Showing 66001 words to 69000 words out of 81464 words

Chapter 23 - MATA'UL HAYAT HAUSA NOVELS BY SAKINAT USMAN.txt

ma shahuran bokaye duk da kasancewarsa gogaggen matsafi masani sosai a harkar, hakan bai sanya ya san wasu hanyoyi da zai assasa mutuwar Sagir cikin sauki ba, don haka bin bokaye shi ne abin da ya ke dacewa a gareshi.
ada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JINDADIN RAYUWA)
¤¤30¤¤
Kafin a samu nasarar abin da yake so, said a aka yi wani gagarumin aiki, wanda ya boye duk wani shiri da Sammanin ke yi bare har Sagir ya gane ya dauki mataki, shi ma shirin kafin yinsa said a aka halakar da mutane uku, don wani shahararren boka ne mai gain har hanji ya yi aikin. Bayan ya tabbatarwa Alh. Sammani cewar, matsawar ana son kawar da Sagir sai an yi wannan shirin. A cikin wannan shiri da aka yi akwai wasu bayin Allah guda uku da suka so tarwatsa shirin, to suma said a bokan ya daure, daurin talala cikin boyeyyen sirri da surkulle irin na mushirikai wadanda Allah ne kadai yake iya karya shirinsu, tunda yasan shi bai isa ya kawar da su daga doron kasa ba. An samu nasarar kowanne shiri da aka yi, wanda ana gobe rasuwar Sagir aka zo gidan gona cikin sirri aka kafa tarkon a dai dai inda yak e ajiye motarasa. Washegari da safe shaukin abin ne ya dinga fizgarsa har yah an masa sukuni, yana son yin kiran gaggawa a kungiya don tattaunawa, amma kasala ta hana shi. A lokacin ne Haj. Karima ta kira shi a waya ta sahida masa Haj. Asmo ta zo daga Katsina. A lokacin kuma ne da zai tafi gida Alh. Sammani ya zo a ofis dinsa, wanda y agama bulbule jikinsa da turarukan da bokan ya ba shi. Ma’anar turaren shi ne, matsawar ya yi tozali da Sagir ya ji kamshin turaren kafin mai afkuwar ta afku, to ba shakka shi ne zai hau karagar mulki sabanin abin da matar Sagir zata Haifa akasin da aka samu bokan y ace kada ya yarda ya yi Magana da wani yayin day a saka turaren, har sai ya je gurin Sagir. To amma day a shigo gidan gonar akwai wadanda suka gaishe shi ya amsa musu, wannan shi ne sanadin day a sa Sagir bai ji kamshin turaren ba. Bayan sun gama tattaunawa game da batun daukar dan Alh. Sammani da za a yi abai wa dodon tsafi, suka rabu lokacin ne Sagir ya fada tarkon da aka kafa masa, ya yi tuntube da kahon LIBHAS wanda aka samo daga kasar Sin, cikin surkullen bokan Alh. Sammani, ya dinga aman jinni har zuwa asibiti…”
Ko da Abubakar ya zo nan alabrinsa sai ya ja baki ya yi shiru, yayin da su kuma duk kasala, damuwa, firgici da komai ma suka lillube musu jiki. Inna Yaduwa kuka ta ke kamar ranta zai fita, shi kansaAlh. Rabi’u kwallan ne a idanunsa, Alh. Sada yace, “Subhan Allahi, tabbasa biri ya yi kam da mutum, akwai lokuta da dama da na dinga mamakin irin dukiyar da Sagir yake da ita, ashe akwai sanadin samuwarta?”
