Showing 57001 words to 60000 words out of 81464 words
Chapter 20 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt
duk musulmi ya dimanci yenta ba wai sai wata matsala ta faru ba. Sannan akwai cutuka wadanda likita bai isa gano makasudin samuwarsu ba bare yasan magungunansu. Shawarar d azan baka, ka kasance mai yin addu’a ba dare ba rana, ko me kake ka yawaita neman tsari daga:-
MIYAGUN MUTANE
MIYAGUN SHAIDANU.
Allah Ya taimakeka ka tsallake siradin da kake a kai, Allah Ya taimakeka ka zamo mutum mai himma wajen SADAUKARWAR da rayuwa akan tafarkin addinin musulnci. Akwai zobenka da yake hannuna wanda ka ba wa Shuhuda lokacin da ka dawo daga Senegal, watakila kaga irinsa a yatsana a haduwarmu burnin Katsina? To na hannunta ma ya dawo hannuna bias wani boyayyen sirri. Wassala! Sai Allah Ya yi mana dawowa idan da rabon ganawa!
Tun kafin ya karasa karanta wannan zungureriyar takarda mai taken ‘Budaddiyar wasika’ gumi ya jike Isah, ya yi sharkaf, idanunsa sun sauya launi, zuciyarsa ta jagule.
Bat a yi karya ba kamar yadda ta fada, dole ne ya shiga rudani akan wannan takardar, ba ma shi kadai ba dak wanda zai karanta takardar dole ne ya shiga rudani. Idan zai iya tace abubuwan day a karanta a cikin wasikar to abu na farko da zai kissima, wannan wani labari ne day a fito daga hannun AJJANA SHUHUDA IBN KHADDAB, bias hujjojin sanin wasu abubuwa da ta ked a su, wanda ya fi karfin sanin bil’adama, koda ace ma wani bil’adama zai zansu, to sai dai ya kasance mai yawan shekaru, kuma wanda yake da alaka da wanda abin yake faruwa akansa. Ita kuwa wannan a yadda ta ke din nan ba zata wuce shekaru ashirin ba, idan ma ta kai ken an. Kuma ba ta zaune da Shuhuda koda yaushe bayan makaranta da ta hada su, bare tasan komai na rayuwarta wanda ita kuma Shuhudan ba tasan wasu abubuwa da suka shafeta ba. Isah mutum ne mai kwanji, amma bai ga alamar yana da kwanjin da zai iya jure wannan sha’ani ba.
Nadama ta zo masa a karo na biyu na dawowars kasarsa ta haihuwa, wato Najeria tunda tun lokacin day a dawo bai samu nutsuwar zuciya ba. Abin day a lura da shi matsawar yana bukatar zaman lafiya da fita daga tarin rudanin da yake ciki game da wannan murdaddiyar al’amari to kawai ya yi kaura da Najeria ya koma Misra ya yi aiki a karkashin kamfanin da malaminsa Dr. Outhman Ibn Abdulfatah ya so ya yi tun da farko.
Sai dai inda yake hangen matsalar bay a wuce ta bangaren mahaifinsa, tunda a farko ma ya so hakan amma mahaifin nasa ya kiya masa, yanzu day a fara aiki a Nigeri zai kuwa yiwu ya amince masa aiki a Misra? Shirme, hauka gami da tsabar rainin hankali shi ne muraran abin da yake ganin su Shuhuda na yi masa. Tunda yasan kauracewa zamansa Nigeria ba abu ne mai yiyuwaba, to kawai ya dauki matakin fatattakar duk wani lamari da zai sada shi da Shuhuda tundabai ga wani abun anfanu a hakan ba. Ya ja wani dogon tsaki yana yarfe gumin day a jike shi, tukunna ya mike tsaye ya tunkari kafar fita daga falon.
Tsau! Yaji wani abu ya ratsa ta dukkan sassan jikinsa, kamar tsoro n eke dirar masa.
