Showing 15001 words to 18000 words out of 101191 words

Chapter 6 - JINNUL AASHIQUE BOOK COMPLETE By Yar Fillo .pdf

08 Jul 2025

3171

mamaki yadubi Umar

"A bayanin dakamin nayimaka gwaji akan abunda nike tunani yana damunka amma banga
komai ba"

Hmmmmmm umar yasauke numfashi

"Dama banyi tunanin zaka komai d'in ba......

Sai kuma ya dakata yana duban Rauda dan ba ya so yayi maganar agabanta

"Madam had'a min ruwan wanka"

Ta mik'e ta hau sama,ya maida kallonsa kan zayyad Yana cigaba da cewa

"Zayyad,zafin dani keji a jikina yawuce yadda zan kwatanta maka,jini keyi kamar ana huramin
wuta acikin jikina"

Zayyad yasauke numfashi yace
"Wai to meke faruwa haka?

Umar ya zayyana mishi abunda yafaru daren jiya a asibiti,da allurar da Aasim yayi masa

Zayyad zaro ido yayi zuciyarsa cike da tsoro

"Yayi shigata yayimaka allura?nashiga uku nikuma me yasakoni a al'amarinsa?

Umar shuru yayi yana kallon zayyad

Zayyad ya ciga ba da cewa
"Amma wannan al'mari akwai rud'ani da rikitar wa wallahi,kace ciwon maka ba na asibiti bane"

Umar ya yi ajiyar zuciya me nawi
"Hmmmmmm zayyad al'amarinnan yafara bani tsoro,duk inda kake tunanin Aasim wallahi ya
wuce Nan,ina fargaban abun da ze iya faruwa gaba"

Zayyad ya jinjina kai cike da tsananin mamaki danshi tunda yike aduniya betab'a jin
makamancin al'amari irin wannan ba Koda kuwa a littafi ballan tana a zahiri

"Gaskiya dole musan abunyi,inaga mushirya mutafi katsinan yanzu kawai"

Umar ya girgiza Kai yace
"Allah bazan iya tafiya me nisa ba,idan ka rok'esa baze yarda a turamai kud'i yazo ba?

Zayyad yad'an yi shuru yana tunani sannan yace

"Babban malami ne gaskiya,kuma koda yaushe gidan shi cike yike taf da jama'a bana tunanin
ze iya barinsu yazo,amma bari na kirasa naji"

Yak'arasa fad'a yana zaro wayarsa a aljihu

Ya danna numban malamin bugu biyu ya d'auka suka gaisa,zayyad yasanar dashi buk'tarsu
akan yazo tare da rok'onsa daya taimaka

Yace ba matsala gobe da safe ze taho

Zayyad yayi mai godiya sannan ya kashe wayar yana kallon Umar yace

"Bari yaturo account numban sai inmai transfer"

Acan bedroom kuwa Rauda,

Ta gama had'a ruwan,zata fito kenan taji wani k'ara




Ta waiga da sauri tana kallon cikin bayin,ruwan data had'a acikin kwamin wanka ne taga yana
ta zakud'owa kamar dakwai wani abu aciki

Ta rufe idanuwanta da sauri jin tsigar jikinta na tashi bakinta na ambaton sunan Allah

"RAUDA!

Taji ankira sunanta da wata kalar murya me tsoratarwa

Tabud'e idanuwanta da sauri tana kallon cikin ruwan inda taji ankira sunannata

Wani mutumi tagani d'an k'arami shi ba wada ba shi ba yayan wada ba,d'an siriri,fatar jikinsa
wata kala kamar gansa kuka,koriya shataf,idanuwansa wasu kala kamar na mage

Futowa yayi daga cikin ruwan yana tahowa inda take

Jikinta na rawa ta murd'a k'ofar bayin zata fita amma gam k'ofar ta rufe

Addu'o i tacigaba dayi dasauri tana jijjiga k'ofar

Ganin ya iso gab da ita yasa tayi sarranda


Ta runtse idanuwanta kawai,jitayi an damk'i hannunta ta ware idanun tana k'wala ihu

"Bazamu tab'a rabuwa dake ba"

Taji yafad'a
Tare da kecewa da wata kalar dariya

Takuma k'wala ihun tare da zubewa a sume,

Umar nafalo, yajuyo ihunta, zayyad ya dubesa yana fad'in

"Kamar ihun Rauda ko?
Umar ya d'aga kai yana mik'ewa

"Bari Naduba Ina zuwa"

Yafad'a yana hayewa sama da sauri

A dur k'ushe yasameta,ya d'agata dasauri yana kiran sunanta

"Rauda!Rauda!

