Showing 33001 words to 36000 words out of 41364 words

Chapter 12 - NI BORA CE BY ZEE MD COMPLETE.pdf

Zee MD   

12 Jul 2025

1636


yaro tuni tafara hango kanta a gidan Alhaji Nasir tana baza mulkinta.....

Kawu Idi ransa ba k'aramin b'aci yayi ba , dama yadad'e yana zargin Safara'u tana son
Alhaji Nasir saboda taga yana da kud'i , yau yaga gaskiya da kansa dan haka taje gata ga
shinan , Abin kunya be dai ace Hanan na gidansa da aure itama tashiga gidan , tabbas zaisan
yadda zaiyi ya hana Alhajin Hana kula Safara'un.....
Bayan su Hanan sungama cin Abinci Nan suka kuma gaisawa da tambayar bayan saduwa ,
Alhaji Murtala yatashi yafita saboda kiran da akayi masa a wajen aikinsu , Hajiya Asma'u kuma
k'anwarta tazo itama ta mik'e suka shiga ciki , yarage sai su Hanan da Nasma da Zunnur da
Ammi , Ammi ta dubi Zunnut tace " yaushe kadawo gida banida labari ? Zunnur ya gyara zama
sannan yace " Akwai muhimmiyar magana a game da Hanan Ammi , Ammi tace "tunda
nagansu haka ita da wacce suka zo nasan ba zuwan dad'ine ba , Nan tace " inajinka kasanar
dani komai banaso ko kad'an a boyemin wani Abu , Nan Zunnur ya shiga gayawa Ammi tun
randa yaje gidan Kawu Idi da yadda sukayi dashi har takawo zuwansa gidanta shida su Hanan
bai b'oye komai ba .......
Ammi tuni taji wani gumi yana karyo mata wato duk mafarkin datake akan Hanan ashe da

walakin , Mik'ewa tsaye tayi tashiga yin safa da marwa a cikin Palor , tabbas Idi yaci Amanar
zumunci wato shine ya aurar da 'Yar ta batare da tasaniba , ta dad'e ahaka sannan tadawo ta
zauna ta dubi Hanan tace "waye mijin naki kuma a ina yake inaso nasan waye wanda ya aura
miki ? Dai dai lokacin Hajiya Asma'u tafito ta nufi cikin kitchen , Abincinci ta zubowa K'anwar
ta ta fito kuma a dai dai lokacin Hanan ta furta Ya aurar dani ga wani me kud'i wanda ake
sakawa a lissafin masu kud'in Jos wato Alhaji Nasir , Tuni farantin Abincin da Hajiya Asma'u ta
d'ebo ya sub'uce daga hannunta , jitayi gabanta ya yanke ya fad'i lokaci d'aya jikinta yafara
rawa , dukansu juyowa suna kallonta kafin suce " Lafiya kuwa ? sauri tayi ta dawo dai dai tare
da cewa " wallahi sub'ucewa yayi daga hannuna , Nasma da sauri ta mik'e ta nufeta tana fad'in
" bai dai fad'o miki a k'afa ba ko ? duban Nasman tayi tana murmushi tace " bai fad'oba 'Yata
koma ki zauna zangyara da kaina , sunan da takira Nasma dashi ba k'aramin dad'i yayiwa
Nasman ba , sunkuyawa tayi tana kwashewa da hannunta tana xubawa cikin filet d'in , Hajiya
Asma'u sai k'ok'arin Hanata takeyi Amman tak'i , saida ta gyara wajen tsaf sannan ta koma ta
zauna , nan Hajiya Asma'u ta shiga sa mata Albarka ......
Lab'ewa Hajiya Asma'u tayi dan tanaso taji labarin Hanan d'in , tabbas tanaji a jikinta
tamkar Alhaji Nasir d'in data sanine za'abada labarinsa .....

