Showing 6001 words to 9000 words out of 81464 words
Chapter 3 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt
tsotsa maimakon kiwo(feeding) nata? Wannan wani bakon al'amari ne mai rudani da daure kai. Su dukkansu aka rasa mai abin cewa kowa yayi shiru da abin da yake sakawa a cikin ransa.
Ba a fi mintina goma sha uku ba Alh Sada ya dura a gidan Ko da ganin abin da yake faruwa hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba ya dubi Inna Yaduwa yace; Inna ta ya aka yi haka ta faru.
Inna Yaduwa tace To tsautsayi ne da ba ya wuce ranarsa Ba musan hikimar tsotsar hannun da Shuhuda take ba na sa aka tsarga hannun ashe nono ne take sha a jikin yatsan?
Alh sada ya jimanta lamarin sannan yace; To shikenan Allah ya kyauta gaba ku taso muje clinic a dinke mata yatsan. Inna Yaduwa Isah gami da Shuhuda suka mike tsaye yayin da salmai take zaune a guri guda ta yi tsuru-tsuru da ita sai kace kazar da aka tsamo a cikin ruwa.
Kai tsaye suka nufi kofar fita sai a sannan Salmai ta samu damar matsawa ita ma tabi bayansu suna fita mota suka shiga ita kuwa Salmai ficewa tayi daga gidan da jakar kayanta tana tafiya sukuku kamar mai tsoron taka kasa.
FABCY CLINIC suka je Dr Ya'u ya jagorancui dinke yatsan /huhuda wanda har suka iso asibitin bai dai na ambaliyar da ruwan nono ba.
Abin mamaki duk inda aka sa allura don dinkewa a jikin yatsan sai gurin ya 6ule nono yayi ta tarara. Shi kanshi Dr Ya'u ba karamin firgici ya shiga ba da ganin yadda lamarin ke gudana.
.
.
Toh pa, ni ma se da na rude har waya ta ta pada ruwan jikin shuhuda...
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤06¤¤
Da ya ga haka sai ya dauko wani garin allura ya zuba a cikin raunin ya kawo bandeji ya lika mata sannan yayi mata allura. Yana cire tsinken allurar daga jikin Shuhuda zance ya sake shan bam-bam domin tsinken allurar ya karye a jikinta.
Da sauri aka shiga theater room da ita aka samu da kyar aka tsinke allurar daga jikinta koda yake ita dakanta ta cire. Daidai lokacin ruwan nonon ya daina tarara sai wani irin nannauyan bacci ya sure ta.
Dr Ya'u ya fito daga dakin tiyatar ya dubi Alh sada yace Alhaji dole sai ta kwana saboda gaskiya yanayin jikin yana bukatar kyakkyawar kulawa.
Kaga bayan an samu an yi mata tiyata an cire tsinken allurar sai wani zazzafan zazza6i ya rufe ta. Yanzu dai ta samu bacci don haka ku yi hakuri ta kwana zuwa washegari sai a sallame ta idan komai ya dai-daita.
Alh Sada ya sauke gauron numfashi cikin matukar jimami yace: 8abu komai Allah ya kaimu goben lafiya ya kuma bata sauki.
Gaba daya suka amsa da ameen. Alh sada ya dubi Inna yaduwa yace Bari naje na kawo miki abubuwan da zaki bukata na amfani. A'ah bara mu je tare ai bacci take har maje mui dawo.
Yace To. Suka shiga dakin da shuhuda take tana kwance tana ta sharar baccinta don haka suka fito su duka ukun suka nufi gida. Sun isa gidan Inna yaduwa ta shiga ciki ke nan wani yaro ya shigo yace; Inna wai ance a fada maki SALMAI MAI HAJA ta RASU. Inna yaduwa ta zabura tare da doka sallallami ido waje tace Salman ce ta rasu? Yanzu fa muka rabu da ita? Yaron yace Eh mota ce ta kade ta take wuyanta ya KARYE, Yanzu ma za arufo ta.
