Showing 60001 words to 63000 words out of 101191 words

Chapter 21 - JINNUL AASHIQUE BOOK COMPLETE By Yar Fillo .pdf

08 Jul 2025

3181


Da yamma tana tsaye tana kallon tvn dake manne jikin bango

Yadda faɗan ya kaure ake nunawa, ga sojoji nan ta ko ina

Nurse ce ta shigo

Rauda tace
"wai yanzu ko kaɗan babu hanyar da mutum ze bi ya koma inda yike"

Nurse ɗin tace

"wallahi babu, dan muma tun rana aikin mu ya ƙare amma waɗanda zasu amshemu basu zoba
ga kuma Waɗan da aka ji ma ciwo ana ta kawo su"

Babu yadda Rauda ta iya dole ta ƙara kwana a asibitin

Washegari hanya ta buɗe ta koma

Bayan sati ɗaya Umar yaji sauƙi sai ɗan abunda ba'a rasa ba, yayin da garin hankali ya kasa
kwanciya

Dan kullum cikin ƙone-ƙone suke da hayaniya

Hakan yasa dole makaranta ta bada hutun gaggawa dan abun harya fara shafan ɗalubai

Ba yadda Umar beyi ba akan Tabari su taho tare amma taƙi

Dan bata son suna kasancewa tare a yanzu so take yi ta nisance sa ko dan ta hani zuciyar ta

Bayan kwana uku da dawowarta,suna zaune tsakar gida ita da mama suna girkin dare

Wayar ta ce ke ta ƙara kuma taƙi ɗagawa dan numban Umar ne

Wani kiran ne ya kuma shigowa mama ta kalli wayar tace

"wai waye ne yike ta kiran ki ba zaki ɗaga ba?

Ta ɗauki wayar ta kashe tana ba mama amsa

"kamfanin mtn ne"

Dai-dai lokacin baba ya shigo, suka mai sannu da zuwa

Ya amsa yana duban Rauda

"kije kina da baƙo a waje"

"baƙo?

Ta tambaya a zuciyar ta amma a fili shuru tayi tana mamakin wani baƙo ne zezo wurin ta

Katse mata tunani baba yayi

"ko baki ji ba, nace kina da baƙo a waje"

Amsawa tayi da to, yayin da baba ya wuce

Mama tace
"baƙo kuma? Wanene?

Rauda tace
" Nima bansani ba mama, dan bamuyi da wani zezo ba, amma bari naje nagani "

Ta Ƙarasa faɗa tana Miƙewa

Dogon hijabi ta zura ta fito ƙofar gida

Ko da mamakin ta, Umar ta gani tsaye ya sha wata maroon ɗin Shadda

Tsaye tayi jikin ƙofa tana kallon sa yayi kyau sosai

Ƙarasa fitowa tayi tana mamakin yadda akai ya san gidan su

Shiko murmushi ya saki yana amsa gaisuwar da ta masa

Ganin har lokacin da mamaki a fuskar sa yasa yace

"ki dena mamaki dan kinganni a ƙofar a gidan ku, nabi kwatancan da kikamin ne na shekarun
da suka wuce"

Gyara tsayuwarta tayi tana yi masa wani irin Kanno masu fassarori da yawa

Ta danne zuciyar ta tare da ɗan ɗaure fuskarta

"to ka kyauta, amma me ya kawo ka gidan mu? Kuma Ƙarasa wanda zaka aika ya kirani sai
mahaifi na?

Murmushi ya kuma yi yace

"adoka ta musulunci idan zaka nemi yarinya ai sai ka fara tambayar izinin iyayen ta, kuma na
tambayi baba ya bani izini innemeki"

Gajeren murmushi tayi wanda ya tsaya mata iya baki kawai wanda ya rasa gane ma'anar sa

"izinin nemana fa kace Umar? To wai ma in tambaye ka, wani neman da ga ciki?

Cikin rashin fahimta yace

"wani nemane kuwa banda na aure?

