Showing 15001 words to 18000 words out of 105124 words

Chapter 6 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16357

ba"


"Umma ni dai dan Allah ki sama mun mafita amma gaskiya bana son ta"


Umma tace "karka kuma cewa baka son ta, ko da wasa karka kuskura ka kalli idon mutumin da yace yana sonka ka gaya masa baka sonsa, ba'a haka kaima Allah ze iya jarabtar ka wataran, tashi kaje seka dawo ma cigaba da maganar"


Umma ta sallami Ammar ya tashi ya tafi yana ƙara zullumi da tunanin wannan lamari a ransa.


Da magariba Ammar ya dawo gida dan yana jin yunwa, bayan yaci Abincin dare, yai sallar isha'i a gida, dan ya rasa jam'i, kuma yana son ya ɗan zaga ya ɗau fasinjan dare, ya gama abunda zeyi ze fita Baban sa ya shigo ya tsaya ya gaida Abban sa, ya kalle shi yace
"fita zaka kuma yine Ammar?"


"Eh Abba zani na ɗan zaga in samu fasinjan dare"


Abba yace "ɗan tsaya kafin ka fita ɗakko min tabarma a ɗaki"
Ammar yaje ya ɗakko tabarma ya shimfiɗa wa Abban sa ya zauna.
Abba yace "kaima zauna"


Ammar ya cire takalmansa ya samu guri ya zauna


Abba ya kalle shi yace


"Ammar mahaifiyarka tayi min bayanin abunda yake faruwa, ance ka fito, nayi farinciki da jin hakan ƙwarai, yanzu abunda nake so da kai zuwa rana ita yau kaje banki ka ɗakko abunda ya samu da kake tarawa zanyi wa kawunka magana, Insha Allah zamuje akai maka kuɗin Aure"


Ƙuuuuuu cikin Ammar ya bada wata irin ƙara ya kalli mahaifin sa yace "Abba wallahi ba sonta nake ba"


Abba yace "mu muna son ta, aini duk wanda yake ƙaunar ku Ammar nima ina ƙaunar sa"


"Abba wallahi yarinya ce sosai, bata fi ayi rainon ta ba"


"Ammar duk yarinyar data nuna tana sonka a yadda kake ɗin nan, ga fushi da saurin zuciya ga jinkai, kai ba kuɗi ba kai ba mulki ba amma tace tana sonka, harta ga yawa mahaifin ta a irin yadda da yawan 'yan matan zamanin nan masu son abun duniya tace taji ta gani tana sonka, wallahi Ammar ka bari yarinyar nan ta suɓuce maka zakayi babbar asara, ina me tabbatar maka zata iya zama da kai a halin akwai ko babu"


"Abba ya za' ayi in zauna da macen da bana so, kuma fa akwai wadda nake zuwa gurin ta fa"


"Ammar ni tunda muke baka taɓa cemin kana da wadda kake zuwa gurin ta ba, dan haka kayi haƙuri Allah yasa haka shine mafi alkhairi"


Gaba ɗaya Ammar be taɓa tunanin abubuwa zasu hargitse masa haka ba, wannan wace irin jaraba ce, daga haɗuwa da yarinya ta zame masa gum
(glue inji bebi 😂) shi sam beta ɓa kawo batun aure a nan kusa ba mussman auren ƙaramar yarinya amma lokaci ɗaya al'amura na ƙoƙarin sauya masa.


*******************


Kwana biyu Mufeeda ta warware harta koma makaranta, Baba be gayawa Mufeeda yadda suka yi da Ammar ba, Sannan ya yanke shawarar a aji biyar na sikandire Mufeeda zata zana jarrabawar kammala sikandire ya aurar da ita.


Ammar be kuma bi takan ya jikin Mufeeda ba, itakam mufeeda addu'a take idan Auren Amma ze zame mata alkhairi Allah ya tabattar idan kuna babu alkhairi Allah ya zaɓa mata mafi Alkhairi amma tabbas zuciyar ta na matukar son Ammar.


Sati ya zagayo cif Ammar be kuma yiwa mahaifin sa batun maganar kai kuɗi ba, ranar kwana na goma da maganar, Ammar yana kwance yana bacci da safe Abba yazo yana buga masa ƙofa, da sauri Ammar ya tashi yazo ya buɗe ƙofar.