Yakub ya karbi zancen da cewa, “wannan shi ne sanadin duk wata matsala da ta faru, abin al’ajab ko rudani da kuka ga sun faru da Shuhuda duk sanadin hakan ne.kamar yadda na fada muku labarin yana dauke da bangare uku, kuma kowane a cikinmu yana da bangaren da zai bayar, to kun ji bangare daya, sannan muna rokonku da kada ku yi fushi ku yafewa da uwanku, kuma danku abin day a aikata, ko don ya samu sassauci”. Babu wanda ya tanka, shi kuma ya ci gaba da cewa.”kafin wani daga cikin mu biyun nan y ace wani abu zan sanar da ku wani abu day a faru, yayin da Sagir ya zo rasuwa Alh. Ahmad ya ga idanuwansa sun sauya launi daga fari da baki kamar yadda idanunsa suke, zuwa launin KORE, DORAWA da BAKI. Tabbasa hakan yana da nasaba da sirrin tsafinsu duk wanda zai mutu dan kungiyar ko kuma aka sha jininsa ta wannan hanyar to sai anga wadannan launuka a idanunsu” ya karashe maganarsa yana duban Uncle Hamza, ya dora da cewa. “nasan daga kai Hamza har Isah kun yi tozali da abubuwan al’ajab daga ciki hard a sirrin NETWARK, sirrin sauya suffa dama dai sauransu. Tun da zare daya na labarin ya kamala, Shuhuda ita zata kamo zare na biyu wanda ke dauke da sirrin NETWORK da wasu abubuwa da suka faru su ma cikin sirri”. Ya yi furucin yan duban Shuhuda Ibn Khaddab. Ita kuwa ta gyara zama sosai tana fuskantar mutanen da ked akin, sannan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ta soma fadin cewa:-
BABI NA SHA TAKWAS
SAKAKKIYA
Yayin da aka haifi Shuhuda ‘ian kungiya sun ji dadi matuka, koda yake akwai alhinin rasuwar shugabansu a tare da su da suka wayi gari bakatantan, to amma wannan bai hana su farin ciki ba. Idan an cire Alh. Sammani wanda tunda ya bar gidan gonar bai zame ko ina ba sai gurin bokansa ya sanar masa ya aikata duk abinda y ace ya aikata. Bokan ya fashe da dariya, sannan y ace. “sammani ka yi kuskure gurin aikata abubuwan da an ace maka tun a gida lokacin da zaka fito ka yi amfani da ruwa, wanda n ace maka kada ka kusanci ruwa yayinda ka fesa turaren. Sannan da ka je gidan gona kafin ka isa gurin Alh. Sager ma’aikata sun gayar da kai, kuma ka amsa musu, ko mantawa ka yi, ko kuwa duk girma da isr ce suka janyo maka? Don haka aiki bai yi kyau ba sam-sam. A bangare daya ne aka sami nasarar wato mutuwar Sagir, domin tabbas ya yi tuntube da kahon dama ka’idarsa na muddin mutum zai yi tuntube dakahon libhas shi lallai babu makawa sai ya tattara inda ba a dawowa. Sai dai an haifi ‘ya mace wadda it ace magajinsa a kungiyarku kamar yadda tsarin kungiyar ta ke, samun galabrka kuwa zai yi wuya”. Tun day a ji wannan bakin labarin hankalinsa ya dugunzuma ya tashi, sun rabu da bokan akan idan wata bukata ta tashi zai dawo masa. A lokacin da aka haifi Shuhuda an ganta tana tsotsar hannu wanda aka yi tunanin sanadin bakunta ne ko kuma tana jin yunwa, wanda a zahiri ba haka ban e, babban makasudin tsotsar hannun Shuhuda shi ne, don nusar da ku akwai wani boyayyen al’amari a tare da ita mai bukatar tallafi, amma ba