Showing 27001 words to 30000 words out of 101191 words
dai-daitan da Rauda ke ciki
Da sallama tashiga, Rauda ta amsa suka gaisa
Napep d'in tacigaba da tafiya
Budurwar da tashi ga napep d'in tace
"Rauda ko?
Da mamaki Rauda ta kalleta jin takira sunanta
"Eh itace"
Budurwar tayi murmushi
"Ni kuma saima"
Rauda tak'ara kallonta, bata tab'a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Saima ta katse mata tunanin da takeyi
"Kinyi mamakin kiran sunanki da nayi ko?
Rauda ta d'aga Kai
"Eh gaskiya danni bansanki ba,to ko makarantar mu kike?
Saima ta girgiza kai alamar aa
"Ba a makarantar ku nike ba malama Rauda"
Rauda ta jinjina Kai
"To ya akayi kikasan sunana?
Saima ta kuma yin murmushi,sunan ki ai sananne awurina,ke bama nikad'ai ba gabad'aya
ahalina,babu wanda be sanki ba"
Mamaki yakuma kama Rauda
"Ahalinki? bangane ba"
Saima ta d'aga kai tace
"Eh,amma bawannan surutun ya kawoni ba,meyasa zuciyarki take saurin amincewa da
mutane?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K'ara cewa komai
Dan ji tayi tsigar jikinta tafara tashi
Saima takuma yin murmushi,tana cigaba da cewa
"Ya kamata dai kirink'a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare dake
akodayaushe
Nabarki lafiya"
Tana gama fad'ar haka ta dire ko cewa me napep d'in ya tsaya batayi ba
Rauda tsoro ne yakamata, jikinta yayi sanyi sosai
Dede lokacin me napep d'in yatsaya a k'ofar shagon saloon d'in
Taciro kud'insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
Me saloon d'in me suna Amira tace
"Yadai customer?lafiya naganki wani iri?
Rauda ta girgiza Kai
"Aa bakomai"
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al'ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta rink'a
ban-bance jinsin mutum da na aljani?
Domin yana tare da ita a kodayaushe?
Maganar Amira ce ta katse mata tunanin data tafi
"Me za'amiki, retouching ko steaming?
"Steaming"
Tabata amsa a tak'aice
Har aka kammala mata bata dawo cikin natsuwarta ba,juyayin abunda yafaru kawai takeyi
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab'a kawota
Amira ce ta amsa tana bashi izinin shiga
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak'i sid'ik yana ta
shek'i
"Wow habibty kinga yadda gashin yayi kyau kuwa?
Amira tayi dariya tana fad'in
"Sai ka biyani da yawa"
Ya rausayar da Kai yace
"Baki da matsala, tunda kina gyara min matata"
Murmushi Rauda jeyi
"Ai nayi zaton bazaka zo ba"
Ya girgiza Kai yace
"Haba nina Isa?muna gama meeting d'in nan nayo direct"
Ta jinjina Kai tana janyo d'an kwalinta zata d'aura gaban makeken madubin da ke manne a
bango
Gabanta ne yafad'i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta cikin
madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi gaggawar kallonsa a fili
Yana tsaye yana bawa amira kud'i sanye da k'anan Kaya
Ta murza idanuwanta dasauri tana ganin kaman gizo idanun ke mata
Takuma kallon madubin, still da kayan sarautar ta k'ara ganinsa
Maganar saima ce tadawo Mata, gabanta yayi wani mugun fad'uwa
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Kallonta yayi yace
"Yadai naganki a daburce meyafaru?
Ta girgiza kai dasauri batare da tace komai ba
Amira tace
"Nima dai yau tunda tashigo haka naganta"
Yakuma kallonta sosai
"Habibty,lafiya?meke faruwa"
Kuma girgiza kai tayi alamar babu komai
Ya jinjina kai amma be yadda babu komai d'in ba
"Shikenan muje"
Yayi gaba yana yiwa amira sallama
Bin bayansa tayi da kallo gabanta na fad'uwa
Yad'an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
"Yadai,ko baki gama bane"
Ta girgiza kai tana d'aga k'afarta datayi mata nawi a tafito
Yabud'e mata motar tashiga,sannan ya shiga ya tada
Yana cewa
"Kifad'a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce ba"
Tayi k'arfin halin danne tarin fargaban da yike zuciyarta
"Aasim,intambaye ka zaka fad'amin gaskiya"
Ya kalleta
"Eh zanfad'a miki indai nasani"
Ta jinjina Kai tace
"Aasim kai mutum ne?
