Showing 75001 words to 78000 words out of 101191 words

Chapter 26 - JINNUL AASHIQUE BOOK COMPLETE By Yar Fillo .pdf

08 Jul 2025

3173

kuma halicce shi, ubangiji
shike da iko akan duk kanmu, dan haka babu abunda ya isa ya mana wanda Allah be yi mana
ba, akwai wani babban malami da na sani zan faɗa masa nasan ze iya ɗaukar mataki a kansa

Amma kicire fargaban cewa ze raba mu, dan wallahi babu wanda isa ya raba ni dake sai Allah"

Kallon sa kawai take yi amma ta kasa ƙara furta komai

Yayi mata murmushin ƙarfafa gwiwa

"ki yarda dani babu abunda ze faru da izinin Allah, abu ɗaya nike so dake kidage da addu'a

Sannan ki kasance koda yaushe kina cikin alwala da kinji alamar sa kiyi addu'a

Kuma kada ki ƙara tanka masa, duk abunda ze ce miki kiyi banza dashi ya kasance bakin ki ba
abunda yike faɗi face ambaton Allah"

Gyaɗa masa kai kawai tayi, yayin da ya miƙe yana faɗin

"yanzu zanje gida inyi wanka sai intafi zaria dan acan malamin yike,dama da mota nazo da
daganan na wuce, amma kinga sai naje gida na ɗauki mota"

Ta sauke numfashi tana kallon sa ƙaunar sa na ƙara ƙaruwa acikin zuciyarta,tabbas shi na
dabanne dan tabbata da wani ne yaji wannan labarin da yace ya haƙura amma shi ko ɗar beji
ba

Katse mata Guntun tunanin da tafi yayi ta hanyar tafa hannun sa

"chuchu Banaso kina wannan tunanin, ki kwantar da hankalinki please"

Ta jinjina kai tare da cewa

"amma shekaran jiya ka koma, kuma yau na saka ka dawo, ka bar zuwa zarian sai gobe kada
ka gaji da yawa"

Ya girgiza kai yace

"ai zama be ganni ba Rauda,anjimannan zan tafi"

"Allah ya kiyaye hanya, ya kaika lafiya"

Ta faɗa
Ya amsa da amin yana yin gaba

"Umar!

Ta Kira sunansa ya waigo yana zuba mata kyawawan idanuwan sa

"nagode da ƙaunar gareni"

Murmushi yayi tare da cewa

"kinga karki ƙaramin irin wannan godiyar muje ki rakani"



*~Ƴarfillo~*

*JINNUL*
*AASHIQUE*
‍♂‍♂
‍♂

NA

HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*




*~We are bearer's of so golden pen~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Dedicated to _little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu_

AGE 2⃣8⃣


_wannan page nakine *shahida* ina alfahari dake a koda yaushe_

*TA AZIYYA*
_ga y'ar uwarmu princess mazadu allah ya jik'an yaya ya gafarta mishi yasa aljannah ce
makomarsa amin_


_7:38_ PM
SUN,JUL 21

_Bismillahir rahmanin rahim_✍✍✍✍✍


sai da ya watsa ruwa ya sauya kaya sannan ya fito hannun sa rik'e da makullin mota

hasina ce ta biyo sa dasauri tana fad'in

"ya umar inzo inrakaka?

girgiza kai yayi yana cigaba da tafiya

"na hutar dake,nasan rakiyar bata tsakani da allah bace dan asaimiki waya ne"

dariya hasina tayi tace

"kai ya umar amma dai kasan ina raka ka ai ko ba maganar waya ko?

ya jinjina kai

"nadai hutar dake kibari anjima in na dawo sai muje in sai miki"

"owo yaya nagane gurin anty rauda zakaje ko?

juyowa yayi yana kallonta dan tana so ta isheshi da surutu

"kinsan bana son yawan magana ko?allah idan kika ban haushi zan fasa siyan wayar"

dariya hasina tayi tana girgiza kai

"aa yi hak'uri yayana,d'an tsaya ma muyi selfie"

ta fad'a tana k'ok'arin kunna cameran wayanta

umar wucewa yayi ya shiga mota batare da ya k'ara saurararta ba

ana kiran sallar magriba ya isa zaria

ya faka motar a k'ofar gidan malan shitu

tare da fitowa lokacin har sun tada sallah shi da almajiran sa

gorar ruwa ya d'auko a motar ya yi alwala ya k'arasa inda suke sallar

sai da suka idar sannan malan shitu ya tashi dasauri yana d'aukar darduman da yike kai yace

"alhaji umar kaine da yamman nan tashi kan tabar man nan in shimfid'ama darduma"

umar yayi murmushi yace

"aa malan barni kan tabarman"

