Showing 30001 words to 33000 words out of 41364 words
d'in d'akin , Shima tsira yake tamkar yadda Alhaji Nasir yake , yana fitowa suka fara
aikata Luwad'i shida saurayin , sai wata k'ara suke suna gurnani tamkar wasu zakuna kafin
sukawo , ina ganin haka najiyo nabar d'akin ina tafe inah kuka , tundagan nafara neman hanyar
barin gidan Alhaji Nasir , kwata kwata nadaina jin dad'in komai a gidan , Komai ya siyo mana
bana amfani dashi saboda natsani kud'insa dan nagama ganewa idona tsafi yakeyi , tuni
nashiga nadama ta aurensa tare dayin dana sani , gashi haryau bansan asalin Alhaji Nasir ba ,
wad'anda yasamu ya turosu gidan mu lokacin aurena suma hayarsu yayi , danayi bincike
akansa aka tabbatar min bad'an garin Jos bane kawai zuwa yayi cirani ......
Suma sauran matan da ya aura saigasu da ciki , Nan yashiga Jaraba yasasu a gaba yana
zagi akan cewa harkud'i yabasu tunkafin suyi aure akan suje ayi musu allura ta hana d'aukar
ciki ......
Kaisu yayi akan azubar da cikin amman fir ciki yak'i zubuwa , haka yaraka kowacce gidansu
da saki , yana dawowa Nima nadunga rashin mutunci Akan sainaje garin mu naga iyayena ,
shikuma ya tubure bazanjeba haka na rufe ido naita gayamasa maganganu , aikuwa ya tunzira
yafara dukana nikuma ina masa Allah ya isa , muna haka akazo masa da labarin matan da
yasaka na farko sukansu sun mutu , da sauri nashiga tsoro ina fad'uwar gaba dan mutuwarsu
ta dokeni sosai , Murmushi naga Alhaji Nasir yayi tare da cewa " duk macen data sake tasan
sirrina to tabbas bazatayi tsayin rai A duniya ba , yana fad'ar hakan yashige yabar wajen , tuni
hankalina yatashi sosai wato Alhaji Nasir yana nufin shine yakashesu ? tambayar dana shiga
yiwa kaina kenan , Bayan kwana biyu yakuma zuwar min da buk'atarsa wacce yasaba , nak'i
yarda inda yazo zaiyi da k'arfinsa nima na tattaro k'arfina na buga mada murfin sif , tuni
goshinsa ya fashe amman bai hak'ura ba haka ya danne ni saida yabiya buk'atarsa ina faman
cizonsa ...... Washe gari da sassafe tuni na had'a kayana na gudu , Tare da Nasma nataho gidan dan
yadda nakeji bazan iya barinta ba , lokacin danazo gida iyayena sunyi mamakin ganina , nan
na sheda musu irin abinda Alhaji Nasir yakeyi , suma sosai sukayi mamaki tare da yimasa
addu'ar shiriya.....
Bayan kwana biyu da zuwana Saiga Alhaji Nasir yazo , sosai yabada hak'uri amman nace
bazan koma ba , tunda yaji nace bazan koma ba yashiga yin rashin mutunci sannan ya kwace
Nasma yace da ita zai tafi , ba yadda ban yiba akan yabarmin 'Yata amman yak'i , cewa yayi
indai inason yarinya ta sai dai mukoma gidansa , Mahaifina yace bazan koma ba yaje da 'Yar
nima nahak'ura , haka inaji ina gani ya d'auki Nasma yatafi da ita.....
Tundaga nan bank'ara ganinta ba kuma sannan bank'ara zuwa jos ba , nasha jinya tun
bayan da yaturomin da takardar sakina , sosai nasha ciwo tamkar bazanyiba har saida aka
fidda raina , Allah cikin ikonsa nasamu wani mutun yabani magani na warke , daga nan nafara
zawarci har Allah yahad'ani da Alhaji Murtala , sosai yanuna min soyayya , dayake tamkar
Yaya yake a guna tuni aka d'aura mana aure , a Lagos yake aikinsa dan haka yataho dani ,
saida na shekara biyu sannan nahaihu a gidan sa , 'Yan biyu na haifa duk maza sannan na haifi
Aminatu da kuma Hafsa , *kunji Labarina*......
