Showing 18001 words to 21000 words out of 105124 words
tasan me'ake nufi ba se ƙoƙarin rashin kunya, zaki cu uban ki kije ki aure shi, zakiyi bayani yadda ya kamata ba dai aure ba? Idan baki goya shi a bayanki ba zaki gane in kin shiga"
Haka suka dinga tsorata ta, Yaya Amina tace "haba Anty Murja dan Allah, wallahi abunda kuke be dace ba ya zaku dinga razana ta, so kuke tace ta fasa? Dan Allah ku dena"
Mufeeda tace "ƙyale su Yaya Amina bazan fasa ba suyi tayi nidai ina son Yaya Ammar sosai"
Ita Amina Tausayin Mufeeda takeji sosai, rayuwar da suka yi tare su Fadeela ba suyi ta tareda Mufeeda ba.
Mama ta shigo ta same su, suka dinga caccake mufeeda wai tayi rashin kunya ga rashin aji yadda take rawar kai akan Ammar, gashi shiba Wani shahararren mutum ba amma se girman kai da isa a cikin sa.
Ƙarshe mufeeda se bar musu ɗakin tayi, dan taji dana sanin zuwan yayyen ta gidan nan.
Yaya Amina ta fita tsakar gida zata je kitchen ta zubo Abinci, ta jiyo sheshsheƙar Mufeeda a ɗaki. fasa zuwa zuba Abincin tayi ta shiga ɗakin ta samu Mufeeda ta haɗa kai da gwiwa tana kuka cikin tausaya wa Amina tace "Mufeeda meyasa kike kuka?"
"Yaya Amina daga ke se Baba ne kawai kuke goyon bayana, Wallahi yaya Amina dana san dagaske Mama zata ƙi Ammar dana haƙura, wallahi ban san yadda akayi nake sonshi haka ba, baki ji yadda nake ji a zuciya ta ba ko sunan sa aka ambata, Amma Mama da su Anty Murja se hantara ta suke yi, idan har Mama bata son auren nan nasan idan nayi bazan zauna lafiya ba"
Mufeeda ta riƙo hannun yayarta tace "kin san wani abu Yaya Amina"
Amina ta girgiza kai cike da Tausayin Mufeeda
"Yaya Amine karki gayawa kowa, nasani Nina ke son Ammar bashi yake sona ba, Amma kullum idan na roƙi Allah abunda yafi Alkhairi se inji ina ƙara ƙaunar sa, idan na roƙi Allah ya zaɓa min abunda yake alkhairi ba son zuciya ta ba se inga al'amura na gudana yadda yakamata, ban taɓa tunanin Ammar ze amince ya kawomin kuɗin auren sa ba a haɗuwa uku rak da muka yi ba, ina da damuwowi da yakamata in tattauna da Mama ko Anty Murja amma sunfi karkata ga kushe abunda da nake so, yaya Fadeela harda wai zan auri matsiyaci ɗan napep, naso in mayar mata amma kinga ta girmeni sosai kuma Mama zata min faɗa, Amma ita soyayyar gaskiya ai ba ruwan ta da wannan, dukda Aurena da Ammar be saɓawa addini ba, Yaya Amina dan Allah ki sani a cikin Addu'arki"
Rungume Mufeeda Amina tayi tace "Autar Baba insha Allah zan ta yaki da addua, Sannan ni har ga Allah ina sonki da Ammar dan ni banga aibunshi ba, musamman yana da nutsuwa ba irin mashiritan matasan nan bane, me ake da namiji mara aji, Ai Ammar ɗin ki yana da class ne shiyasa yawan dariya ai bashi da amfani, karki damu da ana cewa baya fara'a yana da izza wallahi indai zaki masa biyayya kiyi Amfani da wata kissar kin gama da shi, ki dena kuka kinji"
Murmushi Mufeeda tayi tace "shiyasa nake ƙaunar ki Yaya Amina"
Bayan tafiyar su Yaya Fadeela Yaya Amina bata tafi ba saboda mijin ta bezo ɗaukar ta ba, Mufeeda kuma ta tafi Islamiyya.
