Showing 42001 words to 45000 words out of 105124 words

Chapter 15 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16339

yake nema, tana zuwa ta duba wardrobe ɗinsa ta ɗakko masa


"Hmm Yaya Ammar kenan ga kayan anan kusa amma wai be gansu ba, ko ina ya duba oho"


Tana ɗagowa taga ya fito daga wanka, boxers ne kawai a jikin sa yana goge ruwan wanka.


Tsorata Mufeeda tayi ta zare ido, bata taɓa ganin namiji a haka ba, wasu zara zaran gashi ne a jikin sa, tun daga kansa ƙirjinsa zuwa ƙafafuwan sa, taga yayi wani irin girma da kwarjini, nan ta shiga zazzare ido.




Ammar sarai ya ga tsoro a fuskar Mufeeda
Ammar yace "Yawwa kin ɗakko min?"


Jinjina masa kai kawai tayi tana kallon sa, yace "miƙomin su nan, ni ba'a nan nake ajiyewa ba"


Jiki a sanyaye tana kallon sa tana ɗauke ido, ta ƙaraso ta miƙo masa kayan, maimakon ya karɓi kayan seya riƙe ta, ƙara zare ido tayi tana jan numfashi.


"Me kike Kallo" girgiza masa kai tayi tace "bakomai fa" tai maganar kaman za tayi kuka


"A'a sekin gayamin me kike kallo?"


"wallahi bakomai, ba kallon ka nake ba"


"ki gayamin ba abunda zan miki"


"Wallahi bango nake kallo ba kai ba"


Murmushi ya ɗanyi a ransa yana tuna yadda take masa rangwaɗa da shagwaba ashe ma matsoraciya ce haka.


Ya ɗan kashe mata ido yace "ko zaki taɓa gemun ne?"


"A'a aikace ba yanzu ba"


"A'a na canza ra'ayi ki taɓa mana"


Noƙe kafaɗa tayi tace
"A'a Abinci na ze ƙone"


Sakin ta yayi ta fita da sauri hada haɗawa da gudu, sosai ta bawa Ammar Dariya.


Har ya shirya ya fito bata son kallon sa sosai, ko surutun yau babu, da taga zasu haɗa ido seta sunkuyar da kai, idan kuwa suka haɗa ido se Ammar yace "ko in zone? .


Da sauri take cewa A'a


Haka ya karya ya fice yana dariyar yadda tayi da ido daya riƙe ta.
















Domin sharhi, Gyara ko Shawara
Ayshercool
07063065680


✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )








*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com





ELEGANT ONLINE WRITER'S











Page 14


Ammar be kai dare ba yau tun azahar ya dawo gida, amma yana zuwa ya tarar da Mufeeda a falo kwance akan kujera, da ƙyar ta iya amsa masa sallamar sa ya kalleta yace
"ya dai?" tace
"bakomai ya naga ka dawo da wuri yau?"
"kince in dena kaiwa dare, na dawo da wuri kuma kina tambaya ta"


Ɗan murmushi tayi tace "ai ban san zaka dawo yanzu ba, ban girki ba"


"haka kike zama da yunwa in ba na nan, salon Ace bana baki Abinci?"


"Ai bana jin yunwa ne, kuma ga cornflakes can, idan naci ya isheni, Abincin yafi daɗi idan ina ci ina kallon ka"


Murmushi yayi yace "yanzu me zaki ban, ina jin Yunwa"


"ina da miya, bari inje kitchen ɗin in gani"


Ammar ya lura da ita kaman jikin ta babu ƙwari, a hankali take komai, ta dafo masa Abinci ta kawo masa, ta koma kan kujera ta kwanta.


Ammar yace "wai meke damunki ne?"


"Ciki nane yake min ciwo fa"


"Shine kike ta faman haɗe rai haka, wannan ciye ciyen naki ma ya isa su saki ciwon cikin ai"


Shiru tayi masa ta lumshe idon ta, ya kalle ta yace
"ki sakko kici Abinci seki sha magani"


Girgiza masa kai tayi alamar A'a,.
Ammar yaci Abincin sa ya ƙoshi, ya ture Kwanukan gefe, ya ɗakko wayarsa yana game, a tunanin sa Mufeeda ba dagaske take ba.