ina fatan kungamsu da nice Mahaifiyar Nasma , inbaku gamsuba ma akwai wani d'igo a
gefen wuyanta wanda nake dashi nima a duba , a take Ammi ta duba gefen wuyan Hajiya
Asma'u aikuwa taga tabon , sannan ta duba gefen wuyan Nasma itama take taga nata , Cike
da godiya ga Allah Ammi tace " Allahu Akbar Alhamdulillah tabbas Nasma Yarinyar kice , dan
ko yanzu nakuma tabbar dahakan nima ta yadda kuke kama , Nasma take tasaka kukan
wanda tarasa nameye na dad'ine ko na meye oho jikin Hajiya Asma'u tafad'a tana kuka , Hajiya
Asma'u ta ringumeta sosai tanajin k'aunar 'Yarta na ratsa duk wata gab'a ta jikinta ,
Bayan sun nutsu Ammi ta dubi Zunnur tace " Yanzu bawanda yaganka sanda kashigo garin
nan dasu ? Zunnur yace " a gaskiya bawanda yaganmu dan ko gida bamujeba bare aganmu ,
Ammi taja numfashi sannan tace "Inaso ka kwana d'aya gobe saika wuce Sch d'in , zasu zauna
anan banason ko Abban ku yasani dan bayanzu nakeso yasaniba , sannan ina gudun shi
wannan Alhaji Nasir d'in karsuzo nan nemansu tunda kaga dole Idi zaikawosa nan , kaga indai
sukaje gidan Yaya ai zaice musu Hanan batazo ba , tunda sunsan batasan nayi aureba dole
intazo garin zasuce gidan Yaya zata sauka , da wannan shawara ta Ammi sukayi Na'am
dukansu , Hajiya Asma'u tace " dole zamu samu Alhaji Murtala muyi magana , dan sai annemo
musu maganin tsari sosai , nan suka shiga tattauna yadda zasu b'illowa lamarin Yaran
nasu......
*Bayan kwana biyu*
Tuni And'aura auren Alhaji Nasir da Safara'u sosai akasha bidiri a gidan su Safara'u ,
shikuwa Alhaji Nasir kwata kwata baya cikin nutsuwarsa kawai dan dai dodon tsafi ya nuna ya
auri Safara'u shiyasa ya aureta , amman shi yanzu soyake yaga Hanan da Nasma , gashi
Kawu Idi yazo har gidansa yayi masa rashin mutunci da ya lallab'ashi yayi masa kwatancen
inda Mahaifiyar Hanan take , amman zaije ya jik'ashi da kud'i watak'ila ya kulashi inyaga ruwan
nera.....
Ankawo Safara'u gidan mijinta , sai faman hura hanci takeyi tana cika tana batsewa ita ala
dole ta auri me kud'i , lokacin da Alhaji Nasir yazowa Safara'u ta Baya ya nuna mata zai
kusance ta , nuna masa tayi sam batasan wannan batuba , kud'i ya d'auko ya zube mata
dayake yaga daren farko ne tuni Safara'u ta amince masa yayi yadda yakeso da ita , sosai
tasha azaba tamkar kayan cikinta zasu fito amman data tuna kud'inta kwata kwata sai zafin
yatafi......
Hanan kwana biyun dasukayi har sun murmure , Alhaji Murtala sosai ya tausaya musu
dayaji labarin tare dayin Allah wadai da Alhaji Nasir , Nasma kuwa koda yaushe tana manne
da Hajiya Asma'u dan jitake tamkar yanzu tazo duniya , lalle Uwa akwai dad'i sai lallab'asu
akeyi tamkar wasu k'ananan yara ......
Zunnur tunda yakoma yasamu nutsuwa dan kullum suna tare da Hanan a wayar Ammi ,
yanzu abinda yarage masa shine yasan yadda zaiyi yakoma Jos yasa Alhaji Nasir yasaki
Hanan tunda da aurensa akanta haryanzu..........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Zee* *MD* βν ΌνΏ»
22.
Hajiya Asma'u tafara basu labari kamar haka.....
Ni 'Yar asalin garin Kano ce iyayen mu mu biyar suka haifa , mu hud'u mata sai Namiji
guda d'aya wand Shine autan mu , duka Yayyena sunyi aure saini dana rage inah karatu ,
lokacin ina zuwa F.C.E kano a lokacin na had'u da Nasir muka k'ullah soyayyah , Nasir d'an
garin Jos ne yazo kano karatune , Bayan ya kammala karatunsa ya koma Garinsu amman ko
da yaushe muna waya dashi , soyayyar mu tayi k'arfi sosai kwata kwata Mahaifina baya
k'aunar Nasir ko kad'an , niko kwata kwata idanuna sun rufe banaji bana gani akan Nasir , da
Mahaifina yagaji da halina na korar samari yaga banida niyyar kula kowa indai ba Nasir ba ,
samuna yayi da maganar incewa Nasir d'in ya turo mutuk'ar da gaske yakeyi , ranar murna a
wajena ba'a magana tuni nakira Nasir nasanar mai da wannan sak'on , shima murna yayi sosai
tare da yimin alk'awari zaituro iyayen sa cikin satin......