Cak! Ya ja tunga ya tsaya tare da waigawa da sauri, ya duba ko’ina bai ga wani abun da zai tsoratar da shi ba, illa dai haka nan ya samu jininsa da tsinkewa ya yi tsururu tamkar ruwa. Ya dau mintina biyu a haka, sai ya ji kamar zuciyarsa na yin shakulaton bangaro (sharewa) da lamarin Shuhuda, musamman la’akari da abinda budaddiyar wasika ta kunsa. Sai dai a wani bangaren yana karfafawa kansa sharewa da Shuhudan, domin budaddiyar wasika babu abin da ta kuma sanya shi illa wani firgici. Sam bai hango wata hanya da zai shawo kan matsalar rudanin da yake ciki ba. Da azamarsa ya sake ‘yunkurin ficcewa daga falon, amma kamar an daure shi, domin ji ya yi gaba daya babu wata gaba da ke iya motsi a jikinsa. Hatta kansa ya kasa juyawa zuwa bayansa, illa gabansa kawai da yake kallo. A bayan nasa kuwa yana jiyo kamar ana motsi, kamar ma taku yake jiyowa. Da sauri ya ambaci…..
‘INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN, LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH……’
Kafin ya karasa ma tuni ya ji wani irin kuzari ya zo masa, ya kuma fice daga falon yana mai takaicin shigowarsa hurumin dab a nasa ba. Cikin rudanin ya yi saurin rufe gidan da makulli ya koma gidansa, ya zube a falo tare da rafka tagumi.
Hakika duk abin day a faru da shi a cikin gidan su Abubakar lamari ne na sihiri, ko kuma gaba daya ma y ace jinnu idan haka ne kuwa daga Shuhuda Ibn Khaddab har mijinnata Abubakar Ibn Khaddab duk jinnu ne? idan hasashensa ya zama gaskiya ta ya suka samu wannan gida da suke ciki? A matsayinsu na jinnu zasu iya zama a gidan, to amma ina asalin mutanen da ke zaune a gidan? Ko kuwa sun z one a sigar mutane an dauke su aiki har aka bas u muhalli kamar yadda shi ma kamfanin da yake aiki suka yi masa wannan gatanci? Hakika akwai boyayyen al’amari mai matukar rudani da daure zuciyar tunanin duk mai tunani.
(nima n ace, Isah ba kasan dawn garin ba, Shuhuda Ibn Khaddab ta baka haske sosai ta yadda zaka warware lamarin cikin saukakar hanya, (sadin mama)).
BABI NA GOMA SHA BIYAR
TARIHI YA MAIMAITA KANSA
An wayi gari yau laraba, Inna Yaduwa na kishingide a falo idanunta a rufe, ta kara ‘yar karamar radiyo (kachbo) a kunnenta tan a sauraren wani shiri ‘Ku karkade kunnuwanku’ wanda Aisha Bello Mahmud ke gabatarwa a tashar FREEDOM RADIO wanda suke karanta wani littafi mai suna MACE BAIWA na jinjirar marubuciya mai tasowa Naja’atu Haruna Sale.
Tana jin dadi labarin, saboda yadda aka dauko rayuwar da mata suke a karkara aka rubuta, duk wasu tarin matsalolin mata sun kunshi wannan hadaden labari. Da yake yau din it ace rana ta farko da aka soma karanta littafin, sai Inna Yaduwa ta ke ji, ina ma kada lokacin da aka dibarwa shirin ya cika ba tare da an kamala karanta littafin ba?
Kusan da gudu-gudu, sauri-sauri Shuhuda ta fito daga daki da nufin isa bandaki, sai dai kafin ta isa tuni ta soma kyelaya amai, wanda yunkuri da karar sautin zubar aman ne ya farkar da Inna Yaduwa abin da ke faruwa, hart a hanzarta mikewa zaune daga kishingiden da ta ke tana ambaton.