Abba yace "Ammar idan kai baka gudun magana toni baza ka maidani ƙaramin mutum ba, ka amsawa mutane zaka tura magabatanka yau kwana goma dayi maka maganar ka kawo abunda yake hannun ka amma kayi biris dani, ban isa in gaya maka magana kaji ba ko Ammar?"


"Abba bahaka bane, nifa kuɗin da nake da su basu fi dubu talatin ba, kuma ni...


Abba ya katse shi ta hanyar cewa
"Sa kayanka kaje ka ciro su ni akwai dubu ashirin a gurina, gobe insha Allah zamuje mu kai"


"Amma Abba kaga"


"nagama magana Ammar, in na isa da kai kayi abunda nace in ban isa ba kuma shikenan"


Abba ya juya ya fice, Ammar ya zauna akan katifarsa ya dafe kai.


Ya fara tunanin Anya aka kai dubu hamsin baza su raina ba? Mahaifin Mufeeda yana da rufin Asiri kuma yayyen ta suna auran masu kuɗi anya baza'a wulaƙanta shiba, dan shi babban abunda ya tsana kenan a rayuwar sa wulaƙanci, waima yanzu ba abun kunya bane ace kaman shi da shekarunsa ya gama cika baki amma ya auri Mufeeda, yasan Idan ya auri Mufeeda dashi da wanda bashi da aure duk ɗaya dan wannan yarinyar bata isa komai a gurin sa ba.


A fili yace "Allah yasa su raina kuɗin suce baza su karɓa ba"


Hakanan jiki babu ƙwari ya miƙe ya tafi banki ya ciro kuɗi.


***************


Mufeeda ta dawo daga makarantar boko a matuƙar gajiye, data dawo tayi mamakin ganin Mahaifinta a gida a wannan lokacin, taci Abinci tai shirin ta tsaf ta tafi Islamiyya.


Bayan ta dawo da daddare Baban ta yasa akai kiran ta, taje ta sameshi shida Maman ta a zaune.


"Gani Baba"


Baba yace "Mufeeda yau gidan su Ammar suka kawo kuɗin auren ki, sun kawo kuɗin su har naira dubu hamsin, ɗazu da safe kina makaranta kuma nayi dukkanin binkicen da ya kamata inyi akan sa an tabbatar min da cewar mutumin kirki ne ɗan gidan masu mutunci dan haka na tsaida ranar Auren ku nan da watanni shida"


Da sauri ta kalli Baban nata tace "to ai lokacin ban gama makaranta ba"


Baba yace "Eh wannan shekarar zakiyi Waec i know you can do it, zan sama miki gurin extra lesson, kuna kammala jarrabawa mu sha biki"


Se a lokacin wata kunya ta saukar mata, ta ɗanyi murmushi ta tashi ta fita ta bar ɗakin


Mama kam gaba ɗaya ranta a ɓace yake, gani take ta ko ina an cutar mata da yarinya, ga ƙarancin shekaru da Mufeeda ke da su, ga yarinyar ta babu laifi tana da kyau, sannan izifi talatin ne na Al'qur'ani akan ta amma ace dubu hamsin za'a bata kuɗin aure kamar wata bazawara.


Tunda aka kawo kuɗin Mama take mita, Amma ɓangaren Baba yaji daɗin ganin 'yan uwan Ammar, mutane ne masu karamci da yakana, mahaifin Ammar da kanshi ya sanar da Mahaifin Mufeeda cewar "Ammar yayi karatun sa na zamani, Amma rashin aikin yi ya sashi fara sana'ar babur ɗin a daidaita sahu, ya tabbatarwa mahaifin Mufeeda cewar Ammar baya raina sana'a komai ƙanƙartar ta idan ya samu zeyi yasan Insha Allah ze iya riƙe Mufeeda.