Ta jeho mai tambayar da be shirya jinta ba
"Eyeh,mene?mekika ce?
Yafad'a cikin sark'ewar murya
"Nace kai mutum ne?
Yayi shuru na y'an sakwanni sannan yace
"Me yasa kika yimin wannan tambayar?
Ta gyad'a kai fad'uwar gabanta na dad'a tsananta
"Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k'afad'a min gaskiya kai mutum ne?
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Eh ni mutum ne"
Girgiza kai tayi cikin rashin yadda
"Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin madubi?
Ya taka burki da sauri yana kallonta
"Suffata Kuma,ayaushe?saidai in gizo idanun ki suka Miki"
Ta gyad'a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud'e tare da sawa akan yatsanta ta danna
Sai ga jini b'ul-b'ul,
"Miye haka habibty,yanka kanki kikayi fa?
Yafad'a dasauri,ta jinjina
" kai nasani ai,kai ma inaso ka yanki yatsanka,saboda in tabbatar da abunda nike zargi"
Girgiza kai yayi
"Habibty baki yadda dani bane?
"Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad'a min gaskiya ne to ka
amsa kayi abunda nace"
Tafad'a cikin wani irin yanayi na tashin hankali
"Habibty..,.
Katseshi tayi ta hanyar kama hannunsa zata danna rezar
Yayi saurin rik'e hannunta da d'ayan hannunsa
Sai dai ina,kafin yayi wani yunk'uri ta yanke sa
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ja baya tayi dasauri, k'irjinta yayi wani mugun bugawa
Hannunta tasa akai,ta k'wala ihu
Yayi saurin matsowa yana fad'in
"Habibty narok'eki ki kwantar da hankalinki"
K'ok'arin bud'e motar tafarayi da sauri amma Gam,tak'i bud'ewa
Tafara jijjigata da k'arfi tana cigaba da yin ihu
Ya k'ara matsowa yana kiran sunanta
Ganin k'ofar bata da alamun bud'ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had'e hannun ta guri
d'aya cikin kuka da tsananin firgici tace
"Narok'eka kada ka cutar Dani,kayi hak'uri idan laifi nemaka"
Hannunta yakama zeyi magana,ta fizge hannun da sauri
"Kada katab'ani kayiwa Allah kabud'emin infita"
Ajiyar zuciya yasauke tare dacewa
"Kiyi hak'uri ki fahimceni,ki natsu dan Allah"
"Nidai kabud'emin infita,karabu dani kayi hak'uri,kar ka cutar Dani wallahi banyi ma komai
ba......
Tsawa ya daka mata
"Nace ki natsu ko!!!!!!
Shurun ko tayi dan tsawar ta k'ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro ta da ga
cikin k'an-k'ara
Aasim ya cigaba da cewa
"Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al'amarin cutarwa a tare Dani?
Yafad'a cikin yanayin damuwa
Sannan ya sassauta murya
"Kiyi hak'uri na d'aga miki murya,amma dan allah ki kwantar da hankalinki,
Tunda Kingane gaskiya ai dole zanyi miki bayani"
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar da ita d'in
zeyi ba
Ya numfasa sannan yace
"Ayanzu babu abunda zan b'oye Miki,
Zanyi miki bayanin komai,kuma inaso ki saurareni da kunnen basira
Ki kuma fahimci bayanin da zanyi miki kinji?
Tad'aga kai alamar taji
Yacigaba da cewa
"Ni ba mutum bane,kuma ni ba aljani bane amma ni rauhani ne,
Kamar yadda kikasani sunana Aasim, Aasim bin ramzad,
Mahaifina shine sarki ramzad dake mulkar masarautar rauhanai
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud'u da suka wuce,sannan har da y'a a
tsakanina dake"
Zaro ido tayi tana kallonsa
"Aure,harda y'a?kuma Dani?
