Showing 27001 words to 30000 words out of 41364 words
ba a Hayyacinta ta tahoba duba da yanayin kayan jikinta , Nasma kuwa tana
ganin yadda Hanan ta rungume Ammin ta tana murnar ganinta tuni zuciyar ta ta karye tafara
hawaye , cikin Ranta take fad'in " inama itama taga Mamanta , wacece Mamanta ma ita tunda
ta taso batason kowa ba sai Hajiya Hajjo kuma itama daga baya ta tsaneta bata maidata 'Ya ba
, Hajiya Asma'u ta dubi Nasma tace " samu guri kema ki zauna , Nasma tayi saurin goge
hawayen idonta tana zama , Ammi ganin yadda jikinsu yake tasan ba zuwan dad'i sukayi nan
tace su tashi suje suyi wanka suzo suci Abinci inyaso sai suzo a kuma gaisawa........
koda Kawi Idi yashiga cikin gida yasamu Safara'u da maganar da Alhaji Nasir yazo masa da
ita , tuni ta mik'e tanajin wani dad'i na ratsa ta , cikin ranta ta fara furta " Allah yasa baza aga
Hanan d'in ba daga can tayi can dan dama baso takeyi tayi gogayyar miji da itaba , dan tuni
tagama yanke hukuncin shiga cikin gidan Alhaji ko tahalin k'ak'a , duban Kawu tayi tace "yanzu
ina shi Alhajin yake ? Kawu Idi yace " gashican a waje yana jirana gaskiya Yarinyar nan bata
kyauta ba tagama zubar min da mutuncina , Safara'u ta dubi Kawu Idi ta tab'e baki sannan tace
" daman kai har wani mutunci gareka a gunsa ? yana baka abin duniya kana saka hannu ka
karb'e kana rawar jiki har wani mutunci zakayi , ta turesa da duwawu tana fad'in ni gafara naje
wajensa muyi magana , ko mayafi bafa rufa ba daga ita sai waya yololuwar rigar bacci duk
jikinta a waje , da sauri Kawu ya bita yana kiranta tare da fad'in " ahaka zaki fita titi bakida
Hankaline ? ko kallonsa batayi ba ta lek'a a haka tana sakarwa Alhaji Murmushi , Alhaji Nasir
kallonta yashiga yi yana maida wani mugun miyau k'ut , dan iya mace Safara'u mace ce ita
tanada dirin jiki , koda Kawu Idi yaga irin kallon da Alhaji Nasir keyiwa Sarafa' tuni ransa yayi
mugun b'aci baisan sanda ya tsinka mata mari ba , aikuwa ta saki wata k'ara tana nufo Alhaji
Nasir ta fad'a jikinsa duk dan taja hankalinsa , aikuwa Kawu Idi yashiga zaginta yana tsinemata
shikuma Alhaji Nasir sai k'ok'arin tureta yakeyi daga jikinsa ita kuma sai k'ara shigewa takeyi
tana goga masa na shanunta wanda suke tsaye tamkar bata shayar ba......
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Zee* *MD* βν ΌνΏ»
19.
Hanan cike da sarewa da rayuwa tace " shikenan Yau mungama Rayuwa a duniya , A
dai dai lokacin Nasma tagama cire glass d'in k'ofar dukansa , rik'o Hannun Hanan tayi ta
ciccib'ata tace " kizo ki fita tanan Hanan inaso ace koni bantsira ba to ke kitsira kodan Amminki
da Yaya Zunnur , Rayuwarki tafi tawa Amfani Hanan , bani da Uwa banida 'Yan uwa damuke
ciki d'aya banida Dangi dan gaka bani da wani amfani , Hanan tarik'e Hannun Nasma tace "
kina da Amfani sosai Nasma sannan duk abinda kika lissafa kema kina dashi , bazan iya tafiya
nabarki a wannan halin ba , bugu k'ofar da k'arfi da aka sakeyi shine yasa dukansu suka
Razana , da sauri Nasma ta tura Hanan tace " to fara dira nima saina diro daga baya , Hanan
ta tahau sannan ta lek'e wajen , duhu tagani sai hasken farin wata k'adan , direwa tayi aikuwa
ta fad'a kan kwalba , wata k'ara tasaki datasa Nasma saurin d'ane wa itama zata haura , a dai
dai lokacin Alhaji Nasir ya karye k'yauren tare da shigowa cikin Toilet d'in , Nasma ta juyo ta
kallesa rik'e da wata k'warya sanye da wani Jan yadi a jikinsa , suna had'a ido yayi saurin nufu
wajen da niyyar janyota tuni ta dire waje itama , dasauri ta mik'e tare da rik'e Hannun Hanan
tace " tashi Hanan mutafi wallahi Daddy ya ganni , da sauri Hanan ta mik'e k'afarta sai zubar da
jini take suka fara gudu.......
