Showing 30001 words to 33000 words out of 81464 words
Chapter 11 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt
jarrabawar Biology, daliban ilimin kimiyya(science) sun taru a lab. Saboda malamin Biology yace za su yi hotuna, tunda wannan shine karo na karshe na shigarsu lab din Biology.
Uncle hamza yana daga cikin malaman da suka tsaya kai da fata gurin gudanar da jarrabawar, don haka shi ma yana cikin jerin malaman da suka nufo lab din daukar hotunan.
An shirya kowa aka soma dauka, kowane dalibi cike yake da farin ciki, suna ganin darajarsu ga malamai, tunda har suka bukaci yin hotuna da su.
A 6angaren uncle hamza zan iya cewa ya fi kowa farin cikin daukar wadannan hotuna ko ba komai akwai HASKEN ZUCIYARSA a ciki. Tunda dama yana son mallakar hotonta, amma ya rasa ta ina zai fara, sai ga dama ta zo masa, don haka cikin doki ya kosa a dauki hotunan, wanda ya tsaya a bayan Shuhuda yana murmushi.
Bayan an gama daukan hotunan bai samu yin magana da shuhuda ba, sakamakon aikin hada takardun da ya tsare shi.
Lokacin da ya samu sarari sai nemanta ruwa a jallo bai gan ta ba. Yana da tabbacin tuni ta dade da komawa gida. Don wannan al'adarta ce, tun ma kafin soma jarrabawar da zarar an tashi ba ta tsayawa jinkirin komai ta ke tafiya, to dama ita ba kawaye ba bare ace sun tsare ta.
Yayi takaitaccen murmushi, tare da lasar busassun la66ansa tukunna ya wuce izuwa mota.
Ko a cikin motar ma kafin ya tafi ya dauki wani lokaci yana jin dadin daukar hoton. Wannan dama ce da zai yi amfani da ita gurin kwantarwa da Alh Babba hankali, zai nuna masa hoton shuhuda a matsayin matar da zai aura. Inyaso an shafa masa lafiya akan zuwairiyyah, tun da shi dai Allah bai saka masa sonta ko kadan a cikin ruhinsa ba.
Shi kuwa ingancin zaman aure yana ta'allaka ne da ingantacciyar kauna. Da zarar aka ce anyi aure daya ba ya so, dayan ma musamman namiji to kuwa za a yi katari da abubuwa marasa dadi, to bare kuma shi da zuwairiyya wanda akwai karfaffen zumunci a tsakaninsu.
Da wannan tunani ya tayar da motar ya nufi gida.
Washegari aka wanko hotunan, a ranar kuma bau jarabawa, Mr philips ya kira shi a waya ya sanar masa an wanko hotunan. Don dama tunda aka gama dauka yace a wanko masa duk wanda shuhuda ta ke ciki. Har Mr. Philips yana dariya yana cewa: " ko dai ita ce Lobi din ne?"
¤¤¤
.
A lokacin da wayar ta same shi yana kauwar kwari inda zaharaddeen yake gudanar da kasuwancinsu, kaya ne aka kawo daga MALAYSIA, don sun jefa hannun jarinsu da wani kamfanin Material da ke Malaysia shi yasa suke kawo musu kaya akai-akai.
Babu laifi kuma wannan ya kara janyo musu daukaka, don ba karamin abin mamaki ba ne daga fara kasuwancinsu a kasuwar kwari duka-duka shekaru biyu da watanni, amma suin shahara irin haka. Wanda ga wadanda suka share shekaru aru-aru amma ba su yi irin wannan shaharar ba.
To shi da ma kasuwanci ribarsa saukaka abu, da zarar mutum ya yi hakuri da riba kadan, sai ya tarar da tarin alkhairai. Amma muddin za a tsauwala to kuwa akwai ragee kwarjini da kuma dakusar da kasuwancin.
( Don Allah 'yan kasuwa mu duba wannan lamari, barin ma idan Sallah ta zo ko Maulidi sai ka ga an dauki dogon buri an dora a lokacin. Wanda babu wanda ake cuta sai talaka. Shi kuwa talaka abin tausayi ne akan komai na rayuwarsa).
Zaharaddeen ya dago kai ya dube shi da yaga ya mike tsaye yace: Ina kuma zaka je? Uncle hamza ya juyo da kansa yana dubansa, yace: Zan je na dawo ne, ba dadewa zan yi ba.
