Showing 66001 words to 69000 words out of 101191 words
min kallon wacce ta fara taɓuwa Anty ummi, wallahi da gaske ne, kiyarda da abunda
na faɗa miki"
Anty ummi ta sauke doguwar ajiyar zuciya
"bawai banyadda da abunda kika faɗa bane, a'a na yarda dan jinnul aashique mun san kina
dashi amma tabbas baki da hankali
Dan Inba marar hankali ba babu wacce zata yi abunda kika yi, ace kiyar da kirinƙa rayuwa da
jinnu har ki amsa mai zaki rayu dashi har abada kuma ki ɓoye mana"
Rauda gwauron numfashi ta sauke tace
"nidai Anty ummi kiga ya min yadda zanyi bagashi yanzu na faɗa miki ba, ki gaya min ya zanyi
da Umar,ina tsananin ƙaunar sa har yanzu amma idan natuna wulaƙancin da Yamin Abaya sai
inji duk ya fita a raina"
"ke yanzu har ma kya ga laifin Umar,ai wallahi kidena ganin laifin sa dan bayi da laifi
kwata-kwata bayin kansa bane"
Anty ummi ta faɗa zuciyar ta cike da jimami
Rauda tace
"to yanzu yakike ganin zanyi?
Numfasawa Anty ummi tayi tare da nisawa tsayin mintoci
Daga bisani tace
"aganina tunda shi Aasim ɗin bada mugunta yazo miki ba ki kula Umar ɗin kucigaba da soyayya
Idan ya dawo sai ki basa haƙuri kice ya bar ki auri Umar, shi kuma ya cigaba da rayuwa dake a
ɓoye, ina ganin Hakan itace hanya me sauƙi tunda Shima yana sonki"
Rauda ta Lumshe idanuwan ta da suka kaɗa saboda damuwa tace
"da wuya ya yadda, dan yana sona fiye da yadda kike tunani"
Numfashi Anty ummi ta kuma sauke wa
"dolen shi ma ya yarda dan babu inda aka ce aljan da mutum suyi rayuwa, kina ganin Gorin da
ake yi miki akan rashin aurannan dan haka kada ki bari Umar ya kubce miki
Idan ma be yadda ta sauƙi ba ai sai aje gurin malamai ya rabu dake ta tsiya
Rauda ta girgiza kai
"Anty ummi ba zaki gane ba, Aasim ba kamar wanda kike tunani bane, kuma wallahi inajin
tausayin sa a kaina fa......
Katseta Anty ummi tayi
" kinga Rauda kiyi abunda nace miki"
Ta kaɗa kai kawai amma ita ta san akwai babbar ƙura a gaba
Koda ta dawo gida haka ta wuni babu sukuni
Da daddare tana zaune abun duniya ya haɗu ya cunkushe mata kai
Tabbas dole tabi shawarar Anty ummi
Wayar ta ta ɗauko ta danna numban Umar
Kiran Nashiga ya katse, sai ga nashi ya shigo
~ƴarfillo~.
[7/12, 10:51 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u
np pain~*
*JINNUL*
*AASHIQUE*
♂♂
♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
AGE 2⃣3⃣
_Wannan Page ɗin nakine *khadija* marubuci yar ~*ashe kece*~_
_Tare da *khadija hydar* young novelist_
_Na sadaukar dashi gare ku kuyi yadda kuke so dashi_
_12:15_ AM
SUN,JUL 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍✍✍✍✍
Tsura ma wayar ido tayi tana kallon numban sa ta fito ɓaro-ɓaro
Sai da ta kusan tsinkewa sannan ta ɗaga,tare da karawa a kunnen ta
Sassanyar Sallamar sa ce ta karaɗe kunnen ta
Ta Lumshe ido a zuciyar ta tana faɗin
"komai nasa na daban ne"
Sai da yayi sallama sau uku sannan ta amsa
"ya kike? Ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?
Shuru tayi batare da ta bashi amsa ba
"chuchu!
Ya faɗa,jikin ta ne ya ƙara yin sanyi
Dan ko Abaya idan ya kira ta da chuchu wani iri take ji
"bakya jina ne chuchu?
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Umar ka tabbata da gaske kake yi yanzu kana sona,kuma zaka aurani?
Daga can Ɓangaren Umar tashi yayi daga kwancen da yike yana bata amsa
"na tabbata mana chuchu,wallahi a shirye nike da in aure ki koda kuwa anan da sati ɗaya ne"
Hmmmmmmm ta kuma sauke ajiyar zuciya
"shikenan idan da gaske kake yi inaso inga alama idan kuma bada gaske kake yi ba dan Allah
kada ka kuma cutar da zuciya ta"
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar sa
"da gaske chuchu? Yanzu komai ya wuce a wurin ki?
