Showing 39001 words to 42000 words out of 81464 words
Chapter 14 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt
sanni? Yace: Eh, ni ma abin da nake mamaki kenan, tace: wai bincikenta ne ta sanki, wata 'yar fara doguwa, irin matan Misran nan dai.
Shuhuda ta yi dariya, tace: Kai Yaya, su matan Misra har kala daban gare su? Yace: Sosai ma kuwa, domin kina ganinsu kin san su 'yan asalin kasar Misran ne.
Ta jinjina kai, tace: Ni kam zan so na ga wannan shuhuda mai bincike haka. Yace: Nima zan so hakan.......
Ya kawar da maganar da cewa: Jibi ne tafiyarmu katsina ko? Tace: Haka ne. Yace: Ya kamata ki shirya gobe dai mu yo tsaraba ko? Ta narke idanu cikin shagwa6a, tace: Kai Yah Isah ni fa bana son zuwa super market. Yace: Ko akwai dalili?
A'a, haka kawai bana sha'awar zuwa super market. Cewarta.
Yanzu ya kamata ki koyawa kanki sha'awar zuwa tunda ra'ayina ne. Shi ma ya fada yana kallonta. Sai tayi shiru ba ta ce komai ba. Yace: Yanzu ma ba don mun yi alkawari da Salman Alparis zamu hadu ba, ai da yau zamu je, amma yau da gobe duk kayan Allah ne.
Tace: Haka ne, bara na koma tunda fita zaka yi......
Ya katse ta, idn babu takura mu je ki raka ni mana? Tace: Anya? Akwai wani nazari da na ke yi. Yace: Shike nan, sai na dawo. Ai ba jimawa zan yi ba.
Tace: To Allah ya dawo da kai lafiya.
Ya amsa, Amin.
Yana kokarin shiga mota, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. A ranar da dare hira suka sha mai tarin yawa, da amfani ga Isah, domin a cikin hirar ne ya kara tabbatarwa kansa lallai ya yi sa'ar samun mata mai kaifin hankali da basira. Wadda ta san makamar rayuwa, ta kuma san yadda zata farantawa wanda ke tare da shi rai.
Saboda dik hirar ta su ta ta'allaka ne akan yanayin da ma'aurata suke kasancewa idan sun sami matsala. Ya dinga dangantawa da su. Misali: Ace ya aureta matsala ta shigo ta karin aure ba tare da ya sanar mata ba, sai ranar daurin auren ko kuma ana gobe daurin auren.
To idan irin wannan matsalar ta shigo ta ya ya zata magance ta?
Murmushi ta yi, tace: Yah Isah ai ita soyayya ta gaskiya wadda ta zamo jigon aure mutumtata ake yi, kuma a yi uzuri tsakanin juna, tare da kar6ar uzuri. Zata iya yiwuwa saboda tsananin kaunar da kake yi min ne yasa ka kasa sanar da ni zaka yi nin kishiya. Kasan a rayuwar aure nagartacciyar kauna da fahimtar juna ake nema, muddin aka samu haka to kuwa dole ne a samu uzuri.
Kuma duk macen da ka gani ko jin mijinta zai kara aure ta tayar da kayar baya, da tasa rayuwar auren na su ta samu tangarda. To ka tuhumi asalin tushen kafuwar tubalin auren. Mai yiwuwa ne dama can ba kaunar mijin ta ke ba, sha'awa ko burgewa ce ta sa ta aure shi. Ko kuma ta kasance daga cikin jinsin mata wadanda suka dauki KISHI dabi'a mai kyau a gare su.
Wannan dogon bayanin da ta yi masa ya sama masa nutsuwa da gamsuwar cewar, lallai ya yi dace da samun mace ta gari.
Inna yaduwada yake babbar mace ce, tuni ta fassara maganganun nasa, ta yi dariya tace: Isah kenan, ga dukkan alamu kana daga cikin mazan da ke sha'awar tara mata fiye da daya.....
Ya yi saurin katse ta da cewa: Ko daya Inna. Ai samun sahihiyar mace guda daya ya fi ka tara mata hudu da suke tayar maka da hankali. Ni kam a ra'ayina mace daya nake son aure, musamman don na samu zaman lafiya tsakanina da iyalina.
