Showing 27001 words to 30000 words out of 105124 words

Chapter 10 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16341

ce"


"wai dan Allah Meye ƙwaila?"


"Ke kin isheni da surutu bana son yawan magana seda safe"


Mufeeda aran ta tace "bari in nunawa mutumin nan ƙwailar ma mace ce"


Ta kashe murya sosai ta kalle shi cikin shagwaba kaman 'yar yarinya tace


"Mijin Jaririya ban gaji da ganin ka bafa dan Allah ka tsaya in ƙara kallon ka"


Ya haɗe rai yace "ke bana son shirme fa"


"waini komai nayi shirme ne, muje in raka ka ni ban gaji da ganin ka ba"


Haka ta biyo shi wajen gate yace "koma gida rakiyar nagode haka"


"to My love, ka gaida gida ka gaishemin da Mama, ina sonka Yaya Ammar ɗina" ta kashe masa ido ɗaya ta koma gida.


Girgiza kai yayi ya nufi Napep ɗin sa, yana ƙara jinjinaa yarintar mufeeda.


Shi mamakin kansa ma ya dingayi yadda ya tsaya yana sauraren shirmen ta. Ammar ya dinga ji a ransa ina ma Mace ze aura, inama Auren kirki zeyi ba wannan auren shirirtar ba, Yarinyar da sam ba zaman Auren ne a gaban ta ba ita dai tace zata yi aure ne saboda tana sonsa, sam besa ran wani zaman Aure da Mufeeda ba kawai zeyi aurene ya ƙarasawa Mama raino.








Ɗakin Baba ta shiga da sallama ta tarar dashi zaune tare da Mama, Baba yace "Autar Baba kuma Amarya to be"


Murmushi Mufeeda tayi ta ƙarasa ta miƙawa Mama kuɗin da Ammar ya bata, Mama tace
"wannan kuma na menene?"
"Bani yayi wai inyi haƙuri bashi da kuɗi in ƙara inyi wani abu, sannan inyi kitso da ƙunshi a ciki"
Mama tace "roƙon sa kikayi kenan?"
"Ni kin san bana Roƙo shi yace sena karɓa"


Suna cikin maganar ne yaro yayi sallama ya kawo viva yace
"Ammar yace a bawa Mufeeda"




Mufeeda ta karɓo ta shigo ɗakin Baba
Kayane ɗinkakku shadda ce blue da leshi se takalmi da jaka na Amare, ita dai Mufeeda kasa magana tayi se kallon kayan take.


Baba yace "A jikina ina jin Insha Allah yaron nan ze kulamin da Auta, akwai shi da ƙoƙari, yanzu bayan kayan lefe hadda wata hidimar ta daban"


Mama tace "lallai yaron nan akwai ƙarfin hali, bayan hidimar lefe da yayi hadda wata ɗawainiya daban, kuma gashi an riga an sai mata kayan da zata yi fitar biki"


Mufeeda tai farat tace "ni gaskiya na Yaya Ammar zan sa"


Mama tace tashi ki bar ɗakin nan mara kunya kawai, ban taɓa ganin mace mara kunya kamar ke ba, ana maganar aurenki kina tsoma baki shashasha kawai.






Hausawa sukace rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, kwanci tashi asarar rai satin bikin Mufeeda ƙwaila da Oga Ammar ya kama (😜😜😜)


Tunda satin biki ya kama jikin ta yayi sanyi komai a hankali take yi kaman kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.


Yaya Amina da fati sune suka zama tamkar manyan ƙawayen ta.


Tasha lalle anmata gyaran kai tayi kyau matuƙa ga fatarta se sheƙi take yi, Mama daurewa kawai take yi dan har cikin zuciyar ta take jin rabuwa da Autar tata, dukda kullum cikin faɗa suke.




An kama mata gurin kamu, tayi shigar gargajiya anmata simple make up tayi kyau sosai, 'yan gulma se cewa suke wannan amarya' yar yarinya se kace auren ƙauye, hada masu Anya ba magana ta ɗaukowa iyayen ba shiyasa suke so su lallaɓa su aurar da ita ba, kowa da abunda yake faɗa, akayi kamu da sauran Al'adun gargajiya aka watse.