Alhaji Nasir tuni yayo waje tare da nufar k'ofar gate , kwata kwata ya manta a yadda ya fito
yana zuwa ya fara k'ok'arin bud'e gate ya fita , megadin gidan tuni ya mik'e ya d'au sandar sa
yanufi Alhaji Nasir ya buga masa , shi a tunaninsa 'Barawone yashigo cikin gidan , wata k'ara
Alhaji yasaki tare da sakin k'waryar hannunsa , wani ruwa ne dayake ciki ya zube a k'asar wajen
, haske fuskar Alhaji megadi yayi aikuwa yaga Alhaji Nasir tuni jikinsa yafara rawa yana bashi
hak'uri , ko kallonsa Alhaji baiyiba saboda jin zafin Abinda yayi masa , da sauri yadaka masa
tsawa yace " kayi sauri ka zagaya bayan gida ka kamomin su Nasma yanzu yanzu , karka barsu
su b'acemaka , da sauri megadi ya bud'e gate tare da ficewa da mugun gudu .......
Sosai su Hanan suke gudu har suka iso bakin titi , lokacin suka hango Garba me gadi ya
nufosu da mugun gudu , ai tuni suka ci gaba da gudu iya k'arfinsu , Hanan k'afarta sai Jini ne
yake fita saboda azaba , wani lungu suka shiga a nan suka samu wani k'ofar gida a bud'e tuni
suka shige cikin gidan , suna shiga suka maida k'ofar gidan suka rufe tare da neman wajen
b'uya , Bayan wani d'aki sukayi tare da shigewa cikin kayan wanki da suka gani shirgi guda ,
koda Garba me gadi ya shigo lungu rasa inda su Hanan sukayi yayi , take yafara wasuwasi
wanne gida suka shiga a cikin gidaje biyun daya gani ? kowacce k'ofa turasu yayi yajisu duk a
kulle , yadad'e a tsaye a wajen kafin ya juya yatafi.....
Alhaji Nasir tuni yakoma d'akinsa ya canzo kayansa tare da fitowa , nan Garba me gadi yake
gaya masa baigansu ba amman yaga lungun dasuka shiga , take Alhaji Nasir ya d'auke Garba
dawani mahaukacin mari sannan yace " Banza k'aton banza , yanzu ace wad'annan yaran
sungagara kamuwa a wajenka , kashige muje karakani wajen dasukayi barinsu bankama suba
hargari ya waye da matsala.......
Hanan da Nasma suna cikin kaya wanki Sai kuka Hanan takeyi , Nasma cike da k'asa da
murya tace " kiyi shuru Hanan a yanzu addu'a itace zata zamar mana mafita , Hanan ta janyo
wani zani a cikin kayan wankin ta yagashi ta d'aure ciwonta dashi , Nasma tace " ina ganinfa
tashi zamuyi mubar wannan gidan shima dan da Alama ba gida bane na matan aure , Da sauri
Hanan ta dubi Nasma tare da fad'in " gaskiya nidai babu inda zani kina kallon yadda k'afata
takemin wani mugun zafi kuma in muka fita ina kike tunanin zamuje ? motsi sukaji tare da
magana , kasa kunne sukayi tare da yin shuru suka daina motsi , Nasma ta lek'o da kanta dan
ganin ko Daddyn nasune yakuma zuwa wajen nasu kawai sai ganin wasu maza tayi suna shaye
shaye tare da wasu mata , cikin hirar da suke Nasma taji suna fad'in " gaskiya yau dawa batayi
Nama ba kuna ganin da k'yar muka sha a wannan gidan , 'Daya daga cikin matan tace " ai
saboda yana da kayan aiki shi megidan shiyasa amman akwai gaba dole sai munci rabonmu ,
fahimtar da Nasma tayi anan 'Barayine kenan , nan suka gama bushe bushensu sannan suka
fara aikata iskanci da matan , ahaka suka gama sannan suka shige wani d'aki......
Nasma tacewa Hanan " yanzu kinfahimci gidan da muka shigo ko ? to kitashi mubar gidan
nan tun kan gari ya waye mana , Hanan tace " idan muka fita yanzu bamu san inda zamu fad'a
ba , kibari asuba tayi sai mufita tunda ba ganinmu zasuyi ba lokacin , da wannan shawarar
Nasma ta yadda suka yi shuru suna addu'oinsu .......
Alhaji Nasir tunda suka shigo lungu shida Garba yake nazari , tabbas indai wannan lungun
ne ai yasan akwai yaransa dayake nema a cikinsa , wayar sa yazaro ya kira wani yaransa har
ta katse bai d'agaba , sake kira yayi harta kusa katsewa sannan aka d'aga , cikin muryar Bacci
yaron Alhaji Nasir yafara magana " sai megida wanne me k'aran kwanan ne yatab'a mana kai ?