Inna yaduwa ta sake jan sallallami ta dure tace; IDAN AJALI YA YI KIRA koba ciwo sai an tafi. Yanzun nan fa tabar gidan nan? Ta karashe magana tana nuna matukar alhininta. Yaron dai ya yi shiru yana sauraren ta.
Alh sada ya shigo cikin gidan ganin ta jima bata fito ba. Ya tarar da ita cikin halin jimami yace; Inna ya baku fito ba? Kada fa ta farka babu kowa a kusa da ita.
Tace.
Tace Mhm kai dai bari wai Salmai ce ta rasu!! Yace wace Salmai? Tace salmai mai haja mana yanzun nan fa ta bar gidan nan bayan ta tsaga hannun Shuhuda wai mota ta kade ta.
Ya ce Allah sarki kila tsabar rudewa ce ta sa ko gabanta ba ta gani har hakan ta faru. Allah dai ya jikanta ya rahamsheta. Tace Amin jiki ba kuzari ta hada kayan da zata hada suka nufi asibitin. Har lokacin Shuhuda bata farka ba bacci kawai take yi.
Alh sada ya yiwa Inna yaduwa sallama ya tafi tare da Isah suka barta a nan. Sai a washegari ne misalin shida da rabi na safe shuhuda ta farka. Karfe takwas yan uwa da mutanen arziki aka yi ta zuwa ganinta da yi mata sannu da jiki. Misalin sha biyu na rana aka sallame su suka dunguma gida.
******** ********* ******
Zaman gidan Alh jamilu dai babu dadi domin sam karima ba ta da sukuni matansa ba sa sonra sun tsane ta musamman yadda suka ga yana riritata yana kulawa da ita.
A ganinsu ya bam-banta su shi kuwa duk abin da yake yiwa karima ya na yi ne don mantar da ita alhinin rashin tsohon mijinta saboda a zahirin gaskiya karima ta yi rashi babba wanda take bukatar samun wanda zai maye mata gurbinsa.
Alh jamilu adalin namiji ne kuma jarumi gwarzo yasan duk wani salo na soyayya don haka ya yi amfani da wannan damar ya mantar da karima bakin cikin da matansa ke kunsa mata.
Koda yake a wani 6angaren ba ya da masaniyar irin zaman doya da manjan da ake yi a cikin gidan nasa. Saboda ya kasance mutum ba mazauni ba dan kasuwa ne da ke kewaya kasashen duniya.
Ta 6angarenshi kam karima bata da matsalar komai domin ta samu nagartacciyar kulawa daga gare shi matsalarta ga matansa take su ma yayan nasu basu kyalle ba ne domin sam yaran basu da yarbiyyar to su ma ba ta ishe su ba bare su baiwa wasu.
Rashin kunya kamar sa doke ta duj ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga yi mata korafi kenan.
Rashin kunya kamar sa doketa duk ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga korafi kenan wai tana rage kudin cefane. Bayan komai akwai shi a cikin gidan tsakanin mai gidan da matan alheri ne ba ya baiwa mace kudin cefane amma don rashin adalci sai suke cewa tana rage kudin cefane.
Wannan dalilin ya sa karima ba ta zama a falo koda yaushe tana cikin dakinta.
Idan ka ganta a waje to kicin ko bandaki zata shiga kasancewar bandaki daya ne a tsakar gida wanda kowa yake amfani dashi sai kuma na shi mai gidan shi kuma idan ba mace ke da girki ba ba ta da damar shiga.