Abokan Ammar sunyi bajinta, suka haɗa kuɗi suka sai masa ƙaramin inji, suka sai masa dish suka bashi kuɗi naira dubu saba'in, da yake Shima Ammar meyi ne, duk wanda sha'anin sa ya tashi dukda bashi da shi sosai amma ze daki jikin sa yayiwa mutum alheri, gashi shi babu wani babban sha'ani daya taɓa taso masa balle suyi masa kara, shiyasa wannan karon suma suka jajirce suka yi masa wannan abun Alkhairin.


Ammar yaji daɗin kuɗin nan matuƙa, dan haka ya samu Abba ya nuna masa kayan da abokan sa suka bashi, Abba yaita murna yana samu su Albarka.


Ammar ya bawa Abba dubu hamsin yace
"ga sadakin sa nan da za'a bawa Mufeeda"
Abba yace "Madalla Allah yayi maka Albarka, Allah ya Sanya muku Alkhairi"


Yaya jidda na gidan Ammar ya bawa Abba kuɗin sadakin.


Ta dinga mita tana masifa "wannan 'yar mitsilar yarinyar za' a bawa sadaki har dubu hamsin saboda Almubazzaranci wallahi Ammar ni har ka fara bani kunya duk wannan izzar se kashewa ƙaramar yarinya kuɗin ka kake, wallahi zakayi dana sanin auren wannan abar dan banga abunda zaka samu a jikin ta ba, banda abun namiji ga mace kaman Zainab amma ka ɗakko wannan 'yar mitsilar abar"


Ammar yace "Komai girman ta komai ƙanƙantar ta tunda Auren ta zanyi dole in kashe mata kuɗi tunda itama 'yace mutane ne suka haife ta, tunda Auren ta zan yi kulawar ta dole ta dawo ƙarƙashina dole in nema in kashe mata tunda kema naki mijin yana nema yayi miki"


Umma tace "jidda karki ƙara shiga sabgar abunda Ammar zeyiwa Mufeeda, Allah ya riga ya ƙaddara baze auri Zainab ba Mufeeda ze aura"






Duk Events ɗin da akayi babu wanda Ammar ya halarta, Amma danginsa sunje, Amma Amarya dai2 gwargwado tayi kyau matuƙa, Mufeeda tana da kyau ba laifi
(Amma oga yace bata kai mace ba dan haka se a hankali, se anyi rainon ta😂).










Ayimin haƙuri may be zaku ɗan jini shiru kwana biyu


Share please
More Comments More typing
Ayshercool
07063065680
[23/06, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )








*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com





ELEGANT ONLINE WRITER'S









Page 9


Tunda aka fara bikin nan ko waya Mufeeda basu yi da Ammar ba, kan Mufeeda ya ɗau caji sosai, ana i gobe ɗaurin Aure Mufeeda ta fara kuka, ji take kaman tace ta fasa kuka sosai, Mama tun tana rarrashin ta harta bata haushi tace


"da Ubanwa yace kice ke Auren kike so, ki rufemin baki ko in zane miki jikinki"






Yaya Amina ce taje ta samu Baba ta gaya masa ga Autar sa can tana kuka Mama tace zata zane ta, Baba yasa aka kira masa Mufeeda, Ya dinga rarrashin ta yana mata nasiha ƙarshe a ɗakin Baba ta kwana.


Kasancewar bata samu bacci ba sosai daren jiya yasa bayan sallar Asuba tai kwanciyar ta tana bacci, Baba kuma ya hana a tashe ta har ƙarfe tara na safe aka kafa rumufunan ɗaurin Aure tana bacci.






Da ƙyar Baba ya bari aka tashe ta ta karya, sama sama aka mata kwalliya shima tana yi tana kuka.


