Showing 78001 words to 81000 words out of 81464 words
Chapter 27 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt
dama babu yadda matsafa zasu yi da ita, saboda ko inda ta ke bas a iya karasowa.
Shi ma Isah ya fi karfinsu saboda mutum ne ABIDI, ma’ana mai yawan ibada.
Cikin dare shagunan shuhuda da ke cikin kasuwar kwari suka kama da wuta, hankalin Alh. Rabi’u ya tashi kwarai, amma ita shuhuda ko a jikinta, don da zasu bi shawararta ma da an sadaukar da dukiyar gaba dayanta tasan kuma dole zata kare, domin kyalkyal banza ce, kuma dama GARIN BANZA a farau-farau banza yake karewa.
Mabiya kungiya sun tashi da tashin hankalin mutuwar mataimakin shugaba, sun damu tun daga nan wasu suka soma yiwa kungiyar tawaye tunda dama babu wanda ke gundanar da mulki kamar mataimakin shugaba, sai suke gudu wasu kuma suka yi gamayya da wata kungiyar saboda sama akwai abota a tsakaninsu.
Wannan dalilin ya tashi hankalin tsafinsu inda ya bas u tabbacin jinin shuhuda da Isah ya zam dole a sha shi, amma an rasa ta inda za a kama su, hakan ya sa Yakub da ke kallonsu ya sanar da Isah da shuhuda suka nufi kasa mai tsarki don yin umra, suka yi dawai don samun rinjaye akai.
Allah ya bas u nasara gaskiya ta fi karya, alkur’ani waraka ne, sun ce gaba da karantun alkur’ani a masallacin Makka, sanna suka ziyarci Manzon mu a can Madinatul Munawwara.
Cikion kudirar Ubangiji dakin tsafin nasu ya kama da wuta, duk wasu manyan bokayensu da suka yiwa biyayya Allah ya karya su, duk abin da suke tinkaho das hi ya lalace, wasu daga cikinsu Allah ya ganar da su, sun shirya, wasu sun mutu, wasu sun samu tawaya ta rasa wani bangare na jikinsu, wasu kuwa hauka tuburan suka dinga yi, haka komai ya lalace musu.
Shuhuda ta kubuta daga sharrinsu, ta samu lafiya, ta samu jin dadin da ta rasa.
BABIN KARSHE
RAI DA RABO
Jin dadin rayuwa ya samu ga shuhuda Sagir Rabi’u, yanzu ta gano Isah Sada abi’u shi ya sama mata jin dadin rayuwar da ta rasa. Yanzu shuhuda ta zam mutum kamar kowa. Dama can ita yarinya ce mai nutsuwa ga kaifiyya, a yanzu ma abin haka ya ke, ta samu gurbin karatu a B.U.K Kano, yayin da ta tsunduma neman ilimi ka’in da na’in, a yanzu ta dawo baya saboda samun waraka ma’ana tun farko ta soma karatun alkur’ani ta dantsama a sira don sanin tarihin manzannin Allah, kawa ‘idi, Ahlari, Ishmawi, Izziya duk cikin kankanin lokaci ta yi nisa, dama can ita yarinya ce mai kwalwa.
Idan ta samu hutu tana kai wa mahaifiyarta Haj. Karima ziyara can karare.
Dama an bat a dama ne saboda ta samu ilimi cikakke domin a da tana rayuwa ne ga ta nan ga ta nan, shi kuma Isah yana can Ibadan a ma’ikatar da yake aiki, yana samun dudi sosai a rayuwa, domin Allah ya yi masa nasibi.
Ya samu dauka kwarai da gaske, ya kuma fantsama harkar kasuwanci, samun kudin Isah ya tada hankalin Alh. Rabi’u ta inda ya yi kiran mahaifin Isah Sada ya fada masa abin da ke cikin zuciyarsa. Hausawa sun ce, idan maciji ya sare ka to idan ka ga bakin tsumma zak tsorata.
Sun sanya masa ido sun bi komai daki-daki, kuma bas u same shi da wata badala ba, hakika dukiyarsa wankakkiya ce, a yanzu an maida shi Abuja kuma ana ta shirye-shiryen yi masa biki da shuhuda.
Shuhuda kwance idanunta na zubar da hawaye. Inna yaduwa ta shigo ta samu gefenta ta zauna, ta ce.
