Showing 54001 words to 57000 words out of 101191 words
min hankali yike yi"
Rauda tayi ƙoƙorin tsai da kukan ta amma ta kasa dan da ta tuno sa sai taji wani dunƙulen abu
ya to kare mata ƙirji
Kukanne kaɗai yike sa ta samu sassauci
"Salma kiyi haƙuri, baki san abunda nike ji bane, nayi alƙawarin zan faɗa miki amma ba a yanzu
ba, dan yanzu ina buƙatar natsuwa ne"
Salma ta sauke ajiyar zuciya tace
"shikenan ubangiji ya yaye miki, amma ki rage sa kanki cikin wannan muguwar damuwar"
Kaɗa Mata kai kawai tayi alamar taji, amma Saman zuciyar ta ji take yi kamar an ɗaura mata
wani abu me nawi
Tambayar kanta kawai take yi wacce ta rasa bawa kanta amsa
"me yasa dan nagansa hankalina ze tashi haka? Shin ko har yanzu ƙaunar sa bata fita acikin
zuciya ta bane?
Girgiza kai tayi da sauri tana sa hannu ta bubbuga kanta
Dan gani take yi kamar ƙwa-ƙwalwarta na so ta bijiro mata da abunda ya wuce
"Rauda ki natsu, kin riga da kin cire sa aranki,tsayin lokaci,ki cigaba da man tawa da shi kamar
yadda ya umarce ki a baya
Kada ki manta da alƙawarin da kika ɗaukar ma kanki na ko zaki mutu baza ki ƙara ne mansa
ba"
Ta faɗa a fili, sannan ta share fuskar ta Tana ƙoƙarin sai-sai ta natsuwar ta
Tausayin ta Salma taji sosai, dan sai lokacin ta gane abunda take nufi
*Kogon iraq*
(bari mu wai-wayi Aasim)
Zaune yike cikin ƙan-ƙara tsananin sanyi na shiga jikinsa
Wani hayaƙin sanyi ne ke fita a duk yayin da ya buɗe bakin sa
Sunfi su arba'in a wurin
Kallo ɗaya zaka ma sauran rauhanan ka gano tsantsar gajiya da damuwa a tare da su
Domin suna matuƙar shan wuya a training ɗin
Banda Aasim da shi sam babu wannan alamar gajiyar a tare da shi
Abul simnan shine shugaban wurin
Tsohone tukuf fari sol me dogon gemu, dan gemun sa har jan ƙasa yike yi
Yana zaune kan kujerar sa ya na karantar yana yin rauhanan
Turawa yayi aka kira masa Aasim
Aasim ya durƙusa yana gaishe sa
Amsawa Abul simnan yayi yana ƙara karantar yana yin sa
"yaro wani abu ne ya tsaya min a rai ya sa na kira ka, gani nayi gaba ɗaya rauhanan da suke
training sun nuna gajiya warsu da ƙosawar su
Amma kai Kwata-kwata banga Hakan a tare da kai ba, dan wani zubin ma hango ka nike yi
kana murmushi"
Murmushi Aasim yayi yana cewa
"tabbas abunda kafaɗa gaskiya ne, Sam ajikina bana jin gajiya wa,ƙosawa ta ɗaya ce ingama
inje inyi abunda nazo domin sa"
Jinjina kai Abul simnan yayi
"tabbas ba ƙaramar ƙauna kake yi wa bil'adamar can ba, tunda har ka iya rabuwa da ahalinka
da matsayin ka na ɗan babban sarki, ka kuma zo kana shan wahala dan kawai ka cigaba da
rayuwa da ita
Amma kana ganin ba kayi kuskure ba kuwa? Da ka bata yarda ɗari bisa ɗari?