Amina tace "Mama be kamata ki dinga biye su Yaya murja ba akan auren Mufeeda, Mama wasu suna nan saboda se sunyi boko sun bawa shekara talatin baya babu aure, Kuma abunda auta tayi na faɗar aure take so ba tayi laifi ba, da kuma zuwa tayi ta ɗakko muku magana fa? Mama dukkanin mu 'ya' yankine da aurar da Mufeeda cutar da itane Baba baze yadda ba, ɗazu fa kuka ta tafi ɗaki tana yi, bata jin daɗin yadda kuke kushe Ammar dan Allah mama kidena biye wa su Fadeela "
Ajiyar zuciya Mama tayi tace
"ba ƙin abun nake ba Amina Ni gani nake kaman yaron nan zata sha wuyar zama dashi ya mata girma nesa ba kusa ba, zuwan sa fa uku kacal gidan nan sam bata gaban sa ko waya banga suna yi ba"
"Mama kina tunanin akwai hijabi tsakanin mu da addu'ar kine? Tun muna yara kike mana addu'ar miji nagari, ki sawa ranki wannan shi ne mafi alkhairi a gurin auta, Mama ba kuyi tarbiyar mu akan kwaɗayi ba da son abun duniya, kuma a haka muka tashi, shiyasa kika ga Auta ma abun duniya be dame ta ba, duk abunda ta ɗaga tace tana so, to tana son sa dagaske, dan Allah mama kija Auta a jiki tun yanzu itama ki fara nuna mata zamantakewa kaman yadda muma kikayi mana, in ba haka ba ta fara iƙrarin zata fasa tunda bakya so, kuma idan ta fasa mekike tunanin za tayi gaba? "
Ajiyar zuciya Mama tayi dan jikin ta yayi sanyi tace
" hakane Amina, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Amma ni auta da wanne ma zan fara mata ne? Ni ƙanƙantar ta nake gani, ta ina zan fara nuna mata dabarun zaman auren?"
Dariya Amina tayi tace " ta inda kika fara mana"
**************
Abokan Ammar suka tambayeshi cikakken sunan Mufeeda saboda sticker daza'ayi musu amma yace be sani ba
Aminu ya sha mamakin abunda Ammar ya faɗa, Jabir yace "Ammar wannan abubuwan fa da kake yawa ne, haba dan Allah ya za'ayi ace baka san cikakken sunan ta ba?"
Ammar yace "to nasani ne? Nafa gaya muku da haɗuwar mu a titi da saka auren nan haɗuwa uku ce zuwa huɗu rak ta yaya zan san sunan ta, nidai naji ana ce mata kome? Muneefa ko Mufeeda i thinks Mufeeda ne"
Aminu ya riƙe haɓa yace "tirƙashi yau nake ganin ikon Allah, Sunan nata ma baka sani ba, Allah kaɗai yasan dalilin daya haɗaku, Allah yasa itace maganin wannan haɗe ran naka"
Jabir yace "Ammar ka kira ta ka tambaye ta dan Allah"
Ammar ya kallesu "Allah ya kiyaye"
"to bamu mu semu kira ta"
Ammar ya miƙa musu wayar sa, Jabir ya ɗakko wayar sa ze ɗau lambar Mufeeda, Ammar yace
"ka kira ta a waya ta"
Haɗa ido Jabir suka yi da Aminu suka ƙyalƙyale da dariya
Ammar ya ƙara haɗe rai dan baya son raini.
Mufeeda kam tana kitchen tana wa Mama girkin dare wayarta ta fara ringing, tana ganin lambar Ammar jikin ta na rawa ta ɗaga wayar
"Hello Yaya Ammar ɗina"
Jabir yace "Ahh yi haƙuri Amaryar mu bashi bane, fatan kina lafiya?"
Yamutsa fuska Mufeeda tayi, tace "ina Yaya Ammar ɗin?"
"yi haƙuri shi yace a kiraki, cikakken sunan ki yace ki gaya mana akwai abunda za'ayi da shi"
Tura baki tayi cikin shagwaba tace "shi meyasa baze tambayeni da kansa ba? Dan Allah yana ina?"
Jabir yace "taɓ lallai abun naku nayi ne, kai ungo wayar ka"
Ammar ya haɗe rai yace "idan bazata faɗa ba shikenan ba zan karɓa ba, bana son shashanci da yarinta"
Mufeeda na iya jiyo abunda Ammar yace, ji tayi hawaye na ƙoƙarin zubo mata jiki a sanyaye tace
"Shikenan nagode sosai, jin muryarsa da nayi ya tabattar min yana lafiya nagode Allah, my regards to him"
ta kashe wayar ta.