"aa dan allah tashi alhaji umar tabarma ba wurin zaman ka bane,bare wannan tabarman da ta

yayyage"

umar ya kuma yin murmushi yace

"haba malan nida wataran cikin k'asa ma za a turbud'ani miye abun damuwa dan nazauna kan
wannan tabarman?

malan shitu ya jinjina kai yace

"shiyasa a kullum kake burgeni alhaji umar sam baka da girman kai irinna masu kud'i ba ka
nuna k'yamarka ga talakawa sam"

har lokacin da murmushi a fuskar umar

"bamu gaisa ba malan,ina wuni ya d'alubai"

malan ya amsa da lafiya lau

ya hanya,hala hanya ce ta biyo da kai?

umar ya girgiza kai yace

"aa malan wata y'ar matsala ce ta tasoni wallahi"

malan shitu yace
"subhanallah to allah ya warware mana,tashi mushiga d'aki to"

umar ya mik'e yabi bayan malan suka shiga madai-daicin d'akin

bayan sun zauna malan shitu yace

"ina jinka alhaji meke faruwa"

umar ya sauke numfashi yace

"wallahi malan akan yarinyar da nike nema ne"

ya koro masa bayani dallah-dallah

malan shitu ya sauke numfashi bayan ya gama sauraren bayanin umar


"gaskiya wannan al'amari akwai rikitarwa amma bari muyi isikhara mu gani"

umar ya gyad'a kai yana duban sa kawai

malan shitu ya d'auko carbi yafara ja zuwa can ya nisa yace

"gaskiya alhaji umar da zakaji shawarata da ka hak'ura da wannan yarinyar saboda akwai
sark'ak'iya sosai acikin al'amarinnan"

umar ya sauke ajiyar zuciya

"malan bazan iya hak'ura da ita ba,dan ina sonta fiye da yadda kake tunani idan da mafita da
kuma yadda za'ayi ayi kawai"

malan ya gyad'a kai yana kuma d'aukar carbin sannan yace

"dan mafita za asamu mafita da izinin allah amma fa za a sha gwagwarmaya sosai"

umar ya gyara zama yana k'ara fuskantar malan shitu

"malan ashirye nike da in fuskanci duk wata gwagwarmaya indai akanta ne,dan haka karkaji
komai indai akaina ne,kai dai kayi duk abunda kaga ya dace dan allah ga wannan ayi duk
sadakokin da za'ayi"

ya k'arasa fad'a zaro bandir d'in kud'i ya aje a gabansa

malan shitu ya jinjina kai yace

"insha allah zamuyi abunda zamu iya amma kaima fa sai kadage da addu'a sosai,musamman
inzaka kwanta allah ya shige mana gaba"

"amin"

umar ya fad'a yana mik'ewa yace

"to ni zan wuce malan saboda kar dare yayi"

malan ma ya mik'e yace

"shikenan alhaji umar allah ya kiyaye hanya duk abunda ake ciki zankira ka in sanar dakai insha
allah"

bayan kwana uku,bata k'ara jin d'uriyar Aasim ba hakan yasa taji tad'an rage fargaba dan umar
be koma abuja ba kullum sai yazo ya kwantar mata da hankali

yauma suna tare ya d'auko wata leda ya bud'e wacce malan shitu ya aiko mai dashi

ya d'auko wasu turaruka da wani mai a wata kwalba ya mik'o mata yana fad'in

"d'azu malan shitu ya aiko dasu yace kifara amfani dasu a yau........

dagatawa yayi yana kallon yadda ta toshe hanci dan yana bud'e ledar taji wani mugun wari ya
bugi hancin ta

"miye haka kuma?

ya tambaya idanuwansa akanta

"dan allah ka rufe ledar wallahi wari"

ya kalli ledar dan shi sam beji wani wari ba

"wari kuma?

ta d'aga kai tana k'ara toshe hancin dan ji take warin na kuma k'aruwa

"allah wari ka rufe kar inyi amai please"

ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idanuwan sa na kanta

"chuchu baki son hankalin mu ya kwanta ko?

cikin rashin fahimta tace

"kamarya jaana"

ya jinjina kai yace

"eh mana,kinsani muna cikin matsala amma kuma na kawo magani kina toshe hanci"

ta jingina da kujerar motar

bata re da ta k'ara cewa komai ba

"ki amsa maganin kisha fa sa yanzu a gabana"

d'an zaro ido tayi tana kallon sa

"inshafa fa kace"

ya d'aga kai

"eh ko bazaki shafa bane?

ta girgiza kai ahankali tare da cewa

"bawai bazan shafa bane,amma warin maganin yayi yawa"

ya gyara zamansa sosai yana fuskantar ta

"Rauda nasan bazaki ji dad'in amfani da magungunan nanba sam,amma ya zama dole ki daure
ki duba damuwar da nike ciki dan allah "

ta sauke numfashi tare da zame hannayenta da toshe hancin dasu

ta amsa

murmushi umar yayi yace

"yauwa matar kirki nasan dama bazaki yimin musu ba"

dauriya kawai take yi dan warin maganin nema yike yi ya hautsina ta

"ya zanyi amfani da shi?

