Showing 3001 words to 6000 words out of 101191 words
kwana itakadai
Bare awannan katoton gidan
Zama tayi turus gefen gado yayinda taji tashin motarsa
Tayi shuru tana tunanin yadda zatayi
Ga iskar hadari tanata kadawa
Mikewa tayi ta janyo windon dakin dayike abude iska nata kadashi
Rufe windon yayi dede da dauke wutar gidan
Kirjinta yabuga dam take matsanancin tsoro yakamata
Tayi karfin halin dawowa bakin gadon tasa hannu tana laluben wayarta
Jitayi antaba mata kafa dasauri tahaye gadon tana karanto duk addu o in da suka zo bakinta
Yarfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: JINNUL
AASHIQUE
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical
Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will
cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Aisha Ibrahim
AGE 3⃣
Dakyar ta iya lalubo wayar gabadaya firgici da tsoro sungama kamata
Hannunta na rawa takunna fitilar wayar,tahaska tsakar dakin inda takejin kaman akwai wani
atsaye
Saidai bataga kowaba,ajiyar zuciya tasauke me nawi
Tajingina da jikin gadon tana maida numfashi.
Amma idanuwanta sunkasa tsayawa wuri daya kalle-kallen dakin kawai takeyi
Azuciyarta kuma tana karanto addu'o in neman tsari.
Dai-dai lokacin akafara ruwan sama wanda yataho da karfi kaman da bakin kwarya
Hankalinta yakara tashi dantasan yadda ruwan yataho da karfi,to lallai sai anyi tsawa,itakuma
allah ya jarabceta da jin tsoron tsawa
Takurewa tayi guri daya ko motsin kirki takasa yi
Ahankali taji karar bude kofar falon sannan taji anrufe
Daga bisani tajiyo karar tafiya kamar ana haurowa saman
Babu inda baya rawa ajikinta saboda tsabar tsorata,gabadaya ta daburce
Addu'o inma sunbace mata
Inbanda ayatul kursiyyu ba abunda bakinta ke iya furtawa,itama din bata kaiwa karshenta take
dawowa farko.
Jin karar sawun tafiyan daf da kofar dakin datakeciki,yasa ta cusa kanta cikin gwiwo winta
Danbataso taga abunda ze shigo din tasan ba alheri bane
Murda kofar dakin akayi
Da karfi tafara karanta ayatul kursiyyu,amma har lokacin takasa dago kanta bare taga me
shigowar,
Jitayi andafata,takwala ihu tana fadin
"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un !
Muryar umar taji yana fadin
"lafiya madam meke faruwane haka?
Tabude idanuwanta da sauri,ganin shine yasa ta rungume sa dasauri gami da fashewa da kuka.
Zaunawa yayi tana rungume ajinkinsa
"meyake faruwane?fadamin mana"
Cikin kuka tafara magana tana girgiza kai
"bazan iya zama agidannan ba wallahi tsoro nikeji,bazan iyaba"
Yasauke numfashi yana dan bubbuga mata baya ahankali
Cikin sigar rarrashi yace
"ok..ok kiyi shuru hakanan banason kukannan please"
Saida tadan dauki lokaci sannan tadena kukan takomai sauke numfashi ahankali
Ya dagota daga jikinsa yazuba mata kyawawan idanuwansa
"chuchu,meyasa kikeda tsoro dayawane? Bakisan yawan tsoro babu kyau ba?
Ta ajiye numfashi tace
"to ba laifinka bane katafi kabarni a wannan daren,badole inji tsoro ba"
Shima numfashin yasauke
"toyanzu da bandawo ba fa?dole fa kikoyi rage tsoronnan saboda kinsan aikina,
Ana iya kirana ako wani lokaci"
Ta jinjina mai kawai sannan tace
"waima ya akayi kadawo?bakace zakaje kaduba mara lafiya bane,kuma ya akayi banji tsayuwar
motarka ba?
Yayi dan murmushi
"wallahi inazuwa natadda doctor zubairu a asibitin,yanata yima nurse din data kirana fada
Wai akanme tasan yaune natare zata kirani,shine yacemin injuyo shi zeduba marar lafiyan
Karar mota kuma ya zayi kiji?bayan kin sama zuciyarki tsoro,sannan kuma kinmanta ruwa
akeyi?