Amma shuru,d'aukota yayi ya yo falo da ita, zayyad na hangosa ya mik'e yanacewa

"Subhanallah me yasameta?

"Wallahi bansani ba"
Umar yafad'a yana shimfid'ar da ita a kan doguwar kujera

Yazauna gefenta yana d'an girgiza ta,yana cigaba da kiran sunanta

Zayyad da ke tsaye yad'auko ruwa agora ya mik'ama umar yana cewa
"Ina ganin suma tayi,yayyafa mata mugani"

Ya amsa ruwan ya yayyaffa Mata,ko minti biyu beyi da yayyafa mata ruwan ba,tafarfad'o tana
sauke ajiyar zuciya me nawi

Lokaci d'aya ta bud'e idanuwanta ahankali harta gama bud'e su akansa

Ahankali k'wa-k'walwarta ta tariyo mata abunda tagani a bayi

Tashi tayi a zabure ta fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka

"So sukeyi su kasheni,sunce bazasu tab'a rabuwa dani ba wayyoh allahna na shiga uku!

Umar yasauke numfashi zuciyarsa cike da tsananin damuwa,
Kasa cewa komai yayi,ya rungume ta kawai yana sauke numfashi ahankali

Zayyad yayi jugum Yana kallonsu gabad'aya tausayinsu yikeji,lokaci d'aya yanayinsu ya sauya
daga farin ciki zuwa tashin hankali

Be bar gidan ba sai da aka kira sallar magriba

Suko suna falon har lokacin,ba maganar neman abinci dan babu me jin yunwa acikinsu

Zuwa can dai ya dubeta tana kwance akan k'afafunsa yayinda yike zaune kan doguwar kujera
yace

"Mekike buk'atar kici insa me gadi ya siyo Miki?

Girgiza masa kai tayi tace

"Ni banajin yunwa"

"Nasan bakyaji ai,nima baji nike yi ba amma yazama dole munemi wani abu musa acikin mu
dan zama da yunwar itama babbar matsalar ce"

Ta jinjina Kai
"Shikenan kasa yakawo koma miye"

Koda me gadin yasiyo kuwa,kad'an suka tsakura, suka gabatar da sallar magriba da
issha,sannan suka kunna karatun qur'ani acikin a falon

A haka bacci ya d'auke Rauda,shiko umar ko kad'an be runtsa ba dan jikeyi kamar ana
d'add'aure jijiyoyin jikinsa,ga zafin da yike ji Yana dad'a k'aruwa.

Sai wajen asuba Rauda ta farka,taga yadda ya had'a zufa

"Ba kayi bacci bane?

Ta tambayesa da damuwa a fuskarta

Ya girgiza Kai yana k'ok'orin b'oye yanayin da yikeji

"A a nayi Mana kiran sallar da akayi ne ya tasheni"


Hmmmmm tasauke numfashi

"To muje muyi alwala ko"

Suka mik'e atare,jiyayi k'afarsa ta rik'e tana mai zugi

Yad'an tsaya yana kallon k'afar,kallon Rauda tayi tace

"Lafiya?

Yad'an k'ak'aro murmushi
"K'afata ce ta rik'e ina ganin Dan na kwana a zaune ne shiyasa"

Cikin tausaya wa tace
"Meyasa baka tasheni ba to,dana kwanta akan k'afafunka?

Ya kuma yin murmushi
"Taya zan tasheki?zan iya kwana a tsaye ma inhar ke zakiyi baccin cikin kwan ciyar hankali"

Sonsa da k'aunarsa da kuma tausayinsa suka k'ara shiga cikin zuciyarta

Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncinta

Cikin damuwa yace
"Miye kuma na kuka chuchu"

Hannu tasa tashare hawayen tana cewa

"Tabbas samunka matsayin miji agareni,wani babban rabo ne daga ubangiji,na tabbata da bakai
na aura ba da yanzu wanda na aura ya maidani gidanmu danna tabbata babu me iya zama dani
da wannan lalurar atare Dani"

Tak'arasa fad'a wasu sabbin hawayen na gangarowa daga idanunta

Ajiyar zuciya yasauke tare da kama hannayenta yana kallon cikin idonta

"Rauda,allah yayi nine mijinki shiyasa ma ya k'addaro miki wannan al'amarin,dan Allah ki
kwantar da hankalinki banaso inga damuwa a fuskarki,wallahi nikad'ai nasan yadda Nike Jin
zuciyata idan naganki acikin damuwa"