“Anya shuhuda rayuwa zata samu haka?”
Ta daga idanunta dubi inna yaduwa ta ce mata.
“dole ne na yi kuka inna, da ban san komai a rayuwarta ba, duk abin da ya faru gare ni wai-wai nake ji, nasan dai ina rayuwa ne tare da matsafa, ina kuka ne don ina jin tsoron haduwata da Allah”
Inna yaduwa ta ce.
“haka ne shuhuda, amma ina so ki sani Allah ba ya kama bawa da laifin da bai aikata ba, sun juyar miki da tunani ne tun kuruciya”
Sallamar Haj. Karima ta katse ta, ta shigo Inna yaduwa ta yi mata lale marhabin, bayan ta zauna inna yaduwa ta ce.
“Gwanda da Allah ya kawo ki, yarinyar nan taki ta dauki abin nan da ya faru ta saka a zuciyarta, kowane mai raid a irin kaddararsa, ki yi hakuri kinji shuhuda”.
Ta sanya hannu tana goge idanunta da suka yi jijir saboda kuka.
“Ni ina jin haushin Baban ne, ina ji a raina ban yi sa’ar mahaifi ba, in jin haushin Ummata da aure shi, saboda kila don yana da kudi ne ta aure shi, me yasa bat a nema min uba na gari ba?”
Murmushi kawai Haj. Karima ta yi, tana jin radadin kalaman ‘yar tata, tasan auren soyayya suka yi da Sagir duk cewar lakacin da ta aure shi yana da abin hannunsa, amma dukiyarsa ba ta rufe mata idanu ta so shi ba, kuma har yanzu tana jin soyayyarsa a ranta, ba don Alh. Jamilu ya yi mata rukon mutumci ba, kila da har abada ba kuma wani auren ba, tana kuma yi masa addu’ar Allah ya yafe masa kura-kuranse.
Ba karamin rudewa ta yi ba a lokacin da inna yaduwa da Isah suke kora mata bayanin abin day a faru ba, saboda sam Sagir a mu’amala mutumin kirki ne, kila da ya yi TSAWON RAI za ta iya gano illar halin day a sanya kansa.
Hawaye na bin kumatunta ta dubi shuhuda, ta ce.
“shuhuda ke yanzu ba yarinya karama ba ce, domin aure ne a gabanki, ke yanzu kina shirin zam uwa, shin kina irin wannan halin wace tarbiyya za ki ba wa ‘ya’ yanki? Kin san kaddara kuwa? Kin san me ake nufi da kaddara? Shin kin yi imani da Allah kuwa? Ina da ja a kan ki shuhuda, ni mahaifiyarki ce zan sanar da ke abubuwan da har yanzu nag a tunaninki bai zo kai ba.
Kin yi imani da Allah kuwa, ko har yanzu tsafin na cikin kwanyarki ne? ko har yanzu ba ki zam cikakkiyarki mutum kamar mu ba? Bari ki ji abin da ake nufi da imani.
IMANI DA ALLAH
Abin da ake nufi da imani da Allah shi ne, ki yi imani da Allah da kyakkyawar zuciyar, ki shaida cewa akwai Allah, kuma Shi ne mai kowa mai komai, Shi ne wanda Ya kagi duniya da lahira da duk abin da suke a cikinsu. Idan hakan ta samu, toh lallai za ki so Allah, domin son Allah wajibi ne, idan kin so Shi za ki girmama Shi Zuciyarki. Ya zamar wad an adam wajibi ya so Allah, ya kuma girmama Shi, idan mutum ya kasance haka zai guji sabawa Allah da manzanSa, zai kuma nisanci abin da Allah Ya hana idan haka ta samu mutum zai samu jin dadin rayuwa a nan duniya da lahira, kamar fadin Allah (S.W.T) a cikin alkur’ani mai girma.
“wadna ya aikata aiki na gari mace ko namiji a halin yana mumini wallahi zamu rayarda shi rayuwa mai kyau, kuma wallahi zamu saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa”.
IMANI DA MALA’IKU
Kuma idan kana son zama cikakken mai imani dole ka yi imani da Mala’ikun Allah (S.W.T), Shi Ya halicce su, Ya sanya su su dinga gadinka a matsayinka na dan gatan bawanSa. Idan mai imani ya tuna haka zai dada son Ubangiji har ya ji yana da GIRMA sosai, saoda kulawar da Yake bas hi, hakan kuma zai sad an Adam ya godewa Allah.
