yarufe kofofin

Tanazaune saman gado inda yabarta yashigo yana zuba kamshi

Yazauna kusa da ita yasa hannu ya tallabo fuskarta

Suka hada ido
Jitayi gabanta yafadi wanda batasan dalilin faduwar tasa ba

Yasakar mata murmushi
"yadai amarya kinwani yi shuru ko duk jimamin rabuwa da mamane?

Takakaro murmushi
"kaman kasani jinikeyi kaman intashi inkoma"

Yayi yar dariya har fararen hakoransa suka bayyana

"lallai yarinya bakiji dakyau ba keda zuwa kaduna saikin shekara kila ma da jariri zakijemusu"

Dariyar itama tayi
"ai inayin sati biyu zanje"

Ya jinjina kai
"lallai kam"

Tashi kidaukomana plate muci abinci dannasan yau bakici komai


Tamike tabude kofar dakin tafara saukowa daga step tana karema falon kallo
Azuciyarta tana yaba kyansa dakuma kokarin mijinnata

Ta murda kofar kicin din
Komai ashirye yike tsaf-tsaf

Tayi guntun murmushin jindadi

Lallai umar yanasonta dayawa dan ko tsinke kinyarda ayimata yayi shi yayi komai

Tazaro plate daya acikin kitchenwire
Tajuyo zata fita

"kwaram"
Taji karar wani plate din yafado

Tajuya tana cewa garin saurina banciro ahankali ba

Tagyara su tsaf sannan takuma juya

Hartakai bakin kofa takuma jin karar faduwar plates din

Dasauri tajuyo plates biyu tagani akasa

Gabanta yafadi take taji tsoro yafara kamata

Bata koma dauke plates dinba gaba kawai tayi tarufo kofar kicin din

Tafara tafiya dasauri tahau step.

Tahau daya biyu uku tatsaya cak.

Wani fargaba da tsoro yakuma kamata

Jitayi kaman ana bin sawunta

Tayi karfin halin juyawa amma bata ga kowa ba

Dasauri tacigaba da hawa harda tuntube gurin shiga dakin

Kallonta yayi yana fadin
"lafiya madam?

Zama tayi tana dan sauke numfashi

"jinayi kaman wani yanabina"

Dariya yayi
"oh my dear tsoronki yayi yawa wallahi waye zebiyoki?bayan kinsan gidannan dagani saike?

Hmmmmmmmm
Tasauke ajiyar zuciya
"nidai yanzu bazankara fita nikadai ba saidai muje tare"

Yagirgiza kai yana murmushi
"to madam ai duk yadda kikace haka za ayi"


Ya amshi plates din yajuye gasassun kaji biyu aciki

Sannan yafara bata abaki
Saida yaga takoshi dam sannan ya kyaleta

Yakwashe kayan yamaidasu gefe sannan yadauro alwala itama yace tadauro

Sallah raka a biyu sukayi yayimata tambayoyi game da addininta ta amsa mai

Sannan yadafa kanta ya dinga kwarara addu o i

Sunmike kenan yana ninke darduma wayarsa tafara kara

Ganin numban asibi ne yasa ya dauka

Magana uku yayi yace "ook kubashi taimakon gaggawa ganinan zuwa"

Ya ajiye wayar yana dubanta

"baby kirane daga asibiti wai ankawo wani emergency"

Kallonsa tayi sosai
"toyanzu mekake nufi?

"zuwa zanyimana chuchu ceton raine fa?

Waro idanuwanta tayi tana kallon agogo sannan tamaida idanuwanta kansa

"yanzufa karfe shabiyu"
Yadaga kai
"nasani ai amma ai komin dare dole infita tunda aikinane
"

Nan danan idanuwanta suka cicciko da kwalla

Matsowa yayi gab da ita yajanyota jikinsa

"please honey kiyi hakuri naje ance mutumin yana cikin wani hali please....
Dago kanta tayi daga jikinsa

Tazuba masa fararen idanuwanta

"amma kasan bazan iya kwana nikadai acikin gidan nan ba ko?saidai inmutafi tare"

Ya waro ido
"dawa?baze yuwu ba ba bu inda zakije acikin darannan

Nima dan yazamarmin dole ne

Danhaka kikwanta kiyi baccinki inagamawa zandawo

Zata kuma magana ya katseta

"chuchu bata lokacinnan danikeyi bawan allahn can ze iya rasa ransa da haka natafi

Yakarasa fada yana ficewa da sauri

Bin bayansa tayi da kallo cike da tsananin damuwa dan ita ko agida batasaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login