Can ta ɗan fara juyi tana riƙe cikin ta, tana numfarfashi.


Ya kalleta yace "idan banɗaki zaki shiga ki tashi ki tafi mana"


Haushi ne ya kamata, tana fama da kanta amma yana mata wata maganar daban, a hasale tace
"Idan banɗakin zani ai na sani, ko na taɓa fitsari a falo ne? In haka kake gudu seka dinga samun pampers kar in ɓata maka guri tunda dama ni Jaririya ce"


Mamaki ne ya kama Ammar, ko da wasa be taɓa tunanin Mufeeda zata gaya masa baƙar magana ba.


Ƙara riƙe cikin ta tayi tana rintse ido, Ammar binta yake da ido kawai, miƙewa tayi tana durƙusawa ta tafi ɗakin ta.


Ɗan taɓe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, idon sane ya sauka a inda Mufeeda ta tashi, tayi staining na jini a gurin, ɗan zare ido yayi, dama Mufeeda ta isa fara period ne? 🙄


Miƙewa yayi ya samo ruwa da Omo ya goge gurin, da yake bada yawane inda ta ɓata ɗin ba, shi da farko ya ɗauka kawai rigima take ji, se yanzu ya tabattar bata jin daɗi ne.


Ya bita ɗakin dan ganin halin da take ciki, yana shiga ɗakin nata ya tarar ta cire kayan jikin ta, daga ita se underwear hatta ribbon ɗin kanta ta cire shi, gashin ta a wargatse tana durƙushe a gaban gado, ta tattaro bedsheet ɗin kan gadon ta tada kai dashi tana kuka, ga fanka se gudu take amma ita ta haɗa gumi sosai se kace me naƙuda.


Daidaita nutsuwar sa yayi, ya ƙarasa da sauri ya ɗago ta, ya ƙare mata kallo, Mufeeda ba farace tas ba amma chocolate ce me haske, fatar ta tana da matukar ɗaukar ido se sheƙi take, ga wannan sassanyan ƙamshin da take me kashe masa jiki


A hankali yace " sannu ban zaci abun ya kai haka ba, daure kisa kayan ki se muje Asibiti"


Ɗan ƙura masa ido tayi sannan ta ƙara kwanciya a jikin sa tace
"bazan iya tafiya yanzu ba, ka bari ya lafamin, kuma ma daka ƙyaleni ze dena fa"
"No gara muje Asibitin dai"
Ɗan lumshe ido tareda yamutsa fuska alamar tana jin jiki, a hankali kaman me raɗa tace
"bari ya ɗan lafamin, yanzu ina jin ciwon sosai"


"shikenan sannu"
Bata iya amsawa ba se lumshe ido da tayi, a hankali Ammar ya kai hannun sa kan gashin ta yana shafawa, zuciyar Ammar ta shiga bugawa da ƙarfi tana raya masa abubuwa da dama akan Mufeeda, Amma wani ɓangaren na zuciyar sa na ƙoƙarin kawar masa da tunanin da yake.


Ɗan yamutsa fuska ta kuma yi tana miƙe ƙafafuwan ta tace
"Yaya Ammar Ciwo"
Ya riƙe hannayen ta yace "Sannu ze dena Insha Allah"


Gaba ɗaya tausayi take bashi, yana tuna wani littafi daya taɓa karantawa me suna (MATA A LOKACIN HAILA)


Mata na shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, wani yanayi ne wanda inba wanda yake jinin ba baze gane ba, sukan shiga halin takura, yawan ƙunci, kasala tashin zuciya, yawan faɗa da saurin fusata, kwaɗayi kaman masu ƙaramin ciki, yawan kuka ko san kaɗaici da dai sauran su, ga uwa uba Wannan ciwon da wasu matan kan yi, ciwo ne me wahala matuƙa wata duk lokacin da za tayi seta kwanta rashin lafiya sosai, ciwon mara me haɗe da ciwon ciki da gudawa, ko kuma ciwon baya da ƙafafuwa, wasu kuma hada amai da zazzabi ƙuraje su fito su ɓata musu fuska, wannan ma ya ishesu shiga damuwa, wata idan tana wannan ciwon kaman zararriya haka take, wata harta gama Al'ada bata san saka kaya, se dai marasa nauyi, wata kuma komai sanyi zata dinga kwanciya a guri me sanyi ko cin abu me matukar sanyi, da dai sauran su.
Dan haka yake da mahimmanci miji kokuma wanda yake tare da Mace ya gane idan mace tana irin wannan yanayin ayi mata uzuri, ba kowane lokaci mata suke wani abun suna sane ba, sedai dan kusan gaba ɗaya rayuwar su cikin yanayi ne na hormones da suke sauyasu lokacin al'ada, lokacin da suke da ƙaramin ciki ko kuma idan cikin ya tsufa.