Ɗan murmushi tayi tace
" ya wuce amma dan Allah Jaana......
Sai kuma ta kasa Ƙarasa wa dan bata san sanda sunan Jaana ya fito daga bakin ta ba
Shiko Umar wani farin cikine ya ƙara lulluɓesa
"dan Allah me Rauda? Ki faɗi kome kike so wallahi zanyi miki shi a yanzu Ba tare da na ɓata
lokaci ba"
Yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata da ya shiga farin ciki
"dan Allah kada ka kuma cutar da zuciya ta, idan ka kuma yi min abunda kayi Abaya ina
tabbatar maka da zan iya rasa raina......
Katseta yayi da sauri
"ba sai kin roƙe ni ba Rauda a yanzu bani da wacce nike so sama dake acikin zuciya ta,kuma
ina me tabbatar miki da ba zaki sameni me kuma sanya ki damuwa ba, a yanzu buri na inga
nasa ki farin ciki"
Wasu guntayen hawaye ne suka biyo kuncin ta wanda ta rasa na menene su
Na farin ciki ne? Ko kuma na tarin tunanin da ya cunkushe mata ƙwaƙwalwa
"Umar kasan Kaine wanda nike so kai ne zaɓin zuciya ta, me yasa kayi min abunda kayi Abaya
me yasa?
Ta faɗa muryarta na raunanewa
Umar ya sauke dogon numfashi yace
"dan Allah ki dena tuna baya Rauda, na tabbata a yanzu son da nike miki ya ninka wanda kike
min sau dubu"
Share hawayen tayi tace
"shikenan zan kwanta sai da safe"
"shikenan chuchu kiyi bacci me daɗi ina sonki"
Ya faɗa da murmushi a fuskar sa
Ajiye wayar tayi zuciyar ta na tambayar ta
"anya kin kyauta wa kanki kuwa Rauda? Ki tuna Aasim da ya bar ahalinsa matsayin sa da
komai nasa akan ki, shin kina ganin kinyi masa dai-dai? Ya tafi yana fafutukar yadda ze rayu
dake amma ke zaki ci amanar sa?
Ta karkaɗa kanta da sauri wasu sabbin hawayen na ciko idanuwan ta
"ban kyauta ba, ban kyautawa Aasim ba"
Ta faɗa cikin damuwa
"to idan baki amince kin auri jinsin ki ba, haka zaki ƙare rayuwar da jinsin da ba naki ba? Kuma
Umar shine wanda kike so"
Wani sashe na zuciyar ta ya faɗa,
"idan Aasim ya samo abunda yaje nema fa, na bayyana acikin jama'a, baki da hujjar da zaki ce
ya barki kiyi aure tunda dai Shima ze iya rayuwa dake a matsayin mutum batare da kowa ya
sani ba"
Kanta ne ya Sara dan gaba ɗaya tunanin ta ya burki ce
Kwantawa tayi a kujerar da take zaune tana faɗin
"ya Allah ka taimake ni, bansan yadda zanyi Ba"
A haka bacci ɓarawo ya sace ta
Shiko Umar suna gama waya alwala ya ɗauro ya gabatar da nafiloli sannan ya ɗaga hannayen
sa yana godiya ga ubangiji,yana kuma roƙon Allah da ya kaɗe duk wani sharri da ze sa ya
ƙuntata mata
*** **** *****
Zaune suke cikin Sahara suna tattauna yadda suka yi gwaji akan bayyana cikin jama'a
Wani daga cikin rauhanan yace
"ni fa a suffar mace na bayyana, na yi shigar kaya masu kyau na bayyana a wata kasuwa
Idan Kaga yadda mazen bil'adama suke kallo na kai kace haɗiye ni zasu yi
Ina jin wani yana cewa
"wannan kyakkyawar budurwar sai kace ƴammatan aljanna"
Be san garjejen ƙaton rauhani bane"
Suka fashe da dariya wani yana cewa
"amma kai ko ka iya iskanci wallahi, ni a suffar almajiri na bayyana a wurin wani cin a binci
kuma a suffar yaro
Wata mata da ta ganni sai da ta kusan yin kuka
Wai ji ɗan ƙaramin yaro amma yana neman abunda zeci bata san ƙila tun kan a haifi iyayen ta
nike duniya ba"
Dariya suka kuma sawa cike da nishaɗi
Aasim ko na zaune ya jingina da dutse yana kallon su
Jefi-jefi ya kan yi murmushi idan suka faɗi abun dariya
"Aasim kai kowa yana bada labari amma ka zauna kayi shuru, lafiya dai ko?