Inna yaduwa ta sake murmusawa tace: Sai aka ce maka idan mutum ya auri mace fiye da daya ba zai samu kwanciyar hankali ba?
Yace: A'a, amma ni dai ra'ayina mace daya ne, saboda nasan idan na auri biyu daya ta fi kayutata min, sai na nuna rashin adalci a tsakaninsu.
Shuhuda ta shiga cikin zancen tace: Ni kuwa a nawa ra'ayin ina son zama da kishiya, domin 'yar uwa ce, akawai matan da suke mantawa da girman amfanin zama da kishiya, suka dauki kishiya a marsayin abokiyar gabarsu.
Wasu sun iya KISHIN BIRNI su 6oye kishinsu a zahiri, sai dai karfar baka, ko kuma KISAN MUMMUKE, yayin da wasu kishin na su ke gaza 6oyuwa zaka ga ma wasu har buge-buge da yage-yage suke yi a junansu.
An sani dukkan mace an halicce ta da kishi, to amma babu mafi dacewa a yi kishin na nuna kyautatawa ga miji, a ririta shi, a mantar da shi damuwa ba wai a saka masa wata damuwar ba.
Tun da ta fara wannan bayanin ya ke kallonta, mamakin yadda tasan wannan mas'ala yake, a matsayinta na karamar yarinya wadda ba ta ta6a yin aure ba bare zama da kishiya, kuma ta rayu a gidan da babu kishiya.
Hakan ya tabbar masa ko wane mutum da irin NASIBINSA, ita kam ta samu nasibi mai kyau, sai fatan Allah ya sa ta dore da wannan halayya nata.
Inna yaduwa tace: Ke duk ya aka yi kika san haka?
Shuhuda ta yi dariya, tace: Haba Inna, kada ki ba ni kunya mana? A tunanina kinsan mace tana da sani game da lamuran kishi ko da kuwa ba ta shiga fagen ba, sai dai wata idan tana da raunin tunani ba zata gane hakan ba har sai ta shiga fagen. Ni kuwa na sani, kuma ina da ALAKAR da zan sani.
Inna yaduwa tace: Saboda kin zauna da kishiya ko? Shuhuda tace: Ko ban zauna da ita ba, zan iya sani, saboda ALAKAR na sanin.
Inna yaduwa tace: Lallai kam tunda ubanki yana da mata biyu(Alh Sada take nufi) dole ki sani. Sai duk suka yi shiru saboda girman maganar.
Inna yaduwa tace: Ja'iran kawai, ni ka tashi ka bamu wuri haka nan zamu kwanta.
Shuhuda dai ce, idan ba ka manta ba tun kafin ka je kasar masu jajayen kunne na sanar da kai ba zan ba ka aurenta ba.
Shuhuda ta yi tsagal tace: Haba dai! Ai ko ba ki ba shi aurena ba, ni sai na aurasa masa kaina.
Inna yaduwa ta daga hannu zata kaiwa shuhuda duka, sai ta tuna da abin da ya ta6a faruwa lokacin da ta yi yunkurin dukan nata, don haka ta yi saurin sauke hannunta, tana cewa:
Rufe min baki rasa kunya 6eran tanka. Isah yace: Yauwa amaryas, fada mata ta ji da kyau. An fada mata har yanzu kambun nata yana tasiri? Ya karashe maganar yana kokarin mikewa.
Inna yaduwa ta aika masa sakon harara, tace: Na ce ka wuce ina so mu kwanta. Yace: Ba sai kin kore ni ba, ni ma baccin nake ji. Ya soma tofa musu addu'o'i yace: Mu kwana lafiya. Bai jira amsarsu ba ya ficce.
A ranar bai yi mummunan mafarkinsa ba, tunda ya kwanta ko motsawa bai yi ba sai gabanin sallar asuba.
Lallai addu'a makami ce ga dan Adam, dubi dai kwanaki biyu matsalolin da ya samu akan rashin addu'a, amma yau da yake ya yi addu'ar sai ga shi da yin bacci cikin nishadi.
Koda ya gama sallar asuba dakinsu ya nufa, sai dai ya tarar da shuhuda zaune akan sallaya tana Azkar din safe, yayin da Inna yaduwa ta ke kujiba-kujibar dama koko, don ita Allah ya yi ta ba mai ganda ba ce, don haka ma ko 'yar aiki ta ki aminta a ajiye mata.