Murmushin ta kuma yi tana ɗan kaɗa kai

" Umar ke nan, akan mene zaka nemi izinin aurena batare da ka nemi soyayya ta ba?

Yana yin fuskar sa ya sauya zuwa damuwa

"Rauda, ina ce waɗannan abubuwan sun wuce, nasan fa kina sona har yanzu Meyasa zaki ta
maida hannun agogo baya....

Katsesa tayi

"har yanzu ina son ka? A yaushe na faɗa ma haka?

"ki faɗa sau biyu, da rana ta farko da kika je asibiti, da kuma rana ta biyu da kika shigo ɗakin da
daddare

Duk abunda kika faɗa inaji"

"yayi kyau da kaji Hakan, amma ka sani faɗin ina son ka bashi zesa na saurare ka har na kuma
yin wata soyayyar da kai ba, Umar dan Allah ka nisanci rayuwa ta ka gogeni daga rayuwar ka
na roƙeka kamar yadda ka roƙeni a baya"

Ta faɗa cikin damuwa zuciyar ta na harbawa

Idanuwan sa suka kaɗa

"Rauda wallahi ina ƙaunar ki,idan kika amince min a gobe zan iya turo iyayena ayi maganar
aure dan ki tabbatar da da gaske nike, wallahi a yanzu banajin zan iya rayuwa babu ke kuma
nasan kema kanki a yanzu kin fahimci Hakan"

"babu abunda na fahimta, kaje kanemi wata, dan yanzu ina da wanda nike so dan Allah karka
ƙara zuwa inda nike"

Ze kuma yin magana ta shigo gida da sauri

Ɗaki ta shiga ta zauna kan kujera tare da kifa kanta wasu hawaye masu ciwo suna biyo kuncin
ta

Mama ta shigo ɗakin dan taga wucewar ta

Zama tayi tana tambayar lafiya?

Share hawayen tayi tana faɗin babu komai

Mama ta girgiza kai tace
"bangane ba komai ba, hakanan zaki shigo kina kuka dan jin daɗi?

Waye ne wanda ya zo?

Wasu hawayen ne suka kuma gangarowa

" Umar ne"

Mama ta ce
"wani Umar?

Umar da kika sani na da, wanda ba mu taɓa haɗuwa ba

Mama ta ɗan buɗe ido da mamaki tace

"wannan na wayar me kama da Larabawa? To ya aka yi kuka haɗu har yazo nan ba kundena
waya ba tun tuni?

Kwashe komai tayi ta faɗa mata

Mama tayi murmushi

" to miye abun damuwa har da kuka? Ince Umar shine wanda kike so,ban manta ba fa duk
mazajen da kika tsaida da Allah beyi auran ba kin tsaida su ne kawai dan baki samesa ba,
Nasha ganin ki kina kuka kuma nasan duk a kansa ne, to tunda yanzu Allah ya kawo sa ba sai
ki ma Allah godiya ƙila shine alkhairin kuma mijin shiyasa duk Waɗan can da akasa ranar da su
aka fasa kuma yanzu kin tabbata da gaske yike yi?

Rauda ta numfasa tace

"cewa yayi wai a gobe ze iya turo iyayen sa dan intabbatar da gaske yike yi"

Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyar mama

"to ba shikenan ba, ai kin rama abunda ya miki kuma ya gane kuskurensa kawai ki kula sa ki
kuma amince dan nasan maƙiya sai sun kusan mutuwa saboda baƙin ciki"

Kallon mama kawai take yi yadda lokaci ɗaya ta shiga farin ciki tabbas mama tayi gaskiya ƙila
shine alkhairin shiyasa aka fasa da waɗancan amma Aasim fa?

Gabanta ne ya faɗi yayin da ta tuno sa




~ƴarfillo~.
[7/12, 10:51 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u
np pain~*


*JINNUL*

*AASHIQUE*

‍♂ ‍♂
‍♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_


Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_


AGE 2⃣1⃣


_Wannan Page naki ne *safnah* kiyi yadda kike so dashi_


~_Ina da wata buƙata kutayani da addu'a Allah ya biya min,ya cika min burina please_~

_8:50_PM
THU, JUN 20

_Bissmillahir rahmanin rahim_✍✍✍✍✍

"Zayyad me ya sami Umar? Ka faɗamin wani hali yake ciki?