Tausayin ta ya kama su, Aminu yace "A gaskiya Ammar ka canza salon ka, masoyi ko mahaukaci ne be cancanci wulaƙanci ba, ji yadda yarinyar nan ke murna tana ɗoki a baka waya, Amma kalli abunda kayi mata haba Ammar"
Jabir yace "Ammar irinka idan Soyayya ta tashi kama ka ko, se mutum ya tausaya muku, irin wannan halin 'yan matan mu na Hausawa suke tsoro shiyasa basa iya nuna soyayyar su ga maza, Ammar so baya duba girma da shekaru, da yana dubawa da yayi wa Mufeeda Adalci daba ta faɗa soyayya da mutum irin ka ba"
Sosai suka dinga caccakewa Ammar shi kuwa yayi shiru ya ƙyalesu ko uffan be ce musu ba.
*************
Daƙyar Mufeeda ta ƙarasa girkin nan ji take kaman an ɗora mata dutse a kirjin ta, bata taɓa zaton zata so wani ɗa namiji ya dinga yi mata wulaƙanci haka ba, yayin da wani sashi na zuciyar ta ke ƙara azalzalarta da ƙaunar Ammar.
Mama ce ta kira Mufeeda ɗakin ta suka zauna, Mama tace
"Mufeeda ya Saurayin naki?"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Mama tace
"yaushe kuma kika fara jin kunya ta, ɗago kanki magana za muyi, naga tunda aka kawo kuɗin nan bezo ba meyasa? Anya kuwa yana sonki"?
Da sauri Mufeeda ta ɗago tace "yana sona mana"
"to Amma ai ya kamata ai ya dinga zuwa tunda aure zakuyi, da haka zaku fuskanci juna tunda zama zakuje kuyi na dindindin"
"Mama kin san yanayin sana'ar sa baya samun zama"
Mama tace "dukda haka idan har kana son abu yana da kyau ka dinga zaga shi kana ganin sa, yana da kyau ya dinga zuwa yana ganin ki"
Nan Mama ta dinga yiwa mufeeda nasiha game da rayuwar aure da kuma mahimmancin haƙuri, mufeeda a ranta tace
"Mama na kenan duk wannan abubuwan na sansu tun abaya da kike gayawa su Yaya Fadeela na haddace su, amma ta yaya zan gaya miki halin da nake ciki nasan tabbas idan na gaya miki abunda ke faruwa zaki iya soke maganar auren nan ni kuma ina ƙaunar Ammar" A zahiri kuwa shiru tayi tana sauraron Mama, seda ta gama sannan ta sallami Mufeeda.
Ammar daya koma gida yana ta tunanin maganganun su Jabir, idan ya tuna yadda tayi magana a sanyaye daga ƙarshe se yaji babu daɗi Tausayin ta ya kama shi, gefe kuma zuciyar sa tace "ai ba kai kace kana son ta ba, koma menene ita taga zata iya"
Ya zauna yana hira da Umman sa a tsakar gida, Umman sa bata da zance se tsare2 da shirin yadda bikin tilon ɗanta namiji ze kasance.
Umma tace "Ammar yaushe zaka gurin sirikata ne? Ɗazu naje kasuwa naga wata sarƙa me kyau na siyo da sauran kaya a saka mata a lefe"
Ɗan taɓe baki yayi yace
"kaman kin san tana yawan cewa a gaishe ki"
"Allah sarki yarinyar kirki, Amma baka taɓa gayamin ba, nikam Ammar ka nunamin hoton ta mana"
Be ce komai ba ya nunawa Umma hoton mufeeda akan dp ɗin ta, Umma ta karɓa tai shiru tana kallon ta a ranta tace "tabbas yarinya ce ƙarama, Amma ina fatan ta zama mace tagari sannan sanyin idaniya ga ɗana"
A fili tace
"tubarkallah Ammar sirikata ba dai kyau ba masha Allah, Ammar dan Allah ka riƙe yarinyar nan da Amana, jikina yana bani ita alkhairi ce a tare da kai, banda hantara da tsangwama dan Allah Ammar na san halin ka"
Halima ce ta fito daga ɗaki tana faɗin "Umma in ganta"
Ammar ya karɓe wayar sa ya shige ɗaki ba tare da Halima ta ganta ba.