Murmushi Aasim ya kuma yi yana girgiza kai
"ko kaɗan banjin nayi kuskure, domin yadda nike son ta, haka ita ma take sona"
Abu simnan yayi ɗan murmushi
"to shikenan Allah yasa Hakan, amma nasan halin mutane lokaci ɗaya zasu nuna son abu
lokaci ɗaya kuma zasu nuna ba sa so, ina yi maka fatan nasara a rayuwar ka"
Miƙewa yayi ya koma cikin ƙan-ƙarar yana jujjuya maganar abu simnan
Maganar tace ta faɗo masa
_"Aasim ina son ka dan Allah mu cigaba da rayuwa a haka"_
Murmushi yayi yana faɗin
"nasan ba zaki taɓa juya min baya ba Rauda, ina tsananin rashin ki Allah yasa kina kula min da
kanki"
Ya faɗa cikin tsananin begen ta
*** *** ***
Da sassafe Umar ya tashi ya shirya cikin manyan kaya, wani ya din malesia ne me silɓi kalar
navy blue
Yayi kyau sosai ya taje sumar sa tare da fesa turare
Ya ɗauko hula ya saka yana maƙala tsadaddan agogo a hannunsa
_"Jaana idan kasa manyan kaya kana yin kyau, ganin ka nike yi kamar ango"_
Maganar ta tabaya ta dawo masa
Murmushi yayi yana kallon kansa a madubi
Inda ya bayyana na ainihinsa na halfcas
"na sane dan na burge ki Rauda Allah yasa ki saurare ni yau"
Ya faɗa yana komawa bakin gadon yana tashin Zayyad dake ta sharar baccin sa
Zayyad buɗe ido yayi yana miƙa
"wai miye ne ka takuramin ka hanani inyi bacci ne?
Umar yace
" ka ta shi mana mu tafi makarantar su Rauda"
Kallon agogo Zayyad yayi ƙarfe bakwai saura
"me zamuje muyi da sassafe haka? Kabari gari ya waye sosai mana"
Umar ya ce
"ai dama ba yanzu zamu tafi ba, kata shi dai ka shirya dan nasan wannan daɗewar da kake yi a
wanka kamar me canza fata"
Zayyad Miƙewa yayi yana faɗin
"Allah ka cika ta kura umar, sai kaje ka haɗo mana abin kari ai kafin in fito"
Umar zama yayi yana duba agogon hannun sa
_Umar dan Kaga ina son ka shiya sa kake wulaƙan Tani ko? Ka sani cewa bani na ɗaura wa
kaina ba, Allah ne ya ɗaura min"_
Maganar ta tabaya ta kuma yi masa yawo a kunne
Dafa kansa yayi cikin damuwa yana jin haushin kansa
"Meyasa nayi mata haka ne? Me yasa?
Ya faɗa cikin jin ta kai cin abunda yayi mata
Dogon tsaki yaja
Cike da Nadama
Ƙarfe goma da rabi ta fito daga lecture
Dai dai lokacin Umar suka yi parking
Suka fito suka tsaya jikin motar
Tun daga nesa suka hango juna wanda sai da ƙirjinsu ya amsa su duka biyun
Kamar ta juya ta koma sai kuma wata zuciyar tace ta cigaba da tafiya kawai
Tunda ga nesa yike kallon ta,tafiya take yi a natse kamar tana jin tsoron taka ƙasa
Komai nata daban ne, wani numfashi ya sauke tare da ajiyar zuciya
Domin be taɓa sanin haka Allah yayi mata kyau ba
Zayyad ko burgesa tayi ganin yadda ta ɗauke kanta kamar Bata gansu ba
Ta kuma haɗe fuskarta, har ta iso inda suke tana niyyar wucewa
Zayyad ne ya tare ta yana yi mata sallama
Ta amsa, tana neman ya bata hanya
"Rauda dan Allah ki tsaya ki saurare mu, mun san munyi kuskure amma kiyi wa girman Allah da
soyayyar da kike yi wa annabi Muhammadu(s.a.w)"
"sallallahu alaihi was salam"
Ta faɗa tare da tsayawa
"to bawan Allah ina jin ka na tsaya ne ba dan niyya ba sai dan kira fiyayyen halitta da kayi"
Zayyad ya jinjina kai yace
"nagode sosai, amma me ze hana muɗan sami wuri mu zauna, saboda mu tattauna abunda ya
kawo mu a tsana ke?