Nan Hanan tashiga bawa Ammi da Zunnur labarin Rayuwar datayi tundaga lokacin da Kawu
yazo ya d'auketa , har Auranta da Alhaji Nasir da irin wahalar datasha agidansa da kuma yadda
Nasma ke taimaka mata tare da yadda yadunga mu'amalar aure da ita bata b'oye musu komai
ba , Kuka sosai Ammi takeyi ita kanta Hanan d'in Kuka takeyi Nasma kuwa hawayene ke zuba
a idanunta , Zunnu kuwa tuni idonsa ya kad'a yayi jajir , tabbas da yanzu zaiga Alhaji Nasir
baiga abinda zai hana bai kaishi lahiraba , wata muguwar tsanar Kawu Idi yaji ta kamashi
duban Ammi yayi wacce take kuka har wannan lokaci yace " kishare hawayenki Ammi , Yanzu
ba lokocin kuka bane tabbas nayi Alk'awari sai na d'aukarwa Hanan fansar Abinda Sukayi mata
, Hanan ta share hawayenta sannan tace " Abinda ya gudo damu yanzu daga gidan Alhaji
Nasir yanzu kuma shine yana tsafi yakeyi da shan jini , kuma yanzuma haka neman mu yakeyi
yayi tsafin damu , Ammi ta Hanan tace "Itama wannan d'in Matarsa ce ? Hanan tace " 'Yarsa
ce ta cikinsa kuma itama harda ita yakeson Halakamu , duban Nasma Ammi tayi sannan tace "
Tabbas ke 'Ya tagari amman baki sa'ar Uba nagari ba , Mahaifiyarki tana ganin tashin hankali
dan zama da irin wannan mijin tamkar zama a kabarine , Hanan tace " Batasan Mahaifiyar ta
ba tun tana yarinya suka rabu da shi ,

Hajiya Asma'u duk labarin da Hanan takeyi a cikin kunnenta taji komai , Kuka takeyi me
cike da murna dan tabbas tasan ko ba'a fad'a mata ba tasan Nasma 'Yar tace wacce tabar
gidan Babanta tana 'Yar shekara biyu , da sauri ta fito daga cikin kitchen ta nufi wajen Nasma
ta rungumeta tana kuka tana fad'in " tun shigowarki cikin gidan nan naji ajikina tabbas ked'in
jininace , ashe kuwa hakan ce Nasma ked'in 'Yatace wacce na haifa da cikina , duk labarin da
Hanan takeyi inajinku kugafarce ni bana lab'e dan wani abubu sai dan fitowa ta danayi naji
Hanan ta ambaci sunan Alhaji Nasir Jos , to daga nan naji inaso insan labarin dazata bayar ,
tabbas Alhaji Nasir yadad'e yana aikata zunubi a cikin duniya , Dukansu sakin baki sukayi suna
duban Hajiya Asma'u tare da tarin tambayoyi da mamaki a bakunansu , tabbas zasu so jin taya
akayi Nasma tazamo 'Yarta ? taya tasan Alhaji Nasir ? ....

Dubansu tayi dukansu tace " nasan zakuso jin taya nakasance Mahaifiyar Nasma ko ? to
kafin kusani inaso dan Allah ku nutsu sosai ku dubeta sannan kudubeni nasan ko a hakan zaku
gamsu da wani Abun , dukansu kafawa Hajiya Asma'u idanu sukayi sannan suka fara duban
Nasma itama....
Safara' u koda taje gida Iyayenta basu damu ba , dan suma sarakan san kud'ine gado
itama tayi , nan suka karb'i maganar Alhaji Nasir tare da tsaida rana sati d'aya yazo a d'aura
masa aurd da ita , tuni Alhaji Nasir ya jik'asu da kud'i dan yaga suna buk'ata dayawa , yana
tafiya suka fara murna suna suma kwanan nan zasu faso gari , Nan Safara'u tafara hura hanci
tana wani jan Aji ita a dole zata auri me kud'i..........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³


*Zee* *MD* ✍🏻


25.