Tayi mai tambayar cikin rawar murya da tsananin tashin hankali

Zayyad yace

"baki ji me nace bane? Accident yayi kuma duk kece sanadi, dan da kin saurare sa da Be shiga
damuwar da ze fita hayya cin sa ba"

"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, ka kai ni asibitin da yike ka kaini in gansa dan Allah"

Ta faɗa tana runtse idanuwan ta da suka cicciko da hawaye masu zafin gaske

Be ƙara cewa komai ba ya buɗe mota ya shiga

Binsa tayi ta shiga jikin ta na tsuma zuciyar ta cike da tarin fargaba

Ya tada motar ya fige ta aguje

Idanuwan sa sun kaɗa sunyi ja

"duk mutumin da yayi maka laifi ya dawo yace ka yafe masa ai Be kamata kaƙi kula sa ba

Sanin kanki ne Umar ɗin da kika sani da, ba shi bane yanzu

Wani irin roƙo ne be yi miki ba? Wani irin haƙuri ne be baki ba? Amma duk kika nuna baki san
yanayi ba?

Dafa kanta kawai tayi da yike cigaba da sarawa batare da ta ƙara tanka masa ba

Suna isa asibitin suka fito yayi gaba tana Binsa

Ƙofar emergency room ya murɗa ze buɗe

Wata nurse ta ƙara so wurin da sauri tana faɗin

"baiwar Allah kijira a fito dashi daga emergency room tukunna"

Zayyad ya kalli nurse ɗin yace

"baki ga tare dani take bane?

Sun kuyar da kai nurse ɗin tayi

"sorry doctor Naga doka ce ba a shi.....

Be jira jin me zata Ƙarasa cewa ba ya buɗe Ƙofar ya shige

Gabanta na faɗuwa ta kutsa kanta ciki

Kwance ta hango Jikinsa duk bandeji, jikin ta na rawa ta Ƙarasa gaban gadon zuciyar ta na
wani irin rawa

"Umar!

Ta Kira sunan sa,ko motsi Be yi ba ballantana ya amsa mata, idanuwan sa na rufe ruf

Zuba masa ido tayi, gani take yi kamar baya numfashi

Cikin tashin hankali da kiɗima ta fara jijjigasa tana faɗin

"Umar ka tashi, ka tashi dan Allah, Naji na haƙura"

Har lokacin ko motsi beyi ba

Kuka ta fashe da shi tana cigaba da jijjigasa

"na roƙeka katashi, kada ka tafi ka barni Umar"

Maganar ta ya fara ji tana ratsa kunnuwan sa

Ji yike yi kamar mafarki yike yi

"katashi Umar, dan Allah katashi wallahi na haƙura"

Ta kuma faɗa

Buɗe idanuwan sa yayi da suka yi masa nawi

Dishi-dishi ya fara ganin ta

Kafin ya ganta sosai,ita ko ganin ya buɗe idon yasa ta sauke wani nannauyan numfashi

"Rauda"

Ya kira sunan ahankali

Kasa amsawa tayi kallon sa kawai take yi

"Rauda ina son ki, dan Allah ki ce min kin haƙura da abunda nayi miki, ki amsa kin yafe mini"

Zuciyar ta tsinke,janyo kujera tayi ta zauna jin jiri-jiri ya fara ɗiban ta

Ze kuma magana ta katse shi

"Umar,na haƙura ya riga da ya wuce"

Ya Lumshe idanunsa yana faɗin

"nagode"

Hannu tasa ta share fuskar ta da tayi sharkaf da hawaye

Sannan ta ƙara matsawa kusa dashi

Tana kiran sunan sa

Kuma buɗe idanuwan sa yayi ya zuba su a kanta

"kayi haƙuri da jefa ka damuwa da nayi...