Da Baba ya gaya musu ya saka watanni shida lokacin biki ƙanin mahaifin Ammar yace "yallaɓai wata shida ai bamu gama shiri ba abunka da masu ƙaramin ƙarfi"


Baba yace "karku damu, duk abunda ya sawwaƙa kuka kawo zamu karɓa karku takura kanku, aini duk wanda yake son ɗana ya gama min komai, Ammar ɗana ne komai ya kawo Allah ya amfana zan bashi Auta"


Baban Mufeeda yaji daɗin wannan bayanin dan yana son mutane masu gaskiya.


Ganin da Baba yayi Mitar Mama taƙi ƙarewa ya sashi fara yi mata nasiha


"Sarah wani lokacin bakinmu da kuma ayyukan mu suke lalata auren yaranmu, aure beje ko'ina ba aita samun fitintunu, yanzu wannan kushewar da kike wa auren nan ze iya jefa rayuwar Auren ta cikin hatsari, kina maganar duk yaranki babu wadda ta auri talaka kaman Mufeeda, seki ga kaf yaran babu wanda ya samu kwanciyar hankali a gidan aure kamar ta, Sarah Auren me zuciya yafi auren me dukiya, dan Allah kidena kushe auren nan kisa musu albarka kawai "


Ita dai Mama jinsa kawai take amma sam bata ƙaunar auren nan.


Mufeeda kam murna ta dinga yi, tana faɗin
" Yaya Ammar har yana da ƙarfin daze iya bada dubu hamsin kuɗin aure na? Alhamdilillah amma me yasa be gayamin za'a kawo kuɗin ba? "
Har ta ɗauki waya zata kira shi, ta tuna wulaƙancin da yayi mata yace "mata jaririya kuma ƙwaila" fasa kiran sa tayi ta tura masa saƙo






"Yaya Ammar Jaririyar ka tayi mamakin kuɗin da'aka kawo mata, dama darajar ta ta kai haka a gurinka?
Jaririya na godiya, Allah yasaka maka da alheri, Allah ya ƙara Arziki da rufin asiri, nagode sosai Yaya Ammar ɗina"






Tana gama tura masa saƙon ta kira Yaya Amina a waya dan sunfi shiri da ita.


***************




Tunda Baba suka tafi kai kuɗin nan Ammar ya rasa meke masa daɗi daya tuna se yaji wata damuwa ta mamaye zuciyar sa, tunda ya fita da safe be kuma komawa gidan ba se dare.
Yana zuwa kuwa ya tarar da Abba a tsakar gida yana jiran sa.


Ba walwala haka ya shiga gidan, Abba yace "Yawwa dama kai nake jira, naga yau tunda ka fita sam baka dawo gidan ba, balle kaji yadda muka yi da gidan su matar ka"


Ammar a ransa yace "Ji Abba da ɗigimi wai Matata"


Ammar yace "to gani na dawo"


Abba cikin fara'ar sa yace "gaskiya Ammar iyayen yarinyar nan suna da dattako, dana ga gidan su na zata mahaifinta ze raina abunda muka kai, Amma yaita murna yana sa Albarka, dukda banga yarinyar ba naji har raina ina ƙaunar ta, Allah ya sanya muku Alkhairi, Baban ta yace ya saka watanni shida insha Allah za'ai bikin "


"wata shida Baba me nake da shi daza'a saka biki nan da wata shida?"


"Yana hannun Allah Ammar, munyi wa mahaifinta magana akan hakan yace duk abunda kake da shi ka bayar Allah ya amfana, kuma muma ba samaka ido za muyi ba zamu tallafa maka da abunda ya samu, fatanmu dai ka riƙe yarinyar nan Amana"


Shiru Ammar yayi bece komai ba, wannan wane irin lamarine yazo masa a gaggauce haka, ba shiri ba komai abubuwa se faruwa suke.


Umman Ammar ta fito daga ɗaki tana faɗin "Ai Baban Ammar a jikina ina jin Allah ya karɓi addu'armu Ammar ya dace da matar ƙwarai samun irin su ita kanta yarinyar da iyaye masu dattaku wahala yake a yanzu, nidai har raina nake son batun Auren nan Allah ya nuna mana lokacin"


Ammar bin mahaifiyarsa yai da kallo a ransa ya maimaita "wai matar ƙwarai dan basu ga yarinyar ba befi a saka zani a goye ta ba"


Shidai Ammar be kuma cewa komai ba ya miƙe ya fice ya bar gidan.