IMANI DA LITTATTAFAI
Amfanin imani a zuciyar dan Adam zai sa kasan HIKIMAR ALLAH da kulawarsa ga bayinsa dalilin littattafan da Ya saukar wa kowace al’umma. Hakan zai samu gane hikimar Allah cikin abubuwan da Ya shr’antawa kowace al’umma, domin su fuskanci littattafan da suka dace da zamaninsu, sai Ubangiji Ya maida karshen wadannan littattafai shi ne ALKUR’ANIL KAREEM, wanda ya dace da halukan kowa kamar yadda kuma ya dace da kowanne zamani, kuma kowanne bigiri har ya zuwa ranar kiyama. Kai mun godewa Allah da Ya yi mana ni’ima da saukar mana wannan littafi mai tsarki.
IMANI DA MANZANNI
Dole ne mu so manzannin Allah (SWT) domin Allah Ya aiko mana da Annabawa masu daraja da girma don su zama shirya a gare mu, ya kuma aiko mana da fiyayyen halitta don ya zama cikimakin Annabawa. Hakan zai sa mana son Annabawa ya sa kuma mu girmama su, mu yaba musu domin su ne Manzannin Allah, su ne kebabbun bayinSa da suka tsaya akan bautar Allah da isar da sakonsu da yiwa bayin Allah nasiha suka yi matukar hakuri abisa duk wata cuta da ta su a cikin wannan aiki nasu.
IMANI DA RANAR LAHIRA
Dole ka yi imani dar ranar lahira hakan zai kwadaita wa mutum bautar Allah Ta’ala t inda zaka yi kwadayin samun ladan lahira, zai kuma sa mutum ya nisanci sabawa Allah a cikin ranar lahira ne wadda ya guji MATA’ULHAYAT (kyale-kyalen rayuwa) zai shakata da ni’imar Allah, ya ji dadin ladan aikinsa”
Shuhuda jikinta ya yi sanyi da jin bayanin haifiyarta, ta yi sa’ar uwa wacce ta ked a ilimi, sai dai ba ta yi sa’ar uba ba, da ace yana da ilimi kila da bai shiga kungiyar matsafa ba.
Kamar mahaifiyarta ta karci zuciyarta, ta ce.
“Zan miki bayani akan IMANI DA KADDARA, domin na sanar da ke kowanne rai bay a tsallakewa akan abin da Allah ya kaddara masa.
IMANI DA KADDARA
Idan kin dauki kaddara kin yi imani da Annabawansa, dole ki yi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau. Idan ka yi imani da kaddara hakalinka zai kwanta, don zaka samu hutun zuciya, in dai ka yi imani da ita duk wani tunani zaka daina shi, domin duk lokacin da mutum ya fahimci duk abin day a same shi hukuncin Allah ne babu shakka idan ya yarda da hakan zai samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, ya kuma yarda da hukuncin Allah a kansa..
Babu wanda ya kai mai imani da kaddara samun nutsuwa da hutun zuciya, domin idan ka yi imani da haka, sai ranka ya nutsu, ka sakankance ka rungumi kaddara zuciyarka ta saki.
Haka kuma zai korewa mutum duk wani ji ji da kai, inda wani alheri ko wata ni’aima ta same shi sai ka gay a gode Allah, ba zai yi mamaki ba, kuma ba zai kawo wayonsa ko dabararsa c eta ba shi ko iliminsa ba.
Yarda da kaddar zai korewa mutum bacin rai, sai mutum ya yi hakuri da abin day a same shi sai Allah ya bas hi ladan hakurin.
Wannan shi ne manufar Allah (S.W.T) da yake cewa a cikin alkur’ani mai girma.
“Wata masifa bat a taba samuwa ba ko a ban kasa ko kuma cikin kawunanku face duk yana cikin littafin lauhulmahafus, kafin mu halicceta, wato ita wannan kasar da wannan ran lallai wannan abu ne mai sauki ga Allah, domin kada ku bata ranku da abin fa ya kubuce muku, kuma kar ku yi fariya da abin da Allah ya ba ku. Allah bay a son mai yawan takama, mai yawan alfahari.