Girgiza kai yayi a hankali

"a'a Rauda, sam kada ki bani haƙuri na cancan ci fiye da abunda ma kikai min"

Ya faɗa da rauninniyar muryarsa

Kaɗa kai tayi tana kuma share fuskarta gaba ɗaya jikin ta ya mutu.

Miƙewa tayi tace

"zanta fi,anjima zan dawo"

Ta Ƙarasa faɗa tana niyyar juyawa

Ruƙo hannun ta yayi,ta juyo suka zuba ma juna ido

"kar ki tafi Rauda dan Allah,ina buƙatar ganinki a kusa dani"

Ta sauke ajiyar zuciya tace
"kayi haƙuri Nima bana jin daɗi ne, anjima zan dawo"

Ya girgiza kai
"a'a ki tsaya Zayyad ya duba ki, ki tsaya tare dani please"

Hannun ta ta zame tana girgiza kan itama

"a'a akwai wacce zata duba ni"

Bata jira jin me ze ƙara cewa ba tayi gaba,tana tafiya jiri na kwasar ta

Zayyad ya tashi da sauri ya tare ƙofar

"bafa ze yuwu ki tafi cikin wannan halin ba, tunda dai har kinzo asibiti muje induba ki"

Zatai magana Zayyad ya dakatar da ita

"kada ki ce zaki yi musu Rauda, dan Allah"

Numfashi ta sauke tana kaɗa kai dan ta ƙagara ta zauna ji take yi kamar zata faɗi

Zayyad ya dubi Umar ya ce

"bari muje na duba ta yanzu zan dawo"

Umar binsu da ido yayi kawai
Suka fita, wani office suka shiga ya nuna mata kujera ta zauna

"dame-dame kike ji yana damunki?

" ciwon kai, sai jiri da kuma ƙirji"

Ya jinjina kai, sannan yayi mata gwaje-gwaje

Nurses ya kira yace suzo su sa mata drip,da kuma allurai

Dole ta haƙura suka sa mata dan tana buƙata ita ma

Ta Kira Salma ta faɗa mata,ba'a fi minti ashirin ba Salma ta zo asibitin

Da daddare,tana zaune kan gadon asibitin ta tsura ma drip ɗin ido, gani take yi baya sauri dan
kaɗan-kaɗan yike ɗiga, Allah Allah take yi ya ƙare su tafi

Zayyad ya shigo ɗakin yana yi mata ya jiki

Amsawa tayi da "dasauƙi"

Sannan ta ce
"kaɗan ƙara gudun ruwan bana so dare yayi sosai ba mu tafi ba"

Zayyad yace
"ai bayan wannan ma akwai wasu,dole tafiyar ki sai ta kai gobe da yamma saboda da alamu
kinyi ta ciwon a tsattsaye"

Salma tace
"gaskiya gwara kitsaya ki samu sauƙi Ƙawa,kiyi haƙuri zuwa goben"

"Hakan ya kamata,Shima Umar yanzu muka dawo dashi ɗakin dake jikin wannan"

Bata ƙara cewa komai ba ta kwanta,

Bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ta

Ƙarfe ɗaya na dare ta farka,a gigice

Sakamakon mafarkin da tayi wai Umar ya rasu

Lokacin Salma ta daɗe da yin bacci,zare abun ruwan tayi ta sauko ta fito

Babu kowa a harabar wurin ta windon ɗakin da yike ta hango sa

Murɗa ƙofar ɗakin tayi ta shiga ta Ƙarasa gaban gadon

Gabanta na faɗuwa ta dafa ƙirjinsa jin yana numfashi yasa ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare
zauna wa a kujerar dake gaban gadon

Ta tsura mai ido,kyakkyawar fuskar nan nasa tayi fayau, sai dogon hanci

"Umar!