Kai tsaye ɗakin Jabir ya wuce, yana zuwa ya tarar Aminu ma yana can, yana zuwa be kula su ba ya samu guri ya zauna.
Gaba ɗaya suka bishi da kallo Aminu yace
"Mutumin ya akayi ne? Ya muka ganka a haka?"
Shiru ya musu yana jan ƙaramin tsaki, se wani huci yake bayan 'yan mintuna ya kuma jan tsaki sannan yace
"Kuɗin Aure Abba ya kaimin"


Jabir yace "what are you serious Man? Kai wallahi dani mace ne se nayi guɗa, Alhamdilillah"


Aminu yace "to kuma menene abun ɓata ran abun farinciki ya same ka sannan kazo kana cunkushe mana fuska"


Jabir yace "wait wai meyasa baka gaya mana za'a kai kuɗin aurenka ba? Wace me rabon ce ta rabauta da samun a very hardworking man as you?"


Seda Ammar ya kuma tsaki yai musu bayanin komai sannan ya ɗora da cewa "ni faruwar abun har tsoro yake bani ji yadda komai ke faruwa cikin gaggawa"


Aminu yace
"Ammar da yawa suna neman damar daka samu basu samu ba, a wannan marrar ka bawa yarinya budurwa dubu hamsin kuɗin aure iyayen ta su karɓa da murna har suce komai Allah ya hore ma ka kawo zasu baka gaskiya kayi dace"


Ammar yace "wacece budurwar? Ana gaya muku ƙwaila ce kuna wani surutu"


Jabir yace "kai Ammar kai duk wannan ne ya dame ka? Ba'a nan take ba ɗan nuna mana hoton ta mu gani mana muga wai me yasa ka damu da cewar ƙwaila ce"


"Ni bani da hotonta sedai akan dp ɗin ta" ya faɗa yana cunkusa fuska


Yana ɗakko wayar sa yaga message ɗin ta tana godiyar ya kai kuɗin auren ta dubu hamsin.


Shiru yayi yana wani tunani, buɗe what's App ɗinsa yayi ya nuna musu hoton ta na kan DP ɗin ta, ta canza hoto, iya fuskarta ne kawai akai tayi murmushi.


Aminu yace "wow Masha Allah, wallahi Ammar karkayiwa kanka sagededuwa, see fine Baby"


Jabir yace "dan Allah in baka so, ni zan ƙara dubu hamsin abani"


Harar Jabir yayi yasa hannu ya fizge wayar sa sega kira ya shigo, Ammar ya ɗaga kiran kafin yayi magana ta fara


"Yaya Ammar ɗina, bani da lafiya Amma baka kuma cemin ya jiki ba, na turo maka message bakayi responding ba, Anyway nagode sosai ban zaci zaka bada wannan kuɗin a matsayin kuɗin aure na ba, Nagode sosai Baby na"


"What!! Baby kuma?"


Ai take su Jabir suka ƙyalƙyale da dariya dan Ammar ya tsani yaga ana wannan abubuwan.


Mufeeda tace "ba cemin kai ni jariri ya ce ba, gara in maida kai Jariri kaman ni se komai ya tafi daidai, Yaya Ammar dan Allah kazo in ganka please"


"Ke ki rabu dani ki dena wannan rawar kan, Auren nan ba yuwuwa zeyi ba, ni bazan auri ƙaramar yarinyar mara Aji ba kamar ki ba bana son shirirta"


Mufeeda ta kwantar da muryarta cikin kissa da murya me ɗaukar hankali tace


" Ammar ɗina ni kaɗai, kuma Angon ƙwaila to be insha Allah, you know what? Am very lucky daga haɗuwar mu zuwa yanzu komai yana tafiya dai dai, Amma Idan har dan nace ina sonka shine bani da Aji me zakace game da Auran Sayyada khadija da manzon Allah salallahu alaihi wassalam? Idan har kace na maka ƙanƙanta da aure me zaka ce game da Auren Sayyada Aisha da manzon Allah salallahu alaihi wassalam? Haba Yaya Ammar ɗina babu rashin aji a abunda nayi fa"


