Showing 39001 words to 42000 words out of 101191 words
Ko kasaketa karabu da ita,ko kuma ka bar masarautar gabad'aya"
"Abi ni d'anka ne,kaji tausayina........
Sarki Ramzad ya katsesa
"Tunda ni amatsayina na mahaifinka ban isa inbaka umarni kabi ba,yazamar min dole ind'auki
hukunci akanka,dan haka fad'i ina jiranka,wane kazab'a"
Yak'arasa fad'a cikin d'aga murya
"abi,kayi hak'uri ka gafarceni........
"Nace kazab'a d'aya ko?
Sarki Ramzad ya katsesa a fusace
Kallon Rauda yayi wacce gabad'aya itama hankalinta ya gama ta shi
Ya maida kallonsa ga me martaba da yike cewa
"Zan irga uku,idan har na irga uku baka saketa ka rabu da ita ba,to tabbas zaka bar min
masarauta"
"D'aya.....
Biyu........
Cikin tashin hankali Aasim yace
"Abi dan girman allah.........
Sarki Ramzad ya d'an dakata yana jiran jin abunda zece
Amma kuma sai yayi shuru,yana cize leb'ansa da k'arfi tare da runtse idanuwansa
"Uku"
Me martaba yafad'a,ammi ta taso da sauri tana jijjiga Aasim
"Aasim,kadawo hayyacinka,takan mace,macen ma bil'adama zaka zab'i rabuwa da ahalin
ka,maza ka rok'i gafarar mahaifinka ka aiwatar da abunda yace"
Tafad'a a zafafe cikin kid'ima
Bud'e idanuwan sa Aasim yayi yana zuba su akanta
"Ammi kigafarceni,bazan iya rabuwa da ita ba..."
Yafad'a cikin zafin zuciya
Ammi baya tafara ja tana girgiza kai
"Aa,aa, Aasim kada kayi min haka"
Abu saima ne ya mik'e shima cikin tashin hankali dan betab'a zaton Aasim ze zab'i barin
masarautar akan Rauda ba,ga saima can tana kukan inda babu shi bazata iya rayuwa ba,kuma
shi yayi hakanne dan sama ma y'arshi farin ciki dan yasan idan Aasim yarabu da Rauda dole ze
auri saima
"Yarima kasan hukuncin duk wanda ya zab'i barin masarauta kuwa? Dole fa sai ka bi ta tauran
(Tauran wani wurine zagayayye,da yike da k'unci da zafi, Wanda duk bayan minti biyu yike fitar
da wani k'ara me kama da sautin tsawa,wanda duk wanda yike ciki sai hucin k'arannan ya
tsattsaga jikinsa)
Abu saima ya cigaba da cewa
"Wanda sanin kankane sai rauhan yatsaya acikin tauran har sai ya tsallake k'arar tauran guda
arba'in da tara,shin kamanta da azabar dake cikin tauran ne?
Aasim yayi masa wani kallo me cike da tsana dan inba da din munafuncinsa ba da yanzu
wannan abubuwan basu faru ba
"Nasani,kuma na amince ko da hakan zeyi sanadiyyar rasa rayuwata ne"
Gabad'aya fadar zaro ido sukayi cike da al'ajabi
Rauda da jikinta ya gama mutuwa hawaye suka gama wanke mata fuska saboda tsananin
tausayin Aasim,shin wani irin so yike mata da ze zab'i rabuwa da ahalinsa saboda ita?