Ta Kira sunan,da alamu bacci yike yi dan be amsa ba

Ta cigaba da kallon sa zuciyar ta na saƙo mata abubuwa da yawa

Tabbas ta san har yanzu tana ƙaunar sa, dan sonsa da banne acikin zuciyarta

Shine wanda ta fara so, kuma shi kaɗai ne wanda tayi ma so me tsanani

Gashi lokacin ta daɗe tana fatan zuwan sa na ranar da Umar ze ƙauna ce ta yazo, amma sai
dai kash

Aasim,ya riga da ya danne komai, dan Shima tana sonsa amma bazata taɓa haɗa son da take
yima Umar da wanda take yi masa ba

Umar ƙaunar sa daga Allah ne, dan shine ya jarabce ta

Hawaye masu ɗumi suka shiga gangaro mata

"Meyasa sai yanzu Umar? Me yasa kabari lokacin Dana daɗe ina jira ya wuce?

Meyasa?

Ta jingina bayan ta da kujerar tana runtse idanunta wasu sababbin hawayen na gangarowa

"kai ne burina, kai ne zaɓi na, kai ne wanda nayi fatan rayuwa dashi a matsayin miji na har
abada, amma kabari lokaci ya wuce dan bazan iya janye alƙawarin da nayi wa Aasim ba, bazan
iya ba!

Kuka me ƙarfi ne yaci ƙarfin ta, ta kifa kanta jikin gadon tana kuka me tsuma zuciya

Umar duk abunda ta faɗa yana ji, da fari farin ciki ne da jin daɗi ya mamaye zuciyar sa amma
Aasim da ta ambata yasa jikin sa yayi sanyi

Waye shi? Wani irin alƙawari ta ɗaukar masa da take faɗin bazata iya karyawa ba?

Yayi wa kansa tambayoyin,da bayi da amsar su

Ita ko Rauda Miƙewa tayi ta koma, ɗakin da take

Ta kwanta,har lokacin ƙaunar sa ce ke kuma bin jinin ta

Ta dafa sai tin zuciyar ta da take yi mata nawi tace

"dan Allah kada ki bari ƙaunar Umar ta kuma tasiri a zuciyar ki, Aasim shine wanda ya cancan
ce ki, shi ne ya sadaukar da rayuwar sa da komai nasa akan ki, Umar ko shine ya wulaƙanta ki
a lokacin da kike neman kulawar sa"

*** **** ****
Sunɗauki awanni suna gabzawa da manyan ifiritan, yayin da wasu daga cikin rauhanan sun ji
ciwo sosai suka kuma sare

Aasim ne kaɗai har lokacin yike fafatawa dasu,duk da Shima ya galabaitan

Sarauniyar ifiritai tana zaune kan kujerar ta tana kallon abunda yike faruwa

Sai da tagama kallo tsaf, sannan ta cewa ifiritan su dakata

Dakatawar suka yi kuwa, yayin da Aasim da sauran suka tsaya suna mai da numfashi

Gurin yayi tsit,Sarauniyar da har lokacin idanuwan ta na kan Aasim tace

"nadaɗe banga jarumi irin ka ba,sannan kuma na daɗe banga sakarai irin ka ba wanda yike
sadaukar da rayuwar shi dan kawai ya rayu da bil'adama wannan babban kuskure ne"

Aasim Shima da tun da ta fara maganar yike kallon ta yace

"a gareni Sam ba kuskure bane,kuma a shirye nike da inshiga kasadar da tafi wannan in har yin

Hakan ze ƙara min kusanci da ita"

Murmushi Sarauniyar tayi yayin da tagama duba madubin tsafin ta

"tabbas kayi kuskure me girma da ka amince da bil'adama,sannan kuma zaka yi da na sani
domin kuwa duk wannan wahalhalun da kake sha zasu tashi a banza"

Ta ɗan numfasa sannan ta cigaba da cewa

"kun aikata laifi dan kawai ku sami bayyana acikin mutane kuka shigo mana kogo kuka karya
mana doka,amma duk da Hakan jarumtar da ka nuna zata sa inyi abunda bantaɓa yi ba

Wato inbada gudunmuwa wajen karya dokar da kakannina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login