Ammar ya sha shaddrsa fara ƙal yayi kyau kaman a sace shi a gudu se zuba ƙamshi yake, Amma se wani cin magani yake kaman wanda za'ayiwa auren dole, Aminu yace


"gaskiya Ammar ka saki ranka ba ze yuwu muje gurin ɗaurin auren nan kana wannan hade ran ba, se mutanen nan suce azabtar musu da 'ya zakayi, yau ranar farinciki ce a gareka"


Ɗan tsaki Ammar yayi yace


"nikam bana farincikin saboda dani da wanda da wanda ba aure zeba duk ɗaya, ni garama in zauna ba auren, na ɗauki wannan Auren a matsayin ƙaddara ta ne kawai"


Jabir yace "Ammar be kamata ka ɓata Auren ka da bakin ka ba, dukda ƙaramar yarinya ce idan kasa gidan Auren ka ze zame maka dausayi na farinciki, yarinyar nan kai take so zata iya zama da kai a kowane yanayi na rayuwa, dan Allah ka saki ranka ka dena wannan ɓata ran"


Haka suka ci gaba da lallɓa Ammar har suka tafi gurin ɗaurin Auren.


Aka ɗaura Auren Mufeeda da Ammar akan sadaki har Naira dubu hamsin, Mutane sun yi mamaki musamman magulmata, Yaya Fadila ta shigo ɗaki ta samu Mufeeda tace


"Auta buri ya cika an auri Ammar, an zama matan Aure su Mufeeda yanzu nidake mun zama ɗaya fa ko?"


Banza Mufeeda tai mata taƙi ko kallon ta.


Fadeela tace "Yarinya zaki ga abunda muke jiye miki, seki tashi an ɗaura, ki tashi kije za'ayi hotunan ɗaurin Aure"


Kuka Mufeeda ta saka tare da noƙe kafaɗa, Fadila kuwa ta dinga mata dariya tana cewa


"Yarinya da an gayamiki Auren abune me sauƙi? Ai ki adana kukan ki"


Seda Mama tazo tai fama da ita Sannan aka gyara kwalliyar ta fito, Angwaye sun shigo anata gaisawa Mufeeda ta fito.




Tunda ta fito yake kallon ta da alama tana cikin damuwa amma tayi kyau, irin shaddrsa ce ya kawo mata itace a jikin ta, me hoto yazo anata ɗaukar hotuna, dukda haka wasu anayi tana kuka, kallon ta Ammar yake sam kuka ba yamata wahala ko meye na kukan kuma yanzu oho?


Daga cikin abokan Ammar ne wani Faruk yace "haba boss ka rarrashi babyn taka mana, kana kallo tana kuka"


Wata uwar harara Ammar ya watsa masa, ya maze.


Abokan Ammar suka sasu gaba wai za'a musu hoto tare, Mufeeda taƙi tsayawa, Jabir yace


"dan Allah ka rarrashi Amaryar nan taka ayi hoton nan"


Ammar ya ɗanyi ƙasa da muryarsa yace
"wai ba zakiyi shiru ba? Kukan me kike haka waye yace kice kina son Auren? Kidena wannan kukan ko a fasa hoton, maza goge hawayen nan"


Abokan Ammar se ihu suke suna "kunga wani salon Soyayya"


Mufeeda tana kuka amma ta zumɓura baki daidai kunnen Ammar tace "ka bani handkerchief in goge"
"bazan bayar ba in bazaki dena ba kiyi tayi"
"wallahi in baka banba da babbar rigarka zan goge"
Da sauri ya ɗago ya kalleta, babbar rigar sa fara ƙal tasha aiki, Amma tace da ita zata goge hawaye, yanayin kallon da yayi mata ne kaman na soyayya, aka dinga ɗaukar su hoto.


"Ka bani mana Allah zan goge da rigar ka" girgiza kai yayi baya son yayi wani abu daze nuna rashin kyautawa a gaban mutane, amma tabbas yasan zata aikata abunda tace ya ɗakko handkerchief ya miƙa mata ta karɓa ta goge hawayen fuskarta, handkerchief ɗin se tashin ƙamshin turaren Ammar yake.




shi dai Faruk ji yake inama shi ya samu damar da Ammar ya samu, yarinya ƙarama gata me kyau ga shagwaɓa abunda yake matuƙar burgeshi da mace kenan ya samu mace shagwaɓaɓiya.






