Showing 96001 words to 99000 words out of 105124 words

Chapter 33 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16358

nan maza ki tafi gida, Insha Allah da safe zan dawo, tunda nidai nasan ban aikata laifin komai ba"


Mufeeda ta fashe da kuka ta riƙe rigar Ammar tace "Wallahi sedai a haɗa dani, ni Ammar ɗina mutumin kirki ne Officer dan Allah, wallahi bashi ake nufi ba"


"Yi haƙuri 'yan mata maza ki tafi gida, yana division ɗin gangare zamu tuhume shi"


"Maza ki tafi gida dare yanayi, sannan karki sanar da kowa se zuwa gobe in Allah ya kaimu inga yadda hali zeyi"


Aka saka Ammar a motar ' yan sanda, suka tuƙa Napep ɗinsa suka tafi da shi.














Kai masha Allah, ban san haka kuke son book ɗin nan kuke following ɗinsa ba, kwana biyu da ban posting ba nasha kira a waya, ina godiya ta musamman Allah ya bar ƙauna, kar' amanta in an karanta ayimin share dan Allah ba dan halina ba
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏


Wanda sukamin magana akan voting na gasar dana shiga, se an kammala gasar ne za'a bada link ɗin da fans zasu shiga suyi mana voting, nagode da kulawar ku




Domin gyara, sharhi, ko shawara, ƙofa ta a buɗe take
Ayshercool
07063065680..✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com


Please follow me on Wattpad, vote and Comment


ELEGANT ONLINE WRITER'S


NOT EDITED


Page 29






Gaba ɗaya jikin Mufeeda rawa yake, ji take tamakar a mafarki, wace irin masifa ce wannan? Daga wannan se Wancan
"Ya Allah ka fitarmin da mijina"
Haka ta tari Abun hawa ta tafi gida, unguwarsu baƙi ƙirin saboda duhu, har ƙofar gidanta me Napep ya kai ta.


Safa da Marwa Mufeeda ta dinga yi a ɗaki ta rasa me ya kamata tayi, se sharce hawaye take tana tunanin ya Ammar ze iya kwana a ceil, waye yai masa wannan sharri haka?
Tayi tunanin ko ta kira Baba a waya ta gaya masa, seta tuna Ammar yace karta gayawa kowa.
babu Alamar Bacci a tattare da Mufeeda, tai alwala dinga salla tana kai kukan ta ga Allah, har dare ya raba kuka Mufeeda take sosai ga tsoro da take ji.


Tana zaune a tsakar ɗaki ta dunƙule a guri ɗaya tana kuka, ji tayi ana buga gate ɗin gidan, da sauri ta miƙe ta koma kan Gado tana rarraba ido, cigaba da bugun aka yi, wata zuciyar tace idan kuma Ammar nefa ya dawo, da sauri ta sakko daga kan gadon ta buɗe falon ta fito tsakar gida cikin sanɗa.


Buga ƙofar aka cigaba dayi, cikin sanɗa take tahowa ta tsakanin gate da garu Mufeeda ta leƙa yanayin inuwar wanda yake tsayen ba tayi kama data Ammar ba.


Da gudu ta koma ta rufe falon ta, ta koma ɗaki ta kulle ƙofa, ta hau gadon ta ta dinga Karanto Addu'oin da suka zo bakin ta.


Yadda Mufeeda taga rana haka taga dare, cikin tashin hankali ta wayi gari.


A gurguje tai wanka ta shirya, ta girka Abinci ta rufe gida ta fice.


Station ɗin da'aka kai Ammar ta tafi, tun ƙarfe takwas na Safe ta tafi, taita Jira a station ɗin, se ƙarfe Goma aka fito da Ammar daga shi se dogon wando da vest, da alama an dake shi ma, sedai cikin Jarumta yai mata murmushi yace


"meyasa kikayi Sammako haka?"


Kuka ta fashe da shi Sosai, ta kalli ɗan sandan tace "Yallaɓai wai baku gama binciken ba? Dan Allah ku sake shi wallahi Yaya Ammar mutumin kirki ne"


Ɗan sandan yace "Ke kije gida kizo da wani Babba daga gidan ku, ko baban ku ko wani babba, 'yar mitsitsiya dake ba dake za muyi magana ba"


Mufeeda tace "haba Yallaɓai cewa kukayi zakuyi bincike ku sake shi, wallahi mijina mutumin kirki ne"


Zare ido ɗan sandan yayi yace "Miji kuma? Ke yanzu wannan ne mijin ki, kai Ashe banda tuhumar da muke maka, akwai buƙatar Human right su bincike ka, wannan ai child Abuse ne Wannan Yarinyar ce matarka?"