Girgiza kai tayi tace
" a'a nan ma ya isa,ina jinka"
Zayyad yace
"ok to shikenan,dama akan maganar Umar ne, ya ce min kin ƙi kula sa kina ce mai baki san shi
ba, Rauda nasan Umar me laifi ne a wurin ki amma dan Allah kiyi haƙuri....
Dafa kanta tayi cikin damuwa tana kallon Umar da ya zuba mata ido
" oh Allah na,bawan Allah wai ba kaji abunda nafaɗa ma jiya bane? Nace ma ban san ka ba"
Ta mai da kallon ta ga Zayyad tana cewa
"bawan Allah idan baya jin hausa sosai ne kafaɗa masa yadda ze Fahimta bansan sa ba"
Zayyad yayi murmushi
"Rauda nasan zafin zuciya ne yasa kike faɗan haka, yanzu Nima zaki ce baki sanni ba?
Ta ɗaga kai
" eh kaima ban san ka ba, ina ga dai me kama da ni kuka sani amma bani bace gaskiya"
Ta juya gurin Umar tana ci gaba da cewa
"amma ita wacce kuka sanin miye cikakken sunan ta?
Gaba ɗaya kan shi ya ɗaure ganin irin kallon da take masa
" Rauda isma'il"
Ya faɗa cikin rashin sanin abun yi
"gashi sunan mu yazo ɗaya, amma shin ka taɓa haɗuwa da ita ne a baya?
Ya girgiza kai alamar a'a
Ta gyara tsayuwarta tana cigaba da kallon sa
" to a ina ka Santa kenan? Tunda baka taɓa haɗuwa da ita ba?
Cikin damuwa yace
"Rauda sau nawa zan baki haƙuri ne? Idan ma haƙurin da na baki beyi miki bari indurƙusa in
baki amma kidena nuna min bake bace please"
Ya Ƙarasa faɗa yana niyyar durƙusawar
Dakatar dashi tayi da sauri
"ni bance ka dur ƙusa min ba, kadai bani amsar abunda na tambaye ka"
Gauron numfashi ya sauke yana kaɗa kai
"shikenan a waya na Santa"
"Ashe?
Ta tambaya tana buɗe idanuwan ta sosai
" kenan hotuna ta tura maka, ta kuma faɗa maka sunan ta Rauda isma'il
Shin baka tunanin tayi amfani da hotunan da ba nata ba, ta kuma yi maka ƙaryar suna?
Cikin tsananin damuwa da ƙosawa da yadda take masa yace
" idan tayi min ƙaryar suna da kuma hotuna ai bazata aro fuskar ki tasa ba, kinga Rauda kidena
wani kwana-kwana ke ce domin har video call mun sha yi dake"
Taɓe baki tayi tace
"to ni dai ban san ka ba, nafaɗa kuma zan sake faɗa, dan Allah kada ka sake biyo ni inda nike,
kaje ka nemi wacce ka sani amma bani Raudan ba Dan ni ko me kama da kai ban sani ba bare
kuma kai"
Haƙiƙa maganganun ta sunyi masa ciwo amma sai ya danne
Zayyad yace
"Rauda ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana bare tsakanin mu ƴan adam........
