Showing 84001 words to 87000 words out of 101191 words

Chapter 29 - JINNUL AASHIQUE BOOK COMPLETE By Yar Fillo .pdf

08 Jul 2025

3179



Ta shi tayi da sauri ta ɗan ja baya kaɗan tana zazzare ido

Kallon ta umar yayi yace

"lafiya chuchu?

Girgiza kai tayi tace
" babu komai "

Ya gyaɗa kai ba tare da ya ƙara cewa komai ba

Aasim numfashi ya sauke me nawi dan sai lokacin ya ɗanji raɗaɗin da yike ji aransa ya ragu

Fulawar saƙo ce ta sauka a hannun sa ya buɗe ta

Saƙon ammi ne cewa tana son ganin sa ya same ta a iyakar shiga masarauta

Bayyana yayi a wurin, tana tsaye jikin bishiyar da suka saba haɗuwa a wurin, dan bayi da ikon
shiga masarauta tun bayan tsalle ke tauran da yayi

Kallon sa ammi take yi cike da tsananin damuwa a fuskar ta ganin yadda ya lalace duk akan
bil'adama

Cikin girmamawa ya gaishe ta, bata amsa mai ba illa zuba mai ido da tayi

Zuwa can ta kira sunan sa

"Aasim!

" na'am ammi"

Ya amsa yayin da yike ɗagowa yana duban ta

"yanzu kana ganin rayuwar da zaɓarma kanka ta dace da kai kenan?

Ta tambaya tana yi masa wani irin kallo

Ƙaƙaro murmushi Aasim yayi yace

" ammi nafaɗamiki kidena damuwa a kaina ina cikin farin ciki...

"ƙarya kake yi Aasim, dubi yadda ka lalace ka sauya kamar ba yarima ɗan babban sarki ba,da
gatan ka da komai Aasim ka zauna kana wahala akan mace macen ma bil'adama wacce tayi
maka butulci"

Ta ɗan tsaya sannan ta cigaba da cewa

"me yasa bazaka cire ta a ranka ba? Ga mata nan bila adadin a duniya Aasim zaka samu
wacce tafi ta ka dawo masarauta ka nemi gafarar mahaifin ka ka dawo cikin gatan ka inda ake

tarai-rayar ka Sam bana jin daɗin yadda nike ganin ka a haka"

Murmushin takaici yayi dan ya san ammi bazata taɓa ganewa ba, da zata gane son da yike ma
Rauda da Sam bazata rinƙa faɗin maganganu haka ba shi kansa besan dalilin da yasa yike
mata so me tsanani ba ya kuma kasa haƙura da ita

Guntun numfashi ya sauke har lokacin kansa na ƙasa

Ganin bayi da niyyar magana yasa ta girgiza kai cikin damuwa

"shikenan tunda har yau bani da matsayin da zance kayi abu kayi, nagode"

Matsowa yayi kusa da ita ya kamo hannun ta suka zauna still hannun ta na riƙe cikin nasa

Sam ya kasa danne hawayen da suka ciko kwarmin idanunsa

Cikin muryar sa me taushi yace

"ki gafarceni ammi,nasan ni me laifi ne tunda har na bijire wa umarnin ku, amma kimin uzuri dan
Allah ammi, ammi nikaɗai nasan yadda nike ji acikin raina bazan iya rabuwa da ita ba"


Ammi tausayin sa ne ya ƙara ka mata dan tasan duk abunda zesa sa kuka ba ƙaramin abu
bane

Nisawa tayi tana ajiye Gauron numfashi

"shikenan Aasim, Allah ya kawo ma mafita amma ka rage sanya ranka cikin damuwa kaji?

Gyaɗa mata kai yayi ba tare da yace komai ba

Magana tayi wa jakadiyar ta dake can gefe sai gata ta bayyana hannun ta ɗauke da shahida


Shahida na ganin sa ta faɗa jikin sa a guje cike da tsananin farin ciki

Aasim ya ɗagota cike da jin daɗin ganin ta dan tunda ya bar masarauta rabon shi da ya sake
ganin ta dan sarki ramzad ya hana a fita da ita ko ina

"shahida na!

Ya faɗa yana kallon ta, cikin murna ta ƙara shige wa cikin jikin sa

Ammi dake kallon su cikin tausayawa tace

" kullum maganar ta baya wuce ina abban ta, amma me martaba ya hana fita da ita ko nanda
can yau ma dan yayi tafiya ne Shine na samu na ɗauko ta"

Aasim yayi murmushi dan ganin ƴar tasa yasa yaji sanyi

"yaushe ze dawo ammi?