Kawu Idi yadubi Hajiya Hajjo yace " dan Allah ina Hanan take ? tab'e baki tayi
sannan tace " ai sunfi sati biyu basa gidan nan ita da yarinyar wajen Alhaji , kuma yadda yace
mana wai sun gudu ne saboda sunyi masa sata shima neman su yake , sosai Kawu Idi yashiga
mamakin maganar Hajiya Hajjo , sallama yayi mata ya fice cikin ransa yana fad'in dole ya shirya
yaje Lagos ko Hanan taje can .........

Alhaji Nasir nashiga cikin d'akin sa tuni yayi zindir yafara kiran dodon tsafinsa , suna fara
ganawa kenan saiga Safara'u tashigo cikin d'akin dai dai lokacin da Alhaji yake shan jini yana
wanka dashi a cikin wata k'warya , yanayi yana zagaye yana fad'in " Safara'u ! Safara'u !!
aikauwa tuni Safara'u k'irjinta ya buga tafara ja da baya tana ganin wani k'warangwal d'in kai
yana zubar da kud'i kuma fuskar kamar ta matar Alhaji Nasir d'in data mutu , juyowa Alhaji
Nasir yayi sukayi ido biyu da Safara'u tuni yayo kanta da sharb'ebiyar wuk'arsa , ai tuni Safara'u
tajuya tafice da gudu tana neman matsera , Hajiya Hajjo taganta da gudu tana ihu tana fad'in "
Alhaji zai kasheni wallahi shan jini yakeyi , Hajiya Hajjo batagama jin Maganar Safara'u ba taga
Alhaji Nasir zindir shima yataho da gudunsa , tuni itama ta juya da gudu tana neman matsera ,
Alhaji Nasir yana ganin haka yatuna a yadda yafito tuni ya juya yana cizon yatsa na rashin
kama Safara'u dan wallahi yau dasai dai wata ba itaba , amman yanzu ma tunda har tagansa
wallahi saita mutu dan bazata tona masa asiri ba ......

Safara'u tuni tafice daga cikin gidan sai gudu take tamkar zata ci da baka , duk nisan dake
tsakanin gidansu da gidan Alhaji bata ganiba tuni takawo gida , da gudu tashigo tana ihu ba
gyale ba d'ankwali bare takalmi kuma , tana shigowa ahaka suma suka mik'e suna neman
matsera , dan cewa take gashinan da wuk'a zai yankani yasha jinina.....

Hanan ansamu Nassarar yi mata aiki , Alhaji Murtala shine ya biya kud'in da akayi mata
aikin , lokacin Ammi ta yanke shawarar zuwa tasamu Abban su Zunnur tagaya masa duk
abinda ke faruwa , waya ta kira ta tambayi Umman Zunnur tace mata yana gari , dan haka
tashirya daga asibitin ta wuce tabar Nasma a wajen Hanan d'in , dama da ita da Nasma suke
kwana a gunta Hajiya Asma'u kuma kullum sai tazo takawo musu Abinci...

Lokacin dataje gidan tasamu Yayan nata da maganar Hanan d'in , sosai yayi mata fad'an
rashin gayamasa dabatayi ba , sannan yayi Alk'awarin zuwa Kano wajen Kawu Idi yaji dalilin
dayasa yayi wa Hanan d'in hakan , kuma sosai ya jinjinawa Zunnur da irin k'ok'arin dayayi
wajen kawo su Hanan d'in Nan , Afrah najin ance Hanan tazo tana asibiti tuni tafara shirin bin
Ammi dan tace saitaje taga Hanan d'inta....

