Showing 36001 words to 39000 words out of 41364 words

Chapter 13 - NI BORA CE BY ZEE MD COMPLETE.pdf

Zee MD   

12 Jul 2025

1629

k'arfinta tace " kuzo
muje Asibiti ga Alhaji can ya fito da motar......

Acan b'angaren Alhaji Nasir kuwa " Safara'u tafara zuba mulki a cikin gida , dan Hajiya
Hajjo duk bala'inta bata saka Safara'u aiki , dan kusan kullum sai sunyi fad'a da ita , yauma
tamkar kullum Safara'u ce ta fito sai taunar cingum take tamkar wata karuwa , Hajiya Hajjo tana
gayara kayan miya lokacin Safara'u ta dubeta tace " wai daman haryanzu baki d'oramana
Abinci ba kinbar mutane da yunwa ? Hajiya Hajjo tadubeta shek'e k'e tace " ban d'oraba kozaki
yimin hukunci ne daboda hakan ? Safara'u tayi wani shu'umin murmushi sannan tace " bazan
yi miki hukunci ba , sai dai zakiga Abinda zai faru dan wallahi sai kin raina kanki , ta juya ta nufi
d'akin ta tana turo mazaune ......
Alhaji Nasir shida Abokinsa Alhaji Hamza suna gurin dodon su suna magana dashi , Anan ne
dodon nasu yake ce musu yanason shan jinin Mata d'aya da yara guda uku , Bayan sungama
magana dashi Alhaji Nasir ya dubi Alhaji Hamza yace " yanzu kai wanne zaka bayar daga ciki ?
tunda jinin mutum hud'u yakeso dole kai biyu nima biyu haka zamu bashi , Alhaji Hamza yayi
ajiyar zuciya sannan yace " a gaskiya yanzu mata ta taragemin kuma yanzu haka cikine da ita ,
inaso ta haihu saboda kasan yanzu banida d'a ko d'aya duk nabada su , kai kuma kaga gidan
ka akwai mata har guda uku kuma ga yara kana dasu dayawa , Alhaji Nasir yayi shuru yana
nazari suwa yakamata yabawa dodo ? tabbas da Hanan na nan wallahi saiya bada ita ita da
Nasma , ammam yanzu dole ya zauna yayi shawara yaga wad'an da yadace yabayar , da yayi
niyyar bada Safara'u amman yaji tana da dad'in harka ta baya sosai , duk matan da yake aura
ba wacce take bashi had'in kai wajen kusan tar ta ta baya kamar ita , yankewa yayi zai bada
Alawaiyya da kuma wasu daga cikin yaran nasa , duk dayaga mutane sunfara saka ayar
tamabaya akansa ganin yadda akeyin mutuwa agidansa kuma duk iri d'aya........


Tunda aka shigar da Hanan asibiti likitoci suka rufu akanta , Nasma inbanda kuka babu
abinda takeyi , Ammi ta janyota cikin jikinta tana rarrshin ta , dan tasan dole tayi kuka dan ko ita

data haifi Hanan yanzu bazata nuna mata shak'uwa dasukayi ba .....
Likitane yafito daga cikin d'akin Da Hanan take , cewa Alhaji Murtala yayi yabiyoshi Office
yanason magana dashi , tuni Jikinsu Ammi yafara rawa cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba
mutuwa tayi ba , Alhaji Murtala tuni ya mik'e yabi bayansa suka shige cikin office d'in , samun
guri Dr. Yayi ya zauna sannan ya nunawa Alhaji Murtala guri yazauna shima , glass d'in idonsa
yacire sanna yadubi Alhaji Murtala yace " A gaskiya Alhaji wannan yarinyar taka akwai Babbar
matsala atare da ita , wato binciken da mukayi akanta mun gano wata tsutsa da aka saka mata
a cikin cikinta wacce ake sakawa masu yin Mad'igo , ina nufin maza masu neman maza 'Yan
uwansu ta baya , salati Alhaji Murtala yayi sannan yadubi likitan yace " yanzu meye mafita Dr. ?
wallahi Mijinta ne yayi mata wannan Abun haka , Dr. Ya dubi Alhaji Murtala yace " kana nufin
kace tana da aure kuma mijinta ta baya yake kusan tar ta ? Alhaji Murtala yace " tana da aure
amman a yanzu bata dashi kuma saboda hakan aka rabasu da Mijin , numfashi likitan yaja
sannan yace " tabbas wannan mijin nata ya cuceta sosai , dan yanzu haka tana gab da fara
zubar da wani irin ruwa me wari ta gabanta mutuk'ar ba'ayi gaggawar yi mata aiki ba , Alhaji
Murtala yace " Dr. Inaso ayi mata aikin ko nawa zamu biya plss tunkafin tafara zubar dashi d'in ,
Dr. Yadubi Alhaji yace " bamayin irin wannan aikin a wannan asibitin , sai dai akwai wani
Abokina sunayin aikin a Asibitinsu zan had'a ku dashi sai kuyi magana , godiya Alhaji Murtala
ya shiga yiwa likita , nan Dr yabawa Alhaji number Dr Tahir sannan shima yakirashi a waya
sukayi magana a gaban Alhajin , likita yace " sai kuyi gaggawar kaita dan ciwon yadad'e yana
cin jikinta baku sani ba sai yanzu ya nuna , nan Alhaji yayi masa godiya sannan yafito daga
office d'in , su Ammi dukansu suka mik'e suna tamabayar sa lafiya kuwa ? bai ce musu komai
ba ya nufi d'akin da Hanan take a kwance lokacin bacci take sabida alluran da suka yi mata ...
Duk yadda sukayi da Dr. Sai da yagaya musu , salati suka saka tare da yin Allah wadai da
halin Alhaji Nasir , Nan suka d'auketa aka nufi wancan asibitin daza'ayi mata aikin da ita.....

