Showing 3001 words to 6000 words out of 81464 words

Chapter 2 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt

mata da bakin labari tana gudu kada ace ita ma Inna yaduwan ta zo mata da bakin labarin mutuwar mahaifanta ne(Ance idan maciji ya sare ka tsumma ka gani sai ka ruga.
Inna Yaduwa ta lura da halin da Haj karima ta shiga sai tayi murmushi tace; Kwantar da hankalin ki shawara ce zamuyi dake. Ta sauke gwauron nunfashi yayin da Inna yaduwa ta ci gaba da cewa.
Shuhuda yanzu ta samu shekara daya sai dai duk wanda zai ganta zai dauka ta wuce haka saboda girman jikinta ga wayo tana da shi. To sai nake ganin me zai hana wata uku masu zuwa a cire ta daga nono tunda dama ba damuwa tayi da shi sosai ba??
Shiru Haj karima ta yi bata tanka ba saboda alkunya da yakana irin ta mutan da. Sai gwaggo Zuwai ce tayi magana; ............................................................
................. Nima nayi wannan tunanin tunda a yini bai fi tasha nono sau biyu ko sau uku ba musamman ma yadda zawarawa suka fito suna son aurenta sai na ga cire Shuhudan a nono tayi aure zai fi da cewa. Inna Yaduwa tace Sannan kuma mai zai hana Ahmad ya maye gurbin marigayi , tun da shima ya nuna yana bukata? Da sauri Haj karima ta mike tsaye tare da zaro ido waje sai dai bata iya cewa komai ba sai girgiza kai da take yi tana ja da baya. Inna Yaduwa tace Kinga zauna idan bai kwanta miki ba babu dole dama shawara ce saboda shi dan uwan sagir ne zai iya zaunawa dake da yarki amma a wannan zamanin da wuya ne samun mijin da zai rike agola. Koda ya riketa ma sai kinga bambanci,don haka na yi miki sha'awar auren Ahmad to amma tunda bai kwanta miki ba , kada ki damu Allah Ubangiji ya za6a miki miji nagari. Idan lokacin yayen yayi zan zo na kar6e ta na yaye miki ita. Tana karashe fadar haka ta dubi Isah tace; Kai tashi Muje. Yace Kai Inna mun fa yi dake a nan zaki bar ni gurin 'yar uwata. Ta yi dariya Idan na barka makaranta fa? Yace; Ba sai direban ya zo nan ya dauke ni ba? Tace; kai ni taso mu ta fi, ka ta6a ganin maigida na gudun matarsa? Ba don yaso ba dole ya mike, Inna Yaduwa ta dubi Haj karima tace; Mu mun tafi. Jiki a sa6ule Haj karima tace; Shikenan Inna na gode Allah ya sauke ku lafiya. Inna Yaduwa ta amsa da 'Amin' sannan suka fice daga cikin gidan. Bayan tafiyarsu Goggo Zuwai ta dubi Haj Karima tace: Ke kuwa 'yar nan meye aibun Alh Ahmad da kika razana don an yi miki sha'awar aurensa? Idon Haj karima ya kawo kwalla a idonta tace; Kin gane Goggo ba zan iya rayuwar Aure da Alh Ahmad ba, ba wai don baya da kyawawan halaye ba sai dai don idan na dube shi zan dinga tunawa da kaninsa kuma ma dai gaskiya ina jin kunya da tsoron matanshi. Goggo zuwai tace; Hakane to amma ai wanda ya rasu ya riga ya rasu, su kuma matanshi ai sun san akwai aure a tsakanin ku. Tsoron me zaki ji nasu? A kansu zaki zauna ko kuwa? Kowa zaman kansa zai yi don haka ina ganin shi ya dace ki aura. Girgiza kanta tayi tace: Bazan iya aurenshi ba gwaggo. Tace To idan baki aure shi ba wa zaki aura? Kin dai san dole ne ki yi aure ko? Sai tayi shiri ta rasa abinda zata ce Tana da zawarawa da yawa