Ɗaya daga cikin rauhanan ya tambaya
Suka maida hankalin su kansa suna jiran jin me zece
" babu komai"
Ya faɗa
Rauhanin dake fuskantar sa yace
"a'a akwai komai mana, nasan baze wuce tunanin bil'damar ka kake yi ba, to ka kwantar da
hankalinka mana saura wata ɗaya fa mu koma, musha biki"
"aikuwa dan mune nan abokan ango"
Wani Rauhanin ya faɗa, wani kuma yace
"Nikuma nine zan zama waliyyi"
Dariya suka kuma sawa
Jazmi da tunda suka haɗu da Aasim suka zama abokai yace
"abokina a wace ƙasa zaka ci amarcinne? Dan nasan yadda ka zaƙu muna komawa zaka yi
mata maganar aure"
Har lokacin dariya suke yi
Aasim Miƙewa yayi yana murmushi
"ni kunbi kun cika min kunne da surutu bari in baku wuri"
Jazmi dariya yayi yace
"afuwan fa mun manta da yarima ne a wurin, wanda baya son haya niya"
Be kuma saurarar su ba ya wuce can nesa dasu kaɗan ya zauna
Yana kallon yadda iska ke kaɗa saharan
Gaba ɗaya akwanakinnan tunanin ta ya hana sa sukuni, yayi tsananin rashin ta
Ya Lumshe ido yana hango kyakkyawar fuskar ta
"habibty ina tsananin rashin ki,nasan kema kina can kina tunani na, ke ce rayuwa ta habibty"
Ya faɗa cikin tsananin begenta
Motsi yaji a kusa dashi
Ya buɗe idonsa yana kallon inda yike jin motsin
Wata maciji ya ce,me kyau jikin ta fari sol
Hannu ya miƙa mata yace
"kyakkyawar maciji ya, zo inganki"
Macijiyar ta tsura mai ido amma ta kasa matsawa daga inda take
Ƙara kallon ta yayi, sai lokacin ya lura ciwon dake jikin ta
Cikin tausaya wa,ya ɗauko ta yana duba ciwon sosai taji
"ohhh sannu,ashe rauni kikaji, bari in sami ki magani kinji?
Abul simnan ya ƙara so wurin ya zauna
" Aasim ina ka samo maciji ya kuma?
Aasim yayi murmushi yana sama ta maganin
"anan na ganta,taji rauni"
Abul simnan ya jinjina kai yace
"ka kyauta da ka taimaka mata"
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar sa idanuwan sa kuma na kan Macijiyar
"na sa miki magani kinji, kiyi haƙuri zaki samu lafiya"
Ya Ƙarasa faɗa yana ajiye ta a ƙasa
Ta wuce
Ya maida kallon sa ga Abul simnan da yike kallon sa
"kana da kyakkyawar zuciya Aasim"
Aasim ya kuma murmushi
"kullum haka kake cewa Abul simnan"
Abul simnan ya jinjina kai
"da gaske nikeyi kana da kyakkyawar zuciya shiyasa nike tausaya maka"
Aasim ya maida kallon sa ga saharar dake kaɗawa
"kai ma kana da kyakkyawar zuciya,ina kuma godiya da yabo na da kake yi a koda yaushe"
**** ***** ******
Da safe, tana zaune tana tsakurar abun kari dan Sam bata jin cin komai
Wayar tace ta fara ƙara, ta ɗauka ta dubawa Umar ne
Ɗauka tayi tare da karawa a kunnen ta
Tana sallama
Daga can Ɓangaren Umar ya amsa yana faɗin
"barka da safiya chuchu,ina fatan kin tashi lafiya"
"lafiya lau"
Ta bashi amsa
Ya jinjina kai yace
"masha Allah Naji daɗi da Naji Hakan, tun ɗazu naso in kira ki sai nayi tunanin baki tashi ba"
Tayi ɗan murmushi dan jin muryar sa damuwar da ta cunkushe zuciyar ta ta rage
_~Ƴarfillo~_.
[7/12, 10:51 AM] Harira Aliyu Mrbcy: *JINNUL*
*AASHIQUE*
♂ ♂
♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u
np pain~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
AGE 2⃣4⃣
_Wannan Page nakine *maman isqah* kin kasance me dogon sharhi a duk lokacin da nayi
posting ina matuƙar jin daɗin Hakan Allah ya bar zumunci_
*_Fatan alkhairi_*
_Ga *princess mazadu* ina miƙa gaisuwa_
_9:48_ AM
MON, JUL 8
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍✍✍✍✍
"yau na tashi cikin farin ciki sakamakon wani kyakkyawan mafarki da nayi"
Umar ya faɗa
Rauda tace
"mafarki? Mafarkin me?