Kawu Idi yana sane da auren da Safara'u sukayi ita da Alhaji Nasir , yau takanas ya shirya
dan zuwa gidan yaga Hanan dan yaji shuru Alhajin bai ce tadawo ba , yana zuwa gidan dayake
me gadi ya sheda sa tuni yabarsa ya shiga ciki , koda shigar sa yasamu wani yaro daga cikin
yaran Alhajin yace yaje yakira masa Hanan acikin gidan , dayake yaron bashi da wayo dan
haka baisan Hanan d'in ba tuni yashige cikin gidan yana kiran sunan Hanan , dai dai lokacin
Safara'u ta ci uwar kwalliya wai zataje yawo ita ala dole ga matan masu kud'i , tarar yaron tayi
tana fad'in " waye ya aiko ka kairan shegiyar yarinyar data shiga duniya ? yaron yace " wani ne
a waje yana jiranta , Safara'u ana rik'e da mayafi a hannu da jaka akayi hanayar fita , Hajiya
Hajjo tana hango fitar ta tabiyo bayanta sadaf sadaf tana lek'en ta , koda Safara'u ta k'araso
wajen da Kawu yake wani tsaki taja tare da murgud'a baki , cikin kallom rashin mutunci ta
dubesa tace " wai dama kaine kake kiran Hanan d'in ? to mu anan gidan bawata me wannan
sunan , dan haka ka iya jan jiki ka ficemin daga cikin gidan mijina , inkuma ba haka ba wallahi
yanzu zanhad'a maka mutane ince kazo guna kwarton ci , Kawu ya dubeta sama da k'asa wani
takaici yakamasa yace " ni bana magana da wacce bata san mutuncin kanta ba bare na aure ,
tunkafin ranki yayi mugun b'aci inaso kibar wajen nan yanzu yanzu , wata shewa Safara'u tayi
tare da tafa hannuwa tace " nafi k'arfinka ta ko'inah wallahi Idi , kadubeni sama da k'asa ni ba
matar Matsiyaci bace wanda bashi da ko anini , tuni zuciya ta d'ebi Kawu Idi ya d'auke Safara'u
da wani mahaukacin mari , dai dai nan Alhaji ya kunno hancin motar sa cikin gidan , akan

idonsa Safara'u ta cakumi wuyan Kawu Idi tana tura kanta cikin jikinsa tamakar wata k'aramar
yarinya masu kokawa , aikuwa Alhaji Nasir tuni yaji wani kishi ya turnik'eshi wato dama
munafika tana son tsohon mijinta take raina masa hankali , tuni ya bud'e motar a fusace yana
nufo wajen dasuke , yana zuwa ya wanke Safara'u da wani mahaukacin mari yana nunata da
d'an yatsa " wato ni zaki ciwa Amana kenan ? duk irin kud'in danake turamiki sai kin dunga
nemo tsohon mijinki kina munafinta ta , Kawu Idi yace " wanda da Allah ya kawoka Alhaji , dan
tun d'azu take jana wai saina shiga ciki munkwanta da ita , Safara'u jikinta yana rawa tafara
fad'in " wallahi k'arya yakemin bancd masa haka ba , Muryar Hajiya Hajjo sukaji tana fad'in "
bawani k'aryar dayake miki inajinki ina kuma kallonki , tuni ran Alhaji Nasir yakuma b'aci yafasa
bawa dodonsu Alawiya wallahi Safara'u zaibada ya auro wasu matan, tuni ya shige ciki da
sauri tare da tunkarar d'akin sirrinsa , Safara'u ganin haka ta rud'e satake sakinta zaiyi tuni tabi
bayansa batare da yasani ba..........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³


*Zee* *MD*✍🏻


26.