Koda Mufeeda ta koma ɗakin ta, kuka ta zauna tana yi, tana goge hawaye gaba ɗaya ranta babu daɗi, wayar ta ta janyo zata kira Yaya Ameena taga miss Calls ɗin Ammar, take wani farinciki ya mamaye ta amma se wata zuciyar tace mata
"ƙila ma abokan sane suke kira bashi ba" tayi tsaki zata ajiye wayar saƙon Ammar ya shigo wayar ta
"Meyasa bakya ɗaga waya?"
Kallon message ɗin take yi ya kuma kiran ta, ɗagawa tayi tasa a kunnen ta tayi shiru, ya saba idan ya kirata da karsashin ta take ɗaga wayar sa, hakan yasa shi yin Sallama dan tabattar da ko ta ɗaga, a hankali ta amsa sallamar tasa
"har yanzu baki da lafiyar ne?"
"lafiya ta ƙalau"
Ammar yace "Meyasa na kira baki ɗaga ba"
Kawai ta fashe da kuka, tsaki Ammar yayi yace "meya haka? Meye na kuka kuma? Kinsan abunda ba naso kenan"
"Yaya Ammar ji nake kaman inje in cewa Baba na fasa Auren nan"
Maimakon yayi farinciki da abunda tace se yaji ƙirjinsa yayi mummunar bugawa da ƙarfin gaske
Cikin kuka ta cigaba da magana
"Yaya Ammar meyasa kake wahal dani haka? Yaya Ammar ba laifi na bane da nace ina sonka, Ana ta tambaya ta me muke shiryawa game da shirin biki bani da amsa ko ganin ka kaƙi kazo inyi"
ta kasa ƙarasa maganar se fashewa da ta sake yi da kuka, shiru Ammar yayi yace
"Zaki gayamin sunan ne ko zaki cigaba da kukan?"
Cikin fushi tace "bazan faɗa ba ɗin kuka zan cigaba, kuma Insha Allah sena dena sonka tunda baka da tausayi" ta kashe wayar ta.
Sam irin wannan matsalolin Ammar yake gudu shiyasa sam baya soyayya yake mata kallon shirita, musamman Soyayya da ƙanƙanuwar yarinya, banda wannan dalilin akwai abunda zesa yarinya ƙarama kamar Mufeeda tayi masa tsawa haka? Ƙwafa yayi ya ajiye wayar tare da jan ƙaramin tsaki
Daga baya mufeeda taga rashin kyautawar abunda tayi ta zauna ta tsarawa Ammar message ɗin ban haƙuri ta tura masa.
Yayi mamakin abunda tayi beyi zaton zata bashi haƙuri ba, maimakon yayi responding seya shareta daga nan bata ƙara neman sa ba shima kuma be ƙara neman ta ba.
Baba ya biyawa Mufeeda kuɗin WAEC da NECO tana ta zuwa extra lesson, duk yadda suke da Fatee da irin surutun Mufeeda bata gaya mata Ammar ya kawo kuɗin Aure ba.
Mazewa kawai take yi, bata jin daɗin yadda bata samun damar jin muryar Ammar, sam baya nuna damuwar sa game da ita, amma ta dake ta watsar da shi ta ci gaba da Addu'a, dukda ba ƙaramin azabtar da zuciyar ta take ba, Amma hakan baya hana ta ta tura masa saƙonin barka da safiya, barka da juma'a ko kuma saƙonin kwanciya bacci tare da yi masa addu'oin tsari.
Ammar yana gani amma baya tankawa, amma duk lokacin da ya ga saƙonin yana jin daɗi, duk lokacin daya ga tayi jinkirin turo masa saƙo ya dinga duba wayar sa kenan, Amma fa baze iya ce mata ya gode ba, ko kuma yaji daɗin ganin saƙon ba.
Mama tayi mitar tayi tambayar harta gaji akan dalilin da yasa Ammar baya zuwa, ta zuba mata ido tana taya 'yar tata da addua, dan sam ta kasa gane inda wannan al' amri ya dosa ga tana yin magana mahaifin Mufeeda zece tana sukar lamarin auren ne.