Tagyada kai
"hakane amma please jaana karka kara barina nikadai wallahi inajin tsoro sai intajin wasu
abubuwan tsoro dayawa"
yayi murmushi dayakara bayyana kyan fuskarsa
"dama koda yaushe ni inatare dake,danhaka kirage tsoro kinji"
Ta gyada kai tana nata murmushin
"tom insha allahu zan rage"
Yakwanta gamida kwanto da ita jikinsa
"chuchu ina alkawarina na jiya?
Tadanzame
"tomiye nasauri jaana,nifa takace"
Dariya yayi ya kashe fitilar wayartata
Misalin karfe uku da rabi,suna rungume da juna yana shafa sumar kanta
"chuchu allah yayimiki albarka hakika ke tadabance kinsanyani farinciki mara misaltuwa"
Murmushi tayi tanajin wani sanyi acikin zuciyarta
"jaana inasonka,kayimin alkawarin bazaka taba rabuwa dani ba"
hannu yasa yadago fuskarta suna kallon juna
Tasauke ajiyar zuciya
"hmmmmmm hakika nayi dace da miji kyakkyawa wanda samun irinsa aduniya ze yi matukar
wahala,amma ina fargaban kada watarana wata takwacemin kai"
ya girgiza kai
"bakisan irin son danakemiki ba chuchu,zan iyayin komai akanki kuma babu wacce ta isa
takwace soyayyata agareki
Maganar yimiki alkawari kuwa,nayi ada kuma ayanzu ma zankuma yimiki
bazan taba rabuwa dake ba....."
Ta lumshe idanuwanta ahankali farinciki yakuma lullubeta
Gani takeyi kamar ayanzu bata da wata sauran matsala arayuwarta
Kara shigewa jikinsa tayi bacci medadi yadauketa.
Washegari sai wajen karfe bakwai tafarka
ganin haske yagauraye dakin yasa ta kalli agogo
Karfe bakwai harda mintoci.
Takalli gefenta inda yakwanta, baya wurin
Mikewa tayi tashiga toilet tayi wanka tadauro alwala
Ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar ta ninke dardumar tanufi wardrop tanajin jikinta
nayimata tsami dan gabadaya ciwo yikeyi.
Riga doguwa tadauko tasa,sannan tasauko daga saman dantasan yana kasan
Saidai bataganshi a falon ba,taduba kicin nanma baya ciki
"ina yaje"
Tayi wa kanta tambayar
Zuciyarta ce tabata amsa
"kila yaje siyomuku abun kari ne"
Tagyada kai dantasan baze wuce hakan ba
Falon tadawo tazauna adaya daga cikin kujerun
Tadanna kiran numban mama
Ringing biyu tadauka suka fara gaisawa.
Kwan-kwasa kofar akafara yi
Tamike da wayar akunnenta tabude
Umar ne tsaye rike da rigarsa ta likitoci
Suka sakarma juna murmushi
Katse wayar tayi tanacewa
"ina kwana"
Ya janyo hannunta tafada kan faffadan kirjinsa
"wayace miki haka ake tarban miji?kintsaya daga nesa kina wani cewa ina kwana"
Tayi kasa dakanta cike da jin kunyarsa
Suka karasa cikin falon yana rike da ita
A three seater suka zauna,ya ajiye rigar ahannun kujera yanacewa
"wallahi nagaji kokadan jiya ban runtsa ba,amma nasan ke barcinki kikai harda munshari"
Megadi ne yayi sallama
Ya miko ya miko wani kwando cike da kayan karin kumallo yace anty kaltum ce ta aiko dashi
Umar yamike
"kinga jera abincinnan akan dining bari in watso ruwa"
Tadauki kwandon ta kai kan dining din ta jejjera komai,tazauna tana jiransa.
Befi minti goma da shiga ba yafito sanye da three-quater da T-shirt
Yazauna a kujerar dake fuskantarta suka fara karyawa yana janta da fira
"shine ko kitambayeni ya me jiki ko?