Shiru Ammar yayi, yayin da Aminu yai ƙasa da murya yace Jabir "Wallahi yarinyar nan ta fi Ammar iya siyasa, kan uba a yanayin hotonta yarinya ƙarama amma tana tsara zance"


"Baby na zan kwanta bacci ka gaidamin dasu Mama, Sannan ka cewa Abokan ka kowa ya tafi gidan su abarmin kai ka huta dan Allah"








Domin gyara sharhi ko ƙorafi
Ayshercool
07063065680


✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )








*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com





ELEGANT ONLINE WRITER'S



Page 6






Shewa su Jabir sukayi, Jabir yace


"karki ji komai matar mu zamu tafi yanzu mu barshi ya huta"


Tana jin hayaniyar su ta kashe wayar ta tana murna, gaba ɗaya Ammar ransa ƙara ɓaci yayi yace "Jabir meye haka wai kuke yi, sekunsa ta fara rainani meye hakan kukayi?"


Aminu yace "kai Ammar saurara tun wuri kasan abunda yake maka ciwo, wannan yarinyar kana ganin ta a haka nan gaba in bakayi wasa ba seta dinga juya ka, dan ta fika baki kai fushin kawai ka iya da zare ido"


"Allah ya kiyaye wannan abar ta juyani"


Jabir yace "ƙyale shi Aminu ze ga wannan abar ganin idon sa, abun da zamuyi yanzu shi ne, ka bamu sunan ta zamu je ayi muku sticker da keyholder za'a haɗa da chewngum wanda zata rabawa ƙawayen ta"


"Amma bada kuɗi na za'ayi wannan shirmen ba ko?"


Aminu yace "kwantar da hankalin ka da kuɗin mu zamu yi ba, da namu zamu yi dan haka akeyi, Amma lokacin da zakayi na kuɗin naka muna gefe"


Jabir yace "Ammar dan Allah kayiwa yarinyar nan hallaci, karka watsa mata ƙasa a ido ji musamman ta kira take maka godiya akan kuɗin nan dan Allah kadena wannan fushin kaman wanda za'ayiwa auren dole"


Ammar yace "to meye wannan in ba auren dolen ba?"


Aminu yace "ka gama muzuran ka a yanzu in ka shiga hannun ƙwaila se yadda tayi da kai"


Ɗaukar wayar sa Ammar yayi ya fice ya bar ɗakin


************
Haka nan badan mama taso ba ta fara shirye2 da siyayyar kayan auren Mufeeda aka sanar da 'yan uwa da abokan arziƙi an saka ranar auren Autar baba, wasu na san barka wasu na ya akayi ita za' a mata aure yanzu bayan 'yan uwan ta seda suka fara karatu (mutane kenan komai se sunyi magana)


Ɓangaren Ammar ma shiri suka fara yi sosai,' yan uwa da abokan sa na ta taya shi ƙoƙarin haɗa kayan aure, dukda baya son auren saboda Yadda iyayen sa suka ɗaukaki auren nan ya sashi dole shima yake nasa ƙoƙarin.


Yau yayyen mufeeda duk sunzo gida da yake sukanyi haka lokaci lokaci mussman lokacin farinciki, sukai ta caccakar Mufeeda akan tana murna Ammar ya bada dubu ɗari kuɗin auren ta ita dai tai musu banza taƙi kula su.


Yaya Fadeela tace "yarinya man kaza ba dai aure ba? Namiji ko gaki gashi nan, yau shiyace yana son ka yaka ƙarke balle kuma kafi damuwa dashi, inaji Mama tana mitar zuwan sa gidan nan befi uku ba amma kin manne masa ko damuwa beyi dake ba, kuɗin aure ya rasa nawa ze kawo se dubu hamsin"


Anty Murja tace "ni ba wannan bama da ganin wannan koba a faɗa ba yafi ƙarfinki yayi miki girma maimakon ki samo dai dai ke, kin ɗakko wannan murɗaɗen kaman ɗan dambe"


Sarai Mufeeda ta gane inda zancen su ya dosa amma ta basar ta zumɓura baki tace
"ni wallahi bemin girma ba ai ba a bayana zan dinga goya shi ba, ina ruwana da girman sa"


Fadeela tace "Ji shashasha bama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login