Showing 12001 words to 15000 words out of 41364 words
Bayan yayi wanka ya fice da k'yar Hanan ta iya rarrafawa tashiga band'aki ta gasa jikinta
sannan tafito , kuka tashiga yi sosai har zazzab'i ya rufeta , wannan wacce irin masiface haka ,
saikace wani dabba ace yana kusantar ta ta baya , anya ba guduwa zatayi ba takoma can
wajen Ammin ta , wata zuciyar ta tuno mata da maganar Nasma datace " duk wacce Alhaji
yasa keta bata dad'ewa take mutuwa , tsoro ne yakuma kama Hanan ta fashe da wani kuka me
tab'a zuciya a haka har bacci ya d'auketa.....
A can Lagos..
Tunda Kawu Idi yace yataho da Hanan Ammi tashiga damuwa , dan tafi kowa sanin halin
Kawu Idi dakuma Matarsa Safara'u , tabbas tasan Hanan saita shiga damuwa avwajen su sosai
, kullum cikin yiwa 'yarta addu'a take Allah yatsareta duk inda take , Afrah kuwa kullum cikin
zancen Hanan take , koda Abban su Afrah yadawo sosai yayiwa Ammi fad'a akan tacire
damuwa akan Hanan d'in tunda da wayonta ai bak'aramar yarinya bace , Ammi taso ace
yabata goyon baya ta anso 'yarta tarik'eta amman taga hakan baiyu ba , saima turo mata
zawarawa dayakeyi akan tazab'i guda a ciki tayi aure tunda bata wuce aure ba ......
Tunda su Ya Zunnur suka koma Sch karatun ma wani lokacin gagararsa yake , kullum cikin
tunanin Hanan yake , xoben dake hannunsa me farkon sunanta shi yake murzawa yana
sumbata , yanxuma idonsa a rufe sai murmushi yake yana tuna yadda yarik'e mata hannu yana
saka mata zoben , a hankali ya furta Ina Sonki Hanan Beauty , wata zuciyar tace " meyasa
baka gaya mata kana sonta ba ? yanzu idan wani yaje ya tusa mata soyayyar sa a zuciyarta fa
kai kuma azakayi ? tuni yayi saurin dakatar da zuciyar sa yana fad'in " Hanan tawace nikad'ai ,
duk wanda yayi gigin saka santa aransa to saidai yayi dakon asara , wayar sa ya d'auka
yakira Number Ummansa , saida takusa yankewa yaji and'aga muryar Afrah yaji tana fad'in " Ya
Zunnur Umman bata nan tafita tabar wayar a gida , cikin isarsa da ginshira irin tasa yace " wato
sai ke kenan kina d'aukar mata waya kina kiran samari ko ? Afrah ta shagwab'e tace "nifah
banida wani saurayi Ya Zunnur , kawai nima ring d'in naji nashigo d'akin d'aukar kayana ,
Zunnur yace " to intadawo kice nakira ina gaidata , sannan inaso kigayawa Ammi kice " nakira
wayyar ta bata d'agawa lafiya kuwa ? Afrah tace " wallahi tunda wannan Kawun yazo ya d'auki
Hanan yatafi da ita shikenan Ammi tadaina sukuni , wata irin zabura Zunnur yayi tare da fad'in "
what , kina nufin kice Hanan ankomar da ita Jos wannan gidan ? Afrah tace ae. Kusan wata
biyar ma kenan , nifah sanake Abban mu yasanar daku shiyasa , kuma kaga nibani da waya
Umma kuma sai yanzu tayi waya itama , haka Ammi itama , Zunnur salati yashiga yi sannan
yace taje takaiwa Ammi waya.....
Lokacin da Afrah takaiwa Ammi waya samunta tayi tana goge hawaye , tana ganin Afrah tayi
saurin k'ak'alo murmushin dole tana fad'in " oyoyo 'yata har antaso daga Sch d'in ? Afrah jitayi
tausayin Ammin yakamata , tabbas tasan tunanin Hanan takeyi , mik'a mata wayar tayi tace "
ga Ya Zunnur zakuyi magana ta juya ta fice ... Ammi ta kara wayar a kunnenta suka fara gaisawa , sannan yace "Ammi dama Bayan tafiyar
mu babu dad'ewa Akazo akatafi da Hanan amman bamu sani ba ? shuru Ammi tayi batare da
tace dashi komai ba , cigaba da Magana yayi yace " a gaskiya banji dad'in komawar Hanan Jos
ba , saboda kwata kwata nidai bana k'aunar zamanta agidan wannan Kawun nata , Amman
Allah yasa hakan yazame mata Alkairi , kuma insha Allah indai munsamu hutu zanje Jos d'in
naganta , Ammi sosai taji dad'in kalaman Zunnur d'in , dan yana da Hankali sosai yafi
Mahaifinsa tsayawa yayi hangen nesa , sai da suka d'an tab'a hira har saida yaji tasaki ranta
sannan yayi mata sallama ....