Tayi murmushi still hawaye nabin fuskarta

"Zan rink'a b'oye wa dan kawai hankalin naka ya kwanta amma kasan damuwata bazata tab'a
ciruwa ba face na rabu da matsalar dake tattare Dani"

Har lokacin hannayenta na rik'e cikin nasa
"Jikina nabani kinkusa rabuwa da wannan matsalar,ko ince munkusa rabuwa da ita,insha allahu
muna gab da fita daga cikinta"

Ta gyad'a kai kawai dan ita tasan yanzu ma suka fara shiga cikin matsala

"To allah yasa"

Tafad'a,suka shiga cikin bedroom suka d'auro alwala

Shiya jasu sallar, Allah-allah yikeyi ya idar sabida zugin da k'afarsa keyi masa

A daddafe ya sallame sallar,ya mik'ar da k'afar yana mamakin zugin da k'afar ke masa

Jikinta yayi sanyi dan ta fahimci ba kwanan dayayi azaune bane yasa k'afar tasa haka,k'ila
abunda ke shiga cikin jikinsa ne

"Jaana haryanzu k'afar bata dena ba ko?

K'ak'aro murmushi yayi yace

"Aa ta Dena,kawai dai na mik'ar da ita ne"

Ajiyar zuciya tayi tana girgiza Kai,batasan me yasa yike son b'oye mata halin da yike ciki ba

"Jaana dan allah kadena min irin haka, at least in kanajin abu kafad'a min ko kana da wacce tafi
nine?

Nida bani da wanda yafika ai komai naji saina sanar dakai amma Kai......

Ya katseta
"Chuchu kinsani babu abunda zan b'oye Miki,k'afar ta Dena tund'azu"

Ta kauda kanta gefe gudun kada yaga hawayen da ke Shirin zubo Mata

"Chuchu"

Yakira sunanta,saida tashare hawayen sannan ta juyo tana amsawa

"Na'am"

"Zonan"

Yafad'a,ta taso tak'arso gabansa ta durk'usa

Janyota yayi ya rungume ta yana sauke wani numfashi me nawi

"Kizauna ajikina,ko zanji sanyi acikin zuciyata"

Yafad'a yanajin yanayin sa na k'ara canzawa,k'afa da zafin jikin nakuma addabarsa

Runtse idanuwanta tayi wasu sababbin hawayen na ambaliya a fuskarta

Yakuma matseta ajikinsa bakinsa na ambaton

"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalumin"

Ta bud'e jik'akk'un idanunta tana kallon yadda ya runtse idonsa alamar yana jin rad'ad'i

Addu'o i tafara tofa Masa, idanuwanta na fitar da hawayen tausayi da tsantsar damuwa


K'arfe tara tayima zayyad a Tasha,Dan malam aminu ya sanar dashi sunkusa isowa

Ko minti goma beyi da zuwa ba,motarsu ta tsaya

Yafito cikin manyan kayansa da nad'in rawani akansa

Dattijone kamilalle me cike da natsuwa,ya mik'ama zayyad hannu sukai musa baha suka
gaisa,sannan suka shiga motar zayyad d'in

Bayan zayyad yatada motar yace

"Malan sannu da hanya,gaskiya kun iso da wuri motar tayi gudu"

Malan yace
"Ai da wuri nafito ina idar da sallah danma motar tad'an tsaya mana amma da mun iso tund'azu"

Zayyad ya jinjina kai yana cewa
"Allah sarki,kayi hak'uri fa malan,muntasoka mu yakamata ace munzo da kanmu amma halin da
abokinnawa ke ciki yasa nace bari dai kazo d'in"

Malan yayi d'an murmushi
"Babu komai"

Tunda suka iso get d'in gidan malan aminu ya fahimci akwai gagarumar matsala acikin gidan

Hakan yasa ya umarci zayyad da ya dakata da shiga cikin gidan

Sai da yayi addu'o I sosai sannan yace zayyad ya shiga

Zayyad ya shiga yayi parking,sannan suka fito zayyad yafara knocking d'in falon

Har lokacin suna rungume da juna, bakinta kuma bedena karanto addu'o in ba

K'wan-k'wasa k'ofar da zayyad yayine yasa suka bud'e idanuwansu atare

Dede lokacin wayar Umar tafara k'ara ganin numban zayyad yasa yace

"Ina ganin zayyad ne,mukoma falon"