Yana karashe fadar haka bai jira amsar zaharaddeen ba ya sa kai. Sauri-sauri, gudu-gudu har ya isa inda ya ajiye motarsa ya shiga ya tayar da ita. Nan da nan ya isa gidan hoton Mr. Philips, suka gaisa, mr philips yana dariya ya dauko hotunan yana cewa:
Gaskiya yarinyar nan tana da kyau duba ka ga yadda tayi kyau a dukkan hotunan nan, duk fa ta fi kowa yin kyau. Cikin harshen turanci yake maganar uncle hamza ya kai hannu ya kar6a. Idanunsa suka kai ga abin al'ajab! Tashin hankali aka ce wanda ba a saka masa rana.
Ya gigice ya kuma razane duk a sanadin abin da ya gani a jikin hoton. Maimakon ganin shuhuda sai ya ga taswirar zuwairiyya.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤15¤¤
Mr. Philips ya dube shi cike da tsananin mamakin yanayin da ya gani a tare da hamza, yace: Lafiya? Uncle hamza sam wuta ta dauke masa. Abin da yake damunsa shine: ta ya aka yi zuwairiyya ta shigo a cikin hotunannan da suka dauka a makaranta? Ina inuwar shuhuda ta shiga a cikin hotunan da bai ganta ba?
Shuhuda ce ta yi wannan kullalliyar tunda ta kasance aljana. Su kuwa jinnu sukan yi fiye da hakan! Abin da zuciyarsa ta ayyana masa ke nan. Bai san yadda zai yiwa Mr. Philips bayani ya gamsu ba, don haka sai wayancewa ya yi da yin murmushi yace: Kyawun da ta yi ne ya firgita ni.
Mr. Philips ya dan daki kafadarsa yace: Kai mutumina zaka fa more idan ka mallaki wannan zukekiyar yarinyar. Murmushi kawai uncle hamza ya yi ya dauko kudinsa ya bashi, tukunna ya masa bankwana ya tafi.
Travelling bag dinsa ya saka hotunan bai kuma bin ta kansu ba. Haka bai kuma bi ta kan shuhuda ba, don ko da suka dawo yin jarrabawa yana kallonta amma ba ya kulata. Wannan yana daga cikin matakan da ya dauka na kauracewa abin da zai saka shi da-na-sani.
Ranar asabar yana zaune a falonsa yana lissafa wasu kudi da zaharaddeen ya kawo masa na ribar da suka samu a wasu kaya da suka shigo dasu. Wayarsa ta yi kara, yana dubawa lambar yayansa Alh Mukhtar ya gani akai.
Cikin girmamawa ya dauki wayar suka gaisa, Alh Mukhtar yace: Dama Abba ne ba shi da lafiya yana asibiti, sun ba shi gado shine na ce bara na sanar maka. Hankalin uncle hamza ya tashi, cikin rudani yace: Mai yake damunshi?
Alh Mukhtar yace: Ciwon hanta ne, mu ba mu san yana da shi ba, wai ashe dama ya dade yana fama da shi yana zuwa ganin likita a 6oye. Uncle hamza yace: Allah ya ba shi lafiya, ina nan tafe anjima. Suka yi sallama ya tashi ya soma shiri.
Karfe uku na yammaci ya isa birnin katsina, a gidansu ya fara sauka ya tarar da su Goggo binta duk suna gidan har zywairiyyah. Suka gaisa ya ajiye jakarsa ya nufi asibiti.
Ya tarar jikin da sauki, don har ma ya samu bacci, saboda haka ya dawo gida. Ya tarar da tashin hankalin da ya hautsina masa kwalwa a lokacin da ya shigo gidan.
Goggo binta ce rike da hotunansa da ya saka a jakarsa, tana kururuwa wai hamza zai janyo musu MUGUN IRI a zuri'a, tunda yake yawo da hotunan MAYYA a jakarsa! Zuwairiyya kuwa sai kuka take ana rarrashinta, tana kuma rusa ihu barin ma da ta ga uncle hamza ya shigo gidan.
Cikin sanyin jiki da takaicin binciken da aka yi masa ya karasa ya kar6i hotunan ya ga ba ZUWAIRIYYA? to ya haka? Ko kuwa dama idanuwansa ne a wancan lokacin suka yi masa gizo, suka nuna zuwairiyya a maimakon shuhuda?