Cikin kuka ta matsa kusa dashi tana fad'in
"Aa Aasim,kada ka bijirewa umarnin iyayenka akaina"
Girgiza kai yayi yana kallonta da idanuwansa da suka rine
"Rauda ina k'aunar ki,zan iya hak'ura da komai inhar zan rayu dake"
Sarki Ramzad da jikinsa yagama yin sanyi duk da b'acin ran dayike ciki kukan d'annasa na tab'a
masa zuciya
"Na baka daganan zuwa gobe,kaje kanatsu kayanke wa kanka abunda yafi maka,wannan ne
adalci na k'arshe da zan maka
Idan har ka amince da rabuwa da ita,to kazab'i ko y'ar sarkin wace k'asa ce zan aura ma ita
Idan kuma har kakai goben kana kan bakanka na k'in rabuwa da ita to tabbas zaka bar min
masarauta
Sannan kuma zaka tsallake tauran ninki biyu, d'aya na barin masarauta d'aya kuma na jayayya
dani"
Bubbuga k'ofar da akayine ya sa Rauda ta tashi,akan gadon mama ta ganta
Tana jiyo muryar maman tana cewa
"Kitashi kiyi sallah"
Dafa kanta tayi da yike sarawa kamar ze rabe biyu tana girgiza shi
"Aasim,kada kayi haka dan Allah"
Y'arfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONí ½í²«í ½í²«í ½í²«~*
*~â„We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u
np pain~*
*í ¼í¼¹JINNUL*
*AASHIQUE*í ¼í¼¹
í ¾í·žâ€â™‚ í ¾í·žâ€â™‚
í ¾í·žâ€â™‚
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_í ¾í·•í ¼í¿»
_Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu_
í ¼íµ¿AGEí ½í³• 1⃣6⃣
Ina yima É—aukancin masoyana barka da sallah, dafatan anyi sallah lafiya, wannan Page na
baku shi amatsayin barka da sallah, sannan ina me baku haƙuri akan jina shuru da kuka yi bani
da lafiya ne ina buƙatar addu'arku
_7:32_í ½íµ’ PM
FRI, JUN 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_
"Aasim kada kayi haka,kada kayi haka dan Allah"
Tafad'a cikin tsananin damuwa
Bubbuga k'ofar mama ta kuma yi akaro na biyu
Cikin rashin k'warin jiki ta mik'e jiri na d'ibarta,ga kanta da yayi mata mugun nawi tana jin kamar
an d'aura mata gingimemen dutse
Ta zare sakatar falon tana jingina da bango da sauri,dan ji tayi tana neman fad'uwa
Mama ta kalleta sosai tace
"Haryanzu kan bedena ciwon bane?
D'aga mata kai kawai tayi batare da tayi magana ba
Mama tasauke numfashi cikin damuwa tace
"Sannu,ina ganin idan gari yayi haske kawai zamu je k'aramin asibiti adubaki, k'ilan harda
typhoid,kidaure kiyi sallan"
To Rauda tace tafito ta d'au buta tayi alwala,tana rawar sanyi
Lokaci d'aya zazzab'i me zafi ya rufeta,
A gaggauce tayi sallar saboda sanyin datake ji sosai,tana idar da sallar ta koma kan gado ta
lullub'e
B'angaren Aasim kuwa,tunda taron fada ya tashi,yashige d'akinsa tare da kullewa dan
gabad'aya baya son a damesa
Yana jiyo muryar ammi daga bakin k'ofar tana fad'in ya bud'e
Amma yak'i saboda baya son yaga tashin hankalin dake tare da ita,harta gaji ta wuce
Ya na zaune a k'asa kawai, cikin tsananin tashin hankali
K'wan-k'wasa k'ofar aka kuma yi,yaja gajeren tsaki tare da kifa kansa
Daga can k'ofar d'akin muryar mus'ab yaji Wanda ya kasance babban amininsa
Hannunsa ya d'aga yayi nuni da k'ofar, tabud'e
Mus'ab ya shiga d'akin Yana fad'in
"Wai meke damunka ne Aasim? Ace tun daren jiya ka kulle kanka a d'aki kakuma sawa d'akin
takunkumi tayadda bawanda ze iya shigowa"
Aasim numfashi ya sauke yana d'auke kansa da ga kan mus'ab
"Kawai banaso a dameni ne,ina buk'atar natsuwa ne"
Mus'ab ya jinjina kai yace
"Hakan yayi kyau,inafatan a natsuwar da kasamu ka canza abunda ke zuciyarka,
Dan nasan jiya kana cikin rud'ani ne,shiyasa kak'i yin abunda me martaba ya umarce ka"
Aasim Ya sauke gauron numfashi tare da lumshe idanuwansa wad'anda suka kad'a sukayi ja
Mus'ab ya gyara tsugunnuwar da yayi yana k'ara fuskantar Aasim d'in
"Kayi shuru,ba kace komai ba,ko haryanzu kana kan bakannaka?
Ya bud'e idanuwansa yana d'aura su akan mus'ab
"Mus'ab,bazan iya rabuwa da ita ba,bazan iya ba"
Yafad'a cikin wani irin yanayi
Zaro ido mus'ab yayi yana kallonsa cike da mamaki
"Mekake nufi Aasim?kana nufin kazab'i rabuwa da ahalinka,takan bil'adama?