wanda ya yi tsinkaye da hakan. Idan ba ku manta ba a labarin da Abubakar ya bayar yanzu ya sanar da ku cewa, akwai wasu bayin Allah guda uku da aka daure yayin hada tarkon kawar da Sagir daga doron kasa, hakika su wadannan bayin Allah ba mutane ban e , ALJANNU ne masu alaka da KHASHIM TSAGEM, ai kun gane ko wan a ke nufi ko?” cikin mamakin yadda yarinya karama ke ta lailayo labari Alh. Rabi’u y ace. “Idan na fahimce ki, kina nifin kakana wanda ya haifi mahaifina?” t ace, “Tabbas shi nake nufi, wadannan bayin Allah sun kasance masu yiwa Khashi Tsagem hidima tun zamanin yana mahaifarsa (Tsagem) lokacin da yake haziki kuma hafizi don a gurinsa bayin Allah suke daukar karatu, har ya baro Tsagem suna yi masa hidima. Sun ci gaba da bin tsatson Khashi Tsagem suns bas u kariya daga miyagun aljannu, bas u taba sarewa ba, to lokacin da aka daure su aka gudanar da wannan aiki na kafa kahon libhas, Sagir na mutuwa aka kunce su, iya kuka sun koka, duk da dama can suna kuka akan shigar Sagir kungiyar matsafa. To lamari ne wanda yake rubutacce wanda babu wani mahalukin daga bil’adama zuwa jinnu da suka isa su hana ikon Allah tabbatuwa, don haka suna ji suna gain babu yadda suka iya Sagir ya fada wannan kungiya ta matsafa. Damuwar da suka shiga ta ta’azzara, haka ya sa daya daga cikinsu yayi kaura daga kasar Nigeria ya koma can Misra.daya daga ciki kuma ya assasa tsotsar hannun da Shuhuda ke yi, sannan da ta soma girma wata rana da aka yi yunkurin tsaga hannunta ya samara da rowan nono maimakon jinni, don dai a fahimci matsalar da ke tattare da ita, amma ba a fahimatar ba. A can kungiyar matsafa kuwa sun ci gab da kulawa da karagar mulki, domin bayan Alh. Sammani ya bar gurin boka bai hakura da son hawa karagar mulkin ba, don haka da aka samu shekara daya wata rana kawai yah aye karagar a zuwan ya zama shugabansu kamar yadda burinsa, amma nan take ya daskare suka ga naman jikinsa na zagwanyewa har ya zube kaf sai kasusuwansa. Bayan shi ma Izra’el da kwadayin mulkin ya shiga ransa ya jaraba hawa karagar mulkin ya daskare naman jikinsa ya zagwanye. Hakan ya daga musu hankali matuka, amma da dodon tsafin nasu ya sanar musu babu mai iya hawa karagar mulkin a zauna lafiya face wanda aka zaba ya zama magaji sai hankalinsu ya kwanta, sun san akwai wanda zai shugabance su a gaba. A sirrance suna zuwa ganin Shuhuda amma ba a taba bat a wani abu day a danganci naman mutane ko jinni ba, suna dai zuwa dubata a matsayinta na Mgajiya wadda zata zamo shugabarsu nan gaba. Lokacin da Slmai mai haja ta tsaga hannun Shuhudan ‘yan kungiya ne suka kasha Slmai, saboda ta raunata magajiyarsu su kuma ka’idarsu ken an, ba a taba musu shugsba a zauna lafiya. Maganar kwalwa da Shuhuda ta ked a ita, hakan Allah Ya yita ita din mai kwakwalwa ce, sai dai akwai abubuwan da ta yi wanda daya daga cikin bayin Allah nan guda uku ne ya yi jagorancin yinsu. Misali lokacinda tana aji hudu ranar da aka kawo wannan………”
Ta nuna Uncle Hamza ta cigaba da cewa.
a Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤31¤¤
“a matsayin sabon malami, ya yi musu tambaya akan RADIOACTIVITY ta bayar da amsa, amma a zahiri ba it ace ta bayar da amsar ba, saboda a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat a ma inda ake tsammaninta. Sannan irin haka tta sha faruwa da Shuhudan, a dauketa a samara da wata. Mas’ud ya bugi Shuhuda a lokacinda suka je Katsina har ya ji mata rauni don huce haushin dukan da mahaifinsa ya yi masa saboda mahaifiyarta Karima, shi ma yan kungiyane suka halaka shi. Dr Ya’u ma ya rasa ransa net a sanadin kungiya saboda su a ka’idarsu shugabansu bay a rashin lafiya ya je asibiti kai tsaye,suna da likitocin da ke kula da wannan bangaren, kai yawa ne fa da su ta kowanne bangaren ma’aikata da ke Nigeriyar nan, abin kunya ne matuka a garesu ace wani ya fitar da jinni ga shugabansu, sun bar shi da rai Shuhuda ta yi amfani da sunan Izra’el a wajen Uncle Hamza, da nufin sunanta ken an a lokacin ba it ace ta furta hakan ba,BAWAN ALLAH ne ya furta kamar yadda na fada muku a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat a a muhallin, sai an samara da wata, shi yasa lokacin da Uncle Hamza ya sake tambayarta me yasa take amsa sunan Izra’el a matsayin sunanta ta nuna bat a san ta yi hakan ba, tabbas din bat a da masaniya. Hikimar yin hakan shi ne, tun lokacin da bawan Allah ya lura da Uncle Hamza ya shigo rayuwar Shuhuda sai ya yi tunanin ta hanyarsa za a samu a gano matsalar da Shuhudan ked a ita, shi yasa Hamza ya dinga katari da abubuwan rudani game da Shuhudan. Amma sai ya dauki abin kwalwa ce ya yi mata yawa kamar yadda wani abokinsa Dr Ishak ya sanar masa ana samun irin yaranda ked a kwalwa irin tata su kuma kasance da irin abubuwanda yake ganinta da su. Ko kuma yana dubanta a matsayin burkakka mara hankalibkamar yadda Inna Yaduwa itama ta ke ganinta a hakan. Wata rana Inna Yaduwa ta zo dukan Shuhuda hannunta ya srke, bawan Allah ne da alohakin hakan, duk dai akan turbar haska mata akwai babban al’amari a tare da Sahuhuda……….” Alh .Ahmad ya katse Shuhuda Ibn Khaddab da cewa. “wai shin duk a ina kukasami wadannan labaran? Idan dai kun kasance mutane ne ku, to muna bukatar Karin bayanin ta yadda aka yi kuke da sani na abubuwanda zai yi wuya ku iya sani kai tsaye sakamakon karancin shekarunku”. Yakub ya yi murmushi, y ace. “ai cikin sharadinmu da ku, ba zaku yi mana tambaya ba har sai mun gama sanar da ku labaran da muke son sanar da ku. Idan kuma kunce lallai sai mun sanar da ku yadda aka yi muka samu wannan labaran, hakika abin da ake gudu zai faru, zaku rasa Shuhuda ‘yar ku, rasawa ta har abada, wanda hakan ba karamin barazana ban e a gareku ba, domin laifin wani ne ya shafeta”. Sai aka yi shiru, Shuhuda Ibn Khaddab ta ci gaba da cewa bayan ta fasali.
*****
“idan dare ya yi maji dadin kungiyar mai suna Mandus yakan zo ya dauki Shuhuda ya kai ta guraren da ake shakatawa ake casu don girmamawa a gareta. Wannan tsarinsu ne ma ji dadi shi ked a wannanaikin. Wani lokaci Shuhuda ta taba fadawa Hamza takan ganta a wata daula tana rawa tana shan ruwa a cikin koko, bawan Allah ne ya yi hakan duk a cikin abin da yake faruwan na gushewar hankalinta a samara da wata, ya yi hakan ne domin haskawa Hamzan, amma bai gane ba sai ma ya dauki abin a BARA-DA-BANA, saboda an yi amfani da kalmomin sakayau da kuma nannauya. Mu koma sirrin Network wato sabis ken an, lokacin da Inna Yaduwa ta so dukan Shuhuda hannunta ya sake, ta shiga daki ta dauki waya don ta kira wani ta sanar masa halin da ake ciki, amma sai wayar ta mutu. Abin day a faru shi ne, idan har Inna Yaduwa zata yi tunani daga ta zo dukan Shuhuda sai hannunta ya sake haka kawai? Ai dole akwai sanadi, ita ba sanadin ta ke tuhuma ba, a’a burinta ta sanar a zo a dauke mata Shuhuda daga gidanata ba jikanyarta b ace. Wata rana tunani ya yiwa Hamza yawa game da Shuhuda, ya kira lambar da mutumin day a kira kansa da Yayanta ya ba shi, ya kira maimakon ya ji sautin tiring-tirin irin na Mtn, sai ya ji tiring sau daya wanda hakan ke nuna wani layin ne ya kira bayan shi kuma yasan MTN ne. ba a dauka ba, har sau biyu yana kira ba a amsa kiran ba. Can aka kira shi da bakuwar lamba, daga kasar waje aka sanar masa Abubakar Ibn Khaddab ne daga Misra, wai ya kira lambar ne shi a tunanin Hamza matsalar network ne, wanda duk kadan ne daga cikin hikimomin bayin Allah da za a gane akwai wani sirri dangane da Shuhuda”. Ta dan saurara da bayar da labarin tana kallon Uncle Hamza fuskarta cike da murmushi. Y zuwa yanzu ko ba a fada musu ba sun gano ko su waye wadannan bayin Allah wato dais u ukun nana sun e aljanun!