Zaunawa yayi a gefen gadon ya na jiran ta kammala lazimin su gaisa, amma har tsayin lokaci ba ta dakata ba, shi kuma yana son ta datse su gaisa ya koma daki don yin sababben baccinsa, hakan ta gaza samuwa.
Da ya ga ba ta da niyyar tsayar da lazimin nata su gaisa, sai ya mike tsaye ya fice daga dakin.
Yana fitowa falo suka yi kici6us da Inna yaduwa ta fito daga kicin. Ya rusunar da kai yana kokarin shigewa sashensa, Inna yaduwa ta ambaci sunansa, ya juyo yana kallonta. Ita kuma ta zauna akan kujera fuskarta a dan daure.
Ganin ta zauna ya tabbatar magana ta ke son yi da shi, sai ya dawo falon ya zauna ya yi shiru yana sauraren abin da zata fada.
Ta sauke gwauron numfashi, sannan ta dora da cewa: Isah magana zamu yi da kai ta fahimta, kuma shawara da gargadi ne a gare ka. Ka ga wannan yarinyar shuhuda da kake gani ko, bana son abin da zai ta6a ranta ko sakata a damuwa.
Abin da yasa ka ji na fadi wannan maganar wani abu ne yake yi min ciwo a rai, na rasa wanda zan kama na sanar da shi abin.
Yanayinta ya sauya gaba daya, ta koma kalar tausayi, hakan ya sa shi ma Isah yanayinsa ya sauya, ya dai kasa kunnuwa yana saurarenta.
Zata ci gaba da magana ke nan, shuhuda ta shigo falon, Inna yaduwa ra dago kai suka hada idanu, sai ta ga kamar launin idanuwanta sun sauya daga fari da baki zuwa wata WALKIYA, don haka da sauri ta rusunar da kwayar idanunta kasa.
Isah kuwa da ya dago bai ga komai ba, illa ya ga shuhuda tsaye a bakin kofa sanye da hijabin sallarta. Shuhuda tace:
Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi idan ina azkar ba na son tsinkewa saboda idan na koma ba zan iya yin adadin da nake yi a kowacce rana ba.
Yana murmushi yace mata. Kada ki damu. Tana kokarin zama, tace: Hala wannan tsohuwar ta zaunar da kai zata yi maka shirme ko?. Babu wanda ya tanka mata. Bayan ta zauna tace: Yaya barka da kwana. Yace: Min tashi lafiya?.
Tace: Kalau, don na fi wannan tsohuwar, tunda na lura yau tunda ta tashi a suku-suku ta ke, ko kuwa neman rigima ta ke? Ba shakka don mun ce ba zamu je katsina da ita ba ne ta ke neman ayi rigima da ita.
Inna yaduwa ta yi murmushin karfin hali, tace: Sha kuruminki idan dai ni ce ko da kunce ba zaku je da ni ba, ba zan damu ba. Shuhuda tace: Ke dai ki ce kin yi abin nan da Hausawa sukan ce, Wai abin da baka samu gama shi da baka so, ko kuwa yaya? Ya girgiza kai yace: Kwarai kuwa.
Inna yaduwa ta mike tsaye, tace: Isah bai so tashin Inna yaduwa ba, ya so ta sanar da shi abin da yake damunta har ya ji tausayin 'yar tsohuwar ya kama shi. Wata kila ba ta jin dadin zama da shuhuda.
shi kam a yadda yake ganin shuhuda ba ya tunanin tana da wani mugun hali da wanda yake zaune da ita zai koka. Domin ta kasance kamilar budurwa, da ace irin 'yan matan yanzu ne yadda ta ke zaune da kakarta, da kullum sai ta sakata kuka, amma sam shuhuda ba ta da wannan hali, ba ta son ma yin irin wannan haramtaccen wasan na JIKA da KAK , don da yawa wasu wasanni da ake yi jika da kaka ya haramta. Wasa na rashin ganin girma da nuna kuruciya a zahiran.
Bayan tafiyar Inna yaduwa shuhuda ta dubi Isah tace: Yauwa Yah Isah, wai kana da Umdatul Ahkam? Yace: Me zaki yi da shi? Tace: Karatu. Yace: A'a ba ni da shi, amma anjima idan mun fita siyayyar tsaraba sai mu nemo ko?