Tun daga lokacin 'Yan gidan su Safara'u suka fahimci Alhaji Nasir matsafine ,
tunda ga ranar suka fara taka tsantsan suma dan sun tsorata sosai , Safara'u kuwa hauka take
tuburan tana zabure zabure , tuni suka fara fafutukar nema mata magani.......

Alhaji Basir tuni suka gama magana akan zuwa Jos ansowa Hanan takardarta ,dan baza tai
ta zama da igiyar aure akanta ba , Kawu yace " kayi zamanka kawai basai kajeba tunda nine
nahad'a to kuwa nizan rabashi , Hakan kuwa akayi Kawu ya shirya yayi musu sallama ya
koma...
Hanan tuni jikinta yayi sauk'i sosai , yanzu ma Alhaji Bashir yayi magana da Zunnur akan
asamar mata makaranta tafara zuwa , Zunnur tuni ya sanar da Umman sa yanason Hanan ,
sosai taji dad'in Abin amman tace yabari komai ya lafa sai ayi magana , Abban su Zunnur
dagewa yayi akan Hanan ta dawo gidansa amman Alhaji Murtala yak'i , dole haka yabar ta taci
gaba da zama a gidan , Nasma kuwa tuni dangin Hajiya Asma'u suka d'auketa Kano zataga
'Yan uwa , Haidar sosai yaji dad'in zuwan Nasma kano , dan tuni suka koma sch sunfara shirye
shiryen kammala Degree d'insu ,

Kawu Idi so biyu yana zuwa gidan Alhaji Nasir amman a kulle , ko megadi baiganiba cikin
ransa yace " kowa ya gudu kenan , Anan yasamu labari ba kowa a gidan shima megidan kwana
biyu ba'a ganin gilmawar sa , dawowa gida yayi anan ya had'u da k'anin Safara 'u yabashi
labarin Abinda yake faruwa da Safara'u , ko kad'an Kawu Idi bai tausaya mata ba saima Allah
yak'ara dayace , ya kad'a kansa yayi gida dan shiyanzu tsoron duniyar ma yakejin , yanzu

yagama magana da wata bazawara zasuyi aure sati me zuwa .....

Hanan tafara zuwa sch ga wayar ta me kyau da Hajiya Asma'u tasiya musu ita da Nasma
,

Suna waya da Zunnur sosai kusan kullum suna manne a waya , tuni Alhaji Bashir sunje
kotu an ansawa Hanan takardar sakinta wajen Alk'ali , dan kwata kwata annemi Alhaji Nasir
anrasa .....

Nasma tadawo Lagos wajen Hajiya Asma'u da zama , karatun ta taci gaba dayi gefe guda
kuma suna tare da Haidar suna zabga soyayyar su.......

*Kuyi hakuri wlh yau fita nayi*🙏🏻🙏🏻
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³


*Zee* *MD* ✍🏻


28.

*THE* *END*
*THE* *END*
*THE* *END*


Ranar suna yarinya taci sunan Ammi wato Hadiza suke kiranta itama da Ammi , sosai
Ammi taji dad'in karar da akayi mata , Su Hanan ma sosai suka tayata farin ciki , Ana cikin
shagalin suna saiga Safara'u tazo , Da Hanan tafarayin karo a tsakar gida ita da su Nasma ,
sunkuyar da kai tayi k'asa kamar munafuka tana tafiya a hankali , Hanan kuwa tayi murmushi
sannan tace " Aunty Safara'u sannu da zuwa ashe kinanan ? Safara'u ta yashe baki tana fad'in
"la Hanan kune agari haka sannunku da zuwa , Ina Ammin ki ? Hanan tace tana cikin wannan
d'akin , da sauri Safara'u tashige cikin d'akin ta addu'ar Allah yasa Ammi tasa baki Kawu Idi ya
maidata......
Afrah tadubi Hanan tace " Sister wannan ai kamar matar Kawu ta da ? Hanan tayi
murmushi sannan tace "ea itace kinga yadda takoma ko ? ta dubi Nasma tace itama fa saida ta
auri Daddynki kinganta nan duk ta lalace tamkar me Hiv , Nasma tace " ai tunda naji kince aunty
Safara'u naganeta , Allah ya kyauta daman ai wanda ya hau motar kwad'ayi zai sauka a tashar
wulak'anci .......