wadanda sun fito ne domin su aure ta, kuma duk wanda ta za6a tana da yakinin zai kyautata mata sai dai ba zai kai ya mijinta ba. Don haka babu wanda ya kwanta mata. To amma tunda an 6illo da wannan maganar dole ne ta yo wani abu akai ko don tsallake wannan suradin. Maganar Gwaggo zuwai ta katse mata tunani tace; '' Aure a musulunci sunna ne daga cikin sunnonin Manzon Allah Muhammad(S.A.W) dama sauran manzanni da suka gabace shi Allah (S.W.T) Yace; Hakika mun aiki manzanni gabanka kuma mun sanya matan aure garesu da zuriyya(Ra'ad:38). Manzon Allah (S.A.W) yace ' Aure sunnata ce duk wanda yayi kyama ga sunnata to baya tare dani. Allah (S.W.T) yace '' ku auri abinda yayi muku dadi daga mata(Nisa'i:3). Akwai samun nutsuwa da kwanciyar hankali a 6angaren mata da miji. Allah (SWT) Yace 'Daga cikin ayoyinsa ya halitta muku mataye daga kawunan ku don ku natsu zuwa garesu? Ya kuma sanya soyayya da jin kai tsakaninku tabbas a cikin wannan akwai abubuwan lura ga mutane masu tunani kawai.(Rum:21). Manzon Allah yace (S.A.W) yace; '' Muna cewa duk namijin da bai yi aure ba to miskini ne komai yake da dukiya. Haka matar da bata yi aure ba miskiniya ce komai take da wadata''. A 6angare daya kuma duk wanda ya yi aure toya sami rabin addininsa,haka kuma al'umma suna mutunta da kuma fifita mai aure bisa ga wanda ba ya da aure. Idan kika tattara duk wannan bayanan da nayi miki ya isa ki san girma da darajar aure ga al'umma don haka kada ki bari zuciyarki tayi rauni ga gujewa abinda ya wajaba a gareki. Ita ZUCIYA MUGUN NAMA ce ko da yaushe anaso bawa ya dinga neman tsari da sharrinta domin idan ta gyaru gangar jiki ya gyaru,idan ta 6aci gangar jii ma ta 6aci''. ( ALLAHUMMA YA MU SARRIFAL QULUB SABBIT QULUBANA ALA DA'A TIKA) { YA UBANGIJI MAI SARRAFA ZUKATA KA SANYA ZUCIYARMU AKAN DA'ARKA)
.
Tayi shiru daga bayanin data ke yi yayin da Haj Karima ta kai hannu ta share kwallan dake zubowa daga idonta muryarta a raunane tace;
Gwaggo zan yi aure ba zan ta6a gufunsa ba Inshaa Allah zan fitar da miji amma bazan iya auren Alh. Ahmad ba.
Gwaggo zuwai tace Eh hakan ma yayi domin ba zamu tursasa ki auren da bai kwanta miki a rai ba kece zaki zauna da shi don haka idan zuciyarki bata aminta da shi ba ba zaki samu kwanciyar hankali ba Allah Ubangiji ya za6a na gari.
Can kasan makoshi Haj karima ta amsa ''Amin''
***** ***** *****
An shirya ranar juma'a da safe Inna Yaduwa zata zi ta kar6i Shuhuda don yaye ta kamar yadda aka tsara tun farko cewa idan tayi shekara daya da wata uku za a yaye ta.
To tun ranar talata da aka yi maganar yarinyar tayaye kanta anyi-anyi ta kama nono amma taki sai dai tsotson hannun kawai take . Hankalin Haj Karima yayi matukar tashi ganin har yammaci yayi amma shuhuda taki tasha nono abincin ma dan kadan taci kuma babu kuka babu fitina sai ma bacci da take yawan yi.
To a ranar anyu katari Gwaggo zuwai bata nan taje gidan yarta data haihu don haka gidan Haj karima ce kadai. Ta rasa yadda zata yu ita bata ta6a yaye ba hasalima bata ta6a ganin yadda ake yinsa ba saboda mace ce mai matukar tausayi bata son ganin yaro yana kuka yanzu ita ma ta kama kuka.
