Showing 39001 words to 41364 words out of 41364 words

Chapter 14 - NI BORA CE BY ZEE MD COMPLETE.pdf

Zee MD   

12 Jul 2025

1635

amare sosai sukayi shigar
Alfarma da angwaye , Anci ansha anzubar da kud'i sosai Mawak'iya Nabeela sosai ta wak"e
Amare sannan aka tashi ....

Sai kuma Angwaye suma suka shirya Reception suda abokansu da Amaren da k'awayensu
, Ankashe kud'i sosai tamkar ba neman su akeyiba.....

Washe gari aka d'aura aurensu su a k'ofar gidan Alhaji Murtala , Kawu Idi shine waliyin
Hanan da Nasma aka bashi sadakinsu dukansu , Nan aka d'aura aure aka sha yinin biki.....

Magriba nayi tuni Zunnur ya turo da motocin da za'a d'aukar masa Amaryar sa , sai tsokanar
Hanan akeyi akan Angon ta yafiye zumud'i itakuwa jikinta yayi sanyi takasa yimusu magana ,
Nan aka kaita d'akin Ammi dan tayi mata fad'a za'a wuce da ita , Ammi kasa magana tayi kawai
tace Allah yabasu zaman lafiya....
Hanan kuka tashigayi tamkar k'aramar Yarinya har aka fito da ita , lokacin motocin d'aukar
Nasma suma suka zo , haka aka Sakasu cikin motocin tafiya gidansu aka kaisu , Unguwar su
d'aya da Hanan da Nasma , Afrah ce Unguwar ta daban tayi musu nisa amman ba sosai ba ,
gidan Hanan aka fara zuwa ka kaita sannan suka wuce gidan Nasma , sosai gidajen su ya
had'u matuk'a ga kayan Furniture da aka jera musu sosai falukan su suka had'u , dan komai iri
d'aya akayi musu babu bambanci , sai muyi musu fatan zaman lafiya da junan su....

Tuni Abokan Zunnur sun rakoshi suntafi dan cewa yayi bayason dogon zance , dariya
sukeyi sosai suna tsokanar sa har suka fice , gidan Haidar ma suna zuwa sukaga tuni ya kulle
gidan sai waya sukayi masa suna tsokanar sa....

Zunnur yana shigowa yasamu Hanan tana kuka , da k'yar ya lallab'ata tayi shuru yace
tatashi ta d'auro Arwala , sunyi sallar godiya ga Allah sannan yadafa kanta yayi mata addu'ar
neman tsari da dukkan wani abin k'i , bayan ya kammala ya mik'e ya d'auko musu ledojin daya
shigo musu dashi , kajine a ciki da lemuka tare da sauran tarkacen kayan k'walam da ma
k'ulashe , janyota yayi jikinsa yana lallab'ata har saida taci ta k'oshi , shima ci yayi sannn ya
d'auki sauran yaje yasa a frizer....

Wanka ya shiga bayan ya fito itama tashiga tayi , tana fitowa taganshi zaune a gefen gado
dagashi sai gajeran wando , kauda kanta tayi sannan taje gaba mirror tashafa mai sannan ta
shafa had'in kulacca da humra , mik'o mata wata riga yayi yace tasaka ta a kunyace ta ansa
tasaka sannan ya janyota suka kwanta , can Zunnur yafara rikitata da wani irin salo wanda bata
tab'a ji ba , sai da yabari ta fita hayyacinta sannan yafara k'ok'arin shigarta , wata k'ara tasaki

saboda zafin dataji ya ratsata dan tunda take ko Alhaji Nasir baitab'a shiga wajen ba shiyasa
bata saniba , shikuwa Zunnur tuni ya fita hayyacinsa saboda ya d'auki hanyar jindad'i sai
sambatu yake haryasamu yashige ciki , tuni jikinta yafara gayamata sosai yake sarrafata
tamkar wani inji tuntana kuka hartayi shuru saboda azaba , saida yagaji dan kansa sannan ya
k'yaleta , d'aukar ta yayi cak yanufi toilet da ita yayi mata wanka yagasata sosai sannan yabata
magani shima yayi wankan sannan suka kwanta ,

haka suma su Nasma da Afrah ta kasance dasu anasu gidajen , sati d'aya sukayi suna
shan Amarcinsu batare da kowacce tayi girkiba sai dai akawo musu Abinci daga gidan Ammi ,
Zunnur kullum yana manne da Hanan yahanata sakat , wani zubin sai ta had'a masa da kuka
sannan yake k'yaleta......