Nan ma aka dinga surutu 'yan matan layin su Mufeeda da suke ji da kansu su kaita gulma wata tace
"Taɓɗijan wannan yarinyar ya zata yi da wannan mutumin ai yayi mata girma, kalleta' yar mitsitsiya da ita jishi a murɗe kaman ɗan dambe"


Ɗayar tace "ke Amma wallahi ya haɗu koni na samu wannan Auren sa zanyi wallahi yana da kyau, wannan beyi kalar auren 'yar mitsitsiyar yarinya ba, Amma se wani cin magani yake ko fara' ar kirki ba yayi kaman wanda akayiwa auren dole"


"Ke wallahi da na ganshi lokacin da yake zuwa zance ni zanyi ƙoƙari in cusa kaina, amma wannan ai da irin mu ya dace ba wannan fitsararriyar ba"


Ɗayar tace "Allah ya kiyaye in auri me Napep nafi ƙarfin nan"


"A'a wallahi ni banfi ƙarfi ba, ba gamu a zaune a layi ba, ita kuma tayi wuf dame napep wallahi indai zanci in sha na samu kaman wannan tafiya zanyi gamu a zaune ai yarinyar da aka haifa a gaban mu ta shige muna zaune" haka suka ci gaba da surutunsu da gulmace gulmace


Haka aka gama shagalin biki a wunin ranar, Amma uwar gayya kanta har ciwo yake saboda kuka, bayan magariba motocin ɗaukar Amarya suka zo, maƙota suka dinga cika motocin nan suna tafiya zasu je suga ƙwal uwar daka suje ganin gidan mufeeda.




Kusan duk an watse Mufeeda ake jira a tafi da ita amma ta maƙale a jikin mama tana ta kuka, Mama ta aurar da yara mata amma bata taɓa zubda Hawaye danta aurar da 'ya ba se wannan karon tana cikin yiwa Auta nasiha mufeeda ta ƙanƙame ta tana kuka, kawai se Mama itama ta hau kukan, duk faɗan da suke yi da Mufeeda tana matuƙar ƙaunar' yar tata, suka rungume juna suna kuka, Yayan mufeeda ya shigo yace


"Mama dan Allah kidena kukan nan ki ƙyale yarinyar nan akaita ɗakin ta, tun ɗazu su gwaggo sahura na mota ita suke jira amma kin ƙanƙameta kuna kuka, haba Mama baki taɓa kuka dan zaki aurar da 'ya ba se Mufeeda"


Su Anty Murja sukai tayiwa mama mita, Sosai Mama taƙi saurara su ta ƙara rungume auta.


Seda Baba yazo da kansa, ya zauna ya ƙara yiwa Mufeeda nasiha me ratsa zuciya sannan yace ta tashi ta tafi a raka ta, amma Mufeeda tai mursisi ta sake hayewa kan gado bayan Mama tana kuka, Mama ji take kaman tace a ƙyale mata 'yar ta, Mufeeda tayi ƙanƙanta da fara fuskantar ƙalubalen dake cikin rayuwar aure, Amma tana mata addu'a Allah yasa Ammar ya riƙe ta Amana.




Baba ne yace "yaki Auta na zo da kaina zan raka ki ɗakin ki, duk yayyan ki ba wadda na raka, amma dole in raka auta taho muje"


Baba yasa hannu ya kamo na auta, ta sakko daga kan gadon amma ta riƙe hannun Mama, shi kansa Baba daurewa yake yadda suke kuka gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi.


Baba yace
"Sarah dan Allah kiyi hakuri kiyi mata fatan Alkhairi"


Mama ta goge hawayen ta tace


"yi shiru Auta na kinji, kiyi hakuri haka dama rayuwar 'ya mace take, kedai ki riƙe nasihohi da muka yi miki zaki zauna lafiya da kowa a rayuwa Insha Allah, jeki Auta na Allah ya bada sa' a Allah ya sanya alkhairi yasa gidan zamanki ne, Allah ya Sanya alkhairi da haske a rayuwar auren ki Allah ya bada sa'a"


Daƙyar Mufeeda ta saki Mama, Baba ya riƙe hannun ta yasa ta a mota ya tafi kai Autarsa da kansa ɗakin miji.


