Showing 81001 words to 81464 words out of 81464 words
Chapter 28 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt
dariya, ya ce.
“kada mu yi dariya, ya ce.
Zuhura ta yi murnar ganin shuhuda don ba ta yi tsanmmanin za su sake haduwa ba. don ita duk zancen shuhuda ta sanya su a shirme. Ta hidima da su, sun san sun shigo gidan girma.
Shuhud na kallon hotona suna hira, zuhura ta ce.
“Oh shuhuda, labarinki yana matukar damuna a rai, har na sanr da maman shureim wata marubuciya da muke mu’amala, mun yi alkawari da ita idan dai mun hadu zan sanar mata”
Sai ta jawo way ta soma neman wayar maman shureim, sai aka yi rashin sa’a ta tafi makaranta ta bar wayar a goda, sai ‘yarta ce Nusaiba ta dauka ta sanar musu.
Sun yi hira sosai da zuhura labarin rayuwarta, har zuhura ta yi mamakin labarin, sun kuma shirya ranar da zasu samu maman shureim don mata da wannan labara don ta fesawa duniya kila ko mutane sun farga da sharrin MATA’UL-HAYAT.
Rayuwa ta mika cikin shuhuda ya girma, suna zaune a falon inna yaduwa don ta rigima sai an dawo mata da shuhuda wait a haihu a gabanta.
Isah yana zaune, innar na gefensu tana lazimi, ya dubi shuhuda ya ce.
“kullum addu’ata a Haifa min ‘ya mace”
“mace kuma? Kai ko saboda me?”
“na ga mafi yawancin maza sun fi son ‘ya’ ya maza.
Ya ce, “To ni na sha banban das u, kinga ‘ya mace ta fi tausayin iyaye, ta fi imani saboda rauninta, kuma ta fi zumunci, ni da za ki gaji wata kakata aid a na yi murna”
Ta yi murmushi, ta ce.
“Wai kana nufin Hajiya ‘yar Gandu?
Don nasan dai ba inna yaduwa ba”
Ya ce, “Ita mana, kinga haihuwa ta tara duk ‘ya’ya mata, ki duba ki ga dadin da ta ke ciki, ga iyalai masu hadin kai da zamunta, kwadayin haka ke sanya ni son ‘ya’ya mata?
Inna yaduwa ta shafa addu’a ta ce.
“ku dai Allah ya bada na gari, da mace da mijin du kana masu zumunci, masu tausayin”.
Suka ce, “Eh, haka ne”.
Watan haihuwa ya tsaya, ranar juma’a Allah ya sauki shuhuda, ta Haifa danta namiji, ‘yan uwa da abokan arziki sun halarci sunan, an ci an sha, yaro ya ci suna Muhammad Sagir wato sunan mahaifinta, sai ake kiransa SADAUKI.
To Allah ya sa cikon addini ne, amin.
.
TAMMAT BI HAMDU LILLAHI
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maka, muna neman taimakonka, muna rokon afuwarka akan kuskuren da muka yi.
.
Marubuciyar wannan littapin mai cike da ILMANTARWA, PADAKARWA tare da NISHADANTARWA (Zahra'u Baba Yakasai, Maman Shauriem) Ya Allah Ya jin kanta da Rahama, Ya sanya Haske a kabarinta, Ya saka mata da gidan Aljanna, mu kuma Ya kyautata tamu karshen.....ameen.
.
Ashe sabo ya na da dadi, amman rabuwa da zapi, 'yan uwa na, ku tausaya idan nayi muku laipi cikin gan-ganci ko a kuskure, kuce kun yape, ni kuma daman baku min laipi ba!
Allah (SWT) Ya gaparcemu baki daya.