Banza Ammar yayi masa ya kalli Mufeeda yace
"Ina fatan kinyi bacci jiya, dan nasan halinki"


"Wallahi yaya Ammar banyi bacci ba, aka dinga bugamin gida jiya a tsorace na kwana ga hankalina yana kanka" tai ƙarasa maganar tana kuka.


"ki kwantar da hankalin ki, ki kira Aminu a waya ki gaya masa ina nan"


"Yaya Ammar, Har yanzu basu gama binciken ba? nasan ba zaka aikata haka ba"


"Mufeeda ni kaina na kasa gane kan lamarin nan, har yanzu banga fasinjojin da ake zargin nayiwa fashin ba, sun tirsasani in amsa laifina naƙi, Amma ki kira Aminu"


"Yaya Ammar, ba zamu gayawa su Baba ba"


Girgiza mata kai yayi yace "ba yanzu ba, kina gaya musu hankalin su ze tashi, ki bari mu ga yadda hali zeyi"


Haka Mufeeda ta koma harabar station ɗin ta kira Aminu ta sanar da shi halin da'ake ciki, Aminu ya kaɗu sosai da jin Abunda Mufeeda ta gaya masa


Yace "ki kwantar da hankalin ki Mufeeda, gani nan zuwa Insha Allah, Amma abun da mamaki gaskiya"


Befi mintuna Arba'in ba sega Aminu yazo station ɗin.


Ya shiga ya samu officer on duty, suka gaisa Aminu yace
"Yallaɓai nazo ne akan case ɗin ɗan uwana da aka kama"


Ɗan sandan yace "Eh mun kama shine saboda muna zarginsa da haɗa kai da 'yan iska suka yi wa fasinjansa fashin waya da kuɗaɗen sa, munyi2 yaƙi ya amsa laifin sa"


Aminu yace "Amma Yallaɓai ai se mutum ya aikata laifi sannan ze amsa yayi, sannan wanda kuke zargin nan da iyalinsa da mutuncin sa beyi kama da wanda ze aikata wannan laifin ba kag.....


"Kai zaka koyamin yadda zanyi aikina ne? Su mutanen banza a fuska ake gane su?" ɗan sandan ya katse shi


Aminu yace "A'a Allah yabaka haƙuri, yanzu meye abunyi? Ina so abani belin sa"


"zamu bada belinsa amma zaku biya yaron da akayiwa Fashi kayan sa, yaron ɗan makaranta ne yana school yanzu amma in anjima zezo, in bahaka ba mu miƙa ku kotu"


"Amma yallaɓai abunda ba'a tabbatar ba, har a yanke masa wannan hukunci haka"


"kaga idan baku shirya karɓar belinsa ba, zamu tura ku kotu a satin nan kuma kasan hukuncin fashi da makami za'a yanke masa"


Aminu yace "Shikenan ina jinka meye abunda za'a biya yaron?"


"Naira dubu ɗari da goma ne abunda za'a biya"


Da sauri Mufeeda ta ɗago kai ta kalli ɗan sandan, idon ɗan sandan kawai ze nuna maka rashin imani, yanzu ace da ire iren wannan bara gurbin 'yan sandan a cikin Al' ummar mu ta ina za'a zauna lafiya.


Mufeeda tace "Yanzu kai ko tsoron Allah ba kaji ba, dubu ɗari fa saboda mugunta, wallahi se Allah ya saka mana, duk wanda yake da hannu a cikin yiwa mijina sharri se Allah ya wulaƙanta shi, idan da haɗin bakin ku Insha Allah sekun rasa aikin"


"Ke ni kike gayawa haka? A gaban hukuma fa kike"


"Hukumar banza da Wofi, Allah ya Tsinewa hukumar indai irin wannan ce, Azzalumai kawai"


"Ke idan baki wasa ba sena saki a ceil na koya miki hankali, mutuniyar Banza kawai"