*Bayan shakara biyu*

Hanan ta haifi yarinyar ta wacce taci sunan Hajiya Asma'u suke cemata Hibba , Nasma
kuma sunan Umman su Zunnur wato Aminatu suke cemata Meenal , sai Afrah dake goyon
d'anta me suna Areef , dukansu sunzama manyan mata ga Business dasukeyi na kayan
gyaran jiki da turaruka , ga shi suna order kaya daga dubai sosai sukayi suna , Zunnur
yazama wani Hamshak'in me kud'i tuni yagina musu katafaren gida suka tare , lokacin Nasma
tasamu labarin yan uwanta taje ta kwasosu tasiya musu gida tare da maidasu makaranta me
tsada , Hanan itama ta taka rawar gani sosai wajen taimakawa k'annen Nasma , nan suka samu
Labarin mutuwar Hajiya Hajjo , Safara'u kuwa tuni tasamu wani direba ta aura kuma suna
zaune lafiya abinsu , sosai suke zumunci da Sa'ade kuma tana taimaka mata , dan Kawu idi
sosai shima yake samun kud'i yanzu.......


Hanan na saune a falor Hibba sai rigima takeyi mata , ta dubeta tace " mekikeso ne kika
sakani agaba da rigima ? Hibba cikin gwarancin su nayara tace " akaita gidan su Meenal da
Areef , Alhaji Zunnur ne yashigo cikin falor d'auke da murmushi a bakinsa , Hanan tana
ganinsa tace " Abban Hibba tasamu kenan tunda naga kana murmushi , kashe mata ido yayi
sannan yace " ganinai gidan namu yayi mana girma dayawa mu uku kad'ai , dan haka zan
k'aro miki k'anwa wacce zata tayaki rainona nida Hibba , Hanan tayi murmushi tace " ai kishiya
'Yar uwace Allah yabamu tagari , Zunnur ya rungumeta yace " ashe bakya kishina ko Dear ?
kissing d'inta yashiga yi har saida ta turesa tana nuna masa Hibba , murmushi yayi ya durk'usa
ya d'auki Hibba yana cewa " Babyna shine baki min oyoyo ba ko , turo baki tayi sannan cikin
gwarancin ta tace " Daddy inaso ka kaini gidan su Meenal da Areef tunda Mumy tak'i ,
murmushi yayi yana lakace mata hanci yace " zankai ki gobe in Allah yakaimu kinji Babyna ,
bayan yakaita d'akinta tare da d'auko mata kayan wasa da chocolate yafita , yana zuwa ya
d'auki Hanan itama yana fad'in " muje insamowa Hibba k'anwa ko k'ani dan nagaji da kallonki
haka , tana zille zille har suka shige cikin d'akinsu suka rufo k'ofah .......

Anan nima na ajiye alk'alamina ✍dan bana bisu naganowa idona ba

*ALHAMDULILLAH*

*Anan nakawo k'arshen Book d'in Ni Bora ce*

*Abinda nayi ba daidai ba Allah kayafemun , Abinda nayi daidai kuma Allah yasa ya
Amfanemu baki d'aya*


*Nagode sosai Masoyana yadda kuka dunga bibiyata har Allah yasa nakawo k'arshen
wannan littafin nawa , Allah yabar k'auna ina mutuk'ar godiya kuma nima inasonku kamar
yadda kuke sona* _ILuv U All My Fan's_


*Godiya ta Musamman gareku*


*'Yan K'ungiyar Hamdala Writer's Association* *Allah yak'ara d'aukakata*



*'Yar Mutan Kanawa*
_Ce_
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ‍‍


*Zee* *MD* ✍


27.

Kawu tuni yayi aurensa da wata Bazawara me suna Sa'ade , tana da kirki sosai ba
kamar Safara'u ba , tahad'a 'Ya'yan Safara'u tana rik'onsu Amana tamkar itace ta haifesu.....

Hajiya Hajjo gidan Marayu takai 'Yayan Alhaji Nasir , dan batada k'arfin rik'esu wad'an da
tasan gidan iyayensu kuma tuni takaisu , Dan itama yanzu ciwon baya take fama dashi sosai ,
gashi ita ba yaraba bare tasamu masu jinyar ta , sai 'Yayan 'Yan uwa sune suke kula da ita....

Lokacin da Hanan tagama Iddar ta , tuni Su Zunnur sun kammala karatunsu harya samu
aiki a wani Company a anan Lagos d'in , Tuni yabayyanawa Hanan sirrin zuciyarsa , dafarko
bata amince masa ba ta nuna masa itafa ta tabayin aure taya yana saurayi zai aureta , sosai

yayi fushi da ita yadaina kulata , nan tasamu Nasma sukayi magana Nasma tace " gaskiya
Hanan kinyi kuskuren cemasa hakan , ni aganina Zunnur shine masoyin dayafi kowa dacewa
kiyi rayuwa dashi , ai yasan kintab'a auren kuma karki manta irin fad'i tashin dayayi harkika
samu kanki , inaso ki tura masa da message na amincewar ki tare da ban hak'uri , hakan kuwa
akayi tuni Hanan ta karb'i Soyayyar Yayan ta Zunnur da hannu biyu suka fara shan luv kamar
basuba ...