“lafiya”
Amma Shuhuda shiru ta kasa Magana illa ci gaba da kyelaya aman da take yi kamar zata amayar da duk abin da ke cikinta. Hankalin Inna Yaduwa ya tashi matuka, ta isa gaban Shuhuda a rude tana tambayarta abin day a same ta tare da tattaba jikinta. Sai da kyar aman ya tsagaita, amma duk ta galabaita ta fita hayyacinta. Inna Yaduwa ta kamata zuwa bandaki, tab a ta ruwa ta kurkure bakinta, sannan suka dawo falon, Shuhuda ta kwanta akan doguwar kujera, yayin da Inna Yaduwa ta goge gurin da aman ya bata ta dubi Shuhuda cikin tausayawa, t ace “sannu” bat a amsa ba, Inna Yaduwa ta mike ta nufi kan dan karamin firij da wayarta ke ajiye a kai, ta dauko ta duba lambar Alh. Sada wadda ta sanya wa alamar mota, don duk wanda ke cikin wayar akwai alamar da ta ke gane lambarsa da ita. Kasancewar ba ilimin book ta yi ba. Tana kiran wayar yayin da take dawowa don zaunawa kan kujera. Ya dauki wayar cikin ladabi ya isar da sakon gaisuwarsa tukunna t ace masa. ”Shuhuda ce ba lafiya, tana ta amai, idan kana da hali ka zo a kai ta asibiti” y ace “ina direban gidan ne?” t ace, “sun fita da Alhaji”, y ace, “to ni yanzu na yi nisa sosai, amma bari na turo Nuruddeen sai ya kai ku” t ace, “ba damuwa”, Ta kasha wayar tare da tsurawa Shuhuda idanu cike da jin tausayinta. Ba jima sosai ba Nuraddeen ya shigo gidan yana kada makullin mota, fuskarsa a sake y ace,”yar tsohuwa ke bakin cikin shan gumba zaki yi mana, an ce na zo na kai ki asibiti?” ya fadi maganarsa cikin sigar wasa na kaka da jika, fuskarta a daure t ace,” da yake ba ka da idanu shi yasa ka gaza gane ba nice ba ni da lafiya ba…………. Yayarka ce Shuhuda gat a nan bat a da lafiya, it ace za mu kai asibiti”. Sai lokacin ya lura da Shuhuda da ke kwance akan doguwar kujera y ace,”A’a Aunty Shuhuda me ya same ki”? Inna Yaduwa t ace masa. “ka ga muje asibitin tunda ka ganta a kwance ai kasan akwai matsala”. Ta fada tana kokarin tallafa Shuhuda, suka fita su ukun zuwa inda ya yi fakin, ya bude musu gidan baya ta saka Shuhuda. Nuraddeen ya ja motar cikin azama suka isa ZAHTY MEMORIAL HOSPITAL, aka shiga da ita emergency, Tashin farko likitan day a dubata ya bukaci fitsarinta, aka shiga da ita wani ban daki tayi, sannan ya basu magungunan taimakon gaggawa tare da cewa a dawo anjima a karbi sakamako. Bayan sun dawo daga asibitin gidan ya dinga daukar harami, nan da nan ya cika da ‘yan dubiya. Karfe hudu da rabi Alh. Ahmad da Nuruddeen suka je karbo sakamako. Likitan ya tsayar da su kafin ya basu sakamakon, ya dubi Alh. Ahmad fuskarsa cike da fara’a y ace. “Alhaji ina taya ku murna, da fatan Allah ya raba su lafiya. Amma zan so nab a ku sahwara, duk macen da take da farkon ciki kafin ya yi kwari ana bukatar ta rage yin ayyukan da za su wahalar da ita gudn zubewar cikin…………………..”
Zai ci gaba da dogon sharhin nasa Alh. Ahmad ya daga masa hannu fuskarsa a turbine yana cewa, “Dakata don Allah doctor! Ban fahimci mai kake nufi ba fa?”
Ran likitan ya dan baci sai ka ce bad a yaren Hausa yake masa bayani ba?
Yanzu haka irin mutanen nan ne da suke auren yara kanana amma bas a son haihuwa. Don haka sai ya dauki sakamakon gwajin ya mika masa. Alh. Ahmad ya sa hannu ya karba cikin zumudi, ya duba abin da takardar sakamakon ta kunsa. Ba wani abu ba ne face Shuhuda tana dauke da danyen ciki na wata daya da kwanaki biyar.
“INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN!” Alh. Ahmad ya ji gabansa ya soma faduwa, idanunsa suka sauya launi, cikin wata rikitacciyar murya y ace. “Shuhudan ce da ciki? Mun shuga uku! Ina zamu kai wannan tarin abin kunyar?”
Jin kalaman da ke fitowa daga bakin Alh. Ahmad ya sa jikin likitan yayi sanyi, da farko ya dauka Shuhuda mat ace ga shi Alh .Ahmad din, amma yanzu ya fahimci ‘ya ce a gareshi. Sai ya shiga kwantar masa da hankali cikin sanyayan kalamai. Alh. Ahmad y ace cikin dafe kai. “Likita anya ba a samu akasi an sauya sakamakon Shuhuda da na wata ba? Wallahi budurwa ce ba matar aure ba, ta ya kuma za a ce tana da ciki?”