Duk cikin yaran babu wanda yake kulata da maganar arziki ko gaishe da ita ba sayi to bata damu da hakan ba domin ba zamansu take yi ba. Zaman aure take shi kam zaman aure dan hakuri ne dama da mijin ta ke samun matsala wannan da da ciwo. Duk da wannan din ma da ciwo saboda zaman tare wani babban al'amari ne mai girma yana bukatar shakuwa da juna kyautatawa juna gami da taimakekeniya. To su lamarin matan Alh jamilu ba haka bane irin wannan banzan kishin ne suke na kauyanci kai yanzu ko a kauye a daina irin wannan kishin na hauka. Sam babu ragayya ba ta da ikon ta kwanta ta huta muddin aka ce ranar girkin ta ne. Habaici ko da yada bakaken maganganu abin ba a cewa komai har ma ta saba. Karima na kicin tana dafuwar miya ta gama kwashe tuwo miyar ce take son kadawa. Binta uwargidan Alh jamilu ta shigo kicin din tana bangaje karima ta dauko roba. Karima ta ja da baya sam batayi mamaki ba idan da sabo ta saba da irin wannan cin kashin da ake yi mata a gidan. Sai dai a ganinta izuwa yanzu yaci ace sun tsaya sun gina rayuwa mai kyau a tsakaninsu wannan zafin kishin babu inda zai kai su illa halaka. To amma ba yadda za a yi matan ne gasu nan dai kurum. Binta har ta kai kofa zata fita sai ta juyo tace; Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya gana birni, Mace ba kyau ba ba siga ba amma sai shegen kilibibi da karfar baka to ni dai wallahi karyar duk wata juya bata isa ta fitar da ni a gidan mijina ba kowacce shegiya nan tazo ta tarar da ni don haka idan ban fidda mace ba ta yi kadan ta fidda ni.
Karima tace Me ya kawo wannan maganar kuma? Binta tace Ban sani ba sai na ji makara don na lura kwanan nan wani karfi karfi kike ji idan kina magana tamkar zaki daki mutum. To idan kin isa kina ganin kanki ke wata abace ki kwa6e mu daku, kiga idan akwai kutumar da zaki diba a jikina. Karima ta girgiza kanta tace Ni kam bazan iya fada da ke ba ba ma ke ba ni a rayuwata ba na fada kowa kika ganni da shi burina na zauna da shi lafiya. Binta ta daka mata tsawa tace Rufe min baki bakar munafuka baki fada da kowa amma kin iya karfar baka ko? Kin iya ki kalallame miji ki raba shi da matansa ki raba shi da 'yayansa? To wallahi kin ji na rantse miki kin yi kadan kin yi tsururu a gidan nan muddin kika ce wannan mummunar dabi'ar zaki tsuro a gidan nan. Karima tace: Allah ya baki hakuri? Wannan kalami ya sake tunzura Binta tace Kin sa Alhaji ya bugi Mas'ud to idan dai ni na haifi Mas'ud har aban abada ba zai ta6a gayar da ke ba. Duk wani ahali nawa ba zai ta6a yin wata mu amala da ke ba, idan kina so ki burge ni kisa Alhaji ya sa wuka ya yanke kawunan duk wani ahali nawa akan ba sa gaishe ki sannan zan tabbatar da sunanki karima matar so. Ta ja wani dogon tsaki tace Shi kuma Alhajin yayi na farko ya yi na karshe don bashi ya sha min wahalar daukar cikin ba bare ya kama min 'yaya da duka akan wata banzar bazara ruwan kaka, juya wadda tun da ta shigo gidannan komai ya ta6ar6are. Tana karashe maganar ta sa kai ta fice daga kicin din ta bar karima nan tsaye sororo cike da takaici don halayen Binta ba su ba ta mamaki, sai dai tsoro. Ta tabbatar da ace za a bata umarni ta kashe ta ko jinkiri Binta ba zata yi ba zata iya kashe ta saboda wannan zafin kishin nata yayi yawa. Cikin rashin sukuni ta kammala miyar ta dawo daki da nufin ta huta kafin a dawo daga sallar azahar ta zubawa kowa nashi. Tana nan zaune ta jiyo sallama a falonta ta shaida muryar dattijuwa ce mai YAKANAH wadda ta nuna mata halacci ta sota a lokacin da take tare da ita wato Inna Yaduwa. Ai kuwa da sauri ta fito falon ta na lale marhabun da zuwanta. Bayan Inna yaduwa Shuhuda da Isah sun zauna Karima ta je ta zubo musu tuwon shinkafa miyar agushi ta kawo musu gami da ruwan sanyi. Ta zauna suna cin abincin suna gaisawa har suka kammala Inna yaduwa