" kwana uku zeyi"

Ta bashi amsa

Aasim yace
"ammi to dan Allah Kibari in tafi da ita inyaso jibi da sassafe sai in maido da ita"

Ammi ta ɗan yi shuru tana nazari

"dan Allah ammi"

Ya faɗa cikin marai-raicewar murya

"shikenan kutafi"


Ƙarfe sha biyu saura ya dawo gida, kan kujera ya zaunar da ita ya cika mata gabanta da kayan
tanɗe-tanɗe

Sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya tasa a gaba tana ta yi masa surutu

Dariya yike yi sosai, harda riƙe ciki abunda rabon shi da yayi har ya manta

Shahida yarinya ce me wayau da basira, sai da suka kwanta zasu yi barci sannan tace

"Abi ina ammina?

Danne abunda yaji a zuciyar sa yayi da ya tuna inda take ya ƙaƙaro murmushi yace

" kina son ki ganta ne?

Ɗaga mai kai tayi, ya ɗago yace

"to gobe zan kaiki wurin ta kinji, yanzu ki kwanta kiyi barci kinji?

Murmushin jin daɗi tayi, ta kwanta a Jikinsa bata daɗe ba barci ya ɗauke ta

Sai da ya tabbatar da baccin nata yayi nisa sannan ya kwantar da ita ya tsura ma fuskar ta ido
yana jin ƙaunar ta a cikin ƙoƙon ransa

Madubin sa ya saita zuwa wurin Rauda

Tana kwance tana bacci fuskar nan tata tayi fayau kamar wacce ta yi watanni tana ciwo

A hankali yasa hannu ya shafi gefen fuskar ta cikin kalar wani yana yi na shauƙin ta, da yanzu
suna tare suna soyayya amma wannan banzan ya ruguza masa tsarin sa

Lumshe idanuwan sa yayi yana ƙissima abubuwa da yawa a cikin ransa

Ɗan murmush yayi yabuɗe idanun yana kuma ɗaura su a kanta

"Rauda ke tawa ce nikaɗai"

Ya faɗa cikin wata kalar murya



*~Ƴarfillo.~*


*JINNUL*
*AASHIQUE*
‍♂‍♂
‍♂

NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

*~We are bearer's of so golden pen~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu).*



*Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin
Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan
ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba,
sannan ya ce;*

َّمُهَّللَا يِّنِإ َكُريِخَتْس
َأ
،َكِمْلِعِب َكُرِدْقَتْسأَو ،َكِتَرْدُقِب َكُلأْس
َأ
َو ْنِم َكِلْضَف ،ميِظَعْلا َكَّنِإ
َف ُرِدْقَت الَو ،رِدْق
َأ
ُمَلْعَتَو الَو ،مَلْع
َأ
َتْن
َأ
َو ُمّالَع ،ِبويُغلا َّمُهّللا
ْنِإ َتْنُك ُمَلْعَت َّن
َأ
اَذَه -َرْم
َألْا يِّمَسُيَو ُهَتَجاَح - ٌرْيَخ يِل يِف يِنيِد يِشاَعَمَو ِةَبِقاَعَو ،ي
ِ
رْم
َأ
ِهِلِجاَع ِهِلِج
َأ
َو ُهْرُدْقاَف يِل ُهْرِّسَيَو يِل َّمُث ْك
ِ
راَب يِل ،ِهيِف
ْنِإَو َتْنُك ُمَلْعَت َّن
َأ
اَذَه َرْم
َألْا ٌرَش يِل يِف يِنيِد يِشاَعَمَو ِةَبِقاَعَو ،ي
ِ
رْم
َأ
ُهْف
ِ
رْصاَف يِنْف
ِ
رْصاَو ُهْنَع ْرُدْقاَو يِل َرْيَخْلا ُثْيَح َناَك َّمُث يِنِضْر
َأ
.ِهِب


*Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min
fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob,
allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (say your need) khayrun lee fee deenee
wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta
ta'lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee
wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.*

*Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma
ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne
Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa
wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da
kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa Ka
kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka
san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a
wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni,
kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka
sanya ni in yarda da shi".*

*Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama

a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;*

ْمُهْرِواَشَوE يِف
ِ
رْم
َألْا اَذِإ
َف َتْمَزَع ْلَّكَوَتَف ىَلَع Fِهللا


*(Washawirhum Fiyl Amri Fa'iza Azamta Fatawakkal Alallahi).*

*"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".*



Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_

AGE 3⃣8⃣

_wannan page nakine *jamila Aliyu* masoyiyar Aasim, Aasim yana yinki irin sosai ɗinnan_