Kallon ta ya ci gaba daya, bacci ne yayi gaba da ita, dan haka Ammar yasa mata filo ya kwantar da ita ya fita.


Se la'asar sannan ta farka, ta shiga tayi wanka ta samu ta saka kaya a jikin ta, ta gyara gadon ta ta nemi guri ta zauna.


Ammar ya dawo ɗakin yaga har tayi wanka ta canza kaya, ya kalle ta yace "ya jikin?"
"Da sauƙi Alhamdilillah"
"Saka hijjabinki kizo mu tafi"


Kaman tace masa A'a amma ta fasa saboda yanzu seya ɓata rai, haka ta saka hijjabi ta fito.


A hankali take tafiyar, Ammar ya riƙo ta suka fito zuwa cikin a daidai ta sahunsa, Matan layin da yake sana'ar su ce leƙen ƙofar gida suna gulma, suna ganin Ammar ya riƙo Mufeeda sun fito gaba ɗaya hankalin su ya koma kansu, yasa Mufeeda a babur ɗin ya zagaya ya zauna a mazaunin direba ya kunna suka tafi.


Suna tafiya matan layin suka dasa gulmar su, wasu suna itace matar gidan, wasu suna ba ita bace ba sedai ko baƙuwa suka yi ko 'yar uwassa ce, da yake basu san itace matar gidan ba.


Wani Clinic na kuɗi ya kaita, suna zuwa ta samu guri ta zauna Ammar yaje aka buɗe mata file, sannan suka shiga gurin ganin likita.


Suka gaisa da Likitan, ya kalle su yace "to kai ta kawo ko kai ka kawo ta"


Ammar yace "itace ba lafiya"


Likitan ya kalleta yace "meya ke damun ki ne?"


Kallon Ammar tayi tai shiru, Ammar yace "kiyi magana mana"
"Ciki nane yake min ciwo"


Ammar yace "ba ciki ba dai mara ko?"
Kunya ce ta kamata tai shiru tare da sunkuyar da kai.


Likitan yai murmushi yace "Nagane, menstrual cramp ne, yaushe kika fara?"


"haka yake min idan zanyi"


"Yaushe kika fara menstruation?"


"four years back"


Ba Likitan ba har Ammar seda ya kalleta Ammar yace "are you sure?"


"Very sure" ta bashi amsa


Likitan yace
"Ok hakan ba wani abun damuwa bane, mata suna shiga wannan yanayin idan suna Al'ada, sedai a kula da ita da abubuwan da zata ci, Sannan idan ta samu ma nemi a mata Aure, idan akayi musu Aure in akayi sa'a wasu yana raguwa koma su rabu dashi baki ɗaya"


Ita dai Mufeeda ba tace komai ba.
Likitan yace
"tsakanin magani da Allura wanne kike so?"
Kafin tayi magana Ammar yace "Allura zaka rubuta mata"
Zare ido tayi tace "Haba Yaya Ammar wallahi bana son Allura, dan Allah kar ayimin"
"Likita rubuta mata Allura, Allura tafi quick Action, in ba haka ba muka koma gida zuwa zata yi ta cigaba da lanƙwashewa"
Mufeeda tuni ta fara kuka, liktan yace "We have to respect her autonomy, tunda magani take so a rubuta mata"
Ammar yace "No Allura zaka rubuta mata"
Haka likitan ya rubuta mata Allura da sauran magungunan, ya kalle Mufeeda yace
"Sorry Baby Allura ba zafi fa, Wannan Yayan naki yace se an miki Allura"


Basu kuma kulashi ba, Ammar ya sunkuya yace mata "gobe ma ki ƙara min rashin kunya, ina sane nace a miki Allura" zumɓura baki tayi suka fito daga OPD ɗin, Ammar yace ta zauna ya siyo maganin, ta zauna tana jiran sa.