Ita kuwa Ammi daman lokacin ma Bacci takeyi tayi wani mugun mafarki akan Hanan , shine
tana tashi taji hawaye na zuba aidanunta har Afrah tazo tasameta a haka......
Hanan Sosai tayi Bacci har saida akayi isha'i , lokacin Hajiya Hajjo ta aiko kiranta akan
tazo ta d'ora musu Abincin dare , Hanan ganin anyi sallar isha'i duk a tunaninta ai har angama
abincin dare amman saiga aiken kiran ta nan yazo , mik'ewa tayi ta nufi wajen kiran Hajiya
Hajjon , dan Nasma ta gaya mata duk lokacin da Hajiya Hajjo ta kiraka to kome kakeyi kayi
k'ok'arin barinsa kaje , dan hakan shine samun sauk'in ka a wajenta , Hanan na isa gurin Hajiya
Hajjo tasamu tana tsaye tana jiranta , rissinawa tayi tace " gani Hajiya , Hajiya Hajjo tace " ga
garinan maza kije ki tankad'e ki d'ora mana tuwo , inkingama saikizo ki anshi kayan miya ki
d'ora miya , da sauri Hanan ta anshi garin ta wuce cikin kithen d'in , tunda tashiga kitchen d'in
tafara tunanin ta inah zata fara , gashi bataga ko giftawar Nasma ba bare ta taimaka mata ,
shuru tayi tana tunani taji alamar shigowar Mutum ta bayanta , waigowa tayi da sauri sukayi ido
biyu da Nasma tana mata murmushi , zatayi magana Nasma tayi mata alamar tayi shuru , Nan
take Nasma tafara had'a wuta suka d'ora tukunya sannan suka hau tankad'e gari , Nan ma
Hanan bata b'oyewa Nasma komai ba gameda Abinda Daddynsu yakuma yimata d'azu , duk da
a hankali sukeyin maganar gudun kar wani ya lek'o yaga Nasma a ciki , Nasma ta tausaya wa
Hanan d'in sosai , fara tunanin yadda zasu samu mafita yadaina kusantar ta ma kwata kwata
suka shiga yi , a haka har suka kammala tuwo suka d'ora miya , Hanan tace " gaskiya Aunty
Nasma bazan kuma kwana a d'akina ba , inajin wajenki zantaho mudunga kwana tare saboda
banason Abinda Daddyn ku keyi dani , Nasma tace " aa Aunty Hanan zuwanki d'akina akwai
damuwa dosai , kicigaba da hak'uri har allah yasa mugama samo mafita , yanzu haka naji
labarin wacce Wata Suwaiba da Daddyn mu yasaketa ya aureki tana nan bata mutu ba amman
bata da lafiya , inaso naje gurinta kozan samo mana wani k'arin haske game da abinda zamusa
gaba , Hanan tace " yauwa Allah yasa dai karta mutu ni wallahi tsoro ma nakeji sosai , Nasma
tace " nace miki kisaki jiki kidaina nuna tsoro yin hakan zaisa yarage saka miki ido har yafara
barinki fita daga haka zamu b'illo da shirinmu , cikin hikima Nasma tadunga tsarawa Hanan
yadda zata saki jiki da Daddyn nasu har susamu sugama shirinsu , sosai Hankalin Hanan ya
kwanta dan tana jin maganar Nasma sosai tunda ta girmeta , motsin tahowa sukaji alamar
antaho cikin kitchen d'in da sauri Nasma ta b'oye bayan wasu shirgin kaya.......
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Na*
_Zee_ _MD_βν ΌνΏ»
*Hamdala* *Writer's* *Association* ν ½ν²ͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number*
07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* *kusiya* *Kukaranta*
_Cikin_ _Aminci_ ν Ύν΄ν ΌνΏ»ν Ύν΅°
*Last* ν ΌνΆ page. 10
Kuka babu irin wanda banyiba akan Rabuwa da Ammi , Koda aka kira Number Yayan
Ammi aka gaya masa Kawu yazo zai tafi dani Cewa yayi " Abawa Kawun wayar , komai yace
masa Amman Kawu yak'i Amincewa , haka Abban su Afrah yace da Ammi " tabari yatafi dani
kawai inyadawo zasu san yadda za'ayi , haka muka rabu da Afrah tana kuka tamkar zata
shid'e.....
Ammi kuwa kasa magana tayi har muka fice daga gidan nida Kawu , Tunda muka fita yaketa
min fad'a akan nadameshi da Kukan Munafinci , harda cemin ai shine dole na duk inda akaje ,
cikinsu d'aya da Mahaifina dan haka bazai bari 'Yar Yayansa tarayu a wani guri daban ba ,
ahaka har muka isa tasha motar mu takama Hanyar Jos......