Muryar Goggo binta ce ta katse masa tunani, inda ta ke cewa: Wallahi ita ce ta lashe MAS'UD, diyar fa KARIMA kishiyata ce, wadda ta yi sanadin mutuwar aurena! Yarinyar nan muhun iri ce, domin ta lashe ma wata mata daga ta tsarga yatsanta. Gadon mugun abu ta yi, kuma na tabbata tunda na ga hotunanta a tare da hamza shi ma so take ta lashe kurwarsa.......
Haj Mardiyya ta katse surutun da cewa: Ya isa haka binta, ya kamata mutuna halin da muke ciki. Uncle hamza bai ce komai ba, ya saka hotunan a jakarsa ya fice zuwa dakin kaninsa salisu.
Koda ya shiga dakin tunani ya sha masa kai, ya auna maganganun Goggo binta, sannan ya daura al'amuran da suka faru gare shi, shin da gaske mayyar ce? Ko kuwa aljana dai? A'a wata halitta ce daban! Ya rasa inda zai dorata a matsayi, mutum-mayya ko kuwa aljana-hatsabib
iya?
.
****** ******* *****
.
BABI NA BAKWAI
.
.
TSAUTSAYI KO KADDARA?
.
Daya ga watan satumba, wanda ya kasance ranar litinin jirgin Egypt air ya sauka a birnin Egypt bayan da ya taso daga senegal don sauke wasu fasinjoji(pasingers)kafin daga bisani ya yi hutun awa daya da rabi, sannan ya dage zuwa birnin kano.
Kamar yadda yake a bayyane masu Transit visa wucewa zasu yi, idan jirgin nasu ya huta ba tare da ko airpot din sun fita ba.
bare ganin yanayin gari, ko yin wasu mu'amaloli nasu abinsu.
Da yawan mutanen da ke cikin jirgin dalibai ne, wadanda suka kammalo digiri dinsu a kasar senegal, wasu kuwa 'yan kasuwa ne da ke zuwa siyayya, don haka mafiya yawan mutanen ciki kabilu ne farare, dai-daiku ne bajkaken wadanda sauyin gari, cima, yanayi da kuma kwanciyar hankali ya sanya suka saje da fararen fatan, amma dai kana kallonsu kasan asalinsu bakar fata ne.
Bayan jirgin ya sauka, fasinjoji suka soma saukowa, ISAH SADA RABI'U yana daya daga cikin masu saukowa daga jirgin. Amma shi zai shiga cikin gari ne saboda yana son ganawa da wani malaminsa da yake mazauni a kasar Misra, aiki ne ya jai shi can kasar senegal daga baya kuma ya dawo kasarsa ta haihuwa.
To sun yi da Isah idan zai koma Nigeria zai biyo ta nan Misra, hikimar hakan gurin malamin mai suna Dr. Outhman Ibn Abdulfatah shi ne, yana so ya samawa Isah aiki a ma'aikatar karafa da ya bude ta kashin kansa mai suna KHAIR METAL, saboda tun yana koyarwa a makarantar ya aminta da kaifin kwalwa irin na Isah, ba duka dan Nigeria ne ake samunsa da yin karatu idan ya shallake kasarsa ba.
Mafi yawancinsu sun fi mayar da hankali ne ga shashanci wajen kula mata da shaye-shaye, amma shi Isah ko kawance ba ya yi da mata, abin da ya kai shi kasar shi yake yi. Hakan kuwa ya kara masa kwarjini da cikar HAIBA a idanun malaman makarantar.
Yana saukowar daga jirgi tafiya kadan ya yi ya isa inda ake bincike, aka gama yi masa duk wani bincike da ya kamata a yi masa a matsayinsa na bakon kasar. A lokacin ne kuma ya samu layin da ake amfani da shi a kasar ya kira layin Dr Outhman ya sanar da shi ya kammala komai shi kawai yake jira.:
Bayan gama wayar akwai wani guri inda ake zama musamman don irinsa. Wadanda za a zo taryensu, ya zauna yana nazarin wani littafi SHOCK TREATMENT. Kamar an ce ya dago kansa, sai ya yi sai ya yi TOZALI da wata kyakkyawar mace, fara tas. Ma-abociyar cikar zati, idanuwanta narai-narai da kwalli radau a cikinsu.
Tana cikin shiga ta bakar jallabia ta yafa gyalen rigar a kafadarta, sannan ta nade kanta da wani yalolon dan kwali, wanda ya kara fitowa da kyawunta a sarari. Kana ganinta kasan balarabita ce, amma bisa ga tsanin al'ajabi, kai tsaye gurin da yake zaune ta tukaro, kuma koda isowarta cikin harshen Hausa ta yi masa sallama, tun kafin ma ya amsa ta soma jero masa gaisuwa.