Bayan ya siyo maganin ne yaci karo da Faruk, suka gaisa Faruk yace "Ahh mutumina me kake anan?"


"Mufeeda ce bata jin daɗi na kawo ta A duba ta"


"Allah sarki, nima nazo in duba wasu patients ɗina ne da na yiwa CS jiya, muje semu gaisa tunda kuka tare ko leƙoku ban kuma yi ba"


Suka tafi tare suna hira, Faruk yaga Mufeeda ta ƙara ƙiba, dukda kuka take amma tayi wani fresh da ita, Faruk yace "Madam har yanzu ba'a dena rikici ba? Hala laulayi ne?"


Ammar yace "Haihuwa zata yi ba laulayi ba"


Ganin irin kallon da Faruk ke mata yasa Mufeeda tace "Na gaji Mu tafi"


Ammar yace "to Faruk se anjima se munyi waya" ya kama hannun Mufeeda suka tafi Injection room.


Fafur Mufeeda taƙi shiga Nurses suyi mata allurar, Ammar ya fara ƙulewa ya janyo ta zuwa cikin gurin, kuka take sosai kamar wadda za'a yanka.


Ammar yace "haba Autar Baba sonake ki warke da wuri shiyasa nace ayi miki allurar ai, hug me you won't feel the pain"


Ya buɗe mata hannayen sa, a hankali ta ƙarasa ta kwanta a jikin sa, ya riƙe ta, Nurse ɗin tace
"Ikon Allah, dan Allah ƙanwarka ce ko matar ka?" da yake babbar mace ce dan haka Ammar ya bata amsa
"Mata ta ce"


"gaskiya ran haihuwa da kallo, Allura kawai tana wannan abun, Allah ya ƙara maka haƙuri ɗan nan, kana fama da shagwaba" murmushi kawai Ammar yayi.


A hakan ma da ƙyar ta tsaya aka yi, Hawaye sharkaf fuskarta, maimakon da'aka gama ta tashi sema ƙara narke masa da tayi a jiki tana kuka.
Ammar yace
"ya isa haka harfa an gama, Insha Allah yanzu zaki dena jin ciwon"


"Wallahi Allurar da zafi sosai"


"to ai zafin kaɗan ne akan ciwon da kike ciki"
Nan ta shiga zabga shagwaɓarta, ƙarshe nurse ɗin se fita tayi tabar musu room ɗin.


Ammar yace "ki tashi mu tafi kinji an fara kiran sallar magariba"


Noƙe masa kafaɗa tayi,
"idan munje gida zan baki biscuit ai zaki ci ko Jariri ya ta?"
Murmushi tayi masa tana lumshe ido, a hankali ta miƙe ta biyo shi suka fito, suka hau babur ɗin su zuwa gida.


Da sukaje gida Mufeeda tace ita ba zata iya tafiya ba, ƙafar ta ta sage jikin ta babu ƙwari, ƙarshe seda Ammar ya ɗauke ta ya kaita har kan gadon ta a ranta tace
"tunda kasa akamin Allura se kayi jinya kaima"


Ammar yaje yayi salla, ya dafo mata tea ya kawo mata, ta karɓa ta sha sannan ya miƙo mata ledar pharmacy yace
"gashi nan pampers ɗin da kika ce in sai miki ne" ta kalle shi tace
"Pampers kuma?"
"Eh mana ko kin manta ne?"
Karɓar ledar tayi ta duba, pad ce guda uku da sababbin pants guda biyar, wata kunyace ta kama ta, banda abun Ammar panties ɗinta kona lefe bata taɓa ba amma ya sai wasu. Sunkuyar da kai tayi taƙi ɗagowa su haɗa ido.


Yace "zanje masallaci idan nayi sallar isha'i zan ɗan za gaya, kinga yau ban samu nayi aiki ba yadda yakamata"


"Shikenan amma karka yi dare sosai dan Allah"
Jinjina mata kai yayi, ya miƙe ya fita.


