Showing 18001 words to 21000 words out of 81464 words

Chapter 7 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt

Bari na dubuta. Ba ta tanka ba. Ya nufi dakin Shuhuda tarar da ita ya yi zaune akan abin sallah tana lazimi shigowarsa yasa ta tsinke lazimin tace: Baba barka da zuwa. Yace yauwa 'yar baba. Bayan ya zauna saman gadonta ya dora da cewa; Akace baki jin jin dadi? Ta dube shi cikin yanayin rashin fahimta, ta ce: Ni? Kai ni yau garas nake, shekaru sha takwas ne dai na dan yi rashin lafiya, ita ma ban wani jima ba na samu sauki sai dai ko a mafarki ne na ji kamar ba ni lafiya? Fuskarta ta bayyanar da yanayi na tuhumar kanta da kanta. Kafin ya yi magana ta dora da cewa. Amma dai lafiya na ke, jina na ke ma kamar ingarman doki saboda karfi bari ma ka gani. Kawai sai ta mike ta kama tsalle. Bai yi yukurin dakatar da ita ba, tabbas Shuhuda tana da ta6in hankali. Abin da ya ayyana a ransa ke nan. Bayan ta yi tsallen ta koma saman gadon ta zauna tana wata irin dariya ya tsura mata idanu can yace; Ki shirya zamu je Asibiti. Tace: Asibiti? Eh, Ya tabbatar mata. Bata musa ba tac: To. Ya tashi ya fita. A falo ya zauna suna hira da inna yaduwa can Shuhuda ta fito daga dakinta. Inna yaduwa ta wurga mata sakon harara, Shuhuda ta ja tunga turus ta tsaya. Ni fa ki daina hararata idan kina hararata sai na dinga ganinki kin koma min kamar wata dodanniya. Dubi yadda idanuwanki suka yi kulu-kulu kamar kuruga, ina jin sai na rage miki girmansu. Inna yaduwa ta ja tsaki. Sai ki maida hankali tunda ke ce sarauniyar wauta. Shuhuda tace: Au ba ki san ni sarauniya ba ce? To wallahi ki sani an bani sarauta tu lokacin da ya shude, yanzu haka idan fadawana suka ganki sai sun hukunta ki. Alh Ahmad yana so ya yi dariya amma ya gumtse don shi abin na su ma dariya ya soma ba shi. Yace Inna zamu je Asibiti. Tace: Sai kun dawo, ya dubi Shuhuda yace: Wuce mu ta fi. Yana gaba tana binsa a baya har inda ya ajiye motarshi. Sun isa asibitin Fancy Clinic Alh Ahmad ya bukaci ganin Dr Ya'u likitan da ya yiwa Shuhuda tiyata shekarun baya. Anan ne ake sanar da shi ai ya jima da rasuwa. Gaban Alh Ahmad ya fadi yaushe Dr Ya'u ya rasu bai sani ba? Koda yake sun jima ba su zo asibitin ba. Dr Ya'u kwararren likitane da ake ji da shi a wannan asibiti. Ya yi musu aiki lokacin da Shuhuda ta ke tsotsar hannu aka tsaga wanda daga lokacin ne ba ta kuma tsotsar hannu ba. (((( Sai dai abin da Alh Ahmad bai sani ba shine; tun bayan sallamar Shuhuda daga asibitin ya yi ta fama da rashin lafiya wadda bata jin magani daga karshe ya rasu. Sanadin ya faru ne sakamakon allurar da yayi a jikin Shuhudan. wanda idan muka duba tun baya mutum biyu Salmai ta rasu bayan ta tsarga hannun Shuhuda da ta yi. Mas'ud shi ma ya rasa ransa sanadin jinin(ruwan nono) da ya fito daga jikin Shuhuda. Don haka zamu iya tantancewa duk wanda ya yi sanadin fitar jini(ruwan nono) a jikin Shuhuda yakan rasa ransa ne. Me ye sanadin haka?)))). Dole sai wani likitan suka samu ganawa da shi ya yi aune-aunensa da gwaje-gwajensa ga Shuhuda daga karshe ya tura su asibitin mahaukata da ke garin Dawanau don yace yana ganin matsalar tata sai an dangano da can.
YAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤10¤¤
koda suka fito daga wannan asibitin kai tsaye Dawanau suka nufa. A cikin motar Alh Ahmad har lokacin jimamin rasuwar Dr Ya'u yake yi yayin da Shuhuda ta yi lum kamar mai bacci. Suna isa asibitin Dr Ibrahim m Sani suka gani ya yi gwaje-gwaje ga Shuhuda ya dubi Alh Ahmad yace: Na gama bincike ga yarinyar nan abin da binciken nawa ya ba ni, lafiyarta kalau ba ta da wata cuta da ta shafi kwalwarta. Illa iyaka ta kasance daga cikin yara masu kaifin kwalwa (Gifted) don haka za a ga tana bada himma a karatu da sauran al'amura domin ita kwalwar tata ontop ce da an saka mata abu ta ke daukewa. Alh Ahmad yace; Likita ba wai ban aminta da bayaninka ba ne. Ina so ka gane ita wannan yarinyar ba a 6angaren karatu kawai ne ya samu zargin tana da ta6in hankali ba a'a wani lokaci fa idan ana zaune da ita sai ta yi ta sakin maganganu na shirme. Dr ibrahim yayi murmushi; yace: Irin wadannan yara ba su fadar abu na shirme sai dai idan a gaza fahimtarsu amma idan aka nutsu aka yi wa maganganunsu kyakkyawar fahimta za a ga komai suka fada yana akan turba. Alh Ahmad ya jinjina kai cikin sarewa yace; Shi ke nan likita, mun gode. Koda suka taho a hanya Alh Ahmad bai aminta da bayanin da Dr ibrahim ya yi masa ba. Gani yake bai da kwarewa ne akan aikinsa don haka ya yanke shawarar zaije ya fadawa dan uwansa abin da ya wakana inyaso idan ta kama su fita da ita wajen sai a fita da ita don gaskiya duk wanda ya ga abubuwan da Shuhuda ta ke yi yasan tana da ta6uwa a kwalwarta. Baba wai kuna zargin ni mahaukaciya ce? Muryar Shuhuda ta katse masa tunaninsa. Bai bata amsa ba taci gaba da cewa. Ina mamakin yadda ake kallona a matsayin mahaukaciya, shin idan ni mahaukaciya ce da ba a ganni ina shiga bola ba? Ku daina yi min kallon mahaukaciya ni na fi kowa hankali, ko kun manta daga MISRA na fito? Ko kuwa so kuke na koma inda na fito? Ko a yanzu ma ta yi shirmen da zai tabbatar da tana da ta6uwar kwalwa to amma a yanayin da take ciki ba zai nuna hakan ba, gudun kada ya sa ta a wata damuwar. Haka ya kyale ta tana ta zuba surutai na rashin kan-gado har suka isa gida ya sauke ta. Ko shiga cikin gidan bai yi ba ya juya. Yayin da ita kuma ta shiga gida tana gunjin kuka, wai an mayar da ita mahaukaciya bayan kuma an san ta fi kowa hankali. Inna yaduwa tana jinta ta yi kunnen uwar shegun da ita har dai bacci ya dauke ta. Inna yaduwa tana jinta ta yi kunnen uwar shegu da ita har dai bacci ya dauke ta. Ta leko dakin ta ga Shuhuda na sharar bacci ta yi murmushi rac: Ja'irar kawai waye zai ganki yace ba mahaukaciya ba, bayan kina abubuwa na mahukata? Ai ni ba su burge ni ba da ba su sanya igiya sun daure ki ba. Tsalam! Shuhuda ta mike daga kwance idanunta jajur tace: Sai kizo ki daure ni din. Inna yaduwa tace: Au! Ashe ba baccin kike ba? To koma ki kwanta kin fi kowa hankali. Ta karashe maganar tana kokarin juyawa.