"kinga wannan idan zaki kwanta zaki shafa,wannan kuma da rana sai wannan hayak'i ne.........

ya d'an dakata ganin yadda take mashau-mashau da idanu

"lafiya chuchu?

ya tambaya,ta bud'e idanuwanta da suka fara yi mata nawi saboda sarawar da kanta ya fara yi
mata

"kaina ke min ciwo"

cikin tausayawa yace

"sannu ze dena kinji,kiyi hak'uri dama malan yace dole zakiji haka"

kad'a kai kawai tayi tana bud'e turaren ta shafa a goshinta kamar yadda yace

wani kalan nawi taji goshin ya mata kamar an d'aura mata dutse

lumshe idanuwanta tayi tana ambaton sunan sa

"umar!

ta kira sunan cikin wani irin yanayi

gabad'aya tausayinta ya kamasa,

ya amsa yana jin kamar yadawo da ciwon da take ji jikin sa

"jikina na bani kamar wahalar da kanmu kawai zamuyi baza.......

katse ta yayi
"kada ki k'ara fad'in haka,insha allahu zamu yi nasara"

gyad'a kai kawai tayi amma ita zuciyar ta ta karaya

"please rauda kiyimin alk'awarin duk rashin dad'in maganinnan zaki daure kiyi"

ta k'ak'aro murmushin k'arfin hali tana jinjina kai

"zanyi insha allah"

b'angaren Aasim kuwa yana zaune yana kallon su ta madubi

guntun murmushi yayi yana shafa sumar kansa had'i da kallon ummu salma wacce ya d'aure da
wasu mugayen igiyoyi

"tabbas kin tafka kuskure da kikai tunanin wani k'aramin alhakin turaren ki zeyi tasiri akaina,kin
manta waye Aasim ne amma zan tunatar dake yanzu"

cikin tashin hankali da rud'ani ummu salma tace

"ka gafarceni ranka shidad'e kayi min afuwa nasan nayi kuskure ka yafeni dan allah"

hannunsa ya sa yayi nuni da ita sai ga wani haske ya fito ya caki k'irjinta

tasaki wata razananniyar k'arar azaba

ya mik'e yana kallonta da razanannun idanunsa

"zaki kasance a haka har tsawon kwana bakwai,kinga gobe bazaki sake tunanin shiga gona ta
ba"

yana gama fad'ar haka ya b'ace

gurin rauda ya nufa kai tsaye lokacin ta shiga gida dan umar aranar yike so ya koma abuja

tana zaune tana k'ok'orin shafa turarukan da maganin taji tsayuwar sa agabanta

d'ago kanta tayi da sauri suka had'a ido

gabanta ne yafara fad'uwa ganin kallon da yike mata

"habibty intayaki shafawa ne?

ya tambaya yana yimata wani shu'umin murmushi

runtse idanuwanta tayi dasauri tana karanto duk wasu addu'o i da suka zo bakinta

zaunawa yayi kusa da ita yana amsar turaren hannunta yana juyawa

"kinyi shuru ko baki so intayaki ne?ba rabuwa kikeso kiyi dani ba ince wannan.shine maganin
da akace miki ze rabaki dani?

har lokacin addu a kawai take karantowa kamar yadda umar yace tarink'a yi aduk sanda yazo

murmushi ya kuma yi yana rausayar da kai

"ohh na tuna saurayinki yace kidena tankamin ko?


*~y'arfillo~*

*JINNUL*
*AASHIQUE*
‍♂‍♂
‍♂

NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*




*~We are bearer's of so golden pen~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_

AGE 2⃣9⃣


_2:28_ PM
MON,JUL 22

_Bissmillahir rahmaninr rahim_✍✍✍✍✍

"wato da nabaki lokaci ki yanke duk alak'ar dake tsakaninku shine kike neman ma rabuwa dani
ko?

wallahi kinbani mamaki bantab'a tunanin haka daga gareki ba,na d'auki amana.da yardata na
baki amma a k'arshe ni zaki watsa wa wa k'asa a ido"

hmmmm ya k'arasa fad'a yana sauke numfashi sannan ya cigaba da cewa

"Rauda kisani bazan tab'a rabuwa dake ba,kuma bazan tab'a bari wani namiji ya rab'eki
ba,kada ma ki wahalar da kanki wajen yin maganin da ze wahalar dake domin banga maganin
da zeyi shamaki atsakanina dake ba,

sannan kisani kina d'auke da cikina a tare dake dan haka kibi ahankali wajen yin amfani da
wasu magungunan da zasu iya cutar min da yaro ina fatan kingane?