_10:23_PM
Sun, Oct 27

_Bissmillahir rahmanin rahim_✍✍✍✍✍

_(mu yawaita karatun al qur'ani,mu maida al a marin mu ga ubangiji dan shi ze yi mana
maganin komai, Allah ya tsarkake zuciyar mu ya biya mana buƙatun mu amin)_


Tun cikin dare umar ya farka sakamakon wani azazzaben ciwon ciki da ya farkar dashi

Zamowa ƙasa yayi yana riƙe cikin, cikin tsananin wahala

Sai da yayi ta karanto addu'a sannan yaji cikin ya lafa masa, gumi ne kawai ke ta keto masa
duk da ac ɗin da yike ƙure kuwa

_"ya Allah ka kawo min agaji, ka fitar dani daga cikin wannan ƙangin"_

Ya faɗa a hankali,komawa yayi kan gadon ya tsura ma fuskar ta ido,ko kaɗan baya jin a ransa
cewa ze iya rabuwa da ita, ko da kuwa wannan ciwon zeyi ajalin sa ne

Shin wace irin ƙauna ce yike mata, Meyasa yike jinta a cikin jinin jikin sa?

Tabbas ita ɗin ta dabance,haka yayi ta saƙe-saƙe

Washegari jikinsa ya kuma tsanani sosai dan magana ma da ƙyar yike iya yi

Tana tsaye a gefen gadon tana kallon sa, gabaɗaya ya fita hayyacin sa zayyad ne zaune gefen
sa yana goge masa jikin sa da towel

Fita tayi daga ɗakin jin kuka na neman ƙwace mata, ɗakin ta ta shiga ta zauna takifa kanta akan
gwiwarta wasu hawaye masu ciwo suna gangaro mata

Motsi taji a gefen ta, ta ɗago kanta a hankali,shahida tagani a gefen ta

Zuba mata ido tayi taka sa ce mata komai

"ammi"

Shahida ta faɗa cikin murmushi, Rauda tayi ƙoƙarin ƙaƙaro nata murmushin tana faɗin

"shahida, kece? Waya kawo ki?

"abbi"

Ta bata amsa a taƙaice,kallon ta Rauda ta cigaba da yi tana mamakin irin kyan yarinyar

Shahida ta kwantar da kanta kan cinyar ta tana faɗin

"kullum-kullum sai na cema Ammi babba takawoni inganki sai taƙi, Ammi ina son ganin ki
kullum kice ma abi ya barni anan kinji?

Ɗan murmushi Rauda tayi tare da ɗagota tace

" kina son ki zauna tare dani shahida?

Shahida ta ɗaga kai

"shikenan Kibari nan gaba zan sa a dawo min dake nan kinji?

Cikin murna da jin daɗi Shahida tace
" to ammina"

Rungume ta Rauda tayi tana ɗan shafa bayan ta

"ina babanki?

"yana can gida yace ina gama ganin ki ze zo ya ɗaukeni"

Rauda ta gyaɗa kai

Sai bayan awa ɗaya sannan Aasim ya bayyana a cikin ɗakin

Kallo ɗaya yayi ma Rauda ya ɗauke kansa yana duban Shahida

"tuffah zo mu tafi ko?

Maƙale kafaɗa tayi
" nidai anan zan zauna"

"tuffah bakya so na kawo ki gobene? Taso mu tafi kinji?

Shahida ta marairaice fuska tana duban Rauda

"ki tashi ku tafi kinji, baki ji yace ze kawo ki gobe ba"

Rauda ta faɗa, Shahida ta mayar da kallon ta ga Aasim tace

"to abi kace ammi ta tashi mu tafi tare"

Durƙusawa Aasim yayi ya kama hannun ta yana murmushin takaici

"Shahida na anmin ki bazata bimu ba, bata son rayuwa damu kiyi haƙuri kinji"

Shahida zata kuma magana ya girgiza mata kai

"kada ki ƙara cewa komai"

Ya ƙarasa faɗa yana miƙewa tare da ɗaukar ta

Juyawa yayi zetafi batare da ya ƙara duban inda Rauda take ba

"ina son yin magana da kai"

Ta faɗa idanuwanta a kansa

Tsayawa yayi batare da ya juya ba

"inajin ki"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta zagayo gabansa

Kallon cikin ido su kayi ma juna, daga bisani ta zame nata idanun

"gobe ne zan aiwatar da abunda kace saboda na zaɓi lafiyar sa akan zamana dashi"

Ta ɗan numfasa tana ɗago idanuwanta ta kuma ɗaura su akan sa

"zan rabu dashi kamar yadda ka umar ta, amma inaso kasani bazan cigaba da yin tarayya da
kai ba, zan yi rayuwa ta ni kaɗai"

Be bata amsa ba sai da yaɓattar da Shahida zuwa can gida dan baya so yayi magana a gaban
ta

Sannan ya matso gab da ita yana kallon ta da idanuwansa da suka fara canza launi

"ni kike faɗa mawa ba zaki cigaba da yin tarayya dani ba?