Suka mik'e sukayo falon yana d'an ciccije bakinsa dan ciwon dad'a k'aruwa yikeyi

Kan kujera ya zauna,Rauda ta bud'e k'ofar

Ta gaishe da su tana kallon malan aminu Wanda shima ita yazuba ma ido

Ta basu hanya suka shiga sannan ta maida k'ofar tarufe,takoma kusa da Umar tazauna

Yayinda suma suka zauna suna gaisawa da Umar d'in

Malan aminu yatashi ya dafa kan umar yana nazartar abunda ke damunsa

Ya girgiza kai fuskarsa d'auke da damuwa yana duban Rauda sannan itama ya dafa nata kan

Janye hannunsa yayi dasauri yana kallonta fuskarsa d'auke da tsantsar mamaki

A fili yace
"Aasim bin ramzad?
Yasauke numfashi Yana kuma girgiza kai cike da tarin fargaba

"La haula wala k'uwwata illah billah"

Malan aminu yafurta yana komawa kan kujerar ya zauna

Gabad'aya sun zuba mai ido suna jiran suji abunda zece

Ya sauke numfashi yana kallonsu

"Zahiri kuna cikin babbar matsala,domin kuna tare da rauhanin da ba kowani malami bane ze
iya ja dashi"

Yad'an numfasa sannan yacigaba dacewa

"Amma nayi mamaki,Aasim bin ramzad rauhanine,kuma a iya sanina rauhanai basa
cutarwa,wani laifi kuka masa haka da ya tunzurasa yike azabtar daku?

Ya k'arasa maganar Yana kallonsu sosai

Ganin basu bashi amsa ba yasa yacigaba da cewa

"Tabbas akwai laifin dakuka masa mai girma wanda ya tunzurasa ya canza daga
ainihinsa,kuma ni tabbas bazan iya ja dashi ba amma zan iya nemansa inji dalili inkuma jaraba
rok'onsa ko ze iya hak'ura"

Har lokacin babu wanda yayi magana kallonsa kawai sukeyi,umar ne yakatse shurun ta hanyar
cewa

"Malan dan Allah kataimaka kayi iya abunda zaka iya, wallahi muna cikin damuwar da bazamu
iya kwatanta maka ba"

Malan aminu yagyad'a kai yaciro wani turare a aljihunsa ya fesa sannan yafara karanto addu'o I
da basajin me yake fad'a illa bakinsa da suke gani yana motsawa

Ahankali d'akin yafara duhu,saiga shi ya bayyana cikin ainihin suffarsa ta yarima

Malan aminu nagani,yazube a k'asa yana faman jera kirari

"Allah yataimaki yarima,me martaba d'an sarki,basarake me dubbannin dawakuna"

Fuskarnar tasa a tamke ya watsawa malan aminu razanannun idanunsa cikin b'acin rai yace

"Kai wanene,da har ka kai matsayin da zaka nemeni"

Bakin malan aminu na rawa yace
"Ka gafarceni ranka shidad'e,tuba nike allah ya huci zuciyarka"

Ya kad'a kai yana cewa

"Fad'i kiran me kakemini,meke tafe dakai,me Kuma yashigo dakai matsalar da babu
ruwanka,shin kanaso rayuwarka ta salwanta ne?

Jikin malan aminu na kyar-kyarwa yace

"Tuba nike ranka shidad'e,amsa Kira na dakayi kad'ai ya isheni,bakuma nanemeka bane dan na
Isa,illa Dan na rok'eka da ka sassauta ma wad'annan bayin allahn.....

Da wata kalar tsawa ya katsesa
"Kai!
Kashiga taitayinka,kakuma tuna da wanda kake magana,kai baka isa ka nemar musu afuwa
ba,kuma hukuncine nariga da na yanke,mafita ta rage garesu"

Malan aminu bakinsa na rawa saboda kid'imar da yayi
Yace

"Kagafarceni tuba nike allah ya huci zuciyarka"

Aasim ya kalli Rauda da umar yana yimusu wani kallo da shi kad'ai yasan ma anarsa

"Nafad'a kuma zansake fad'a muku,ko ku rabu da juna kokuma daga yanzu kicigaba da
fuskantar barazana,kuma gubata akullum k'ara ratsaka zatayi wallahi sai ka gwammace
mutuwarka da halin da zaka shiga