Idan ke ba ki daure ni ba, ni zan daure ki domin na ga alama kin soma shiga bola kina tsin-tsince dubi yarga6a66un kayan jikinki kin wani daura dankwalin kaya ..... Hahaha mahaukaciya 'yar larai ku yi mata yeho. Ta saka dariya. Inna yaduwa ta tabbatar dai akwai haukan a tare da Shuhuda ta sa kai ta ficce ba ta kuma saurararta ba, don idan ta biye mata shirme zata yi ta zuba mata. ==========================----
--------------------------------------- ========BABI NA BIYAR=======***
*******BARA DA BANA******* Ina da hujjoji da ya sanya nake tababa da zamantowata cikin irin halittunka na mutane. Wadanda idan ka dube su da kyau zaka gasgata hakan. kaga kamar misali: Ni idan dare yayi nakan samu kaina a wata daula ana kidan kalangu ina rawa tamkar mazari. Sannan nakan sha ruwa a cikin koko har ma na watsa a jikina ana zagaye da ni wasu na hidima a gare ni. Da zarar sanyin asuba ya ratsa gangar jikina sai kuma na tsinci kaina a cikin kasar Misra ina ta ibadu..... Da safe kuwa sai na dinga jina wata iri bana tantance halin da nake ciki na farin ciki ko bakin ciki? Haka nan nake jina sakayau, kuma nannauya har ma na rasa a ina nake......... Shuhuda ke nan da ta ke fadawa Uncle Hamza lokacin da ya sake rutsata a cikin ajin nasu, bayan dalibai sun fita break. Ta daina ba shi mamaki, sai dai maganganunta babu tababa za a ajiye su a matsayin BARA DA BANA idan akayi duba wai tana jinta SAKAYAU kuma NANNAIYA wannan anyi ba ayi ba ke nan. Tunda tana samun kanta a wannan yanayin. Ya kawar da shirunsu da cewa: Kin san me nake so da ke? Girgiza kai ta yi ba tare da tayi magana ba. Yac: Gidanku nake son sani. Ta fito da idanu waje. Gidanmu? Ya daga mata gura alamun tabbatarwa. Tace ; Ayya ka MAKARO domin gidanmu yana da nisa. Yace Eh, duk nisan sa ina son sani. Tace Misra fa? Kasan kuwa nisan da ke da akwai daga nan zuwa Misra? Ya girgiza kai. Tace; Nisa ne mai tarin yawa. Yace: Ke ta ya kike zuwa kina kuma dawowa makaranta?
Ta yi dariya tac: Ai ni akan wani keken doki nake zuwa. Yace; Kinga ni ma sai na hau keken dokin naki ko? Ta sake yin dariya har tana tuntsirawa tac: Ai ba ka iya hawa. Yace: Saboda me?
Saboda ba ka da guri, kuma iska zai yi maka lahani tunda ba ka saba ba. Yace; Ke mai yasa bai yi miki lahani ba kafin ki saba? Tace: Ni? Ai babu abin da ke min lahani irin iska, kullum fa na koma gida sai na suma, mamata ta yi ta kwara min ruwa sannan na ke farfadowa.
Wannan yarinya ta gama raina masa hankali, abin da ya ayyana ke nan a ransa. Koda yake ya shiga tababa shi ma na zamantowarta mutum kamar yadda ita kanta ta ke tababa. Shi kam yaci alwashi ko ma aljana ce zai ci gaba da bibiyarta har ya gano ko wace ce ita. Da farko ya so sharewa da lamarinta amma a cikin kwanaki hudun da bai kulata ba, zuciyarsa ce ke azalzalarsa, ya shiga wani irin bahagon, yanayi na mararinta daurewa kawai ya yi yana kawar da kai ga duk abin da zai alakanta shi da ita, amma hakan ya ci tura.
Ya dai yarda ya kuma amince ya kamu da matsanancin son halittar da bai san tartibin daga cikin halittun da ta fito ba.
Ya ja gauron numfashi kafin yace: Kinga ni ma idan iskan ya yi min lahani sai maman taki ta kwara min ruwa na farfado. Wannan karon ma sai da ta kuma yin dariyarta, sannan tace;
Gaskiya mamana ba ta bari na je mata gida da wani, wai ba ta son ganin bakuwar fuska a gidanta. Ta fi son kullum ta ga fuskar da ta sani.
Ko me ye dalilin hakan? Ya bukata yana tsare ta da idanu.
Nima ban san dalili ba. Ta bashi amsa cikin yanayin damuwa. Na dai lura baki son naje gidanku.