Ganoin yadda shuhuda taki kama nono sai ta dinga tunani ko dama haka ake yayen kafin ranar tazo yaro ya daina shan nono? An gama sallar magrib Gwaggo zuwai ta dawo gidan Haj karima ta kora mata bayanin duk abin da ya faru. Dariya tayi tace; Ai sai ki gode Allah dama haka wasu suke idan suka ji za a yaye su to sai su yi fushi da shan nono wasu kuwa lokacin ma zaki ga sun tsananta shan nonon.
Saukinmu daya daurin nan ya huda mata jiki don haka idan Allah ya kaimu safiya lafiya sai a kaiwa surukar taki ita..
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤05¤¤
Haka kuwa aka yi gari na wayewa Gwaggo zuwai ta goye shuihuda a bayanta ta nufi gidan Inna Yaduwa da ita. Tun bayan tafiyarsu Haj karima shigewa daki tayi ta kama rusar kuka ta tabbata sai wani ikon Allah Shuhuda ta rayu a hannunta saboda ta lura da take-taken surukar tata so kawai take taga ta kar6e shuhudan tunda ai tana gidan mai rasuwar inna yaduwa ta kar6o Isah dan Alh Sada ya dawo hannunta tun daga yaye. Kwana biyu yarinya sai harkokinta take bata kuka sam! Sai dai tana da yawan bacci idan ta farka kuma shiru zaka ji tayi tamkar kurma,haka Isah zai zauna a kusa da ita yayi ta mata wasa. Idan yaje makaranta makaranta yayi mata siye-siyen kayan kwalam da ragowar kudin da ake bashi na tara(break). Shuhuda ta samu wata shida da yaye Allah ya fitowa Haj karimatu miji duk da ba wani kwanta mata arai yayi sosai ba,ta daure ta amince dashi saboda yadda mahaifanta da danginta suka dame ta da maganar aure dadin-dadawa kuma gashi Alh Ahmad na yawan zuwa gidan. Ita kuma ta gama karantarshi tsaf fuskace dai bata ba bashi ba shi yasa bai yi mata maganar ba. Alh Jamilu Ahmad Karare, dan asalin karamar hukuimar Batsari ne a wani kauye mai suna karare cikin jihar katsina Dan kasuwa ne sosai yana da mata biyu da yaya shidda maza da mata. Haj karima ta aminta da aurenn Alh Jamilu ne kawai don ba yadda zata yi ya fito ne 6angaren mahaifinta amma ba tursasata yayi ba, ya dai nuna mata idan ta auri Alh Jamilun zai ji dadi zai yi farin ciki yana da yakinin zata samu zaman lafiya a gidan aurenta. Duka-duka haduwarsu da komai bai fi wata daya ba aka daura aure sati daya zata tare. Ta shiga tunanin yadda za ayi ta kar6o shuhuda daga hannun Inna Yaduwa. Ranar Alh Jamilu yazo gurinta suna zaune a falo ta ke cewa dashi. Alh. Wata alfarma nake roko gurinka. Yana murmushi yace mata. Fada ai kin wuce haka a gurina. Tace Dama so nake na kar6o Shuhuda na riketa a gurina. Yayi jim na wani lokaci sannan yace; Babu komai ai da na kowa ne musamman ma rikon maraya lada ne da shi. Sai dai inda gizo yake sakar da ta nemi a bata shuhuda sam kin amincewa suka yi suka ce ba su yarda Shuhuda tayi zaman agolanci ba dole a hannun Inna Yaduwa zata zauna. Haj karima bata iya musu iya musu ba don haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta bar musu Shuhuda. Amma a yadda ta so, ta so ace ta rayu da Shuhuda a inuwa daya domin ta dinga debe mata kewar mijinta data rasa sai dai ba yadda zata yi ita mace ce mai kawaici da hakuri don haka a nan din ma dole hakurin ta sakawa ranta. A haka har ranar tarewa tazo aka shiryata aka mikata gidan mijinta can cikin jihar katsina cikin karamar hukumar Batsari a karare inda gidan Alh Jamilu yake. Tun durar yan rakiyar amarya da ita kanta amaryar suka soma cin karo da cin mutunci saboda matan Alh Jamilu irin matan nan ne na kauye wadanda suka dauki kishi da zafi ,amma kowaccensu baka raina haduwarta ba.don kana ganin uwargidan kaga barumayar asali ita ma ta tsakiyar barumayar ce farare tas dasu illa rashin iya zama da miji da kyautata masa kadai dake dawainiya dasu. Sai uwa-uba kazanta ga rashin iya girki mai dandano ba.