Ke Kuma....yanuna Rauda sannan yacigaba da cewa

"Yanzu ne zaki fahimci ko ni waye dakuma matsayin da nike dashi"

Yana gama fad'ar haka yab'a ce

Nan danan haske ya gauraye falon ya dawo yadda yike

Gabad'aya malan aminu ya jik'e sharkaf da zufa,shiko zayyad harda fitsari ya saki saboda
tsananin tsorata

Malan aminu yasauke doguwar ajiyar zuciya yace

"Agaskiya bazan iya ba,ku gafarceni amma ya wuce k'arfin da kuke tunani,bazan iya ba dan
allah karku sake nemana dan rayuwata zata iya shiga cikin hatsari"

Yak'arasa fad'a yana mik'ewa ze fita

Zayyad na kiransa amma be tsaya sauraronsa ba ya k'arasa ficewa daga falon dan gabad'aya
ya firgita

Rauda ta runtse idanuwanta cikin tashin hankali maganganun malan aminu nayimata yawo
acikin kunnuwanta

"Aasim bin ramzad rauhanine kuma rauhanai basa cutarwa tabbas kunyi masa laifin dakuka
tunzurasa wanda yasa ya canza daga ainihinsa"

Wasu hawaye ne masu zafi suka cigaba da gangaro mata

Ahankali ta furta

"Tabbas ban kyauta ba maka ba,amma ban cancanci wannan hukuncin daga gareka ba"

Wanene Aasim? Menene had'insa da Rauda? Me suka masa da ya canza sa daga ainihinsa?

Muhad'u a page dan jin yadda zata cigaba da kasancewa taku a kullum



Y'arfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: JINNUL
AASHIQUE

‍♂‍♂
‍♂

NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)

✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍

❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical
Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will
cause you no pain_❄



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu


AGE


_Wannan Page naki ne anty Nabeelt Allah nike rok'o ya baki lafiya, yasa kaffara ne ya kuma
k'ara dank'on zumunci a tsakaninmu Amiiiin_

Maman ummi kema ina Allah yak'ara lafiya yasa kaffarane yakuma nuna mana auran ummi
lafiya�

Ban manta da ke ba safnah‍. Ina godiya da addu'o in ki gareni

_GAISUWA DA JINJINA_

*_Ga ya ommer allah yak'ara k'warin ido muna godiya da zak'ulo mana kura-kuran mu daka
keyi, da kuma gyara dakake mana, bazamu iya biyanka ba ya Ommer wlh muna jin dad'in
shugabancin ka sosai Allah ya bar mana kai da rai da lafiya mai anfani, ya kawo bata tagari kuje
har katsina musha ringen-rigegen_*

Bissmillahir rahmanin rahim✍✍✍✍


FARKON LABARI

Cikin katafariyar jami'ar dake cikin katsina

D'alubai ne sukayi dandazo a wani wuri da alama sakamon jarabawarsu da sukayi suke
dubawa

Hayaniya da turereniya sunyi yawa a wurin,dan ko wani d'alubi burinsa yaga sakamakon sa


Tafiya Rauda Take yi cikin sauri har da gudu-gudu yayinda ta hango dandazon d'aluban

Gabanta na fad'uwa, k'irjinta na dukan uku-uku ta isa wurin

Ganin yadda maza da mata suka cakud'e yasa tasamu gefe ta tsaya,dan bazata iya shiga cikin
maza ba

Saida taga d'aluban sun ragu,sannan ta k'arasa wurin gabanta na fad'uwa

Bata ma fara duba sunan ta daga sama ba,daga tsakiya tafara tanayin k'asa

K'irjinta yayi mugun bugawa yayinda taga abunda taci

Takasa d'auke hannun ta awurin sakamakon sanyin da jikinta yayi

Wasu y'ammata masu ji da kansu dake gefenta suka fashe da dariya

Cikin haibaci d'ayar me suna laurat wacce itace take fitowa da first class a department
d'insu,takalli d'ayar me suna farida tace

"Farida waike wace irin k'wa-k'walwa kike da itane,ace kowani semester bakya iya fitowa da ko
third class sai dai probation"

Farida taga ne nufin laurat sarai hakan yasa ta fashe da dariya tace

"Kannawa ne a toshe yike, kwata-kwata baya iya d'aukar komai,saboda dattin talauci da kuma
miyar kuka sun toshesa"

Dariya suka sakeyi gabad'aya su biyun cikin nishad'i da annashuwa

Rauda tasan da ita suke,hakan yasa tabar gurin jikinta a sanyaye ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login