Sam walwalar Mufeeda tayi baya, duk ta rame.
Yauma tana kwance akan gadonta ta zubawa fankar dake saman ɗakin ta Ido Mama ta shigo ɗakin ta kalleta tace
"to seki tashi yau yaga damar zuwa, yace ai masa sallama dake"
Mufeeda najin haka ta miƙe zaune da sauri, Mama ta kalle ta ta girgiza kai, Mufeeda bata taɓa tunanin Ammar zezo ba, ba tayi zatonsa a wannan lokacin ba.
Mufeeda ta shiga ta wanke fuskarta, ta zira doguwar rigar material baƙi da ja tayi rolling da mayafi baƙi ta fesa turare ta fita.
Yau shida wani ta ganshi sunzo wanda bata san wanene ba, suna ƙofar gida a tsaye, a hankali ta ƙarasa inda suke ta kalli abokin nasa tace "ina wuni?"
Jabir ya kalleta yace "lafiya ƙalau Amaryar mu, ya haƙuri da abokin mu?"
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
Ammar ya lura tayi rama kome ke damunta oho? So yake su haɗa ido amma taƙi dan ƙwalla ce a idon ta, a hankali tace
"mu shiga ciki"
Jabir yace "ina nan a sha soyayya lafiya"
Hararar Jabir Ammar yayi sannan yabi bayan Mufeeda cikin takunsa na ƙasaita.
Cikin sitting room dake harabar gidan ta shiga yana biye da ita.
Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren sa, Guri Ammar ya samu ya zauna, Mufeeda ta samu guri itama ta zauna.
Ba tare da ta kalle shi ba tace
"ina wuni?"
"lafiya, ya Mutan gidan?"
Goge hawayen ta tayi tace "suna lafiya"
Ɗan ƙura mata ido yayi sannan yace "ke wai ke kuka baya baki wahala ne? Me kuma nayi miki yanzu?"
Tura baki tayi tace "ni meye ma ba kayi min ba, Yaya Ammar yaushe rabon da in ganka? In tura maka saƙo babu reply, baka kira na a waya, ji nake kaman in haƙura kowa cemin yake baka sona"
Ƙura mata ido yayi yadda take magana tana tura baki, tana shagwaɓe fuska tana wani lanƙwasa wuya kaman karta dena.
Ammar ya kalleta yace "Aini dama ban iya soyayya ba, ban san yadda ake yi ba, ke kikace kina sona, ni dama irin wannan shirmen ƙuruciyar ne bana so shiyasa nake son in auri babbar mace wadda ta gama hankali"
Murmushi tayi dukda fuskarta da guntun hawaye tace
"Hmmm ni bani da hankali kenan?"
"ina me hankali ze zauna yaita kuka kaman ƙaramin yaro koda yake ai yarinyar ce, dan baki fi a sa zani goya ki ba"
A ranta tace aikuwa zaka ga yarinta yadda ya kamata, Sosai tayi dariya tace "daza'a goya ni da naji daɗima, dana dena kukan"
Ɗan murmushi yayi abunda bata taɓa gani yayi kenan ba, dama idan yayi murmushi yana matuƙar yin kyau haka?
Leda ya miƙa mata bata karɓa ba tace "menene wannan?"
"karɓi ki gani mana"
Hannu tasa ta karɓa, shi kuma ya miƙe ze tafi ita ma ta miƙe da sauri
"Haba Yaya Ammar mintunanka nawa zaka tafi? Ni dan Allah karka tafi yanzu"
Ɗan tsuke fuska yayi yace "Zaki fara ko?"
"Yaya Ammar yaushe zaka dawo?"
"Se wani lokacin"
"idan ka tafi seka daɗe baka zoba fa"
"Me zanzo inyi miki? Kallon wannan shiriritar taki da yarintar ta kokuwa?"
"Nice nake shiritar ko? Shikenan ka gaida Mama, Nagode sosai Allah ya ƙara Arziki"
Be amsa ba ya juya ze fice tace "Yaya Ammar"
Ya waigo, ta tako gaban sa, ta ɗan ɗauke idon ta daga kallon cikin idon sa tace
"I Love you so much My Ammar" ji yayi zuciyar sa ta shiga bugawa da sauri da sauri.
Ta raɓa ta gefen sa ta wuce
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨
( *Sai Mata* )