***************


Ammar ya kammala shiryawa se zuba ƙamshi yake, abokan sa na waje suna jiran sa, gidan su Ammar wasu duk sun tafi gidan Amarya, yayin da wasu ke ƙarasa Wanke-Wanke da gyaran gida, Ammar ya shiga ɗakin Abban sa ya tarar da shi zaune da shi da Ummansa yaje ya durƙusa gaban su yace
"Abba zan tafi"




Abba yai murmushi yace "Ango ka sha ƙamshi, ubangiji Allah ya Sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, dan Allah dan Annabi Ammar yadda suka baka 'yar su cikin mutunci ka girmama musu yarinya ka kula da ita, ka sauke dukkanin haƙƙoƙin ta dake wuyan ka, ka rage wannan zafin zuciyar naka da izza da wannan yawan faɗan naka, kaga yarinya ce ƙarama ka kula da ita Ammar "


Ammar ya jinjina kai yace
" Insha Allah Abba "


Umma tace
"to Ammar duk abunda zan gaya maka na riga na faɗa maka a baya, kuma mahaifin kama ya gaya maka, yarinyar nan da iyayen ta sun mana halacci, kaji tsoron Allah ka riƙe musu yarinyar su Amana, sannan ka tuna kaima akwai 'yan uwanka mata dake aure a gidan wasu, idan ka muzgunawa' yar wasu to tabbas kaima za'a cuzguna ma naka, ka riƙe ta da amana sannan kuma kayi haƙuri, kayi haƙuri rayuwar aure gaba ɗayan ta haƙuri ce, Allah ya baku zaman lafiya "


Ammar kasa cewa komai yayi, a hankali yace " Abba a zaman mu daku nasan baza'a rasa abubuwa marasa daɗi da nayi muku ba ina roƙon afuwar ku"


Abba yace "Aini dama matsala ta da kai ɗaya, rashin Aure ga miskilanci, amma duk wannan ba komai bane akan tarin alkhairan ka a gare mu, mun yafe maka Allah yayi maka albarka"


Ya amsa da Ameen, sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya fito tsakar gida, sauran 'yan biki suka dinga masa guɗa suna masa fatan Alkhairi, wasu har sunje sunga gida sun dawo.


Yayar sa Maryam wadda ita yake bi ta ja shi gefe tace




"To ɗan uwana ina maka fatan Alkhairi, Allah ya Sanya albarka yasa anyi kenan, sannan abunda nake so in gaya maka shine, ka kula sosai karka fifita matarka akan iyayen ka, sannan karka fifita buƙatun mu 'yan uwanka akan Na matarka, mu a gidan mazajen mu muke, duk wadda tazo maka da buƙatar ta indai bata da wani mahimmanci ka ƙyale namu buƙatar ka sauke haƙƙin matar ka, dan Allah ze tambaye ka akan amanar da ka ɗakko, Sannan Ammar tsakanin ka da iyayenka da mu 'yan uwanka daban, tsakanin ka da matar ka daban, dan haka ka yi wa matar ka abu ba lallai se mun sani ba, haka dan ka yi wa iyayenka abu base lallai ta sani ba, hakan ze toshe kafar samun matsala, Sannan kasan Auren nan naka yana da maƙiya mussman a gurin bikin nan na ƙara gani, kasan Yaya jidda bata son Auren nan, Sannan karka manta ko kuma in baka sani ba yanzu in gaya maka, Fa'izar Kawu Bala tana ɗaya daga cikin masu ƙaunar ka, ƙiri Ƙiri take nuna adawarta tareda kushe Auren nan, dan haka seka kula sosai, Allah ya baku zaman lafiya ƙanina"


Mamakine ya kama Ammar sosai, wai Fa'iza Yarinyar da ko gaisawar kirki ba sayi ace itake sonsa, da yake duk cikin 'yan uwan sa yana jituwa da maryam sosai dan haka yace


"Shikenan Sayyada Maryama, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah ya huta gajiya"


Yai gaba tana ɗaga masa hannu.


Yana fita nan ma abokan sa suka dinga tsokanar sa, daga nan suka hau abun hawa zuwa gidan Ammar.


Mutane kusan duk an watse, suka je suka tarar da Mufeeda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login