To ai ban san me yasa kake son zuwa gidanmu ba. Ta fada. Ina son na gaishe da mahaifinki. Inji shi.
Ba zato ba tsammani yaga hawaye sha-shar na zuba daga idanuwanta, kafin yace wani abu ta ci gaba da cew:
Mahaifina Allah yayi masa rasuwa a gidan gonarsa, sanadin tuntu6e da ya yi da kahon LIBHAS, ya dinga aman jini daga karshe aka dangana shi izuwa asibit acan ya rasu, kuma a ranar aka haife ni.
Cikin yanayin tausayi da rudani yace: Me ye LIBHAS? Tace; Nima ban sani ba, kawai dai an fada min da shi ne yayi tuntu6e.
Wa ya fada miki? Ya bukata. Ta daga kanta sama kamar mai tunani can tace.
Ni ko shi mahaifin nawa ne ya fada min? Ko kuwa YAKUB ne? Inna Yaduwa? Kai ni na manta, ban ma dai sani ba. Amma kuma kamar da KAHON LIBHAS ya yi tuntu6en.......
Akwai alamar tambaya mai karfi na zamantowar Shuhuda mutum, saboda ya za a yi mutum da ta ce a ranar da ya rasu ta zo duniya kuma har ya samu damar fada mata da ya yi tuntu6e da shi? Kaddara ma shi din ne ya fada, sai dai ga waninsa da ta yi wayo kuma aka sanar mata.
Waye Yakub da Inna Yaduwa? Duk yadda aka yi tana da alaka da su kuma zai iya yiwuwa cikinsu din ne wani ya fada mata. Idan haka ne me ye gaskiyar lamarin MTUMCE ITA KO ALJANA?
.
Mu taru littafi na biyu.
.
.
MATA UL HAYAT BOOK 2
......... Yadda TSAUTSAYI ya hada mu
yanzu a gaba KADDARA zata hada mu......
....... Kafin hannun ya isa jikin Shuhuda sai ya sandare Inna yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu jini a tare da hannun.
..... An fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun....
...... Ai dik yawona ban kai TANZIF ba, wanda yana iya zuwa kasa goma a kwana goma.....
...... Na fada maka bana iya amsa tambaya don ni kaina ina da tambayoyin da zan yiwa kaina, to amma saboda wannan dalili yasa na kan ajiye tambayoyina har zuwa ranar da zan samu MATA'UL HAYAT......
...... Amma cikinta na juyawa kamar ana wana wani abu, kwatankwacin yadda idan an harba kwallo take.......
....... Wannan Shuhudar itace muka hadu fa da ita a birnin.......
Wadannan tare da wasu zallan chakwakiya dik zaku samu amsar su sinqi-sinqi a sassanqame a cikin wannan gida me Albarka.
.
.
Taku har kullum
Zahra'aru Baba yakasai
Maman Shureim.
.
Allah ya jikanta ya gafarta mata Ameen
.
Ta ku a kullum kuma a koda yaushe me muku posting Sadiq Halima (Sadin Mama) er mutan NIGER.