Tun daga yan rakiyar har ita Hajiya kariman ba wanda ya kula da cin kashin da kishiyoyin suke yi haka suka gama komai suka ba wa Haj karima hakuri akan ta jure duk abin da zata gani ga matan nan idan ta yi haka sai ta ga komai ba komai ba. Suka yi mata sallama aka kwashe su cikin motocin da aka kawo su aka koma da su. ***** ****** ****** BABI NA DAYA IDAN AJALI YAYI KIRA........ Shuhuda ta tashi da wata irin bahaguwar rayuwa. Idan tana tsotsar hannun ko abincin bata cika ci ba . Inna yaduwa tayi fadan har ta gaji amma ba abinda ya ragu. Wata irin shakuwa ce tsakanin Shuhuda da dan' uwanta Isah ya kasance komai zai yi yana tare da Shuhuda makaranta ce kadai idan zai tafi yake rabuwa da ita. Har Inna Yaduwa na tsokanarshi tana cewa: Ka gama wayon naka amma baka isa kayi min kishiya da wannan bagidajiyar mai tsotsan hannu ba. Sai dai yayi murmushi kawai wani lokaci kuma yace; Kece bagidajiya amma shuhuda ba bagidajiya bace. Shuhuda tana da shekaru shidda aka sakata a makarantar islamiyya yarinyar tana da kwalwa sosai sai dai matsalar dake damunta tsorsar hannun nan nata. Yan ajinsu su yi ta tsokanarta wai ta girma tana tsotsar hannu bata damuwa don bata yi wayon da zata fahimci me suke nufi da hakan ba. Jarabawarsu ta farko sai ga shi Shuhudan ce tayi na daya har kyautuka aka yi mata a makarantar. Inna Yaduwa ta sanyata a gaba tana cewa: ' Kinga Shuhuda da zaki daina tsotsar hannu da sai kin fi haka kokari saboda mata masu tsotsar hannu ba sa da kokai. Don haka ki daina tsotsar hannu kin ji?? Tayi Shiru kawai ba tare da ta ce komai ba kuma ba ta daina tsotsar hannun ba. Shuhuda tana da kwalwa da kaifin basira ba ta yadda za a yi a koya mata abu ba ta dauke shi a kanta ba. Alh Sada suna matukar kulawa da ita tare da dukiyarta da mahaifinta ya rasu ya bari duk wata kadara tasa tun daga nan gida Nigeria zuwa kasashen waje babu abin da ba a kiblatasu ba kuma an ci gaba da tafiyar da harkokin kasuwancin yadda aka saba tun can baya.
Yau ya kama ranar lahadi Shuhuda tana zaune ita da yayanta yana koya mata karatun Islamiyya a lokacin ba ta fi mintina sha biyar daga tashi a bacci ba. Inna Yaduwa na zaune gefensu tana kallonsu Ta gaza hakuri saboda yadda taga ana koyawa Shuhuda karatu amma ta zurmuka ya tsanta a baki sai tsotsa take yi.
Ta mike tsaye da sauri cike da 6acin rai ta karasa inda Shuhuda take ta sa hannu ta gwa6e yatsan da take tsotsa. Ke kam kin ji haushin kanki kullum a yi ta abu daya dake sai kace mai kwalwar tumaki to na ga kin kara tsotsar hannun a gidan nan.
Isah yace; Ke Shuhuda ki daina tsotsar hannu kin ji ko? Ta yi shiru hannunta na ajiye a kasa Inna Yaduwa ta koma ta zauna akan kujera tana bambamin fadanta. Ai kuwa tana zama Shuhuda ta maida yatsan a cikin baki tana tsotsa Inna Yaduwa ta sake harzuka tace; Wai ni uban me kike tsotsa a yatsan nan ne da ba zaki dai na ba?
Dai-dai lokacin Salmai mai haja ta yi sallama a cikin falon Sam Inna yaduwa ba ta tsinkayo muryarta ba saboda tana rigima da Shuhuda tana son cire mata yatsan daga baki ita kuma Shuhuda ta kiya sai kakaniya suke.