Daga can Ɓangaren Umar gyara zama yayi yana ɗan jingina da kujerar da yike zaune
"mafarki nayi munyi aure,kin haifa min kyawawan yara ƴan uku, masu kama da ke"
"ƴan uku fa? Amma a mafarkin naka na mutu ko?
Dariya Umar yayi yace
"dan kin haifi ƴan uku kuma sai ki mutu?
Ras na ganki kina ta yi musu wasa"
Wani murmushin ta kuma yi
"a'a nikam bazan iya haifar ƴan uku ba"
"zaki iya mana chuchu, ke fa jaruma ce"
Ta girgiza kai kamar yana ganin ta
"Allah bazan iya ba"
Jin tana amsa mai faran-faran yasa yaji ya ƙara shiga cikin nishaɗi
"inma ba zaki iya ba, ranar haihuwar sai mu raba in haifi biyu ki haifi ɗaya"
Dariya tayi tace
"to shikenan Allah ya nuna mana lokacin"
Amin ya faɗa haɗi da cewa
"wa yaga Umar na naƙuda, ai inaga duk faɗin garin Abuja sai sun taru"
Dariya ta kuma yi sosai, Shima ya taya ta
Yana cigaba da cewa
"Allah da gaske"
Rausayar da kanta tayi tace
"kawai dan kana rago"
"ke haihuwa fa, cap ai kudai mata sai dai mu muku fatan shiga aljannah amma zahiri kuna
mugun ƙoƙari"
Ajiyar zuciya ta sauke, dan tunda ta fara jin muryar sa taji natsuwa na saukar mata
Tabbas ƙaunar sa daga allah ce
Katse mata gajeren tunanin da tafi yayi ta hanyar kiran sunan ta
"Rauda!
Ta kuma sauke ajiyar zuciya gami da amsawa
" na'am "
"kin karya?
Ya tambaya
" ina kan karyawan"
"ook to kigama sai in kuma kira, ko inzo yanzu ne?
Ta ajiye kofin tea ɗin da ya gama hucewa tace
" yanzu kuma? Safiya ce fa
Umar yace
"na sani kawai ina buƙatar inganki ne"
Murmushi tayi tace
"a'a kadai bari sai da yamma, ko da daddare"
Yace
"to shikenan Allah ya kai mu ki kula min da kanki"
"nagode"
Ta faɗa tana ajiye wayar
Ranar wuni tayi cikin farin ciki dan firar da suka yi ce kawai take mata yawo a kunne
Ya kira ta yafi sau biyar
Sai dai data tuna Aasim sai taji Gabanta ya faɗi
Tunda ga wannan ranar wata soyayya me ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin su
Koda yaushe suna manne a waya dan ya koma Abuja
Amma duk weekend sai yazo Kaduna ya ganta
Mama ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba
Ganin yadda su umma suke nuna hassadar su ƙarara
Dan duk wanda yaga Umar sai yayi mamaki ga kuɗi ka ga kyau ga kwarjini, duka Allah ya haɗa
masa
Yau Asabar, tun ƙarfe huɗu Umar ya taso kuma tunda ya taso suke waya
Fira suke yi sosai me cike da annashuwa
Mama ta fito daga uwaɗɗaka tana faɗin
"wai ni Rauda yau wayar nan ba zata ƙare bane? Muna da aiki fa ga yamma nayi"
Murmushi Rauda tayi tana yin ƙasa da muryar ta tace
"mama na min magana, bari zan kira ka"
Tana gama faɗa ta kashe wayar tana duban mama dake ta zuba murmushin jin daɗi
"mama me za'a dafa ne?
Mama tace
"soyayya da mai da yaji"
Rauda tayi dariya tana faɗin
"kai mama"
Mama ma dariyar tayi tace
"eh mana, ace waya anfi ƙarfin awa ana yin ta"
Ƙasa Rauda tayi da kanta cike da jin kunya tana tura mai saƙo
_zamu ɗaura girki yanzu,Allah ya tsare hanya ya kawo ka lafiya_
Batafi minti biyu da turawa ba nashi saƙon ya shigo
_amin chuchu, ki kula min da kanki, ki kuma sa girkin dani zanci, ina sonki_
Murmushin jin daɗi tayi bayan ta gama karantawa a zuciyar ta tana faɗin
"na yarda da ake cewa addu'a bata faɗuwa ƙasa, kuma duk daren daɗewa Allah ze amsa ka"