Mamaki ya cika shi don bai yi tsammanin jin harshen Hausa a bakin wannan Balarabiyar da ke gabansa ba.
Baya da haka kuma yana mamakin saukin kai irin nata wanda har ya sa ta zo inda yake ta gaishe shi ba tare da shi ya yi hakan ba a matsayinsa na namiji wanda ya ga mace yana so zai tunkara.
Duk da ba ya mu'amala da mata, ya sha jin yadda aka tsayar da suke da girman kai musamman idan aka tsayar da su. To amma ita wannan mai sanyin hali ce, ko kuwa ita ma daga senegal din ta baro, sun yi tarayya a makaranta daya?
Murmushi ya sakar mata cikin harshen Hausa yace:
Kai duk ni kadai wannan gaisuwan? Ita ma murmushin ta yi masa, tukunna tace: Ai ka isa ne, gani na yi kamar na sanka, don Allah kai dan Najeriya ne, a birnin Kano ko?
Bai yi mamaki ba, don ya sha jin ana cewa duk inda DAN KANO ya shiga ba ya 6uya, wata kila hakan ne ya sa ta canki wannan tambayar. (Ta6! Ai ba ma hakan bane. Ni dai ban yadda ba. In dai ba mayintan san kudi ba, kanawa ba su san komai ba, sai shirme. Da ma dai 'yan zaria ne sune suka fita zakka a fagen gogewa da komai. Lolx)
Gira ya daga mata ba tare da ya yi magana ba. Tace; Haba, kofa naji, unguwar SALLARI ko?
Yanzu kam ya sha mamaki, don jin ta ambaci sunan unguwar su kakansa, yana dubanta yace:
Hala ke ma 'yar can unguwar ce a kano, kuma Najeriya? Ta girgiza kai tace: .......
.
1- Abubakar Ibn Khaddab
2- Shuhuda Ibn Khaddab
3- Yusuf Ibn Khaddab
Uncle hamza ya hadu da Abubakar ibn khaddab.
Isah kuma ya hadu da Shuhuda ibn khaddab
To ni kuma bari na arce watakil nine zan hadu da Yusuf ibn khaddab.
ada Hausa Book stories
MATAUL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤16¤¤
Ta girgiza kai tace: A'a, Ai ni 'yar wannan kasar ta Misra ce, na dai sanka, ko ba kai ne YAYAN SHUHUDA SAGIR RABI'U ba?
To yanzu fa mamakinsa ya kuma hau-hawa akan na dazun. Ya dube ta da kyau, yace: Kin ce ba a Najeriya kike ba, ya aka yi kika san garinmu, unguwarmu, dama kanwata?
Tayi murmushi, sannan ta ce dashi. " Ai sunanmu daya da kanwarka, ni kuwa duk inda mai sunana ta ke sai nasan wace ce ita.
Murmushi ya yi mata, saboda ya fahimci wasa ta ke, ita ma din 'yar Najeriya ce. Yace: Kina nufin ki ce min saboda sunanku daya dakanwata shi yasa kika santa, har kuma kika san ina da alaka da ita. Yadda duk inda kika ganni za ki iya shaida hakan?
Ta daga masa kai cikin tabbatarwa, ita ma fuskarta dauke da murmushi.
Yace: Ban yarda wannan zai zama karfaffiyar hujja ba, don haka kada ki wahalar da kanki gurin zolayata ta wannan hanyar, don ba ni kadai ba, duk wanda ya ji ma ba zai gasgata ba.
Tace: Wallahi rantsuwar dan musulmi ke nan ko? Na sanka, na san kai kuma yayan Shuhuda ne, da Babanta mai rasuwa da Babanka mai rai uwa daya uba daya suke.
Shi kam dariya ta ba shi matuka, yana daritar yace: Eh, ai ba cewa nayi ba ki sanni ba, na aminta kin san duk wadannan alakar da ke tsakanina da shuhuda, amma hujjar da kika bayar cewar saboda sunanku daya da shuhuda kanwata kika san haka ba mai kar6uwa ba ce. Idan ma har zata kar6un to cikin dayan biyu.
Ko dai kin hadu da shuhuda ko wani da yake da alaka da tsatsonmu, ko kuma kacokam a kasarmu, jaharmu kuma unguwarmu kike. Idan ba ta wadannan hanyoyin ba bazan ta6a yarda da abin da zaki ce ba.