Shuhuda ta fashe da kuka, yanzu ta fahimci Ummanta, ta gano kuskurenta ta yarda da kaddara.
Ta dubi mahaifiyar tata, ta ce.
“A da na yi alkawarin har na bar duniya b azan taba yiwa babana addu’a ba. Amma yanzu kin karya lagona, zan kasance mai roka masa rahmar Ubangiji”
Inna yaduwa ta dubi Haj. Karima, ta ce.
“Shi yasa na ke sonki, har yanzu in bakin cikin rabuwarmu da ke a tsatsonmu”
Haj. Karima ta ce.
“Inna ya zamu yi da hukuncin Ubangiji? Haka Allah ya tsara mana, sai na yi aure a wani gurbin”
Ta yi murmushi, tukunna ta ce.
“Muna zaune lafiya, ni da zai yarda da na ba shi shawara ya dawo da uwar ‘ya’yansa tunda ta fi mu gaskiya akan zargin mutumwar danta”
Jin hirar da suke shuhuda ta mike ta fice a falon, inna yaduwa ta ce.
“A’a. kada ki soma wannan dayen hukuncin, yanzu gas hi kin yi kyau, kin yi kibarki, kin san fa su jarababbun mata daban suke, kuma mai hali ba ya fasa halinsa sai dai ya yi sauki ku dai yi zamanku lafiya, Allah ya bata wani mijin”
Bakin Uncle Hamza da Zuwairiyya ya tashi, kamar ba a yi ba, haka nan dai ya daure ya amince zai aureta ko don jiran da ta yi masa.
Isah da shuhuda sun halarci bakin, sun kuma yi masa gudunmawa wacece tat say masa a zuciya.
Sanye ta ke da doguwar riga ta yi daurin daidai da zamani, flat shoe ne a kafarta ta sanya dankunne da awarwaro hard a zobe, duk macin hannynta dauke da ledar tana tafiya kamshin turarensa kawai ta shaka don kanta a kasa yak e, tad ago fuska tana murmushi. Isah ya ce.
“Sai ina haka ‘yanmatan?”
Ta ce, “Wajen su Hajiya zan zaga”
Ya ce, “Bari na yi rakiya”
Ya ce sanya hannu ya karbi ledar hannunta, tad an tsaya ta marairaice cikin shagwaba ta ce.
“Ni a’a ba sai mun je da kai ba”
Ya ce, “kin san dama mu tun muna yara tif da taya ne, raba mu sai Allah, ko bah aka ba ‘yar amaryata?
Yarinya day a fada ya ba ta dariya. Sun jera cikin gida kananan yara suka tso da gudu,
“Aunty Shuhuda oyoyo”
Ta samu gefe ta zauna suna gaisawa da matan gidan, yaran suka ringa lekenta sai suka sake gaishe ta, sun gaishe ta ya fi sau uku said a Isah ya kore su, sai ta farga alewar da ta saba raba musu ce bat a bas u ba, shi ne suke ta gaishe ta, ta amshi ledar hannun Isah ta ce.
“Gas hi ku je ku sha, mantawa na yi”
Su Haj. Asibi suka ringa dariya akan kuruciyar su Hadiza auta.
Komai aka saw a rana wa’adi gare shi, kuma saurin zuwa yake, aka ce RAI DA RABO, yau Allah kawo ranar bikin Isah da shuhuda, an sakata a lalle mahaifiyarta tun ana gobe kamu tai so garin tare da ‘yan uwanta suka kawo kayan daki rantsattsu hard a furniture wanda Alh. Jamilu ne ya yi komai da uba yake yi.
A nan ma iyayenta sun yi mata kaya na gani na fada, dayya aka shirya gidan shuhuda tamkar ba za a mutu ba. An shirya gagarumin biki na ‘yargata, Inna yaduwa ta godewa Allah akan TSAWON RAI da ta yi har ta ga auren Isah da shuhuda, ta dinga tuna kurunciyarsu.
Manyan malamai sun yi laccar aure, sun kuma tunar da iyaye akan sanya ido ga rayuwar ‘ya’ yansu, domin rayuwar yanzu rayuwa ce mai cike da hadari a cikinta.