Bata jira jin me ze gama cewa ba tayi gaba
Umar ze bita zayyad ya dakatar dashi
"Umar shiga mota mu tafi ko kabita bazata saurare ka ba, kuma Kaga hankalin mutane ya fara
dawowa kanmu"
Be ce komai ba ya buɗe motar ya shiga, zayyad ya mara masa baya yana tada motar
Lumshe idanuwan sa yayi kawai yana jin kansa na sa rawa
"zayyad kafaɗamin yadda zanyi in shawo kanta, wallahi ina jin zuciya ta tana min nawi, ina
sonta zayyad"
Zayyad ya ɗan kallesa sannan ya maida kallon sa ga titi
Tabbas a yanzu ya yadda Umar da gaske yi ke yi yana sonta, ganin duk irin zafin sa amma
yana niyyar durƙusa mata
Amma Sam shi bega laifin ta ba, dan Umar ya cancan ci hukuncin da ya wuce haka ma a wurin
ta
Guntun numfashi ya sauke yace
"kai ma Umar ka san ba ka kyauta mata ba,abunda da yawa maza ba su gane ba shine
A memakon su nuna kulawar su ga matan da suka nuna suna sonsu
Sai su yi amfani da wannan damar su dinga wulaƙanta mace, bayan sun mance cewa ita mace
kunya gareta
Amma ta danne wannan kunyar ta nuna tana sonsu,
Wace magana ce ban gaya maka ba a wancan lokacin Umar?
Har roƙonka nayi akan ka sassauta jan ajin da kake mata
A gabana sai ta yi maka kira fin ashirin
Amma ka ɗauka ne kake ganin asara, kuma idan ka ɗaukan ma a daƙile kake yi mata magana
Idan taji baka da lafiya nikaina sai tamin kira fin goma tana tambayar ya jikin ka
Amma kai sau nawa tana faɗa ma tana gadon asibiti amma ka iya kira ko sau ɗaya ne kace
mata ya jiki ba kayi
Umar maganar gaskiya ka wulaƙanta tata, dole ma tayi ma haka wallahi"
Umar ya runtse idon sa zuciyar sa cike da takaicin kansa
"zayyad dan Allah ka dena tuna min abunda ya wuce nasan ni me kuskure ne ka faɗa min
yadda zanyi kawai"
Zayyad ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"ka cigaba da zuwa kana bata haƙuri insha Allah zata sauko"
Rauda na shiga ɗaki tafaɗa kan katifa tana maida numfashi dan zahiri ba ƙaramar dauriya tayi
ba
Gaba ɗaya hankalin ta ya tashi,haƙiƙa ƙaunar sa ne ma take yi ta dawo mata
Ta rasa irin sa,ba ƙaramar wahala tasha ba wajen ya kice sa a zuciyar ta
Amma gashi yazo yana so ya burki ta mata lissafi
Tabbas ta san yadda taso Umar, babu wani mahaluki a duniya da za taso kamar yadda ta sosa
Tasha yin kuka,kasa barci akan ƙaunar sa kai har rashin lafiya
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta yayin da ta tuno wahalar da tasha a kan ƙaunar sa
"me yasa Umar? Me yasa kamin haka? Me yasa baka zo a sanda nike buƙatar ka ba sai bayan
na cire ka a zuciyata?
Ta faɗa a fili tana share hawayen dake biyo kwarmin idanun ta
Dafa ƙirjinta tayi tana jingina da filo
"dan Allah zuciya ta kada ki dawo min da ƙaunar shi,ki ci gaba da manta wa da shi"
Ta faɗa cikin karyewar zuciya
Bayan sati ɗaya
Umar ya fita hayyacin sa sosai dan babu ranar da baze je makarantar su Rauda ba
Amma still nuna take yi bata Sansa ba, wani zubin ma ko saurarar sa bata tsaya wa yi
Ya Rame sosai, dan ko abincin kirki baya iya ci
Zayyad tun baya jin tausayin sa har ya fara bashi tausayi
Kamar kullum yana tsaye inda ya saba tsayawa
Ta fito zata je ɗaukar darasi
Daga nesa ta hango sa ya jingina da jikin mota
Gaban ta ne ya faɗi yayin da taga yadda ya Rame acikin ƴan kwana ki
Dauriya tayi ta cigaba da tafiya har tazo wuce wa ta inda yike
"Rauda!
Ya kira sunan ta cikin wani irin yana yi
Yadda ya kira sunan tan yasa taji jikin ta yayi sanyi
Ji tayi bazata iya wuce sa ba
Ta tsaya kawai batare da ta juya inda yike ba
Zagayo wa yayi Gabanta ya zuba mata kyawawan idanuwan sa
" Rauda ya kamata ki tausaya min, ki sassauta min haka, wallahi ko barci bana iya yi,Rauda ina
ƙaunar ki a yanzu fiye da yadda kike tunani........