Salmai tace Haba Yaduwa ni da me ye haka? Inna yaduwa tace Bar ni da yar nan Salmai ta raina ni ne, kullum sai nayi fama da ita akan tsotsar hannu amma kamar mai kunnen kashi ta ki ta daina ta maidani mahaukaciya.
Salmai tace Ayyah! Ai laifinki ne idan yaro yana tsotsar yatsa aka yi-akayi da shi ya ki dainawa mai dungurugum ake yi masa sai a samu zaman lafiya.
Inna Yaduwa ta yamutsa fuska cikin rashin fahimta tace. Ban gane mai dungurugum ba? Salmai ta yi dariya dai-dai lokacin da ta ajiye jakar hajarta kasa tace.
Tsarga hannun ake a saka masa borkono gobe ko cewa aka yi ya tsotsi hannun ba zai fara ba. Inna Yaduwa ta ce Ai ni tausayi nake ji bana iya tsarga hannunta da tuni na yi maganin abun.Salmai tace aikuwa idan ba ayi maganin abun da wuri ba haka zata mike har girmanta... Ke har ma ta haihu tana tsotsar hannu ga 'ya'ya a gabanta suna kallo wannan kuwa kuwa ai ba karamin faduwa bane.
Inna Yaduwa ta jinjina kanta tace ; Lallai kam to ni yanzu ban san ya zan yi da wannan 'ya ba taurin kanta har mamaki yake bani ga ta 'yar karama yarinya amma idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tankwarata.
Ai haka dama wasu yaran suke akan tsotsar hannu ka rasa me suke tsotsa. Haka kawai yaro ya sanyawa kansa fitina ko abinci sai ki ga sai an yi da gaske yaro ke ci. To ni zan yi miki maganin abun dauko min dakakken barkono da sabuwar reza kiga ikon Allah.
Isah ya yi sauri yace: Don Allah Inna kada ku tsaga mata hannu wannan zalunci ne!......
Inna Yaduwa ta kai mishi bugu. Kai ni rufe min baki sai a bar yarinya ta yi ta tsotsar hannu?
Ta mike a zafafe ta dauko barkono da sabuwar reza ta kawo wa Salmai, amma ta kasa rike Shuhuda wai bata iya ganin tsarga hannun saboda tausayi.
Ita kuwa Salmai ta kama Shuhuda take ta kokarun kwacewa, amma ina aikin gama ya gama. Tuni Salmai ta tsarge mata yatsa.!!!!
Tashin hankali wanda ba a saka masa rana ai ko da tsarge yatsan sai RUWAN NONO fari kal ya dinga ambaliya maimakon JINI!!!!!
Yau mun shiga uku!
Yayin da Isah duk ya kidime ita kam wadda abin ya faru gare ta babu alamar tsoro ko razana a tare da ita sai ma daga yatsan tayi sama tana gyarawa nonon gurin zuba.
Inna Yaduwa tana ganin abin da ya faru ga Shuhuda ita ma kidimewa tayi ta matso gurin tana sallallami. Isah yace; Inna kin ga abin da ake gudu ya faru. Ta juyo da dubanta gare shi tare da cewa :
Yi sauri ka kira min mahaifinka a waya. Jikinsa na mazari ya kira lambar Alh Sada kara daya ya dauka yace: Ya dai Isamanu dan maryama? A figice Isah yace Abba kazi inji Inna za a kai Shuhuda asibiti
Alh Sada yace Me ya samu Shuhudab ne???
.
Isah yace Rauni ne a hannunta. Yace To gani nan zuwa. Inna Yaduwa ta dubi hannun Shuhuda har yanzu nonon ne yake tarara iya rudewa kam ta rude da wannan murdadden al'amari.
Ita kuwa Salmai tsuru-tsuru ta yi hankalinta a matukar tashe ta rasa yadda aka yi hakan ta faru ita dai a saninta jini ne a jikin kowanne dan Adan, to ya akayi ita Shuhuda aka samu akasin haka?
Gaba daya jikinta nono ko kuwa a yatsan nata kadai ne ke da nonon a maimakon jini? Idan a yatsan kadai ne ke da nonon shi ta ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login