Bayan ya idar da Sallar isha'ine Aminu ya kira shi yace "yana so su haɗu za suje gidan Jabir"


Haka kuwa akayi a gidan Jabir suka haɗu, Jabir yayi farincikin zuwan su, Yace
"Kai Ammar Mufeeda ta ɓoye ka, ko a hanya sam bama haɗuwa, ga yadda kayi kumatu"
Yaita zolayar Ammar sannan yai musu iso zuwa cikin gidan, falon sa ya kaisu suka zauna suka dinga hira, Can Ammar yace


"Jabir abar hirar nan muyi abunda ya kawo mu? Ina matar gidan ne?"
Jabir yace
"tana gidan ɗakin ta"


"a gaskiya naji wani labari dabe min daɗi ba game da auren ka, Jabir ya'akayi haka ta faru?"


Jabir yace "bari Ammar ai nayi zaɓen tumun dare dana san haka Auren yake da banyi ba, wallahi mata basu da mutunci nayi dana sanin Auren Saima"


Ammar yace "Dana sanin mene?"


"Yarinyar nan sam bata da Mutunci bata ganin girma na, bata da tarbiyya Sam, ban isa in gaya mata taji ba, wallahi badan ina tsoron abunda iyayena zasu ce ba da tuni na sake ta"


Aminu zeyi Magana sega Saima ta fito, tana ganin su ta faɗaɗa murmushin ta tace
"Manyan Baƙi aini har nayi fushi, sau ɗaya kuka zo mana tun bayan bikin mu, Ammar ina Amaryar?"


"tana gida, idan ma baku zoba zan kawo ta Insha Allah"
Saima tace
"Insha Allah ai zanzo har gida mu gaisa, Jabir baka gayamin sunzo ba ai be kamata abar baƙi babu ko ruwan sha ba, bari in baku ruwa"


Ta wuce ta nufi kitchen, Jabir yaja wani uban tsaki yace
"Munafukar Banza"
Aminu yace "Subhanallah, haba Jabir a gaban mu kake kiran ta Munafuka"


"mece idan ba Munafukar ba, danta ganku take nuna ita ta Allah ce, Amma tafi sheɗan iya rashin mutunci"


Saima ta dawo da lemuka da ruwa faranti da kofuna, ta ajiye Musu a gaban su.
Saima ta kalli Su Ammar idon ta fal Hawaye tace
"Aminu wallahi Abokin ku Azzalumi ne, dan Allah ku gaya masa idan mutum ya auri mace baya na nufin ya auro baiwa bane, Jabir Jahili ne besan darajar ɗan Adam ba"
Miƙewa Jabir yayi yana zare ido, ya fara narko mata Ashar, Saima tace


"Wallahi ba iyaye na ba sedai naka"


Da sauri Aminu ya miƙe ya riƙe jabir yace "Jabir meye haka? Matarka ta Aure kake wa wannan mummuna ashar agaban abokan ka?"


Saima tace "baka ga komai ba a gurin sa, dana san haka yake wallahi bazan Aure shi ba, mutanen kirki suka fito suna sona na liƙe nabi soyayya nace seshi, amma bayan Auren mu, shine kullum cikin chatting da 'yan mata, ba dare ba rana lokacin da nake buƙatar lokacin sa lokacin ne yake chatting, idan nayi magana seya ce wai na taɓa ganin anyi campaign bayan zaɓe? Da ina haƙuri ina ƙyale shi, Amma Ba damar inyi masa laifi se ya fara zagarmin iyaye, wallahi baka isa ba iyaye basu fi iyaye ba kakuma zagarmin iyaye sena zagi naka iyayen "


Ammar yace
"Saima yi haƙuri ki koma ɗaki, zamuyi magana da Jabir "


Haka ta wuce ɗaki tana kuka, Aminu yace
"gaskiya Jabir kaine mafarin samar da matsala a cikin gidan ka, ta yaya zaka dinga ce mata ba'a campaign bayan zaɓe, hakan fa na nuna bata da wani mahimmanci a gurin ka, haba dan Allah Jabir kaman ba wayayye ba kaima fa kana da ƙanne mata baza kaso ayi musu haka ba, kuma wallahi in gaya maka kaida ta ƙara ganin mutuncin ka har gaban abada sedai tayi pretending, amma a matsayin ka na namiji daga lokacin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login