tace: Karimatu ki yi hakuri don Allah da jinkirin da aka samu na kawo miki Shuhuda tsayin watanni tara. Kinsan lamarin zaman gidan wani wuya gare shi musamman ma yadda na lura halayen abokanan zamanki ba ya da kyau. Karima tacr Lah! Wallahi Inna ba komai ai ana kawota don wannan karon an samu jinkiri sai ya zama wani abu? Wallahi ba komai. Shuhuda ta mike tsaye Inna yaduwa tace Ina zaki? Tace Fitsari zan yo? Ta fita Inna yaduwa ta dawo da dubanta ga karima ta ce; Ga fa danki kin san dul cikin satin nan ba zancen da yake sai naki yau dai ya takura sai na zo. Karima ta yi murmushi tace Isah ke nan? Ai shi kam da Mamansa sai Allah. Inna yaduwa ta dan saka nutsuwa tace. A nan zamu bar Shuhuda za ta yi miki sati biyu saboda mako mai kamawa zata soma zuwa Makarantar boko kuma kin san yaro idan ya na karatu baya da wani sukuni bare ga kuma Islamiyya.
Karima taji dadi har cikin ranta da jin wannan batu saboda a yau zata kwana da gudan jininta 'ya daya tilo ta mallaka a duniya. Wadda in baci ita da sai ta aminta da maganar su Binta ke fada akanta cewar ita din juya ce to amma kasancewar ta san ta ta6a haihuwa sai zancen na su bai dauke ta ya nana da kasa ba. Ta san cewa tsawon shekaru biyar data shafe a gidan Alh jamilu Allah ne bai hukunto haihuwar da shi ba idan lokaci yayi zata haifa din. Kukan Shuhuda da suka jiyo ne a tsakar gida ya sa gaba daya suka mike tsaye a zabure suka nufo tsakar gidan. Mas'ud yaro dan shekaru sha tara suka hango ya kama Shuhuda yana jibga kamar wata tsaran shi. Sai dai suka ja tunga suka tsaya, Inna yaduwa ta dubi karima cike da tsananin mamaki ita karimar Inna yaduwan take kallo. Isah kam tuni ya kaiwa 'yar uwarshi dauki ya cakumi wuyan rigarshi ya yi wurgi da shi tare da kai mishi wani irin wawan naushi. Rigima ta raku6e tsakaninsu Shuhuda kuwa tana kwance. Karima ta yi saurin shiga tsakanin su ta raba su amma Mas'ud ya tattakura ya kaima ta naushi a gefen cikinta ba arziki kuwa ta ja baya. Inna yaduwa ita ta raba fadan yayin da Binta ta fito daga dakinta dama duk abinda yake faruwa akan idonta ne abinda yasa tun dazun ba ta fito ba tasan Mas'ud yana da taurin rai mawuyaci ne ayi fada da shi bai samu galaba ba amma yau sai ga shi zance ya sha bam-bam. Duk girman jiki irin na Mas'ud amma Isah ya fi shi zafin nama da karfi domoin ba don Inna yaduwa ta raba fadan ba wata kila sai dai a dauki Mas'udin ranga-ranga. Binta na fitowa daga dakinta ta balbale Inna yaduwa da masifa har tana kiranta tsohuwar akwala wai tana shiga fadan yara. Inna yaduwa ta rike ha6a kawai tana karewa Binta kallo mamaki take yi 'yar da ta haife ta a cikinta amma ita ce take yi mata wadannan munanan furucin. Binta jin ba wanda ya tanka mata sai ta kama hannun Mas'ud tace: Mu je ciki Alhajin ya dawo Ni na gaji da wannan masifa mata kin zame min ciwon ido mai wuyar magani a gida? To wallahi ba zata sa6u ba bindiga a ruwa yau alo tsiya alo danja sai an san mai yiwyuwa. Inna yaduwa suka karasa inda Shuhuda take kwance duk ya farfasa mata jiki, amma a madadin a ga JINI a gurin da ya farfasa mata sai suka ga RUWAN NONO fari kal yana zuba. Wannan lamari ya hargitsa tunanin karima don bata da masaniyar wancan al'amari da ya ta6a faruwa. To ita kanta Inna Yaduwan da Isah abin ya kara hautsina masu kwanya shin ita Shuhuda wacce irin halitta ce da gaba daya jikinta babu jini sai Ruwan nono? Dama akwai mutumin da jikinsa yake dauke da ruwan nono sa6anin jini kuma yana rayuwa? Amsar data yi musu wuya kenan suka taitaye ta zuwa daki. Kwallah ne kawai ke zuba a idon karima yayin da Inna yaduwa tace. Karima shin dama baki zaman lafiya da matan gidan nan ne? Sam ta kasa magana zubar hawaye kawai take. Inna yaduwa ta jinjina kai tace; To Allah ya sauwake tunda abin haka ne bazamu bar shuhuda a gidan nan ba.