Hada Hausa Book stories
====MATA'UL HAYAT BOOK 2====- ==========¤¤11¤¤==========- Katse masa tunani ta yi da cewa. Mahaifina na sona amma sai Allah bai nufa za a haife ni a lokacin da yake da rai ba. Bayan mahaifina mutum daya ne yaso ni kamar mahaifin nawa, shi kuma ya ta fi kasar Senegal karatu. Uncle Hamza yace: Da gaske kike? Ta yamutsa fuska sannan tace: Ban gane ba? Yace: Mahaifinki ya rasu? Tace; Tabbas! To ina mahaifiyarki? Ko ita ce Inna Yaduwa? Ta girgiza kai, Ba ita ba ce Inna yaduwa, mahaifiyata ta yi aure. Ina zaune ne a hannun Inna yaduwa wadda ta haifi mahaifina. Yace: Allah ya jikan mahaifinki........ Ba ta amsa ba, sai suka yi shiru su duka can ya dago kai yana dubanta, yace; Rannan kin shigar da korafin kada na yi miki tambaya wadda ta shafi bil'adama ko me ye sanadi? Tayi murmushi tace: Saboda ka yi min bayanin waye dan Adam kuma na gamsu. A matsayinka na malamina nasan kana son dorani akan abubuwan da ban sani ba. To shi yasa na ce maka haka. Ka ga sai ka yi min tambaya a wasu halittun wata kila kai ba ka sani ba, ni kuma na sani sai na ba ka haske kamar yadda ka yi a gaske. Zai yi magana ke nan 'yan ajin wajen su goma suka danno kai, sakamakon lokacin da ya kare don haka ya fasa maganarsa. Ya mike tsaye ya koma gaban allo a inda kujerar malamai ta ke, don dama shi ne da darasi da zarar an dawo. Ya yi zaune yana tunanin maganganun da suka yi da Shuhuda ya dinga auna su a mizanin da ya dace ya ajiye su, amma dai ya gaza gane inda suka fi cancanta ya dora maganganun nata. A haka dalibai suka dawo gaba daya ya ci gaba da gabatar musu da darasi. ******** ********* ******* Tun daga wannan rana Uncle Hamza bai kuma samun sararin tsayawa da Shuhuda ba kasancewar ana cikin lokacin karatu ka'in da na'in sakamakon jarrabawar da ke tunkarowa. Gaba daya ya tattara al'amarinta ya kyale idan ma ya shiga ajin ba ya bari ko kwayar idanunsa ta gani koda yaushe cikin bakin gilashi ya ke. A haka suka cinye wannan zangon karatun aka yi musu hutu. Wata ranar laraba Shuhuda na kicin danwake ta ke yi. Yau tunda ta shi ta ke mitar a yi dan waken. Ita kuma Inna yaduwa ta tace ba zata yi ba, idan tana bukata ta shiga kicin din ai ita ma mace ce.
Dariya Shuhuda ta yi ta nufi kicin tana cewa: Kin dai san zan iya girkawa ko? Shi ne ta shigo kicin tana hakilon yin danwaken.
Inna yaduwa na falo tana kallon yadda Shuhuda ta ke shige da fice daga kicin zuwa falo.
Ta gama danwaken ta zo falon ta zauna ta yanka tumatiri, Inna yaduwa ta kawar da kai gefe guda ta nuna kamar ba tasan da shigowar Shuhuda ba.
Ana haka ne wani yaro ya yi sallama Inna yaduwa ta amsa? Yaron yace:: Wai an ce Shuhuda ta zo ana kira a waje. Shuhuda ta dago kai da sauri ta dubi yaron, tare da cewa: Ni din ake kira a waje? Yaron ya daga mata kai alamun tabbatarwa.
Tace: Ka je kace nan gidan babu Shuhuda. Yaron ya juya zai fita Inna yaduwa ta tsayar da shi. Kai tsaya. Ta aikawa Shuhuda sakon harara. Don tsiya an aiko kiranki za ki ce babu Shuhuda a gidan nan?
Shuhuda ta juyo ga Inna yaduwa idanunta jajur tace: To ina Shuhudan? Ina ce ni sunana YAKUB?
Inna yaduwa ta sake kulewa, ta kaiwa Shuhuda bugu da hannu. Amma kafin hannun ya isa jikin Shuhuda sai ya sandare, Inna Yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu jini a tare da hannun. Shuhuda tace:
an fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun.
Bisa ga tsanani al'ajabi sai hannun ya koma Shafal, Inna yaduwa ta tsorata ainun ga wannan lamari, shi kuwa yaron dariya ya kama yi, don bai da isasshen wayo.
Shuhuda ta dubi yaron tace: Ka je ka cewa wanda ya aiko ka nan gidan babu Shuhuda. Yaron ya juya yana dariya, ita kam Inna yaduwa gaba daya tsurewa ya yi. An ya kuwa wannan yarinyar ba aljana bace?
Jikinta na 6ari ta mike ta nufi dakinta. Waya ta dauka domin kiran 'ya'yanta ta sanar da su abin da yake faruwa. Amma wani rudanin da ta lalubo lambar da zata kira, tana kira sai kawai wayar ta kashe kanta, kuma ga cikakken caji, amma kiran ya ki yiyuwa.
Ta yi jigum tana mamaki, wannan aikin jinnu ne, babu tababa Shuhuda aljana ce, idan ta yi la'akari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login