Tafad'a cikin rawar murya da kuma mamaki
Ya jinjina Kai
"Eh Rauda,shahida da kika gani y'arki ce kece mahaifiyar ta"
Ta kuma zaro ido tana kallonsa
Yacigaba dacewa
"Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare da kinsani
ba"
Typing dakwai wahala Allah, muhad'u a Page 13
Yarfillo. JINNUL
AASHIQUE
♂ ♂
♂
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
AGE 1⃣2⃣
Wannan Page d'in nakine mamana,allah ya k'ara miki lafiya yasa kaffarane, ina k'aunarki
araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.
NA KASA MANTAWA DAKE
Dede da rana d'aya, kodayaushe cikin tuna ki nikeyi, hak'ik'a nayi babban rashi da na rasaki,y'ar
uwata hajara aliyu allah Nike rok'o ya jik'anki da rahama,ya gafarta Miki,yasa aljannah ce
makomarki Amin
8:57am. SUN,APR 21✍✍✍✍✍
Bissmillahir rahmanin rahimYa sauke numfashi idanuwansa na kanta,yace
"Akwai wani sabon restaurant da aka bud'e babu kalar abincin gargajiyan da basa
saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo"
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
"Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike yi?
Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek'a ko wajen makaranta ba"
Tayi dariya tana gyad'a Kai
"Hakane,to nagode allah ya k'ara bud'i "
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike rawa kad'an
saboda sanyin dake kad'ata
"Wai shin kai baka jin sanyi ne?
Ya bata amsa
"Me kikagani?
Rauda tace
"Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi"
Aasim yayi murmushi
"Kafinnazo nan inajin sanyi sosai,amma ina had'a ido dake,sai naji wani d'umi na ratsani,
gabad'aya sai naji sanyin ya tafi"
Tayi dariya tana girgiza Kai
"Kai ko?
Shima dariyar yayi yana kwai-kwayar yadda take magana
"Ni me nayi?
Dariya takuma yi sosai tace
"Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d'inka,da dariyar da kake sani,tunda
nahad'u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin ciki ina godiya sosai"
Murmushi yayi me cike da abubuwa da yawa
"Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki"
Itama murmushin takeyi
"Dagaske?zaka iya yin komai akaina?
Ya jinjina kai
"Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki"
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin zuciyarta
Ta d'aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad'a ganyayyakinta,suna kad'awa
ahankali
"Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba"
Yad'an matso gab da ita suna kallon juna
Yace
"Nima kaina bansan meyasa ba,abu d'aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne ya
jarabceni da k'aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi tunanin nafad'a
mikine dan kawai soyayya
Wallahi dagaske nikeyi,ina k'aunar ki"
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y'an sakwanni sannan tace
"Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu cikin farin
ciki idan na kasance tare da Kai"
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad'a tayi masa dad'i sosai
"Nagode habibty,bari nabarki kikoma ciki,tunda sanyin na damunki"
Ta gyad'a kai tace
"Shikenan nagode, Saida safe"
"To sai da safe"
Tafad'a tana juyawa,harta d'an yi nisa tajuyo
Yana tsaye inda tabarsa yana kallonta
Tace
"Yadai da magana ne indawo?
Ya girgiza kai yace
"Aa,kawai inaso inga shigarki ne tukunna sai inwuce"
Ta gyad'a Kai tana murmushi
Sannan taci gaba da tafiya
"Rauda!
Ya Kira sunanta,ta waigo tana kallonsa batare da ta amsa ba
"Ina sonki"
Yafad'a,takuma yin murmushi tare da juyawa dasauri,tashige ciki
Koda ta koma d'aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton sannan ta
kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata ba
yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Ta ciro wayarta ta latsa numbansa taji a kashe
Ta maida wayar jaka taciga ba da tafiya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
Tashiga damuwa sosai,dan bata tab'a kiran wayarsa taji a kashe ba
Har ta koma hostel, tana k'ara trying d'in kiran
Amma still a kashe
Ta yada jakar ta a k'asa tana zubewa a kan katifa
Salma dake zaune ta kalleta tana cewa
"Yadai?duk gajiyar ce?
Ta d'aga kai alamar eh tare da cewa
"Da gajiyar da kuma damuwa"
Salma tace
"Damuwa Kuma? Tamece?
Ta sauke numfashi tana tashi tazauna
"Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi wallahi,dan
bantab'a kiransa naji irin haka ba"
Salma ta jinjina kai
"Gaskiya dole kishiga damuwa,to ko wayar tasa ta fad'i ne?
"Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad'uwa wayar tayi,da yazo yafad'a min kuma da na
gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje bangansa
ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba"
Salma ta jinjina kai
"Gaskiya, to amma kik'ara gwadawa anjima insha'allah zata shiga,k'ila abubuwane suka mai
yawa ya kashe"
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau d'ari amma
abu d'aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab'a sanin tana k'aunar sa ba sai a lokacin
Ahaka aka kwashe kwana uku, lokacin tagama jigata da rashin sa
Hakan yasa bayan tafito daga lectures tayanke shawarar zuwa department d'insu ta tambaya
Suka ci karo da salma ita ma tafito daga nata lectures d'in
"Yadai Rauda ina zakije?
Salma ta tambaya,
"Zan lek'a b'angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani Hali yike
ciki"
Salma ta jinjina Kai
"To muje inrakaki nima abun nadamuna wallahi"
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d'alubai na zaune suyi group-group sunata fira da
shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
Wani matashi suka gani a zaune shikad'ai da handout a hannunsa
Suka k'arasa gurin suka mai sallama
Ya amsa fuskarsa a sake suka gaisa,sannan Rauda tace
"Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
"Aasim?
Matashin ya tambaya, Rauda ta d'aga kai tana fad'in
"Eh "
Yace
"Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen gabad'aya kuma
shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da yawa"
Yak'arasa fad'a yanayimata nuni da wani
Rauda ta jinjina kai
"Hakane,nagode sai anjima"
Tafad'a sannan suka k'arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
Sannan suka tambayeshi
Shima mai-maita sunan yayi
"Aasim, Aasim,anya anan department d'in kuwa?Ta d'aga kai
"Eh"
Yad'an yi shuru yana nazari sannan yace
"Gaskiya bangane shi ba,abokina ko kasan me suna irin haka haka?
Yak'arasa fad'a yana kallon wanda yike kusa da shi
Shima girgiza kai yayi alamar be sani ba
Wanda suka fara tambayar yace
"To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d'inmu yike ba"
Rauda ta girgiza kai tace
"Anan fa yace yike,yananan zaka ganshi wani fari dogo haka"
Ya ajiye numfashi yace
"Nafad'a miki bansanshi ba gaskiya"
Ta gyad'a kai cike da damuwa a cikin zuciyata
"Shikenan nagode,mutafi Salma"
Suka juyo jiki babu k'wari
Salma tace
"To ya akayi haka Rauda?ni al'amarinnan yafara d'aure min kai fa,ace a department d'insu babu
wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad'aya jikinta yayi sanyi
Wata mota ce tasha gabansu,cikin b'acin rai salma Tafara fad'a
"Wannan wani irin wulak'anci ne zaka wani.......
Kasa k'arsawa tayi yayinda ya sauke Glass d'in motar
Rauda ko kanta na k'asa ko kallon motar batayi ba dan damuwar dake zuciyarta nema takeyi
tafi k'arfinta
"Habibty...
Taji anfad'a, dasauri tad'ago kanta,suka had'a ido
Ya sakar mata lallausan murmushi
"Habibty,bazaki amsa kiran nawa bane,duk fushi dani d'inne ya jawo haka?
A memakon tabashi amsa,sai kawai idanunta suka cicciko da k'walla
Nan da nan hawaye yafara wanke mata fuska
Dasauri ya bud'e marfin motar,yafito yana fad'in
"Subhanallah,kuka habibty,me yake faruwa?
Ya tambaya hankalinsa a tashe
Ji tayi k'afafunta suna neman kasa d'aukarta,hakan yasa ta durk'usa tana cigaba da yin kukan
"Habibty please kiyi hak'uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo kanki"
Kasa mik'ewa tayi saida Salma ta kamata tukunna,sannan tashiga motar
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin kukan da ta
rasa ko na menene
Ya sauke numfashi yana cewa
"Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin zuciya yike yi"
D'agowa tayi tana kallonsa da jik'akk'un idanunta
"Inyi shuru fa kace?kasa nashiga tashin hankali da tsananin damuwa,ina fargaban ko ba lafiya
kake ba,inata fargaban ko wani abune ya sameka,ashe lafiyar ka k'alau.....
"Please kiyi hak'uri nasan nayi kuskure, Amma ba