Tace: Allah ya kaimu. Yace: Amin, amma kafin nan bari idan na shiga daki zan fito miki da wani littafin addini, don na lura kina son karance-karance.
Tace: Sosai ma kuwa, don littafan da na karanta na addini suna da yawa, ka ga kamar littafin Fikhul Wadii na ji dadinsa sosai, yadda aka yi bayani game da yadda al'adar mata ta ke zuwa, da kuma yadda take daukewa, har ma idan ta zowa mutum da matsala.
Kasan mafi akasarin mata ba su san jinin haila ba, ba su san rabe-rabensa ba, da kuma yadda idan sun dauki lokaci ba su yi ba, ba su san me ya haddasa hakan ba, su ba ruwansu kawai sun san cewa, idan wata ya zo karshe suna fitar da jini, babu maganar akwai matsala ko akasin ta idan ba gani sukayi sun kwanta ba......
Isah ya katse ta da cewa: Me ye matsalar matan? Sai ta yi murmushi tace: Au, na fa manta kai namiji ne ko?. Ta mike tsaye cike da jin kunya ta koma daki. Bai yi yunkurin tsayar da ita ba, ya yi mata uzuri, sai ya tashi ya koma dakinsa, don dama bacci ne ke cinsa.
Da yammacin ranar suka je Sahad store da Alh. Shehu super market suka yo siyayyar abubuwan da zasu yi tsaraba da shi, sannan suka wuce kasuwar kurmi shuhuda ta za6o littafan addini, daga bisani suka dawo Gida.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤20¤¤
Duk yadda ya so kadaicewa da Inna yaduwa don jin damuwarta hakan bai yiyuwa ba, saboda duk lokacin da ya shigo falon sai ya tarar da ita tare da shuhuda.
Washegari ma tun da safe ya nufo falon bai ga Inna yaduwa ba, ya leka kicin wai ko ya tarar da ita kamar yadda tayi jiya, amma sai ya tarar da shuhuda.
Bai wani jata da labari ba, saboda yana ganin dama ce ta samu, kawai ya je daki ya tarar da Inna yaduwa ya ji matsalarta tunda shuhuda na kicin.
Yana zuwa dakin ya tarar da ita kwance akan gado, idanunta a lumshe, yace: Matar bacci kike? Sai ta bude ido ta kalle shi tace: A'a jikina ne yake ciwo. Yace: Ayya, Allah kawo sauki. Tace: Amin, ai da saukin, kawai surutu ne ban so, ga shi ina so na dama koko.
Yace; Ai ga shuhuda can na yi. Sai suka yi shiru na wani lokaci, kafin daga bisani ya katse shirun da cewa: Jiya muna magana ba mu karasa ba shuhuda ta shigo?. Tace: Eh wallahi, ga shi kuma na manta abin da nake son sanar da kai. Ya dube ta cikin tuhuma, sai ta jinjina kai alamun tabbatarwa. Sannan tacce: Karfe nawa zaku tafi katsinan? Yace: Sai sha daya. Tace: Allah ya kaimu. Ya amsa da, Amin.
BABI NA TARA
RUDANI
Babu mai magana a cikin su biyun, tafiya kawai suke tamkar kurame, kowanne da abin da yake sakawa a cikin ransa. Ga karar kira'ar Sheik Ahamad Sudeis na tashi cikin tausasshiyar muryarsa, SURATUL MUHAMMAD ce ke tashi, wadda ta ke magana akan Manzon Rahama, Manzon tsira, Manzon da babu kamarsa duk cikin Manzanni. Dan Amina baban fadima, Angon nana khadija da nana A'isha, suruki ga sayyidina Aliyu(A.S) kaka ga Hassan da Hussain, wato Annabin Annabawa, amintaccen Allah, Yardajjen Allah, Annabi Muhammad(S.A.W).
Surah ce wadda ta ke da muhimmanci akan kowanne musulmi yasanta, duk da cewa babu surar da ba ta da muhimmanci ga kowanne musulmi ya sani a cikin littafi mai tsarki(Alkur'arni mai girma).