Yafada yana kai kofin tea bakinsa
"yihakuri yanzu nike shirin intambayeka"
Ya gyada kai
"ook ai bawan allahnnan ya jigata dayawa motarsa karkashin traler fa tashige da kyar muka iya
ceto ransa danni banyi zaton ma zeyi rai ba"
Tadakata daga kurban tea din datakeyi tana kallonsa dan bata fahimci abunda yike nufi ba
Shima kalonnata yayi ganin takafashe da ido yasa yace
"yadai?naga kinayimin wani irin kallo,kamar bakigane abunda nike cewa ba"
Ta jinjina kai
"to gani nayi ba kai kayi aikinnan ba,doctor zubairu ne yayi amma kana cewa da kyar kuka ceto
rayuwarsa
Kallon rashin fahimtar shima yafara yimata
"bangane ba,wani doctor zubairu kuma?
"doctor zubairu na asibitin ku mana"
Tabashi amsa atakaice
Yagyara zamansa yana maida hankalinsa akanta
"wai wani doctor zubairun kike magana akansa?
Doctor zubairun da watansa biyu kenan a kasar china"
Takauda idanuwanta akansa,tamaida kan wayar ta, tana duba sakon da aka turo mata
"to nidai bansani ba,kaida bakinka jiya kace doctor zubairu yace kadawo gida bekamata kafita
aiki a daren jiya ba"
Har lokacin idanuwansa nakanta
"ayaushe nace miki hakan?
"a jiya da kadawo mana"
Tabashi amsa cikin kosawa da zancen dan dan tafahimci so yike yamaida abun wasa
"nifa bandawo gidannan jiya ba"
Yafada
Tadago kanta daga kan wayar suka hada idanu
"mekace?
Ta tambaya dan tabbatar da jin abunda yace
"nace bandawo jiya bani,tunda mukai natafi asibiti bandawo gidannan ba sai a safiyarnan"
Ganin fuskarsa ba bu alamar wasa yasa tace
"wai meyasa kaketa wasu maganganu da bangane bane,jiya bakadawo ba,misalin shabiyu da
rabi?
Ta girgiza kai
"saidai in mafarki kikayi danni lokacin ma ina emergency room"
Ta gyada kai
"dan allah kabar wasannan haka"
Hannunta yakama
"kedai zancema wa kibar wasan haka,nida na kwana asibiti zaki wani ce wai nadawo
gida...........
Takatse shi
"jaana please wasan ya isa haka"
Ya jingina bayansa da kujerar dining yana kallonta
"chuchu i'm serious saidai in mafarki kikayi amma ni wallahi bandawo gidannan ba"
Jin yayi rantsuwa yasa gabanta yafara faduwa
"jaana harda rantsuwa?
Ya jinjina kai
"to nafadamiki mafarki kikayi baki yarda ba.......
"to dawaye na kwana jiya?
Takatsesa da sauri
"kwana kuma?banganeba"
Ta jinjina kai yanayinta yafara komawa na firgici
"jaana wallahi jiya kadawo kacemin doctor zubairu ya amsheka,kuma tare dakai muka kwana."
Wani kallo yayimata gami da cewa
"kidawo hankalinki please,ban kwana agidannan ba..............
Yarfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: JINNUL
AASHIQUE
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical
Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will
cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Aisha Ibrahim
Wannan page din nakine anty nabila ina godiya da kokarinki gareni allah yabar zumunci
AGE 4⃣
Dire kofin tayi,ranta yadan soma baci,akanmene yikeso yayi mata wasa da hankali?
"wai meke damunka ne? Indawo hankalina kamar yaya?tayaya munkwana dakai zaka cemin
kai ba a gidannan kakwana ba........
Buga teburin yayi dan shima nashi ran yasoma bacin
"nace miki a asibiti nakwana!
Jikinta yasoma bari,zuciyarta tafara rawa
Zagayawa tayi inda yike ta durkusa tadafa gwiwowinsa
"jaana kasan bama irin wasannan ko?dan allah kafadamin dagaske ne baka kwana agidana?
Wani irin kallo yikemata nawacce tafara tabuwa
"chuchu wallahi a asibiti nakwana......
matsawa tayi arazane idanuwanta suka cicciko
Cikin rawar murya tace
"inna lillahi wa inna ilaihi ra'ji un.......