*
(kun sani typing cikin dare ina yi ina hawaye :’( :’( :’( ……………)
Ko da yake J ALLAH na tare da ni don addu’a it ace takobin mumini ALHAMDULILLAH Sadin Mama)
*
Dukkansu matsanancin tsoro ne ya dirar musu, domin bas u taba tunanin hakan ba, Shuhuda= Ibn Khaddab ta ci gaba da cewa “Hamza an turo maka rudadden sako wand azan iya cewa ya juyar da tunanika, da ka kira lambar kuma sai ka yi katari da samun kanwarka kuma wadda ta ke son ka aureta ZUWAIRIYYA. Alal hakika Zuwairiyya ta fi ka gaskiya, domin itama ta turo maka sako a lokacin tana Magana game da irin son da take yi maka kai kuma ka yi watsi da hakan, shi yasa ta yi mamaki da ka nemi juyar da tunaninta. Ranar littinin ne suke yawaita yin taron kungiya. An hasasa maka Shuhuda tana rayuwa cikin kunci saboda azal din day a fada mata shi yasa wanda ya turo maka sakon yake jin tausayinta. Hikimar juye suffer Shuhuda a hotoin da kuka dauka a library lokacin yin candy dinsu, don ka gane akwai boyayyen sirri, matsalar kasancewarka mai zurfin ilimin addini. Amma sai hakan ya sanya ka rudani, ka rasa wace ce aljana a cikin su biyun, Shuhudan ko Zuwairiyya? Karshe kai kanka said a ka dinga tabbatar zamowarka bil’adama”.
Shuhuda Ibn Khaddab ta mayar da dubanta ga Isah, sannan ta ci gaba da cewa tana dai murmushi. “mun hadu da kai a birnin Misra ranar da ka baro Senegal, sannan mun hadu da kai a Katsina, mun sake haduwa da kai a Ibadan har ka samu budaddiyar wasika, koda yake kafin haduwarmu da kai a Katsina da Ibdadan, wasu murdaddun abubuwa sun faru, masu SARKAKKIYA, misali, furtawa Shuhuda da ka yi kana sonta ta ki amincewa, a ranar ne ka yi mafarki Shuhuda ta kima Zakanya tana cinye kananan dabbobi. Da ka je dakinsu ka tarar cikinta na juyawa kamar kwallo wannan duk aikin bawan Allah ne. washegari kan son yi mata maganar amma ka rasa yadda zaka furta a haka har kwanaki biyu, ka taba cikin a cikon kwanaki na biyun, wanda daga lokacin ne ba ka kuma mafarki da Shuhuda ba, kuma a washe garin ta amsa soyayyarka. Dalilan da suka sa Inna Yaduwa ta dinga jin tsoron Shuhuda a dukblokacin da ta so furta wani al’amari shi ne, an shirya kasha Inna Yaduwa a can kungiya, saboda dodon tsai ya bukaci hakan, har aka bai wa Shuhudan wani kaho wanda zata zuki jinin Inna Yaduwar hakan bai samu ba.wannan shi ne sanadin da bawan Allah yayi kafi a gidan hatta Shuhuda said a aka neme ta a kungiya sama ko kasa bas a ganinta muddin dai a gidan za a zo daukarta to ba za a ganta ba. Wannan mataki da bawan Allah ya dauka ya samo shi ne daga sarakunan fararen aljannu na lardin kasar Misra. Shekara da shekaru bawan Allah na neman hanyar da zai kubutar da Shuhuda daga halaka, amma bai samu ba, sai wannan lokaci day a soma samun nasara ta batar da gidan nan daga idanun masu sirri, wannan rufaffiyar robar it ace sirrin batar da gidan. Wannan shi ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login