Aminu na ƙoƙarin rarrashin ɗan sanda, amma Mufeeda ta hasala ƙarshe tace


"Kai ka isa kasani a ceil, wallahi ka sani a ceil seka rasa aikin ka har gaban Abada, indai Alfarma ce nima inada wanda zasu tsayamin a fitar da mijina, sannan a hukunta ku"


Da ƙyar Aminu yasa Mufeeda tayi shiru yasa ta tafi gida, dan indai tana nan ƙarshen ta Ammar baze fita a yau ba, seda aka kai ruwa rana Aminu yaita fama sannan aka bari Aminu yaga Ammar, Aminu ya gaya masa abunda suka ce, Ammar yace


"shikenan, Mufeeda ta ɗau wayata tayi maka transfer ɗin dubu tamanin da biyar, su kenan a Account ɗina, dama ina tara kuɗinne saboda in fara yiwa Mufeeda siyayyar haihuwa, ka ciro ka basu in bar gurin nan, na barwa Allah"








Mufeeda na Adaidaita sahu zata koma gida tana ta kuka a Napep ɗin, Aminu ya kira ta ya sanar da ita abunda Ammar yace, tace
"to bari in ƙarasa gidan, se in turo maka"


A titi ta sauka ta biya me Napep kuɗin sa, ta fara tafiya sedai tana zuwa bakin layin taci karo da motar Alhaji Idris yana zaune akan motar, yana ganin ta ya sakko da Ƙaton cikin sa yana wangale mata baki yace
" 'yan matan daga ina haka? Naga kamar kina kuka, da safe naga fitar ki, shine na zauna ina jiran dawowarki"


Shiru tayi masa tana ƙoƙarin raɓawa ta gefe ta wuce, amma ya sha gaban ta yace
"Naji labarin ashema mijin naki ɗan ta' adda ne, yana hannun 'yan sanda, matsalar Auren mutane irin mijin nan naki kenan, ki kwantar da hankalin ki, kici Arziki ki barshi a inda yake, ni me ƙaunar kine, tunda an riga an kama shi ki manta da shi kawai"


Cike da ɓacin rai Mufeeda tace
"Kaji labari ko kuma kasa aka kama min Miji saboda son zuciyar ka? , kuma kasan baya gida kazo gidana cikin dare kana ƙwanƙwasamin ƙofa, kasa an cajemu kuɗi masu yawa, to insha Allah Ammar baze ƙara kwana a hannun hukuma ba, ze fito, kuma kasani shi Allah baya bacci idan har dasa hannun ka akan abunda ya samu mijina, ko bance komai ba Allah yana kallon ka"
Ta ƙarasa maganar cikin hawaye, ta raɓa gefen motarsa ta wuce, ya girgiza kai yace
"wannan Yarinyar akwai shegen taurin kak, baki da rabo amma muje zuwa da kanki zaki kawo kanki, dan talauci masifa ne, sannan bazan iya haƙura da yarinyar nan ba"


Mufeeda tana zuwa gida ta turawa Aminu kuɗin nan, tana kuka gami da tausayin Ammar ta tura kuɗin nan. Ammar yana matuƙar ƙoƙari da gwagwarmayar neman halak, ya tara kuɗinsa da ƙyar beci ba be sha ba, A banza an raba shi da haƙƙin sa, sosai ta dinga kuka tana tunanin wannan wane irin zalunci ne haka?


Bayan ta tura kuɗin ne ta shiga kitchen ta duba me zata girkawa Ammar kafin ya dawo, kayan Abincin su duk sun ƙare, ranar daza'a kama shi yace mata tayi masa list ɗin abunda ya ƙare ya siyo, Amma wannan ƙaddarar ta haushi.








Aminu ne ya cika kusan dubu Arba'in sannan kuɗin suka cika ya biya, da zasu taho daga station ɗin Ammar yace a bashi mukullin Babur ɗinsa, amma suka ce ba zasu bashi ba, zasu riƙe Babur ɗin se sun kammala bincike.