Alhaji Nasir yace" inada
Wasu tsuntsaye ne da suka shigo cakwalinku , da sauri ya mik'e daga kwancen dayake yace "
kace akwai Nama tare da Zuma bari intashi sauran mufito , Cikin k'ank'anin lokaci duk suka
tashi tare da fitowa wajen Alhaji Nasir , su Nasma k'arajin motsi sukayi dan haka suka kuma
tsorata , Nasma tacewa Hanan bari naje nagano mana ko dai wani Abin ne , Hanan ta rik'e
hannun Nasma tana girgiza mata kai alamun kartaje , Nasma tace " badad'ewa zanyiba fa a
hankali zan lek'a naga ko meye yanzu zandawo , a hankali Hanan ta saki Hannunta ta juya
tafara tafiya a hankali......
Zunnur mafarkin dayayi shine yayi bala'in tsoratashi da sauri ya farka , tunani ya shiga yi
yadda yaga Hanan tana kuka wasu maza na binta tana gudu , wai sai kiran sunan sa takeyi da
sunan Ammin ta , tashi yayi yayo arwala tare dayin sallah raka'a biyu sannan yashiga yiwa
Hanan addu'ar kariya a duk inda take , Cikin zuciyar sa yana fad'in duk inda kike Hanan gobe
sainayi tozali dake , dan tun yanzu zanfita zuwa tasha nasan duk inda akayi sallar asuba dole
motoci zasu fara tafiya .....
Nasma na lek'awa taga Daddyn ta tare da wad'an nan 'Yan fashin yana fad'a musu yadda
zasu nemo su , Nan yace sufito su zauna cikin lungun da gefen lungu tabbas baza su wuce
gurinba , Nan suka zazzauna tare da busa sigari suna cewa " ka kwantar da hankalinka indai
suna cikin lungun nan to tabbas kamar sunzo hannunka , dan wancan gidan na Maman Iyabo
innan suka shiga da asuba zata korosu da bala'i , Nan Alhaji yace " zaije gida duk abinda ake
ciki suyi masa waya , sannan lallai karsu bari yaran nan su tsere......
Nasma da gudu tadawo wajen Hanan tana fad'in " kinga irinta ko Hanan , sai da nace miki
tund'azu mubar wannan gidan ni hankalina bai kwanta dashi ba , gashinan Daddy yazo ashe
yasan masu gidan nan , wata irin zabura Hanan tayi tana duban Nasma cike da tsoro sannan
tace " shikenan kashin mu ya bushe dama bamu fito munsha wannan wahalar ba gashi yanzu
abinda muke gudu shine dai zai afku , Nasma tayi jugum dan ita kanta yanzu batasan mafitar
suba , ta inah zasu fita daga wannan gidan ? sannan insunce sai gari ya waye nan ma basu
tsiraba , tabbas suna cikin tashin hankali , Hanan tuni tafara shashshekar kuka tare da cewa "
kiyi magana Nasma kece me nemo mana mafita , Nasma tace dole muzama jarume a wannan
lokacin inba haka ba bazamu tsira da ranmu ba tunda har Daddy yasaka a nemo mu har haka ,
yanzu dole kiyi d'amara dan gudu ne zamuyi sa sosai in anjima kad'an , kinsan dole wad'an
nan zasuyi bacci tunda a bige suke to a wannan lokacin zamu samu mufice daga wannan
gidan.......
Tun kiran farko Zunnur ya fito ya nufi tasha , Allah yataimakesa yasamu abin hawa , yana
zuwa yasamu wata motar me gudu wacce zataje Jos , haka ya hau me motar yace mutum biyu
zasu jira sannan sutafi , Nan Zunnur yace " zai biya kud'in Mutum biyun kawai su shige sutafi ,
take yabiya kud'in Direba ya d'au hanyar Jos.....
Ana kiran sallah Nasma ta zunguri Hanan wacce take gyangyad'in wahala , firgigit ta mik'e
tana duban Nasma , a hankali Nasma tace mata " ki shirya Hanan lokacin fitarmu yayi , a
hankali suka fito daga inda suka b'uya hanyar waje sukayo a hankali suna sand'a , dayake
k'ofar gidan a bud'e take shiyasa basu sha wuya ba wajen zura k'afafunsu suka fita , suna fita
sukaga Yaran da Alhaji yasa su kawosu dukansu idonsu biyu , sai dai da alama basu da wani
kuzari saboda a buge suke da k'waya , suna ganin su Nasma sunfito aka fara kallon kallo ,
d'aya daga ciki yace " daman kuna cikin gidan mu kuka wahalar damu haka ? su Nasma suka
tattare zani suka ranta ana kare , suma Yaran Alhaji tuni suka mik'e tare da rufa musu baya....