Ɗaga masa hannu tayi idanuwan ta na ciccikowa da hawaye
"na roƙeka ka fita da ga rayuwa ta kadena zuwa inda nike, dan Allah"
Umar ya kaɗa idanuwan sa da suka yi ja
Tare da cize lips ɗinsa
"ina sonki Rauda bazan iya rayuwa babu ke ba, dan girman Allah ki yafemin abunda nayi miki"
Ya Ƙarasa faɗa ya na durƙusawa bisa gwiwowin sa Be damu da jama'ar dake kallon sa ba
Ji tayi kuka na so ya ci ƙarfin ta,da sauri tabar wurin tana dafa ƙirjinta da yike yi mata suya
Can ƙarshen aji ta zauna ta kifa kanta tana kuka
Salma ta dafa ta dan a idon ta komai ya faru
"Rauda dan Allah ki sassauta masa haka, wallahi ya galabaita kuma kema fa har yanzu kina
son sa"
Rauda ta ɗago jiƙaƙƙun idanun ta tana kallon salma
"Salma ya zanyi da raina? Ki faɗamin ji nikeyi kamar zuciya ta zata fashe"
Salma sauke numfashi tace
"haƙuri zaki yi ki yafe masa, tunda ya amsa yayi kuskure"
_kada ki ƙara kirana ko nemana kisa aranki cewa baki taɓa sanina ba ki gogeni daga rayuwar
ki_
Girgiza kai tayi da sauri yayin da zafafan kalaman sa suka sake yi mata yawo a kunne
"bazan iya ba Salma, bazan iya ba idan nayi haka ban kyauta wa kaina ba, shi da bakin sa yace
in goge sa daga rayuwa ta, nayi kuma abunda yace Meyasa yanzu ze dawo gareni Meyasa?
Ta Ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka
Salma ta sauke numfashi tana cewa
" shikenan ya isa haka kukan, kinga lecturer ya shigo"
Share hawayen ta tayi tana kallon lecturen da ya fara darasi
Gaba ɗaya babu abunda take fahimta,dan kanta ya cushe
Tunda ya koma mota yike jin zuciyar sa na ƙuna tuƙi kawai yike yi batare da yana kallon hanya
sosai ba
Gaba ɗaya ya rikice, jijiyoyin kansa sunyi burɗum-burɗum
Sakamakon tsananin ciwo da kansa keyi,
Ya zeyi mata ta fahimci ƙaunar da yike mata?
Ya zeyi ya goge laifin sa a gareta?
Tambayoyin da yayi ma kansa kenan wanda ya rasa amsar su
Runtse ido yayi cike da tsananin damuwa
Ƙarar horn yaji daf dashi
Ya buɗe idanuwan sa da sauri wata ƙatuwar mota ya gani gab da shi
Ya juya sitiyari da sauri dan ya kauce mata
Sai dai duk da haka Be tsira ba dan wata ƙatuwar bishiya ya daka
Ya yin da motar ta dawo baya ta daki jikin waccan motar
Ta kuma yo gaba ta tuntsura
*** *** ****
Tsattsaye suke sunyi layi gaban wani kogo
Wanda yike fitar da turi ri acikin sa
Abul simnan ne tsaye a gaban su inda yike yi musu jawabi
"kamar yadda muka gama da horon ƙan-ƙara yanzu zamu shiga kogon marzaj
Kogone dake ɗauke da tsumi wanda dashi ne zan haɗa muku bayyana acikin jama'a
Sai dai kusani kafin kuje inda tsumin yike akwai wasu baƙaƙen ifiritai wanda suke da sarauniyar
su guda
Sanin kanku ne kamar yadda muke da ƙarfi haka suma ifiritai suke da shi
Dan haka sai kun dage dan idan ba kuyi da gaske ba, za ku iya rasa rayukan ku
Dan haka sai kun kula da kyau,