Yad'an numfasa sannan ya cigaba da cewa
"Ni wallahi banga abunda kagani agurin waccan bil'adamar ba,da yasa gabad'aya ka rikita
tunaninka,
Dan allah kadawo cikin hankalinka,akwai kyawawan mata aduniya,ga kuma saima..........
Katsesa yayi ta hanyar d'aga masa hannu
"Dan allah kada ka k'ara b'ata min Rai,ni ita nike so kuma ita na zab'a zanyi rayuwa da
ita,abunda nagani da ya rikita min tunani akanta kuma
Wannan ba damuwar ka bane,idan zaka bani shawara a matsayinka na aboki na kabani,idan
kuma maganganun banza kazo kafad'a min ga hanya"
Ya k'arasa fad'a yana nuna mai hanyar fita
Mus'ab ya sauke ajiyar zuciya cike da juyayin al'amarin abokinnasa
"Aasim nikake fad'a ma haka?
Aasim ya d'aga kai yace
"To mekake so ince maka? A matsayinka na aminina kamata yayi kabani shawarar yadda zanyi
insamu mafita amma kazo kana fad'a min abunda kasan ze k'ara min b'acin ran danike ciki"
Mus'ab yakuma sauke numfashi yana kad'a kai
"Shikenan,allah ya baka hak'uri"
Yafad'a yana mik'e wa ze fita
Sannan yace
"Bazan takuraka ba,akan fasa abunda kayi niyya,amma ina me baka shawara da kada ka
bijirewa umarnin mahaifinka,katuna da haihuwar ka da yayi,da kuma rainonka har izuwa
girmanka ko ba komai yaci wannan arzik'in "
Yana gama fad'ar haka ya fice
Doguwar ajiyar zuciya Aasim ya sauke tare da jinginar da kanshi
Tabbas yasan abunda yike shirin yi ba dai-dai bane,to amma ya zeyi? Ya zeyi da muradin
zuciyarshi?
Ya runtse idanuwansa yana hango kyakkyawar fuskarta
"Bazan iya rayuwa babu keba *Rauda*"
Yafad'a tare da furzar da wata iska me zafi
Mik'ewa yayi yana fad'in
"Nasan zaka fahimceni abi,idan nak'ara yimaka bayanin yadda nike jinta a cikin zuciyata"
B'acewa yayi,be bayyana a ko ina ba sai abakin falon sarki inda yike hutawa
Kallo d'aya yayima kuyangin dake tsattsaye bakin k'ofar ya kauda kai tare da cewa
"Ku isar da zuwa na"
D'aya da ga cikinsu wacce take daf da k'ofar tace
"Yarima Aasim na buk'atar iso ranka shi dad'e"
Tafad'a cikin d'aga murya
Daga ciki aka basu izinin su bud'e k'ofar
Suka bud'e suna rusunawa
Gabanshi na fad'uwa ya shiga k'asaitaccen falon da akayi masa ado da zinarai kala-kala
Sarki Ramzad na zaune kan wata kujera me d'an fad'i ya jingina idanuwansa a lumshe
Shigowar Aasim d'inne yasa ya bud'e idanuwansa yana zubasu akansa
Cikin ladabi Aasim ya rusuna yana fad'in
"Barka me martaba,ina fatan kana cikin k'oshin lafiya"
Sarki Ramzad ya ce
"Lafiya,Ina fatan kaima haka?
Aasim yace
"Nima ina lafiya"
Sarki Ramzad ya gyad'a kai yana kauda kansa daga kallonsa
"Me ke tafe dakai?
Aasim ya d'an yi shuru sannan yace
"Inason magana dakai ne"
Jinjina kai sarki Ramzad yayi yana yima wazirin sa nuni da hannu alamar yafita ya basu guri
Cikin girmamawa wazirin ya rusuna tare da b'acewa
Sarki Ramzad ya maida hankalinsa kan Aasim yana cewa
"To ina jinka,fad'amin abunda kayanke ko sai munje fada tukunna?