*Bayan shekara d'aya*
Abubuwa sunfaru da dama ciki harda Haihuwar Ammi , ta haifi d'anta santalele me kama
da Mahaifinsa , murna a gurin su Hanan ba'a magana , Anyi shagalin suna sosai yaro yaci
sunan Mahaifin Hanan wato Mahmood suke cemasa Aman. lokacin Aka saka ranar Auren
Hanan da Zunnur itakuma Nasma da Haidar sai kuma Afrah da Usman Abokin Haidar ...
Matar Kawu Idi koda yaushe suna waya dasu Hanan , lokacin da Ammi ta haifi Aman Har
suna tazo suna zuminci sosai ,....
Bugo musu waya Kawu Idi yayi yace itama ta haihu , nan su Hanan suka fara tsalle zasuje
Jos suna , da farko Ammi cewa tayi Hanan bazataje ba ita da Nasma , nan sukaita magiya dan
Allah tabarsu suje insha Allah babu abinda zaifaru , Ana gobe zasu tafi Zunnur yazo shima, da
farko shima tuburewa yayi akan Hanan d'in bazataje Jos ba , sai da Nasma tasaka baki suka
lallab'ashi yace to ya yadda amman shine zai kaisu , haka kuwa akayi washe gari suka d'au
Hanya da Ammi da Hanan da Afrah sai Zunnur ......

Sun isa lafiya Abinsu sunsamu tarba me kyau dan Sa'ade akwai mutunci , Bayan sun huta
Nasma tacewa Afrah da Hanan suzo su rakata gidan wata k'awarta , Ammi nacan tana hira da
'Yan uwan Sa'ade suka fice zururu Abinsu , Zunnur shima tuni yashiga gari dan akwai wani
Abokinsa da sukayi karatu tare shine zai kai masa ziyara......
Bayan su Hanan sunje gidan k'awar Nasma sunfito , Nasma tace " inaso dan Allah muje
gidan Babana dan ina kewar 'Yan uwana sosai , Hanan tace " Amman kinsan kasada zamuyi
zuwan mu gidan ku ko , Nasma tace " basai munshiga ciki ba kawai sonake ko megadi ne insa
yaturo mana su ingansu plss , ganin Yadda Nasma ta marairai ce yasa Su Hanan suka Amince
mata , haka suka nufi gidan su Nasma gidan Alhaji Nasir .....

Koda zuwansu suka samu k'ofar gidan cike da mutane , da sauri suka k'arasa suna
tambayar wani yaro meyake faruwa ? Nan yace musu gidan ne yake wani irin wari , gashi 'Yan
unguwa har sunfara amsi da gudawa saboda warin gidan , shine aka kirawo jami'an lafiya dan
suduba sugani ko meye a ciki , Adai dai lokacin aka fito da Gawar Alhaji Nasir harya fara zama
tsutsa , da sauri mutane suka fara gudu suna toshe hancinsu , Hanan ma da Afrah tuni suka ja
da baya suna toshe hancinsu , Nasma kuwa tsayawa tayi tana kallon gawar Mahaifin nata ana
k'ok'arin sakashi a cikin Ambulance , Hawaye idanunta yashiga yi ba k'ak'k'autawa tamkar
anbud'e famfo , yanzu wannan gawar mahaifintace ya mutu a wulak'ance tabbas wanda yayi
nagari kansa , can saigashi anfito da kawunan mutane dayawa sunafara zama k'warangwal

acikin gidan , take mutane suka fara tsinewa Alhaji Nasir suna fad'in " inama bai mutu ba wallahi
dasai sun k'oneshi da taya , Kuka sosai Nasma tashiga yi tamakar ranta zai fita , Hanan da
Afrah tuni suka kamata suka bar wajen da ita.....

Basu suka dawo gida ba sai magriba , suna shigowa sukaga Ammi da Zunnur a tsaye Ammi
na goya Aman zasuje neman su , yanayin da suka gansu dakuma Nasma yasa suka san ba
lafiya ba , Samun waje sukayi suka zauna sannan suka shiga gayawa su Ammi duk Abinda ya
faru , Nan Ammi tashiga lallashin Nasma tare da cewa tayi masa addu'a tasanadin hakan saiya
samu sassauci , Kawu Idi shima yana shigowa da zancen yayi karo , cikin ransa yayi godiya
tare da addu'ar arrage mugun iri , amman saboda Nasma saida ya tausaya.....

Safara'u da k'yar tasamu sauk'i , tunda taji sauk'i takeson zuwa wajen Kawu Idi ta nemi
gafararsa, sai dai takasa zuwa saboda tanajin Nauyin irin abuwan datayi masa , haka dai ta
yanke shawara yau zataje tabashi hak'uri tare da neman gafara ko Allah zaisa ya maidata....


*Insha Allah gobe zan kammala Littafin Ni bora ce*
*Inaso kowa gobe yafito dan tayani murna tare da celebration*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login