Mufeeda ta shiga tana duba kitchen, Taliyace da ita guda biyu ta ɗauki ɗaya ta dafa, tana da sauran miya ta gyara ta, ta zuzzuba a Flask ta ajiye masa tana dakon dawowarsa, se la'asar sannan taji ana knocking ɗin gate, da sauri ta tashi taje ta buɗe, Ammar ne shida Aminu, suna shigowa Mufeeda ta rungume Ammar tana kuka tace
"Allah ya saka mana Yaya Ammar, Allah ya ƙwatar maka haƙƙin ka, duk wanda yayi maka sharrin nan Allah ya saka maka"
Sosai suka bawa Aminu tausayi, Mutum me ƙaramin ƙarfi kamar Ammar ya tara 'yan kuɗaɗen sa da ƙyar Amma lokaci ɗaya a raba shi dasu abun da tausayi.


Aminu ya Jajanta musu, Sannan yace Insha Allah ze cigaba da bibiyar case ɗin a samu Ammar ya karɓi babur ɗinsa, Ammar yayi masa godiya da irin gudunmuwar da ya basu.


Ammar yayi wanka ya fito amma Mufeeda kuka take bata dena ba, ya zauna ya dinga rarrashinta, shi yanzu babban abunda ya dame shi shine babur ɗinsa da'aka riƙe, da Allah ya dogara da babur ɗin nan ya dogara, gashi kusan komai nasu na Abinci ya ƙare, ya daɗe yana tara kuɗaɗen sa gashi dare ɗaya babu su.


*******************


Saima ta fara samun Sauƙi, tunda akayi wannan sa'insar tsakanin kawunta da gwaggonta, gidan mariƙanta babu wanda ya sake zuwa duba ta, gwaggonta ce kawai a gurin ta take ta kula da ita se sauran wanda ba'a rasa ba, Jabir ma ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa, ya samu Nutsuwar ci gaba da neman Auren Fatiyya.


Da'aka Sallameta tabi gwaggonta gidan ta, dukda itama me ƙaramin ƙarfice ga nata marayun Amma haka ta tafi da Saima tace Allah baze hanata yadda zata yi ta riƙe su gaba ɗaya ba.


******************


Rayuwa ta fara yiwa su Ammar wahala, da ƙyar yake iya samo abunda zasu ci inya fita, wataran sedai ya samo abunda Mufeeda zata ci shikuma ya haƙura.
Duk wata Sana'a da Ammar zeyi ta ƙarfi dan ya samu ya riƙe gidan sa yanayi komai ƙasƙancinta, Cikin Mufeeda ya shiga wata na biyar, ga wani irin yawan cin Abinci da take yi.


Duk Abunda ya kawo ya bata, bata raina wa hannu biyu take karɓa da murna tana Godiya koda kuwa abun be mata ba.
Itace ma take ƙoƙarin kwantar masa da hankali.


Gari ya waye da Safe, Ammar yana kallon ta ta ɗakko tuwon masara ta yayyankashi ƙanana tasa masa gishiri ta zauna tana cin Abunta da uwar safaiyar nan, saboda babu abunda zasu ci da Safen, tana yi tana kallon bollywood da suke wani shiri, yadda aketa sarrafa Naman kaji, tai shiru tana kallo gwanin ban tausayi da alama tana son ci ne. Ammar ji yayi kamar yayi kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi.


Ammar a rayuwar sa idan akwai abunda ya tsana be wuce ya keta bullensa yayi roƙo ba, tun yana ƙarami yake da wannan ɗabi'ar, idan har kaga ya nemi taimakon wani sedai idan ya rasa yadda zeyi ne abubuwa sunyi matuƙar ƙure masa


A hankali ya kalli ta yace "Mufeeda"
Ta juyo ta kalle shi, tare da yi masa murmushi tace
"Na'am my sugar"
"Dan Allah kiyi haƙuri, ni kaina bana jin daɗin halin da muke ciki, a halin da kike ciki be kamata ace kina cin wannan Abincin da sassafen nan ba, Dan Allah ki ƙara haƙuri Mufeeda, sannan naji daɗi da kika rufamin Asiri baki gayawa kowa halin da muke ciki ba, Insha Allah komai ze wuce"
Ya ƙarasa maganar kamar zuciyar sa ta fashe dan ɓacin rai.