Littafin da ya shafe kowanne littafi, tun daga kan Injila, Attaura, gami da zabura. Domin littafin alkur'ani ya tattaro dukkan bayani kama daga kan asalin halittar dan Adam, abin da ke da akwai a aljanna da wuta. Bayani na kissoshiin Annabawa, bayani akan ranar tashin alkiyama da yadda aka halicci duniya da lahira, gami da abubuwan da Allah ya yi rantsuwa da su.
Lallai Allah(S.W.A) gwanin HIKIMA ne, Arrahim ke nan mai saukar da rahma, Arrahim(mai jinkan bayinsa). Arrazzaku(mai azurta bayinsa), Alfahatu(mai budawa bawa kofofin budi).
" An kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar, manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta suratul GASHIYA, to Allah zai yi masa hisabi mai sauki. Kuma wanda ya karantata akan rumbun abincinsa to ya aminta daga cutarwarsa.
Haka kuma an kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar; Manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta suratul BALAD har zuwa karshen surar, to Allah zai amintar da shi daga fushinsa ranar alakiyama.
Manzon Allah(S.AW) yace: Wanda ya karanta suratul LAIL, to Allah zai tseratar da shi daga duhu guda biyu, duhun zunubi da kuma duhun kabari. Wanda ya lazimci karanta suratul Lail sau dari har tsawon kwana arba'in tare da yin azumi da Riyadh(wato nisantar sa6o) to Allah zai yi masa khasafi(wato zai samar da shi 6oyayyun ilmi).
Wata rana Annabi(S.AW) ya cewa sahabbansa, shin ko kuna son Allah ya yi muku katanga daga shaidan kamar yadda ya katange Yajuju da Majuju? Sai suka ce: Eh, Sai yace: To ku karanta suratul QADR bayan sallar magriba, da bayan sallar asuba sau uku-uku kafin ku tashi daga wajen da kuka yi sallar. Sannan sai kace: " Ya Allahu, Ya sahibul kadri farraji auni hammi wakarbii"(ma'an
a:- Ya Allah, Ya mai iko, ka yaye min bakin ciki da 6acin rai).
Wannan duk daga cikin falalar alkur'ani ne, don haka alkur'ani rahma ne ga dukkan musulmi, karanta shi na saka nishadi, sauraren kira'arsa na gusar da bakin ciki.
Har suka isa birnin katsina babu wanda ya yi magana daga cikinsu.
Sai da suka zo Welcome to katsina(sabon garin Dandagoro) a sannan ne Isah ya dago kai ya dubi shuhuda tare da rage sautin karatun alkur'anin da ke tashi, yace:
Zamu biya NNPC mu sha mai, don na ga man ba zai ishe mu zuwa karare ba. Tace: To. Yaci gaba da sulalawa da motarsa har ya shiga gidan man, ya jera layi a bayan motoci hudu da suke gabanshi.
Shuhuda ta yi wata irin zabura tare da cewa: Subhanallah!! Da sauri Isah ya dago kai ya dube ta, kokarin fita take daga cikin motar, ya riko gefen hijabin da ke jikinta, yace: Me ya faru? Ina zaki??
Fuskarta cike da fara'a da kuma doki, tace: Wata kawata ce na gani, ga ta can, fita zata yi daga gidan man. Ta karashe maganar tana nuna masa budurwar da ke kokarin shiga motarta kirar hummer jeep da aka gama zubawa mai.
Kafin ya yi magana tuni har ta fita, ta karasa inda ta ke tana cewa. Shuhuda dama kina raye? Wadda aka kira da suna shuhuda ta juyo cike da farin ciki suka rungume juna suna masu murnar haduwa.
Isah da yake cikin mota yana hango su, ya ga kamar ya ta6a ganin fuskar.
Da farko da zai share, amma zargin da ya ke na kamar wata FUSKA da ya ta6a haduwa da ita watanni hudu da suka shude a birnin MISRA ya sa ya gaza hakuri, ya yi fit! Ya bude mota ya tunkare su.
Yana isa ya soma nuna bakuwar fuskar da dan yatsansa yana cewa: SHUHUDA IBN KHADDAB? Ta dube shi cikin yanayin tuhuma gami da mamaki. Ita kanta shuhuda mamakin ne bayyane a fuskarta, tace: Yaya ina kasan Shuhuda?
Bai amsa mata tambayarta ba, yace da dayar shuhudan.
Yaushe kika zi Najeriya? Ko kuwa dama dai maganata ce ta zama gaskiya ke