ada Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤07¤¤
Karima ta girgiza kai da sauri amma ba ta iya cewa komai ba Inna yaduwa tace; A'a ba za mu barta ba ba zan so sanadinta ki sake samun rashin jituwa tsakiniki da abokan zamanki ba har yayi sanadin mutuwar aurenki. Idan dai an kwana biyu za a dinga kawota ta yinar miki a koma da ita amma don Allah kici gaba da halinki na hakuri, shi dama zaman aure gaba dayansa hakuri ne jigonsa, da zarar aka ce babu hakuri to babu zaman aure. Ba yadda yi haka ta hakura sai dai abin na damunta a rai ganin ruwan nonon da ya zuba a raunikan Shuhuda amma ta yi alkunya ba ta tanka ba saboda kasancewa Shuhuda 'yar fari ce. Ita din ma Inna yaduwa ba ta maida kai kan al'amarin ba ta sa ruwa ta wanke wa Shuhuda raunukan. Da yammaci su kayi bankwana suka ta fi cike da alhinin abinda ya faru. Bayan sallar magruba Alh Jamilu ya dawo gida a gajiye saboda aiki da yayi masa yawa. Kai tsaye bandaki ya shiga yayi wanka. Yana fitowa ya tarar da Binta zaune akan kujera sai huci take tamkar kububuwa. Yana ganin yanayin ta ya san korafi ne ya kawota dakin don haka ya gumtse fuskarsa ya zauna gefen gado yana murza mai a jikinsa. Binta ta kara kulewa ganin yadda ya banzantar da ita cikin 6acin rai tace: Gaskiya Alhaji na gaji wannan matar ko 'yar gwal ce sai haka bare kuma ba abinda ta fi wani cikin gidan nan. Ya dago kai ya dube ta. Mai kuma ya faru? Cikin isa-isa tace; Kawai ta gayyato gayyar danginta sunzo sun kama Mas'ud da duka ba don na fito ba kila da kashe shi za su yi. Domin na lura wannan tsohuwar kwararon so tayi ta shake masa wuya ya mutu? Yace Shikenan a saurare ni zan bincika lamarin. Tace Ni fa gaskiya duk laifinka ne domin kai ka nuna iyalanka ba su da gata a gurinka.... Ya daga mata hannu ransa a dan 6ace yace: Kinga ya isa haka, kin fada min nace zan bincika ba shikenan ba? Ta mike tsaye. Ai don ka sani ne bazan lamunta da dik wani iya shege ba. Duk wanda ya ta6a min 'yaya sai na ji dalili. Ta karashe maganar tana kokarin fita. Ya bita da kallo kawai batare da ya tanka ba su dai korafi shine abin yin su inda yake jin dadin karima kenan. Sam bata kawo mishi korafin wani, duk abin da zata yi wanda zai sanya shi farin ciki shi take yi. Yana kokarin saka jallabiya