bud'e idanuwanta tayi sosai tana kallon sa

yayinda ya mik'e ya durk'uso saitinta gami da sa hannu akan cikinta ya shafa

"ki kulamin da yarona sosai"

be jira jin me zatace ba ya b'ace

"nashiga uku!

ta fad'a tana duban cikin,wasu hawayen tashin hankali suka fara biyo kuncinta

kwantawa tayi zuciyarta cike da tsananin damuwa

washegari umar na zaune a office bayan yagama duba iya adadin patient d'in da yace ze duba

kulle office d'in dan yana buk'atar ya huta sakamakon rashin baccin da bayayi kwana biyu dan
duk dare tashi yike yi yay ta kai kukansa ga ubangiji akan wannan matsalar

wani sak'o ne ya shigo wayar sa ya bud'e yana dubawa

tsaki yaja ganin wasu kalar shirmen rubutu da besan ko na menene ba

d'agowa yayi ze aje wayar karaf idonshi yayi gamo da Aasim wanda ke zaune a kujerar dake
gaban tasa

kallonsa umar yayi da mamaki dan shi sam beji shigowar mutum ba hasali ma k'ofar office d'in a
rufe take to ta ina ya shigo?

yayi wa kansa tambayar

Aasim yayi murmushi tare da mik'amai hannu yana mai sallama

umar ya amsa kawai batare da ya mik'a masa nasa hannun ba

Aasim ya janye hannunsa yana cewa

"kayi hak'uri nashigo ma office batare da izinin ka ba"

umar ya gyad'a kai yace

"ok meke tafe dakai?

Aasim ya gyara zama

"kamata yayi kafara tambayar waye ni,kafin ka tambayi abunda nazo dashi"

umar ya jinjina kai

"to inajinka waye kai?

"sunana Aasim mijin wacce kake neman aure"

umar ya kallesa da sauri mamaki k'arara a fuskar sa,amma ko kad'an beji wani tsoro ba

hasalima d'an murmushi yayi

Aasim ya cigaba da cewa

"nazone inyi maka gargad'i cikin lalama,ka rabu da matata dan zan iyayin komai akanta"

umar ya sauke ajiyar zuciya yace

"naji dad'in zuwanka da kuma yadda kazomin cikin salama,hakan ya tabbatar min da kana da
sauk'in kai

amma ina so kasani bazan iya rabuwa da rauda ba domin inason ta fiye da yadda kake tunani"

Aasim yayi murmushin takaici

"ba damuwa ta bane yawan son da kake mata,dannasan babu wanda zeso rauda fiye dani
aduniya,inaso karabu da ita ayau ba sai gobe ba"

umar ya sauke numfashi yana girgiza kai

"bazan tab'a rabuwa da ita ba,domin itace zab'ina"

Aasim ya kad'a kai yace

"shikenan ni zan rabaka da ita dole,kashirya ma shiga tashin hankali kasa aranka cewa daga
yau kun k'ulla abota da damuwa"

umar ya kad'a kai

"indai akanta ne,nashirya taryan komai"

Aasim ya mik'e yana jinjina

"shikenan mu zuba ni dakai"

numfashi me nawi umar ya sauke bayan b'acewar Aasim

yasa handkerchif ya share gumin da yafara tsattsafo masa tabbas wannan abun bana zama
bane

zaro wayarsa yayi ya kira malan shitu ya sanar dashi

daga can b'angaren malan shitu yace

"gaskiya al'amarinnan me girma ne,amma ina ganin zanje gurin wani kakana gobe dan yana da
lak'anin da yafi nawa inyaso sai muji abunda zece shi"

umar yace

"shikenan malan dan allah ka k'ok'arta"

sukayi sallama ya ajiye wayar

haka suka cigaba da gwagwarmaya,har na tsawon wata d'aya amma babu canji

inbanda wahala ma babu abunda rauda kesha,dan arana sai tayi suma fin biyar

babu wanda besan matsalar da ake ciki ba a gidan

rauda ta rame sosai,dan ita kad'ai tasan azabar da take sha dan Aasim yace muddin bata rabu
da umar ba to bazata samu sassauci ba

b'angaren umar ma kullum cikin kawo masa farmaki akeyi,amma da yike jarumi ne shi kuma
yana tsaye da addu'o i shiyasa shi nashi ya zo dasauk'i

duk inda sukaji wani malami sai sunje amma a banza,dan babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login