Kallonta kawai yikeyi
Maganar malan ce tadawo mata
"kirike wannan lemun tsamin kitabbatar dakin shiga dashi cikin gidanki
Aranar da kika kwana daya kibude kullin da lemun tsamin ke ciki
Idan kiga yananan akalarsa to tabbas munyi nasara a wannan aikin da mukayi na karshe
Idan kuma kiga yacanza kala zuwa ja,to tabbas akwai matsala
Wannan lemun tsamin yana dauke da magunguna masu karfin gaske kitabbata kinshiga dashi"
Mikewa tayi dasauri tafara hawa step dagudu
Tanajin umar yana kiranta bata tsaya ba,harsaida tashiga bedroom dinta
Handbag din ta tadauko ta zazzage kayan dake ciki
Hannunta na rawa tadauki kullin lemun tsamin tafara kwancewa
Gabanta nafaduwa
Saidai me,tana gama kwance kullin taga lemun tsamin yayi jawur
Ihu takwala ta wurgar dashi
Dai-dai lokacin umar yashigo dakin
"chuchu me kikeyi ne wai.......
Kankamesa tayi dasauri jikinta narawa
"Aasim!Aasim!"
Yadagota dasauri
"Aasim kuma?
Cikin kuka tafara cewa
"nashiga uku jaana Aasim yanatare dani haryanzu,wallahi jiya ba mafarki nayi ba shi yazomin a
suffarka.........
Kamata yayi suka zauna akan gadon yakura mata ido yana karantar yanayinta
"Aasim chuchu?ba malan yace anriga da ankullesa a kwalba ba?
Ta jinjina kai dasauri
"haka yace amma lemun tsamin dayabani yacanza kala kuma.....kuma jiya inatajin anatsoratani
sannan yazomin asuffarka"
Rungumeta yayi yana shafa bayanta
"okay,okay,kwantar da hankalinki please bari inkira wayar malan din"
Yazaro wayarsa daga aljihu yadanna numban malan saidai kira biyu yana masa bedauka ba
Yakuma danna kiran a karo na uku,saida takusan tsinkewa sannan aka daga
Yayi sallama yana fadin
"ina kwana malan,antashi lafiya?
Daga can bangaren wani ne ya amsa
"ba malan bane,malan allah yayi masa rasuwa jiya da daddare yanzu haka muna shirin kaisa
makwancinsa"
"inna lillahi wa inna ilaihi ra'ji un,ya rasu?hatsari yayi kome?
daga can bangaren ya amsa
"wallahi lafiyarsa lau ya kwanta saidai dubawa akayi akaga yarasu"
Ajiye wayar yayi yana share gumin da ke keto masa a goshi
Itako kuka tafashe dashi tana fadin
"wayyoh allah na,nashiga uku!!
Be hanata kukantaba,zura mata ido kawai yayi zuciyarsa cike da damuwa
Da tarin fargaba,me yike shirin faruwa da sune?
Jiyayi kansa yayi wani dum
"la ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin"
Bakinsa ya furta ahankali
Sannan
Ya kira sunanta a sanyaye
"Rauda.....
Sanin kankine kukannan ba bu maganin da zemana face yajanyo miki ciwon kai,
Kiyi shuru kidaina kukan haka,munemi mafita......
Dagaowa tayi tana kallonsa da jikakkun idanunta
"mafita?a ina zamu samo mafitar jaana?gurin malan isah ne kadai muka sa ran zamu sami
mafita,
Amma gashi,sanadiyyar taimakona har ya rasa ransa nasan.......
Ya girgiza kai
"malan kwanan sa ne yakare,kuma na tabbata zamu samu waraka awani gurin.
Abinda nikeso dake,ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta jinjina mai kai kawai amma ita kadai tasan tashin hankalin datake ciki.
Shima din dauriya yayi kawai amma zuciyar sa cike taf da da damuwa.
Yarasa wani irin al'amarine wannan me cike da rudani
Ya kalli fuskarta,tayi kuka harta gaji bacci yadauketa.