Zunnur tunda yaji Ance Hanan ba lafiya dama gashi sunsami hutun sati Uku , tuni suka
had'o kayansu suka nufo Lagos....
Afrah tana ganin Hanan tasaka kuka ganin yadda Hanan d'in takoma, dak'yar Ammi ta
lallab'ata Nasma ma tasa baki sannan tayi shuru , Hanan kuwa haryanzu bawani gane mutane
take ba saboda wuyar datasha sosai , dan likitan dayayi mata aiki cewa yayi data k'ara wasu
watannin da tsutsotsi ne zasu fara fitowa ta gabanta , gashi dole zata koma tana neman maza
ko mata kuma ta baya , lokacin daya fad'i wannan maganar sosai su Hajiya Asma'u da Ammi
sukayi kuka , Abban su Zunnur shima sunzu shida Umman Zunnur sosai suka tausayawa
Hanan , sosai yayiwa Alhaji Murtala godiya ganin yadda yanuna damuwa akan Hanan d'in
tamkar shine ya haifeta , kullum daga gidan Su Afrah sai ankai musu Abinci nan ma......
Su Zunnur suna da wowa ko hutawa baiyiba yashirya ya nufi Asibiti , yana zuwa lokacin
Hanan tana bacci su Ammi da Afrah da Nasma suna zaune a reception sai hira suke , shima
zama yayi yana d'an tayasu kafin Hanan d'in tatashi .....

Safara'u tuni tazama k'aramar Mahaukaciya , dan kullum cikin zabura take tana ihun fad'in
gashin yazo da wuk'a zai yankata , lokacin da Alhaji Nasir yazo guduwa tayi d'aki tasa sakata
tafara ihu , Babanta yace ya k'yaleta kawai intaji sauk'i ta dawo , haka Alhaji Nasir yatafi yana
shirya ta yadda zai d'auketa daga gidan...

*Bayan kwana biyu*
Hanan sosai jikinta yayi sauk'i , har hira suke ita dasu Zunnur daya tare a Asibitin , Haidar ma
yana zuwa sosai saboda yaga Nasma dan yana ganinta yaji tashiga ransa , itama sosai take
sakin jiki suyi hira da shi , ga Afrah data zama tamkar 'Yar uwarta saboda shak'uwa , Koda jikin
Hanan yayi sauk'i sosai aka sallamesu suka koma gida....
Kawu Idi ne ya dira a gidan su Zunnur , Yayi sa'a kuwa yasamu Alhaji Bashir wato Baban su
Zunnur d'in , nuna masa yayi baisan Hanan tazoba saboda yaji da wacce yazo , aikuwa Kawu
ya karkace yanafad'in wai Hanan sunyiwa Alhaji Nasir sata ita da 'Yarsa sungudu , shine yazo
nemanta ko Allah yasa sunzo nan , aikuwa tuni ran Alhaji Bashir yakuma b'aci tuni yafara fad'a "

Hanan sunzo nan tunda acan ana neman kasheta bata da gata , Nan yashiga yiwa Kawu
sababi tare da sheda masa komai da Alhaji Nasir yakeyiwa Hanan d'in , tuni jikin Kawu Idi yayi
sanyi yafara hawaye sosai , Alhaji Bashir yaci gaba da cewa " karka ga wannan abun dakayi ko
Allah zai barka dole sai Allah yasaka mata , kana matsayin Mahaifin a gunta saboda san abin
duniya ka d'auketa kabawa me shan jini ita , sosai Nadama ta shiga Kawu yadunga kuka yana
neman afuwa tare da cewa araka shi gidan Ammi yaga Hanan d'in ya rok'eta gafara , tare suka
shirya shida Alhaji Bashir suka nufi gidan Ammi.....

Alhaji Nasir yanzu hankalinsa a mugun tashe yake saboda Dodon tsafinsu yana buk'atar jini
, gashi Hajiya Hajjo ta kwashe yaran gidan duka sungudu har Alawiya ba wanda aka bari ,
neman duniya yayi musu amman bai gansuba , dan tun randa Hajiya Hajjo tagansa da wuk'a
tafara yadda da rad'e rad'in mutane , shiyasa ta sulale ita da yaran gidan suka gudu tare da
Alawaiya .....