Mufeeda tayi masa shiru ta cigaba da cin Abincin ta, tuwon data ci ma ba ƙoshi tayi ba, taci ta ƙarasa da ruwa, ta kalle shi tace
"Mijina, idan har na gujeka kona ɗaga maka hankali saboda yanayin da muke ciki Allah ma baze barni ba, duk abunda ya same ka ni ya sama, lokacin da kake samu dukda ba ƙarfi ne da kai ba, daidai gwargwado babu abunda baka bani na jin daɗin rayuwa iya ƙarfin ka, to wani dalili ne zesa in ɗaga maka hankali a yanzu, Jarrabawa ce Allah ne ya jarabce mu ina fatan Allah ya kawo mana mafita "


Shiru Ammar yayi yana kallon ta, ya kasa cewa komai.


"Yaya Ammar rufin Asirin ka nawa ne, Ina sonka Yaya Ammar fiye da yadda kake tunani, zan iya zama da kai a duk halin da kake ciki,saboda haka duk abunda ka kawo ka bani zan karɓa inyi Amfani da shi komai ƙanƙantar sa, sannan ina Amarya lokacin da su Baba suka zo sun ban dubu Goma, ban gaya maka ba saboda nasan zakamin faɗa kace meyasa na karɓa, shiyasa na haɗa da kuɗin da wanda kake bani kusan dubu goma sha biyar na bawa Yaya Amina nace ta yi Business dashi, idan ina buƙata zan mata magana, yanzu nayi mata magana na bata Account Number ɗinka zata sakomin kuɗin, seka ɗau dubu goma ka bani biyar tunda fridge ɗina biyu ne kuma ana samun wuta se in fara saida kayan sanyi, Amma me kace? "


Ajiyar zuciya yayi yace "zaki iya sana'a a haka? Karki wahalar da kanki fa"


"zan iya Yaya Ammar, zaman haka baze yuwu ba, kaga da ina Sana'a da abun yazo mana da sauƙi"


"Shikenan, Amma be kamata in karɓar miki kuɗi ba, sedai ko rance in Allah ya hore in mayar miki"


Haɗe rai tayi tace "Niba rance zan baka ba, kyauta zan baka kayi abunda ya dace dasu, kaga da Abba ze yadda a cikin dabbobi na ya baka ka siyar da wasu ka haɗa"


"A'a kin san halin Abba, baze yadda ba, Naji daɗi Sosai Mufeeda Nagode, Nag.....


"Shhhhh babu wannan tsakani na da abun sona, dan Allah Yaya Ammar ka kwantar da hankalin ka kaji, ni ba zan ɗaga maka hankali ba, mubi komai A sannu, Allah yasa haka shine mafi Alkhairi"


Ya amsa mata da Ameen, sannan yace "ranar Litinin ya kamata ki koma awo, amma baki je ba, Amma in Allah ya kaimu sati me zuwa zaki koma Awo ina sane, Insha Allah"


Jinjina masa kai tayi tana masa murmushi.


*******************
Mijin Jidda ya dage kai da fata seya ƙara Aure, duk wani abu data san zata yi ta tayar masa ds hankali tayi amma kamar tana ƙara ziga shi, haka ta haƙura ta shiga gyare2, ya gina sabon gidan sa inda zasu koma gaba ɗaya ya haɗe su.


Tana so ta koma da sababbun furnitures, tace ya canza mata yace bashi da kuɗi, ita kuma kuɗinta ba zasu kai ba, tace bari taje tasa Ammar a gaba ya cika mata.


Sedai da taje ta tarar Ammar baya nan, Rashin mutuncin nata dai data sabawa yiwa Mufeeda bata dena ba, taita zuba ido Mufeeda ta zubo mata Abinci amma shiru nan ma ta samu nayi, ita dai Mufeeda ko uffan ba tace mata ba, ana haka Ammar ya dawo ya tarar da Jidda.


Se wani harare hararw take tana hura hanci ita ga me ɗan uwa, Bayan sun gaisa ta gaya masa abunda takeso yayi mata.


Ammar yace "A gaskiya Jidda sedai kiyi haƙuri, bani da hali a yanzu bani da kuɗi, naga kayan kujerun naki aiba wani abun suka yi ba, ki tare dasu mana"


"dalla Yimin shiru, kace dai bazaka bani ba, ka taɓe a gindin mace se abunda take so, tunda kayi Auren nan ko ɗan Alherin da kakewa Mutane ka dena, Saboda wannan lotsatsiyar Yarinyar mara hankali"


"Ya isheki Yaya Jidda, a baya da ne miki babu nauyin kowa a kaina, kuma kinsan ina miki, yanzu kuma Akwai Nauyin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login