Kwantar da ita yayi
Ya mike,yana zagagaye acikin dakin yana tunanin ta inda ze bullo ma al'amarin
Itako Rauda mafarki takeyi cikin barcinta,malan isa tagani zaune yana lazumi
Saiga hayaki yafara shigowa dakin dayike,kan kace kwabo jijiyoyin wuyansa sun
mummurde,idanuwansa sun kakkafe
Zuwa can taga yazame kasa,alamun numfashin sa yadauke
Dariya taji anfara yi me tsoratarwa daga bisani taga wani farin saurayi yabayanna
Dariyar ya cigaba dayi,lokaci daya kuma ya murtuke fuska kamar bashi yagama yin dariyar ba.
Yakalli malan isa yana nuna sa da da yatsa
"kallesa,wai shi ze ja dani,ni Aasim"
Ya girgiza kai yana cigaba dacewa
"bazaka iya ba! Bazaka iya ba!
Na gargadeka tun farko amma kayi taurin kai kana ganin kaman zaka iya ja dani......"
Yadan durkusa sai saitin malan isan
"tashi mana! Tashi kaciga ba da aikin da kakeyi.........bazaka iya ba,bazaka iya ba ko?
Ya mike tsaye yana cigaba da yin dariyar sannan ya dubeta da razanannun idanunsa
"kinsa nayi abunda ban taba yi ba,tunda nike aduniya bantaba kisa ba
Amma gashi sanadinki kinsa nafara,kinsa naka sheshi.......
Yakara sa fada idanuwansa na kuma runewa
"Kiyi babban kuskure a rayuwanki,da kika karya sharuddan dana gindaya akanki
Mafi girman kuskuren da kikayi kuwa,shine dakika bari na kusanceki azahiri..."
"kisani daga yanzu kinrabu da farin ciki,kwanciyar hankali sannan abunda zance miki na karshe
shine
Idan har kinason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki dan duk ranar daya yi
hakan to tabbas ze mutu kamar yadda wannan ya mutu!!!!!
Yakara sa fada yana nuna malan isa sannan yakuma fashewa da dariya
A razane tafarka jikinta nabari
Umar dake ta patrol acikin dakin yadawo bakin gadon dasauri
Rirrikesa tayi tana waige-waige
"shine yakashe shi,wayyoh allah na!!!
Bayi da bukatar tambayarta dan yasan mafarki tayi
Rungumeta yayi kawai,azuciyarsa yana jin tausayinta
"dan allah kada kabarni koda na minti dayane,cutar dani zeyi"
Tafada jikinta na kakkarwa
Ya jinjina kai
"zan kasance tare dake,akodayaushe,babu abunda zesameki da izinin allah"
Yarfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: JINNUL
AASHIQUE
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical
Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will
cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little Hajjo
*_A kullum forum dinmu Kara bunk'asa yakeyi,mutanen cikinsa Kara basira da fasaha
sukeyi,ina jinjina ma golden writters Allah yabar zumunci a tsakaninmu_*
_GAISUWA Ga *MATAN K'WARAI* group *yar fillo* na godiya da addu'o inku gareta,ina Kuma
Jin dadin yadda kuke yaba labarina,ina godiya sosai_
AGE 5⃣
Hannunsa takama,Tana kallonsa da jik'akk'un idanuwanta da suka yi luhu-luhu
"Jaana,kayi min alkawarin duk rintsi bazaka taba rabuwa Dani ba,nasan matsala yanzu muka
fara ganinta......
Ya sauke numfashi Yana kallon cikin idanuwanta
"Chuchu kina tunanin akwai abunda ze bani tsoro har yasa nai tunanin rabuwa dake?”
Ya girgiza Kai sannan yaciga ba da cewa
"Son Dana ke yimiki,ba k'aramin so bane,kuma bana tunanin akwai abunda ze razanani
akanki,nasan yayi hakane Dan yasanya shakku da fitina atsakaninmu Amma ni ina k'aunarki
Kuma ko me zeyi sai dai yayi Amma tarayya dake yanzu nafara Kuma ashirye Nike da indauki
duk wani abun da zezo dashi"
Ta maida kanta kan k'irjinsa,tanajin zuciyarta babu dadi
"Nasan zaka iya jure komai,Amma ina Jin tsoro,nafi kowa sanin waye Aasim,abunda ze iya?da
abunda baze iya ba.
Nasan ze iyayin komai domin yaga yarabani da kowa,baze cutar Dani ba,ina da tabbacin hakan