Likitan y ace cikin nuna tausayawa. “Wallahi ba wani akasi da aka samu, hasalima duk yau ita kadai aka yiwa awon ciki a asibitin nan, shi ma dalilin da yasa aka yi mata, lokacin da aka kawo ta yanayi na mai shigar ciki duk sun bayyanar da kansu a tare da ita, hakan ce ta san a bada umurnin a yi mata awon cikin, sai kuma shi hakan ya tabbata”. Nuruddeen wanda tun fadr cikin ya sandare, sai yanzu y ace. “Abba idan dai har cikin ne da mamaki, saboda kowa yasan tarbiyya ta gidanmu”.
Alh. Ahmad ya dafe kansa, ya nutsa tunanin yadda abin ya faru, iya tunaninsa bai hango wata baraka da zata sa Shuhuda fadawa wannan rayuwar banzar ba. Lokaci daya ya ayyana a ransa, duk yadda aka yi Isah ne yayi mata cikin, musamman idan ya yi la’akari daga kasar waje ya dawo, wata kila dama abinda yake aikatawa ke nana tun zuwansa kasar. Likitan ya girgiza kai, y ace, “Alhaji wannan duk baa bin damuwa ban e, kawai ku kawo ta sai a zubar da cikin asiri a rufe”. Nuradden ya yi saurin cewa. “Haka kawai ma ya dace”.
Alh. Ahmad y ace da Nuraddeen, “muje”.
Suka yi sallama da likitan suka nufo gida kowanne zuciyarsa cike da kunci, wai Shuhuda da ciki na wata daya da kwanaki biyar?
Kafin su isa gidan Alh. Ahmad ya kira yayansa Alh. Sada ya ce su hadu can gida. Suna isa harabar gidan shi ma Alh Sadan ya karaso gidan. Gaba daya suka karaso falo. A cike falon yake, don haka aka wuce dakin mahaifinsu Alh. Rabiu. Dattijon yana zaune akan sallaya yana lazimi, suka zube a gabansa suka kwashi gaisuwa. Alh. Rabi'u ya dubi dansa Alh. Ahmad ya ce. "Ahmadu ya aka yi na ga duk kun shigo gaba daya?" Yayi shiru yana tunanin ta inda zai yanko maganar abin kunyar da Shuhuda ta tafka muusu. Alh. Sada ya magantu ganin shirun ya yi yawa, ya ce. "Ahmadu kai muke saurare, ka kirani a waya ka ce mu hadu nan, kuma ka yi shiru". Ya dago kai cikin dauriya da shanye damuwarsa, ya ce, "Sakamako ne bai yi kyau ba, domin Shuhuda ciki ne da ita na wata daya da kwanaki biyar!" Gaba daya dakin suka dauki sallalami har shi kansa Alh. Amad din. Bayan sun dure sallalamin, Alh. Rabiu ya dora da cewa "Lallai yarinyar nan ba ta kyauta mana ba". Alh. Sada mutum ne mai zafi, idan aka bata masa rai bai iya daukar hukun ba. Yanzu ma cikin matsanancin bacin rai ya nufi falo, kira yake, "Ina Shuhuda???"