Tunda muka sauka garin Jos duk wani farin ciki bana cikinsa , Ammina kawai nake tunani
da halin datake ciki yanzu , duk danasan Ammi tana cikin gidan da ko tari tayi sai antambaye ta
lafiya , nice yanzu Abar tausayi.....
Muna isowa cikin gidan mu nafara karo da muryar Aunty Safara'u wato matar Kawu , fad'a
takeyiwa 'Danta Mahmud wanda yaci sunan Baffa na wai yazubar mata da tsakin tuwo , tana
ganin mu mun shigo ta dubeni shek'ek'e tana tab'e baki , Sallama Kawu yayi yashigo cikin gidan
dayake yatsaya gaisawa da Abokinsa a waje , amsawa tayi tana fad'in " wato zuwa kayi ashe
kadawo dasu saboda Jaraba irin taka , dubanta yayi yace " Nine Jarabar Kenan Safara'u ?
nadawo gida ko sannu da zuwa bakiyimin ba nayi tafiyar kwana biyu sai kitareni da rashin
mutunci kin kyauta , shigewa cikin d'akin yayi , nikuma na durk'usa ina gaida ta , Amsa min tayi
ciki ciki sannan tace "Ina ita Uwar taki take ? Nace batare muka taho da itaba , sai Sannan naga
tasaki fara'a tana yashar baki tamkar anyi mata albishir me dad'i , dubana tayi tace "kice ita
bazata dawoba kenan? wannan karon haushi ne yakamani na mik'e tsaye nace " Nima
bansaniba na wuce na nufi d'akin mu.......
Tunda nadawo gidan mu bank'ara samun kwanciyar hankali ba , kullum nice nake aiki acikin
gidan tamkar zan mutu saboda wuya , ga Abincin da Aunty Safara'u kebani d'an kad'an ne ,
wani zubin ma k'anzo take bani saboda mugunta , duk nabi na rame na lalace , Tunda aka
koma Sch banje ko sau d'aya ba sun hanani zuwa , Wai Inna tafi waye zai dunga yimata aikin
cikin gidan ......
Tun ina damuwa inshiga d'aki insha Kuka harnazo nafara dangana , dan yanzu *NI*
*BORA* _Ce_ acikin gidan nan , kowa ya kwaso shirginsa niza ace nayi masa wanki , gashi
duk arrabani da k'awayena wanda nake dasu wai suna zugani ....
Kamal kuwa Saurayina wanda yakesona tun kafin mutafi Lagos Kawu ya dakatar dashi wai
bashida sana'ar arzik'i..
A haka har nayi wata Hud'u da dawowa nasaba da wahalar cikin gidan Kawu , inada
masoya sosai masu zuwa suce suna sona Amman kawu daga yaga babu na lasawa sai yace "
Yayimin miji , indai kaga Kawu na rawar jiki da Saurayi inyazo gurina to tabbas zai moreshi ne
, ana haka Har Allah yakawo Alhaji Nasir " wato Mahaifinki Nasma , lokacin dayazo sosai
Kawu yayi Murna , Dan tashin farko Alhaji Nasir yasiyawa Kawu Abin Hawa wato Machine ,
Sannan yabashi jari metsoka , tuni Kawu yacewa Alhaji Nasir yabashi ni kawai yaturo a d'aura
aure , Alhaji Nasir bai b'ata lokaci ba yaturo da kud'in Aurena , Sati Uku Aka saka tamkar angaji
dani , lokacin da Alhaji Nasir yazo wajena nagansa bantab'a jin inason sa ba ko sau d'aya , duk
zuwan dazai yi inna fito bana cemasa cikanka , sai dai shi yak'araci surutunsa yagama yatafi ,
Aunty Safara'u tamkar itace Amarya haka tashiga gyara d'akinta harda canza funutures , kud'in
da Alhaji Nasir ke bawa Kawu haryaso yayi yawa , dan tuni aka gyara gidan mu tas harda saka
k'aramin gate , Kawu har wani tumbi yayi saboda kud'i .....
Kullum ina cikin d'aki ina Kuka tamkar zanyi hauka , gashi banida wayar dazan nemi Ammi
na in gaya mata damuwata , bani dawata k'awa wacce muke tare kowacce Kawu ya koreta , A
haka Biki yak'araso Saura sati d'aya ..