Hakan kuwa akayi cikin sati iyayen Nasir sukazo daga jos , Nan aka tsaida lokacin bikinmu
wata biyu masu zuwa , karkiga murna a wajena duk da inajin zanyi kewar iyayena , dan duk
cikin Yayyena bawacce aka kaita nesa ..
Akwana a tashi ba wuya saigashi lokacin biki yazo , sosai Nasir yayimin lefe d'an Ubansu ga
kaya kamar me dan yawa , nayi mamakin ganin irin kayan da Nasir yasakomin a lefe , tunda
nidai yadda yake cemin kullum wai aikin koyarwa yake , saikuma yana d'an tab'a kasuwanci ,
amman lefena kowa yagani a lokacin saiya k'ara gani saboda yawansu , Anyi biki lafiya
angama washe gari aka wuce dani jos , sosai nayi kukan rabuwa da iyayena da kuma 'yan
uwana , haka aka kawoni gidan Nasir me kyau dashi aka ajiyeni...
Bayan kwana biyu dangina suka yimin sallama tare da tarin nasihohi akan rayuwar aure
sannan suka wuce...
Sosai Nasir yake tattalina tare faranta raina , kullum cikin yimin hidima yake tamkar ya
maidani ciki , matsala ta farko dana fara fuskanta shine rashin ganin kowa nashi yazo , kullum
cikin tambayar sa nake banga 'Yan uwansa ba amman saiyace min " wai sunsamu matsala tun
lokacin bikina da sukace dole saiya auri 'Yar uwarsa ya had'amu mu biyu , haka nagaji da
tambaya na k'yalesa har na cika wata uku .....
Matsala ta biyu dana k'ara fuskanta kwata kwata Nasir baya fita ko inah , kullum yana gida
daga bacci sai cin Abinci da kallo , gashi koda yashe cikin kashe kud'i yake sababbi tamkar me
aikin Bank , Nan ma nayi masa magana yace mun bayason yawan bincike a lamarinsa dan
haka ido ne nawa , koda nashiga wata na hud'u a lokacin Allah yabani ciki sosai nakeshan
wahala saboda laulayi , kwata kwata yadda na fahimci Nasir baya murna da wannan ciki ,
kuma a lokacin yabiya kud'in tafiya Hajji , yana ta shirin tafiya na rok'esa a kan ya maidani garin
mu can gidan mu inyadawo sai nadawo nima , fir Nasir yak'i yace bayason a nuna gazawarsa
dan haka zai kawomin 'Yar uwa wacce zamu zauna tare , duk bankawo komai ba ana saura
kwana hud'u yatafi nafa ana gyara d'aya d'akin dake jikin nawa , akazo akayi jere dare nayi naji
gud'a ankawomin Amarya .....
Sosai nayi mamakin Abinda Nasir yayimin naci kuka nagode Allah batare da nafad'awa kowa
ba , haka ya shigo gidan yahad'amu nida Amaryar sa yayi mana fad'an zama lafiya , Amarya
wacce naji yakira da suna Hajjo tace " insha Allah daga gurinta babu matsala nima hakan nace
tare da mik'ewa nabar d'akin.....
Ranar Tafiyar sa haka yatafi Saudi'a Abinsa yabarmu da tarin kud'i me yawa , Yadda na
fahimci Hajjo tana da son Abin duniya , gata da bak'in kishi tamkar itace uwargida , Anan
nakejin wai bazawara ce ita aurenta hud'u duk bata haihuwa shiyasa Nasir ya aurota , Anan
nagane maganar ta inda ta nufa wato ni tunda nayi ciki bayaso bari ya auro wacce bata
haihuwa , watan Alhaji Nasir Biyu yadawo gida lokacin cikina yafara girma .....
Koda yadawo bamu dad'e a wannan gidan ba muka tashi ya gina mana wani babban gida ,
gidan yahad'u sosai tamkar gidan wani gwamna , kullum cikin raina mamakin irin kud'in Alhaji
Nasir nake , dan kullum yawa suke k'arayi tamkar ana turo masa su , gashi nayi nayi yasanar
dani irin sana'ar dayakeyi fir yak'i yafad'an , dan har cewa yayi indai nakuma damunsa to
wallahi abakin aurena , haka na hak'ura na k'yalesa har Allah yasaukeni lafiya nasamu 'Ya
mace , ba laifi yayi murna amman bai d'auketa ba tunda aka haifeta , Ranar suna Yarinya taci
Sunan Ummana Halimatu muke cemata *Nasma* 'yan uwana duk sunzo suna , sun nuna suna
so sutafi dani wanka amman fir Alhaji Nasir yahana dole aka k'yaleni..