Gidansa da ke shagari Quarter a nan cikin jihar Kano aka kai ta. Satinta daya suka wuce honey moon, sun zagaya kasashe shida, a China ne suka hadu da Zuhran ya Deen (KANIN MAJINA) wadda ita ta ji ta aminta da ita domin ita dama bat a yi wasu kawaye ba, Isah ne mijinta kuma amininta.
Shuhuda ta samu gata a bangaren mijinta, yana riritata, domin ita ma mace ce wacce tasan kanta, ma’ana tana kula da jikinta ta fannin gyara, sannan tana ba wa duk wani abu na mijinta muhimmanci ta fannin abinci saban wasu matan da ba su mayar da hankali akan abin da majinsu yake so ba.
Tana ba shi kulawa ta musamman, sai ta kosar da shi, hakan ba ta taba barinsa da wata bukata har sai ta kosar da bukatunsa, tana tattilin mijinta kamar yadda yake riritata.
Da safe idan ta tashi sai ta yi kwalliyar da zata tsaya masa a rai, bat a barin kofar da mijinta zai hango kyawun wata macen a waje.
Kamshin jikinta kamshi ne na musamman duk mecen da tasan sirrin kanshi, kuma tasan kanta dile ne ta kula da kikinta ta hanyar kamshe yadda zai wadata jikinta, domin mu mata jikinmu lunguna-lunguna ne das hi, idan har za ki bari miji ya ji wani wari a jikinki, lallar za ki gundure shi har idan kina da kishiya ki ringa zargin ta raba ki da mijinki, alhalin ke kika raba kanki das hi.
Dole ne mata mu kula da kamshi a jikinmu, domin shi kansa kamshi yana motsa sha’awa, baki yana da muhimmance a kula da shi, domin idan har zaki yi Magana a ji tashin wari lallai zaki ga ko mata ne za su ringa kawar da kai bare kuma mijinki.
Hamata ita ma a kula da gyaranta, kada a barta da gashi domin tsafta tana taka muhimmiyar rawa wajen zaman takewar aure, kada ki ce, to ni dab a ni da shi, da me zan sanya turare? ‘Yan uwanna mata akwai turaruka masu kamshi da saukin kudi ba lallai sai kin yi amfani da mai matukar tsada ba.
Sai uwa-uba ma kwanciya, lallai mace tasan salo-salon wasanni da zata zo wa majinta da shi don ta gamsar da shi, Muddin za ki kosar da shi babu yadda zai yi ya yi kwadayi a waje balle ya fada hannayen kurayen dawa (karuwar).
A gaskiya wasu matan su ke sakaci wajen sanya mazansu bin matan banza, komai sai ka ji mace ta ce, sai ka ce wata ‘yar iska, ni ba zan iya ba, abin da mu matan gida ba mu gano ba shi ne, su matan wajen da me suka fi mu? Mun fi su komai namiji zai fi samun nutsuwa akan ta waje, amma sai mu sau bakin zare idan an aure mana yarinya ki ji an ce ‘yar yarinya c e, amma idonta a bushe yake, saboda me ke ba zaki bude idonki ba ki ba wa mijinki kulawa ta musamman don ki kwato shi daga hannunn kuraye?
Shuhuda kwance ta yi filo da cinyar Isah, shi kuma hankalinsa na kan labaran da yake kallo, ta ga ya sauya tasha ta tabbarta y agama jin labaran, ta ce.
“yah Isah?”
Ya maida dubansa a gare ta ya ce.
“Ya aka yi ne matar?”
Ta ce “kasan na yiwa zuhura alkawarin idan mun shigo kano zamu kai mata ziyara.
Ya ce allah ya kaimu za mu je ne.
Sun je gidan zuhuran Deen ta kira wayarta ta bata adresse sosai suka iso gidan suna shigowa get din gidan a lokacin suka hango deeni sun yi fakin kusa da su, ya dubi Isah ya gane shi suka gaisa, ya ce.
“A’a ashe kun iso kano? Ya Abujan ne?
Suka gaisa da wasu yara, ya ce.
“A’a duk naku ne wadannan yaran?
Isah y ace “Eh, wai za su je gidanmu ne su gaida baffa su yi masa week end.
Isah ya ce “A’a, kai dai ka ce kun kori yara zakuji dadinku”
Deeni ya yi