Aasim ya sauke numfashi yana mik'e wa ya k'arasa gaban sa
Ya durk'usa tare da d'aura kansa a kan k'afafuwan mahaifinsa
Wasu hawaye masu zafi suka shiga gangarowa daga idanuwansa
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare dasa hannunsa yadafa bayan sa
Tabbas babu abunda yi keso sama da Aasim, yana matuƙar jinsa acikin zuciyarsa
Kuma babu abunda yafiso irin yaga Aasim cikin farin ciki
Amma dole ne ya dakatar dashi
Cikin kwantar da hankali yace
"Aasim, ka sani bawai na hanaka abunda kake so bane, dan jin daÉ—ina
A'a, saboda adalci ne, domin babu wani rauhani daya isa yayi haka a ƙyalesa, Kaga ko
bekamata na ƙyaleka ba dan kana ɗan dana haifa
Kasani da zarar akace babu ni, to kaine mai mulkin wannan masarautar
Ya kamata ka fahimce ni, nayi maka alƙawarin ko ƴar gidan wacece idan Kaga tayi maka zan
auramaka in har a jinsin ka ce
Amma baze yuwu in barka ka cigaba da rayuwa da bil adama ba bazeyu ba"
Aasim ya É—ago kansa cikin muryarsa da ta dishe yace
"Abi,dan Allah kabarni nayi rayuwa tare da ita,ita kaÉ—ai nike so banajin zan iya rayuwa da wata
mace a duniya in ba ita ba........
" dakata!
Sarki ramzad ya katse sa, sannan ya cigaba da cewa
"nabika ta faÉ—a bakaji ba, na bika ta lallami nanma bakaji ba
To kasani bazan takura ka ba, tunda har ban isa dakai ba, nan da awa É—aya zamu je fada, duk
abunda kayanke kafaÉ—a acan"
Aasim ze kuma magana ya dakatar dashi ta hanyar É—aga masa hannu
"bana son na kuma jin komai daga gareka, tashi ka bani wuri"
"Abi.....
Be ƙarasa ba, sarki ramzad yasa hannu ya ɓatar dashi
Ƙarfe takwas suka isa ƙaramin asibitin gwamnatin, sun tadda mutane da yawa akan Layin ganin
likita
Hakan yasa suka zauna suna jiran layi yazo kansu
Kallo É—aya zakama Rauda, kagano ramar da tayi acikin kwana É—aya kacal
Kallon jama'ar dake wurin kawai take yi amma zahiri hankalinta baya gurin
Damuwarta ta kuma ƙaruwa yayin da taga har zuwa lokacin bata ji wani alamun Aasim ba,
Me ya faru dashi, bayan dawowarta? Shin ya amince ya rabu da itanne ko yaya?
Tambayar da tayi ma kanta kenan wacce bata da amsar ta
Maganar sa ce ta dawo mata
_"Rauda ina ƙaunarki, zan iya haƙura da komai inhar zan rayu dake"_
"baze amince ya rabu dani ba nasani"
TafaÉ—a a fili batare da tasan maganar ta fito filin ba
Mama dake zaune kusa da ita ta kalleta cikin rashin fahimta tace
"mene?
Kallon maman tayi itama cikin rashin fahimtar
" waye baze amince ya rabu dake ba?
Mama ta jefo mata Tambayar tana kafeta da ido
Daburcewa Rauda tayi, dan ita bata san maganar da tayi a zuciya ta fito fili ba, ta rasa me zata
ce
Numfashi mama ta sauke tana kaɗa kai, lokacin layi yazo kansu tamiƙe tayi gaba batare da ta
kuma cewa komai ba
Rauda tabi bayan ta, gwajin farko da likita yayi ya gano BP ɗinta yayi ƙasa sosai
Kallon ta yayi yana cewa
"meke damunki? Da BP ɗinki yayi ƙasa haka?
Shuru Rauda tayi, likitan ya cigaba da cewa
" BP ɗinki yayi ƙasa sosai, shi yasa kike jin ciwon kai da kuma jiri, zan rubuta miki magunguna
Asiya kisha, sannan kidena barin kina shiga cikin tunani Allah ya ƙara lafiya"
Mama ta amshi takaddar maganin suka, fito kowanne zuciyarsa babu daÉ—i
Napep suka hau ta kawo su gida suna gab da tsayawa taji maganar Aasim
_"kisameni a bayi yanzu"_
ko tsayawa bata bari mai nepep É—in ya gama yi ba ta diro
Cikin faÉ—a mama tace
"wani irin ganganci ne wannan? miye kikema sauri da ba zaki tsaya yagama tsayawa ba?