Bayan wata biyu da haihuwar Nasma nafara ganin sauyi a tare da Alhaji , kullum inyazo min
kwanciyar aure sai yace ta Bayana zai kusance ni , nikuma nak'i yadda fir tunda ganan muka
fara samun matsala , domin kwata kwata ya fita daga sabgata , gashi yahanani zuwa ganin gida
firr , akwana atashi saiga Alhaji Nasir ya auro mata biyu rana d'aya , Nayi mamaki dabai
gayamin zaiyi aureba amman haka nakuma dannewa batare da nanuna damuwa ta ba , a
kullum banida burin sai son sanin ta ina Alhaji Nasir yake samun kud'i , dan kullum Abin yana
bani tsoro sosai , kuma gashi har na haihu dashi amman bantab'a ganin danginsa ko
d'ayaba...........
*Kumin Afuwa yau Posting d'in Ni bora ce kad'ai zaku samu*
*Shid'inma kuma kuyi hak'uri bayawa*βν ΌνΏ»βν ΌνΏ»
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Zee* *MD* βν ΌνΏ»
21.
Tuni mutane suka fara cika a wajen ana bawa Kawu Idi hak'uri , amman ko
takansu baibiba ya shige gidansa tare da rufowa , Alhaji Nasir shima nufar motar sa yayi zai
shige yatafi Safara'u tayi tsagal tace " Alhaji dan Allah kataimaka min ka kaini gidan mu , ko
jiyowa Alhaji Nasir baiyiba yace tashiga motar kawai......
Bayan su Hanan sunyi wanka Ammi ta d'auko musu dogayen riguna a cikin kayanta , mik'a
musu tayi tace " gashinan kowacce tasaka sai kuzo palor kuci Abinci , Hannu biyu suka saka
suka ansa tare da cema to , Bayan fitar ta Nasma ta dubi Hanan tace " gaskiya Hanan kinyi
sa'ar Uwa tagari gata me fara'a dason mutane , nifah dana ganta wallahi saikace bata haifeki ba
gashi tafiki kyauma , Hanan tayi murmushin jin dad'i tace " kedai kawai kice kinkoma Bayan
Ammi yanzu nikuma an zubar dani , itama Nasma Murmushin tayi tace " in ma hakan ne ai ba
laifi nayi ba dan kinsan Ina ganinta naji tamkar naga Ummata duk da bansan taba , Hanan tace
" insha Allah zaki santa nan bada dad'ewa ba , Nasma tace " Allah yasa hakan dan inaso ko
yayane nima naji d'uminta atare dani ......
Bayan sunsaka kaya suka fito daga cikin d'akin suka nufo palor , Zunnur tunda suka taho
idonsa yake kan Hanan , gani yayi tarame sosai dai dai ta k'ara haske sosai ga idanunta
sunkuma fitowa masu shek'i dasu , suna k'arasowa ya d'auke idonsa daga kallonta , samun
guri sukayi suka zauna Hajiya Asma'u tuni ta kawo musu Abinci , jollof d'in shinkafa ce data
wadatu da kayan lambu sai kuma Naman rago soyayye akai , gefe d'aya kuma ruwan roba ne
da lemo , Zunnur shima anzuba masa nasa daban , nan sukayi bisimillah tare da fara cin
Abincin su.......
Safara'u tana zaune cikin motar Alhaji tamkar ba itace tasha duka ba , ta dubi Alhaji Nasir
tawani kashe murya tace " Alhaji nidama naga baka dace da wannan yarinyar ba kwata kwata ,
kasan Hanan bata da wayewa ko kad'an mezai hana ka hak'ura da neman ta kawai kamaye
gurbinta dani , tawani kashe masa ido ta mirro d'in motar tana wani k'ara turo k'irji , Alhaji
Nasir yayi wani guntun murmushi sannan yace " ai duk wannan me sauk'ine , tunda har kinga
nayi miki to kije gida kigama idda sai inzo muyi magana , Safara'u wani dad'ine ya rufeta
tamkar tamik'e tafara tsalle tace " wacce Idda Alhaji ni ko gobe ka fito da wuri zantaho gareka ,
ko ka manta bari ya wuce shine ke kawo rabon wani , Alhaji yace " Amman kina ganin mijinki
bazai zargin dama hakan ce takawoni ba harna kashe miki aure ? tab'e baki tayi sannan tace "
k'yale wannan mara zuciyar ai ko inah gidansa kanuna kana sona dole zai hak'ura yabarmaka
ni , bare yanzu yariga da yasakeni agaban mutane , Alhaji tunowa yayi da maganar dodon su
dayake cewa " jinin Safara'u zaiyi musu Amfani , take Alhaji Ya Amincewa Safara'u tare da
cemata Nan da kwana biyu zaizo neman auren ta , Murna a wajen Safara'u ba kama hannun