Tace: Ni asalina 'yar wannan kasar ce, ban ta6a zuwa Najeriya ba, amma nasan kanwarka shuhuda sagir Rabi'u ta hanyar tsananin bincike da KAIFIYYA irin tawa...... Ba ma kanwarka kadai ba, a kasarku kuma jiharku, na san masu sunana SHUHUDA sama da trilliom, saboda haka kada ka yi mamaki.
Ya jinjina kai alamar jinjinawa, yace: Lallai kam kina da kokari tunda har kika yi wannan bincike, amma dai duk da haka kin san wani abu?
Ya nemi kawar da wancan zancen tunda ya lura 'yar barkwanci ce. Ta girgiza kai, tare da fadar: Sai ka fada.
Yace: Kin burge ni, har na ji ina son mu-amala da ke.
Ta yi murmushi, wanda ya bayyanar da siririyar wushiryarta, ba ta yi magana ba don haka ya ci gaba cewa. Da gaske sunanki shuhuda, kuma wannan kasar kike?
Ta jinjina kai. Tabbas sunana Shuhuda Ibn Khaddab, mu uku ne gurin mahaifinmu, ni da 'yan uwana Abubakar da Yusufa, iyaye da kakanni dukkansu 'yan kasar nan ne, sai me bayan haka?
Yana murmushi, yace: da ita: Lambar wayarki, da adireshin gidanku.
Tace: Tabdijan, lambar waya? Yanayinsa ya nuna tuhuma, yace: Ban gane mamakin da kika yi ba?
Tace: Eh, to ni da ba zama kasa daya nake yi ba, wace lamba zan baka idan ba so kake ka yi ta nemana ba ka samu ba? Yanzu ma fa kasar sudan zan je, kuma daga can wata kasar zan je?
Yanayinsa ya sake nuna damuwa yace: Ke kam duk me ya janyo miki wannan yawo haka sai ka ce 'yar kasuwa?
Ta yi dariya, tace: Haba dai? Ai duk yawona ban kai TANZIF ba, wanda yana iya zuwa kasa goma a kwana goma. Bare ni da idan na je kasa nakan samu kwana goma ban barta ba.
Isah yace: Waye kuma TANZIF? Tace: Ba ka sanshi ba. Yace: To amsa min tambayata me kike zuwa yi kasashe?
Tace: Yawanci ina zuwa majalisi ne na malamai. Sannan nakan ta6a kasuwanci.
Ya jinjina kai. Cewa zaki yi Ustaziya ce? Don haka ma daga yau haka zan dinga kiranki USTAZIYA SHUHUDA.
Ta duba agogon da ke daure hannunta tace: Ka ga har mun ci lokaci da yawa, sai nace sai gani na biyu ke nan?
Ya yamutsa fuska yace: To idan kin ce sai gani na biyu ta ya zamu sake haduwa, ba ki bani adireshinki ba?
Tace: Haka ne, amma.......
yadda TSAUTSAYI ya hada mu yanzu, a gaba KADDARA zata hada mu.
Yace: TSAUTSAYI KO KADDARA? Ban gane ba. Ta yi dariya wadda ga dukkan alamu dabi'arta ce, dariya ba ta mata wuya. Tace:
Idan na ce TSAUTSAYI, ina nufin tsautsayin haduwarmu bayan kuma zamu dade ba mu sake haduwa ba, wata kila kuma har abada.
Sannan idan na ce KADDARA ina nufin KADDARAR ALLAH ta hadamu sanadin mai sunana, idan na biyota har kasarta don........
Karar maganar da ke fita daga abin maganar da ke kafe a gurin ta soma bayar umarni ana neman wadanda zasu SUDAN don yin setting dinsu ta katse maganar da shuhuda ke yi. Tana dan hanzari tace da shi.
SAI WATA RANA!
Ya yi sauri yace:
Dan tsaya na ba ki lambata........
Tace: A'a kada ka damu, sai ka jini.
Ba ta jira abin da zai kuma fada ba, ta yi gaba ta barshi galala da baki cike da alhini, wannan yarinya da barkwanci ta ke.
Lokaci daya ya ji wani nishadi na kwarara a zuciyarsa, tunda yake a rayuwarsa bai ta6a yin soyayya ba. Don haka ya kira abin da yake ji game da yarinyar SOYAYYA.
( Kai wannan gayen akwai shirme,