Ranar ina Zaune naji Aunty Safara'u nacewa Kawu "wai kagayawa Uwar waccen yarinyar
Bikin kuwa ? jinayi Kawu yana cewa " Banfad'a musu ba haryanzu , kinsan haushina sukeji dan
naje nataho da ita , dana barta ina zansamu wannan Abin Arzik'in , wallahi sai dai su mutu dan
Haushi , Shewa Aunty Safara'u tasaka tana fad'in " ai inajin ma Hajjin Bana in Allah yaci damu
kaga ya biya mana , da sauri Kawu yace " Yaci dani dai , ke yanzu in anbiya miki Hajji a dalilin
wa kenan? Cike da rashin kunya tace "au Abin harda gori kenan ? Kawu yace " ba gori ba ko
goruba zakice nayi , tunda bikin nan yataho banga kina yiwa yarinyar nan gyara naku irin na
mata ba , kuma na tabbata da 'Yarki ce saikin gyarata , a hakan kike jiran a biya miki aikin Hajjin
yajita ba gyara , Safara'u ta tab'e baki tace "Kaima inka gyarata ai ba fad'uwa kayi ba ......
Haka akayi Bikina Nida Alhaji Nasir batare da Ammina tasani ba ita da 'Dan uwanta , dan
Kawu yace bazai gaya musu ba tunda suma basu nemeni ba , Haka aka kawo ni gidan nan
naku gashi yanzu nafara ganin wata rayuwar bacin waccd nabaro......
*K'arshen* *Labarin* *Hanan* datake bawa Nasma ,
*Cigaban* *Labari*
Nasma ajiyar Zuciya tayi sannan tace " tabbas kinga rayuwa a zaman ki na gidan Kawu ,
sannan nan gidan ma akwai tarin k'alubale wanda zaki fuskanta , dan nan d'inma bawani gidan
zama bane , Hanan ta goge Hawayen dake fuskar ta tace " wallahi Babu abinda yabani tsoro
game da cikin gidan nan tamkar yadda Alhaji ya kusanceni ta baya , Bantab'a sanin Namiji ba
amman nasan Ance haramun ne kusantar mace tabaya , Nasma a tsorace ta dubi Hanan
tace " ta baya fa Aunty Hanan ? Kai Hanan ta d'agawa Nasma Alamar Ae dagaske , Salati
Nasma tafarayi tana tafa hannu , can tace " kenan wannan dalilin ne yasa duk Matan da Abba
yake aure suke ficewa , Tabbas ina mamakin Yadda akayi duk wacce Abba zai aura a ta hud'u
saita fita , ashe wanna ce take faruwa dasu , Lallai Yau na tabbata Abba bashida Imani da
tausayi , sannan bashida cikakken ilimi akansa , da sauri Hanan ta toshewa Nasma baki tana
fad'in "kidaina wannan furucin ga Mahaifinki , duk lalacewar Uba dole za'a kirasa da Uba ,
addu'a yakamata ace kinayi mishi Allah ya shiryashi yaganar dashi , Nasma Hawayene ke
zuba ta cikin Idanunta tana ayyana wa a zuciyar ta " Inama bashine Mahaifinta ba , inama ba
agidan aka haifeta ba tabbas wannan ba Mahaifin k'warai bane , Hanan tace " Inaso insan
labarin cikin gidan nan wanda kikace zaki gayamin Shi ....
Nasma ta goge hawaye tace " yanzu zanfad'a miki yadda cikin gidan nan yake , sai dai
akwai wani abinda yake bani tsoro Aunty Hanan, Hanan tace "Kamar me kenan ? duk
wad'anda Abbana yake aura yana saka to tabbas zakiga basa dadewa suke Mutuwa , take
Hanan taji hanjin cikinta ya Juya wani zawo taji yana neman zubo mata , ta dubi Nasma tace
"Shikenan nashiga Uku ni Hanan , yanzu banida ranar dazan fita daga gidan nan kenan ? in
kuma nafita Mutuwa zanyi kenan ? Kuka ta fashe dashi tana fad'in "Wayyo Ammina shikenan
bazan k'ara ganinkiba , shikenan Afrah dasu Ya Zunnur kowa bazan sake ganinsaba , Zoben da
Ya Zunnur yasa mata a hannuwanta tafara dubawa tamkar shi take gani , murzasa take tana
zubar da hawaye tabbas sai yanzu tagane San Ya Zunnur takeyi , dan kullum kafin ayi mata
aure intashiga damuwa tana duba Zoben takejin sanyi , Nasma ce ta dafata tace " Inaso ki
nutsu ki daina damuwa ki cire komai aranki , insha Allah saikin bar wannan gidan cikin k'oshin
lafiya batare da kin Mutu ba , nayi miki Alk'awarin zanfitar dake daga gidan nan namu batare da
kindad'e ba.........
*Last* *Page* βν ΌνΏ»
*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta wannan* *Number*
07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* _Kusiya_ _Kukaranta_
_Cikin_ _Aminci_ ν Ύν΄ν ΌνΏ»ν Ύν΅°
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ν ½νΈν ΌνΌΉ
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
βν ΌνΏ» *MD.*
12.
Hajiya Hajjo ce tashigo cikin kitchen