Lokacin da Kawu yaje gidan Ammi suna ganinsa Hanan ta b'uya a bayan Hajiya Asma'u ,
gaisawa sukayi da Hajiya Asma'u itakuwa Ammi ko kallonsa batayi ba , sosai Kawu yanuna
nadamar sa akan Abinda yayiwa Hanan d'in , Anan yakejin Nasma 'Yar gidan Alhaji Nasir itama
ta had'u da Mahaifiyar ta , sosai yayi dad'i tare da neman afuwar Hanan d'in , tayafe masa inda
suka tsaida ranar tafiya Jos dan zuwa karb'owa Hanan takardar sakinta...


Alhaji Nasir cikin dare ya fito da niyyar zuwa gidan su Safara'u , dan Dodonsa yabashi
kwana biyu akan indai bai zubar masa da jini ba to duk zai nemi dukiyar sa yarasa ta , yana
zuwa gidan su Safara'u yasamu gidan nasu a bud'e ba'a rufe ba , lokacin zafi akeyi duk suna
tsakar gida a kwance , yana zuwa yafara lalub'en Safara'u ita kuwa lokacin tana cikin d'aki tana
surutan ta wanda tasaba , aikuwa kamar an mintsineta tafito tsakar gida aikuwa sukayi ido biyu
da Alhaji Nasir take ta kurma ihu tana fad'in " gashinan yazo yankani wayyo , dukansu suka
mik'e aikuwa sukaga Alhaji Nasir tuni suka bishi da gudu aikuwa yayi maza ya fad'a motar sa
yagudu........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³


*Zee* *MD* ✍🏻


24.

Su Hanan sunyi k'alau dasu tamkar basu ba , tuni sun sake a cikin gidan tamkar
daman sundad'e da zuwa , Ammi kullum cikin siya musu kayan k'yale k'yale take , itama Hajiya
Asma'u haka ga 'Yayanta suna girma ma su Hanan , yanzu abinda yake damun Hanan shine
yawan ciwon ciki dayasako ta a gaba , gashi tak'i tafad'awa kowa tana ciwon ciki , Nasma ma
dasu kwana tare itama batasani ba , Yauma kamar kullum suna cikin d'aki a kwance wajen

k'arfe goma da rabi na dare , ciwon cikin ne yafara mintsinin Hanan tafara cije leb'e tamkar me
Nak'uda , Nasma ta dubeta tace " ke kuma meye yake damunki haka ? tund'azu naga sai cije
leb'e kike tamkar wacce take labour room , Hanan data fara fita hayyacinta tace wa Nasma "
kiramin Ammi Dan Allah wayyo cikina wallahi inajin mutuwa zanyi , da sauri Nasma tatashi
zaune tana dubanta ganin da gaske Hanan tana wani irin Abu yasa Nasma fita da gudu tana
kiran Ammi ....
Lokacin Ammi tana zaune kan sallaya tana karatun Alkur'ani me girma , jitayi ana kiranta
kuma daga jin kiran ba na lafiya bane , da sauri ta rufe Alkur'anin tana shirin mik'ewa , dai dai
lokacin Nasma ta shigo tana fad'in " Ammi kizo Hanan bata da lafiya da sauri suka juya zuwa
d'akin Hanan d'in , lokacin Hajiya Asma'u itama tafito daga d'akin Alhaji Murtala , dukansu suka
shiga d'akin da Hanan d'in take , suna zuwa suka sameta wata kumfa na fitowa daga bakinta
tamkar wacce tasha guba , da gudu sudukansu sukayi kanta suna kiran sunanta , Nasma tuni
tafara kuka tana fad'in " dan Allah Hanan karki mutu kibarni , duk duniya dake nasaba bazan iya
bud'e ido inga bakya tare dani ba , tuni Hajiya Asma'u tafita kiran Alhaji Murtala dan suje asibiti ,
Ammi kuwa tana rungume da Hanan sai addu'a take tofah mata hawaye na zubowa ta cikin
idanunta , Hajiya Asma'u ce tadawo ta sunkuya ta d'auki Hanan da dukka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login