Ki tuna cewa kinyi alƙawarin yin rayuwa dani har abada, dan haka baki isa ki janye wannan
alƙawarin ba ki shirya ma cigaba da rayuwa dani har zuwa tsufanki"

Be jira yaji abunda zata ƙara cewa ba ya ɓace

Dafa kanta tayi da yike mugun sarawa,ta lalubo layin anty ummi ta sanar mata halin da ake ciki
da kuma abunda zata yi

Cikin kuka take mata magana, ta ƙara da cewa

"kije gida ki sanar ma su mama dan zuwa nan da kwana uku zan taho"

Anty ummi cikin damuwa tace

"amma Rauda aganina karki aikata wannan abun,ki ƙara jira aƙara gwada na wasu malamai"

Girgiza kai Rauda tayi tace

"dan baki ga halin da yike ciki bane anty, yaufa ko magana baya iya yi, haka Allah ya so kawai"

Katse wayar tayi tana cigaba da yin kuka

Anty kaltum da ta daɗe tsaye a bakin ƙofa ta sauke numfashi tana ƙarasa shigowa cikin ɗakin

Zaunawa tayi gefen ta tace

"Rauda dan Allah ki kwantar da hankalin ki,ki dena kukannan haka dan ba maganin da ze yi
miki"

Cikin shesshekar kuka tace

"shi kaɗai yike ragemin raɗaɗin da nike ji anty"

Anty kaltum ta kuma sauke numfashi a karo na biyu

"bana so kina sawa ranki damuwa,ina da yaƙinin komai ze wuce ya zama tarihi Insha Allahu"

Kaɗa kai kawai Rauda tayi,suka yi shuru naɗan lokaci sannan anty kaltum tace

"nida zayyad mun gama shirya komai, gobe idan Allah ya kai mu sai kiyi abunda yace ɗin,
amma duk da haka ba zamu zauna ba dan ma yadda jikinna sa yayi tsanani ne da ba zaki yi
abunda yace ba,amma nan da sati ɗaya zantafi Sudan wata ƙawata ta cemin akwai wani
malami ƙwararre acan,zanje gurin sa"
Rauda ta jinjina kai kawai dan a yanzu itama maganar wahala take yi mata

Yana zaune ƙasan wata bishiya yana kallon shahida dake ta tsalle-tsallenta dan ita ta matsa sai
ya fito da ita

Gabaɗaya ya Lula cikin tunani maganar ta ce kawai take yi masa yawo a kunne


_"zan rabu dashi kamar yadda ka umar ta, amma inaso kasani bazan cigaba da yin tarayya da
kai ba, zan yi rayuwa ta ni kaɗai"_

Ajiyar zuciya ya sauke,tare da miƙewa ya kama hannun shahida

"tuffah mu tafi gida ko, kinga anfara kiran sallah"

Shahida ta ajiye sandar da take wasa da ita suka fara tafiya, sun zo wuce wa ta wani gida wata
yarinya ta watso ruwan zafi sai a ƙafar shahida

Ƙara shida ta saki, Aasim yayi saurin durƙusawa yana duba ƙafar

Ita ko wacce ta watso ruwan ko a jikinta harkokin ta ma ta cigaba da yi dan ita bata san akwai
wasu bayin Allah a wurin ba

Mahaifiyar ta dake zaune nesa kaɗan da ita tace

"wai bana hanaki zubar da ruwan zafi ƙasa bane?

Aasim numfashi ya sauke ya ɗauki shahida ya wuce

Kan kujera ya zaunar da ita yana sa mata ruwan sanyi a ƙafa

Sai da taci kukan ta sosai yana lallashin ta sannan tayi shuru

Zuwa can tace

" abi Meyasa baka yi mata magana ba, ƙonani fa tayi kuma naji zafi"

Murmushi Aasim yayi yana kama hannun ta yace

"shahida na,ki sani mu halitta ne da Muke rayuwa a ɓoye dole ne sai mun sa haƙuri a zuciyar
mu, kinga ita bata san mun zo wuce wa ta wurin ba tunda bata ganin mu,kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login