Ganin yadda ransa yake a bace yasa Inna Yaduwa tasan da walakin, akwai gagarumin laifin da Shuhuda ta yi wanda yake nemanta, a yadda kuwa ta gani a kwayar idanunsa idan ya damku Shuhuda watakila shi ne sanadin ajalinta. Ta ce. "Tana daki, lafiya?" Bai tsaya bata amsa ba, yana huhhutai ya nufi dakin. Da sauri Inna Yaduwa ta bi bayansam. Yana shiga Shuhuda na kwance akan gado ya wani damko wuyanta, ya daga hannu ke nan zai kifa mata mari Inna Yaduwa ta buda muraya da karfi ta ca, "Idan har ka sake ka daki yarinyar nan ban yafe maka ba!al Cak! Jininsa ya tsaya, Inna yaduwa. Ta ci gaba da cewa. "Abin da nutsuwa bata yi shi ba, daga jijiyar wuya ma ba zai yi shi ba. Komai ta yi maka yadda bata da lafiyan nan karbar hukunci ba nata ba ne". Dalilin Inna Yaduwa kuwa na dakatar da shi daga dukan Shuhudan bai rasa nasaba da tuna halin da ta riski kanta a ciki lokacin da ta jaraba dukan Shuhudan din ba, hannunta ya sankare, abin da har yanzu kuwa babu wanda yasan da faruwarsa. Sai ya saki wuyan Shuhudan ya fice, ita ma Inna yaduwa ta bi bayansa. Ya shiga dakin mahaifinsa ya kifa kai a bango kwallan da ke makale a gurbin idanunsa suka samu damar zubowa. Inna Yaduwa da ta shigo dakin ta gansu sun yi jugum-jugum ta shiga tambayar abin da ya faru, Alh Ahmad ne ya yi karfin halin fada mata komai.m Itama kukan ta fashe da shi, Alh. Rabi'u ya ce. "Kinga daina kukan haka,ku nutstu mu tunkari kalubalen da ke gabanmu". Duk suka yi shiru zuwa wani loka ci, sai can daga bisani Alh, Sada ya dago kai ya ce. "Cikin mutane biyun nan dole a samu daya wanda ya yi mana wannan muguwar ta'asar, don haka a kira yaron nan a tambaye shi ko shi yayi mata ciki". Alh Rabi'u ya dube shi, ya ce, "Wane yaro ke nan?" Ya ce, "Malaminta, wanda ya same ni da maganar yana son aurenta. Hamza sunanasa, shi ma Isah zan kira shi a waya duk abinda yake ya bar shi ya zo domin sanin gaskiyar lamari". Alh. Rabi'u ya girgiza kai, ya ce, "Ba haka za a yi ba, kuu bar min komai. Zan tuhumi yarinyar idan yiwuwar kiransu ya kama sai dai a bari sai lahadi don kada abin ya shafi aikinsu". Inna Yaduwa ta sharce kwalla, sannan ta ce, "Malam ni a ganina kawai a zubar da cikinnan asiri a rufe ba sai wasu sun ji ba". Alh. Rabi'u ya girgiza kai ya ce. "Ko day ban yarda da wannan gurguwar dabarar ba, mutane suna daukar zubar da ciki wani abin rufin asiri, bayan kuma babban tonon asiri ne, kuma budewa yaro kofar shiga bariki ne. Ciki dai an sameshi, kuma ko mun so ko mun ki dale ne mu yarda da kaddarar da ta fada manam Saboda haka maganar ma zubar da ciki ba ta taso ba, ku dai saurareni".
Da wannan shawarar suka tashi, Alh. Ahmad da Alh. Sada kowa ya kwashi zugar iyalinsa da suka zo dubiyar suka koma gida bayan gargadin da suka yiwa Nura ddeen akan kar ya sake ya fasa zancen ko da ga mahaifiyarsa ce. Alh.Rabi'u bai samu ganawa da Shuhusa a ranan ba, sai washegari da safe ya sa Inna Yaduwa ta yi masa kiranta.
Shuhuda ta shigo dakin ta durkushe. A agabansa, kanta asunkuye ta gaishe da shi, ya amsa. Shiru na wani lokaci ya biyoo bayan gaisuwar, can ya daga harshe ya ce, "Shuhuda wani mummunan labari ne ya zo min game da rashin lafiyar ki, wanda ya daga min hankali, shin me ye gaskiyar lamarin? Da gaske wai kin siyar da mutmcinki har kin samu ciki ba tare da aure ba?" Ba ta dago kai ba bare yaga wani yanayi na tsorata ko razani game da jin furucinsa ba. Ta dai yi bakam kamar an dasa dutse. Ransa ya baci ya dan daga murya cikin barazanarwa ya ce. "Magana nake miki, ki ba ni amsa". Har yanzu dai ba ta tanka ba, sai shi ma ya yi shirun yana ci gaba da tsare ta da idanunsa. Ganin ba ta da niyyar tanka masa ya sa ya ci gaba da cewa. "Shuhuda ba ki kyauta ba, kin kuma zubar mana da mutumci duk da cewa kkanki kika yiwa illa. A matsayinki na marainiya maimakon ki rungumi maraicinki da kyau, amma sai kika yi watsi da kyakkayawar rayuwa. Shin wane rudin soyayya ne ya kai ki ga aikata wannan mummunan