Safara'u koda tashiga cikin d'akin da Ammi take kasa ganeta Ammi tayi , da k'yar tagane
ta suka gaisa Ammi tashiga mamkin yadda Safara'un takoma , duk da Kawu yabasu labarin

Abinda tayi kaf amman saida ta tausaya mata , nan Safara'u tafashe da kuka tana rok'on Ammi
gafara duk abinda tayi mata , Ammi tausayin tane yakamata tace " Allah yayafe mana baki
d'aya , Sa'ade ce tashigo cikin d'akin Safara'u ta kalleta , ko ba'afad'a mata ba tasan wannan
itace matar da Kawu Idi ya aura , dan yaranta insunje suna gayamata yadda take yi musu
komai tamkar uwar data haifesu , Safara'u tagaida Sa'ade tare dayi mata barka , Sa'ade bata
gane taba amman ta amsa cike da fara'a , Ammi tacewa Sa'ade " Babar su Baffa ce fa naga
baki ganeta ba , Sa'ade tace " au itace Safara'u wallahi bansanta ba shiyasa , sake gaisawa
sukayi Safara'u tayi mata godiyar hidima da yara , Sa'ade tace " bakomai yiwa kaine ai .....

Kawu Idi yashigo gidan ai anshi Abincin su shida Abokansa , Safara'u yagani take ya canza
fuska tamkar bashine me dariya ba , tuni ta zube kan gwuiwoyin ta tana kuka tana neman
gafarar sa , kowa dayake gidan saida yatausaya mata ganin yadda takoma , Sai da Ammi tasa
baki sannan yace ya yafe mata , batun komowa gidan sa kuma yace tayi hak'uri bazai iyaba
Allah yabata wani mijin ........

Washe gari su Ammi suka shirya komawa gida , dan Zunnur yadamesu da sutafi yagaji
kuma ogansa kwana biyu yabashi , haka sukayi wa su Kawu sallama suka d'au hanyar
lagos......

Bikin su Hanan sai tahowa yakeyi , dan tuni Hajiya Asma'u tasasu gaba su ukun suka nufi
garin kano za'ayi musu gyaran sati biyu , tunda da suka sauka A gidan su Hajiya Asma'u
kwanan su d'aya suka nufi gidan *MD* me gyaran Amare da da k'amshi , tuni tafara yi musu
dilka da gyara na musamman saiga su sunfara canzawa , Hanan tamkar balarabiya haka
takoma saboda tsabar kyau , Zunnur kullum suna mak'ale a waya tamakar su cinye kansu ,
takuramata yayi da tayi masa pic d'inta ta turo masa yayi missing d'inta sosai , Hanan tace " My
Dear kayi hak'uri bazaka k'ara ganina ba sai acikin gidanka , Shagwab'e mata Zunnur yayi
tamkar k'aramin yaro yana kukan wasa , itama kwai kwayonsa tashigayi tana masa dariya ,
sunyi nisa a hakan Nasma tashigo ta d'aga mata duka tace " to Laila da Majnun ki fito Mama
tana kira , kinwani shige cikin d'aki kamar zaku cinye juna , Hanan ta gallawa Nasma hararar
wasa tace " wai meyasa kika rainamu mufa yayyenki ne dan haka ki bimu a hankali , Afrah ce
tashigo tana fad'in "Sister Mama na kiranki fa zakisha tsuminki muma duk munsha namu ,
Hanan ta dafe kai tana yiwa Afrah nuni datayi shuru waya take , Zunnur dayake jinsu duk
abinda suke cewa a hankali yace " Dear kije a tsumamin ke kinsan zansha aiki ranar , da sauri
Hanan ta katse wayar tana dariya......

Sati biyun da sukayi sosai suka sha gyara , inkagansu saika zata wankan inji akayi musu
saboda kyau , ga wani sihirtaccen K'amshi dake tasowa a jikinsu gaba d'aya tamkar an musu
b'arin turare , tuni Haidar ya iso kano dan yace yagaji da rashin Habibty d'insa , sosai Yabawa
su Hajiya Asma'u dariya ganin yadda ya susuce daga ganin Nasma , haka suka tattaro suka
baro kano a jirgi saboda Haidar yace baza akalle masa mata ba......


Suna dawowa gida suka shiga rabon katin bikinsu , Zunnur k'ememe yahana Hanan

yawon rabon kati sai Nasma da Afrah sune suke rabawa ,
Ranar Kamu a gidan Alhaji Bashir akayi wato gidan su Zunnur , sosai Amare sukayi kyau
cikin shigar lifaya sai k'amshi suke , an yi musu kamu sannan *Aunty Hadiza D Auta* tayi
musu lacca me ratsa zuciya akan zaman gidan aure , sannan taja hankulansu da yin biyayya
da mazajensu tarufe taro da addu'a , Washe gari Hajiya Asma'u ta shirya musu Dinner
lafiyayya a wani Babban holl , komai ita tad'auki nauyinsa nan ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login