Cikin sauri Rauda tace
" bayi nikeso na shiga"
guntun tsaki mama ta ja,tana zage Jakarta zata ba mai Napep É—in kuÉ—i
itako Rauda ta ƙagara tagansa,juyawa tayi da sauri ta shige cikin gidan
Ko buta bata tsaya É—auka ba ta shiga bayin
A tsaye tagansa,rufe ƙofar bayin tayi da sauri tare da ƙarasawa inda yike
"Aasim, kana lafiya? Me ya faru na jika shuru? Ince dai ba wani abu a kayi maka ba?
Ta jero mai tambayoyin cikin zaƙuwa da son jin abunda ta tambaye sa
Be bata amsa ba, illa rungumeta da yayi,yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya
Ita É—inma ajiyar zuciyar ta sauke, tana jin sonsa na bin duk wani sassa na jikin ta
"kabani amsa mana Aasim"
ÆŠagota yayi ya zuba ma fuskar ta ido amma kuma har lokacin beyi magana ba
Kawai yana hango yadda za ace yayi rayuwa babu ita ne
Girgiza kai yayi yana ƙara rungumeta sosai
"baze yuwu ba, baze yuwu ba"
YafaÉ—a cikin tsananin damuwa
"miye baze yuwu ba, kayi min magana yadda zan fahimta dan Allah"
Kuma ÆŠagota yayi yasa hannayensa duka biyu ya tallabo fuskarta yace
"Rauda inaso kiyimin alƙawarin cewa ba zaki taɓa rabuwa dani ba,har ƙarshen rayuwarki"
Kallon sa ta keyi sosai,
"Aasim kasani ai, bazan iya rabuwa dakai ba"
Girgiza kai yayi, yace
"nasani a yanzu, amma bansan meze iya faruwa nan gaba ba, shi yasa nikeso kiÉ—aukar min
alƙawari da kanki da kuma bakinki"
KaÉ—a kai tayi tare da cewa
"shi kenan nayi alƙawari bazan taɓa rabuwa da kai ba"
Gauron numfashi ya sauke yana gyaÉ—a kai
"nagode, wannan alƙawarin da kika ɗauka a yanzu ya kuma ƙarfafamin gwiwa,zanje in sanar
dasu abunda na yanke"
"amma Aasim, bekamata.......
Katseta yayi
" kinga Rauda kada kice komai,na san watarana zamu dai-daita dasu, amma ke bazan iya jurar
rashinki dai-dai da rana É—aya ba"
Be jira jin mezata ce ya ɓace
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi, tare da fitowa daga bayin, É—aki ta shiga ta zauna akan gado
Maganar daya faÉ—a ce kawai take yi mata yawo a kunne
_"kinga Rauda kada kice komai nasan wata rana zamu dai-daita dasu amma ke bazan iya jurar
rashinki dai dai da rana É—aya ba"_
Sauke ajiyar zuciya tayi, ta janyo filo ta É—aura kanta
Meyasa ze zaɓi rabuwa da ahalinsa saboda ita? Me yasa?
Tayi wa kanta tambayar
Lumshe idanuwan ta tayi, tana fatan ace har yanzu Mafarki take yi
Dan har lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa
Æangaren Aasim kuwa, lokacin da ya koma masarauta saura Æ´an mintoci a tafi fada
Yana zaune a ɗakinsa ya zuba tagumi, fulawar saƙo ta shigo ɗakin
Hannu yasa ya damƙe, saƙon ammi ne tana son ganin sa
Kamar baze je ba, sai kuma yaga rashin dacewar Hakan
Miƙewa yayi ya bayyana a ƙofar sashenta
"ku isar da zuwa na"
Yace ma kuyangin dake bakin ƙofar
Tun kan su kai gayin magana aka basu izinin buÉ—ewa
Shiga yayi da sallama yana rusunawa
Ammi tayi ma jakadiyarta nuni data fita sannan ta dawo da kallon ta kansa
"Aasim ni kake wulaƙantawa ko? Ace tun jiya nikeson yin magana da kai amma ka sawa
Æangaren ka takun kumi ko?
Ƙasa yayi da kansa