Gudu suke baji ba gani tamkar su tuntsira , suma kuma binsu suke iya k'arfinsu , dayake
titi na da nisa da wajen ga duwatsuna shiyasa su Hanan suka fara gajiya , dan tuni tafama
ciwonta da ta d'aure sai jini ne yake zuba , Nasma itama a lokacin tayi tuntub'e da wani dutse
aikuwa ta fad'i tim a k'asa , take goshinta ya fashe jini ya wanke mata fuska , da sauri Hanan
taje tana k'ok'arin tashinta , lokacin Yaran Alhaji tuni sunkusa k'arasowa , a hankali Nasma ta
yunk'ura ta mik'e tare da taimakon Hanan suka ci gaba da gudun su , suna fara hango titi suka
ga Yaran Alhaji sai k'ara k'aimi sukeyi suka masu , suma k'ara gudu sukayi har suka iso titi , da
gudu suka ga wata motar ta taho hannu Nasma ta shiga d'agawa alamar ta tsaya , sunayi suna
waiwayen Yaran Alhaji wanda shuka kusa k'arasowa , aikuwa Direban motar da kamar bazai
tsayaba sai kuma wata zuciyar tace ka tsaya ko cetonsu zakayi , da sauri yataka burki su
Hanan suka tafi da gudu suma Yaran Alhaji suka rufa musu baya , suna zuwa suka ga anbud'e
musu k'ofah da gudu suk shige suna rufowa Direban yatasheta da gudu dan yagane biyosu
akayi.......
Yaran Alhaji cizon yatsun su sukayi tare da zubewa wajen suna zage zage ,
Hanan tunda ta fad'a cikin motar tajita ta fad'a jikin wani mutum , samun kanta tayi da kuma
kwanciya tana maida numfashi , shima wanda tafad'a jikinsa jitayi dai dai saitin zuciyar sa yana
bugawa da sauri da sauri........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Zee* *MD* βν ΌνΏ»
23.
Bayan wasu watanni Matan nan biyu kowacce tasamu ciki a cikinsu , Alhaji kullum
cikin yi musu rashin mutunci yake , ina ganin hakan nagama yadda Alhaji bason haihuwa
yakeba , a dole naje asibiti sukamin allura na tsaida haihuwa , dan tuni Alhaji yasaki
wad'annan matan yarage dagani sai Hajjo , Kuma har wannan lokacin Alhaji baya kulani ,
gashi yahanani naje naga iyayena , duk nabi nadamu kaina dan haka nafara rama , Nasma na
da shekara d'aya da rabi na Yayeta , lokacin Mahaifina yazo garin jos dan ganina tunda ni nak'i
zuwa a cewar su , koda yazo sosai Alhaji Nasir yayi masa tarba ta musamman , a nan ne muka
shirya dan Mahaifina kwana biyu yayi , randa zai tafi shatara ta arzik'i Alhaji Nasir yayi masa
sannan yasa Direba ya maida shi , sosai naji dad'in yadda Alhaji Nasir ya girmama Mahaifina
har hawaye nayi lokacin dazai tafi , Bayan tafiyar Babana da kwana biyu Alhaji ya shigo
d'akina , Nan yana nuna yana buk'atar mu kwanta amman ta baya yakeso , Nan ma na bijire
masa Amman da k'arfi da yaji sai da yayi hakan dani , sosai nayi kuka tamkar raina zai fita
gawani rad'ad'i danakeji ta k'asana , Haka nasha kuka na lokocin dayake da Rana ne Nasma
tadunga min gwaranci tana gogemin hawaye ....
Tunda ganan nadaina kula Alhaji Nasir nasamu kaina da mugun tsanar sa , ana haka aka
kawo masa yaran sa wad'an da matansa suka haifa masa , yana ansar su yabawa Hajjo dan
itace yake shiri da ita sosai , Ba'ad'auki lokaci me tsayiba saiga shi Alhaji Nasir yakuma yin aure
wasu matan biyu , tunda ganan nashiga tsoron lamarin Alhaji Nasir sosai ...... Wata rana da daddare natashi ba wanda yasani na nufi b'angaren Alhaji Nasir , ina zuwa
nasamu a bud'e sad'af sad'af nadunga tafiya har zuwa cikin bedroom d'insa , Anan naga abin
Al'ajabi dan Alhaji Nasir nagani zindir haihuwar Uwar sa yana shan wani Abu a cikin k'warya ,
lab'ewa nayi nashiga lek'owa ina ganin Abinda yakeyi kawai sai gani nayi wani Saurayi ya fito
daga toilet