Showing 6001 words to 9000 words out of 105124 words
kazo mana taro kace ba zaka karɓi komai ba"
Mufeeda Ta shiga ta haɗo masa kayan ɗaurin Aure fal viva, kaji da lemuka, kayan snacks, Alewa da goro seda ta cika viva da shi, da ta fito da ledar Seda Mama ta bita da kallo ganin haukan da Mufeeda tayi, ba damar tayi magana tunda a cikin taro ne.
Yana tafe tana biye da shi har bakin Napep ɗin sa, yace
"bani key ɗina kuma bazan ƙara zuwa gidan ku ba"
"Saboda me?"
"Saboda kin fiye rawar kai, ni kuma bana son rawar kai"
"to yi haƙuri na dena"
Wani kallo yai mata sannan yace "bani mukulli na in tafi"
Miƙa masa key ɗin sa tayi, Amma ta tsaya a jikin Napep ɗin ta zubawa Ammar ilahirin idanuwan ta tana ƙare masa kallo.
A ran ta tace "Masha Allah gaskiya Ammar yana da kyau"
Ammar ya fara fusata da lamarin Mufeeda, dan dana sanin zuwa gurin ɗaurin auren ma yake, a zuciye yace
"ke Matsa zan tafi, kin sani a gaba kina ta ƙare min kallo"
Memakon taji haushin tsawar da yayi mata, sajen sa ne ya ƙara birgeta, ga ƙamshin turaren sa duk ya gauraye gurin a hankali cikin wani salo me cike da jan hankali ta furta
"Yaya Ammar"
Wani Yarrr yaji a jikin sa, tsigar jikin sa ta tashi sakamakon yadda ta furta sunan nasa, ɗagowa yayi yana kallon ta
"Yaya Ammar se yaushe?"
Kallon ta yayi galala
"kamar ya se yaushe? Me zanzo inyi miki? Kin bar kayan ki na kawo miki, kin gayyace ni biki nazo miki, me kuma ya rage?"
"Alfarma ɗaya nake so kamin Yaya na"
"Ina jinki"
Seda ta ƙara kwantar da murya cikin shagwaba tace
"Zaka min kuwa?"
Gaba ɗaya yadda ƙwailar yarinyar ke magana na nema ya jefa shi cikin wani yanayi dabe zata ba.
A ƙagauce yace "ina jinki"
Miƙa masa wayar ta tayi ta ƙara ƙasa da muryar ta tace
"dan Allah ka samun lambar ka Yaya na"
Hararar ta yayi yace
"ke bana son damu bana son shirme matsa ki ban guri, ko in bige ki da babur ɗin nan"
Noƙe kafaɗa tayi "Allah bazan tafi ba se dai muyi ta tsayuwa, ko ka bigeni da babur ɗin, kuma fa ba damun ka zanyi ba, gaisawa kawai zamu dinga yi fa"
Dafe kai Ammar yayi, wasa2 sun kai mintuna Ashirin a tsaye a gurin nan.
"ke wai bakya ganewa ne ko ba kya ji? Ki matsa nace!"
Seda hantar cikin ta ta kaɗa, Amma memakon yaga tsoro ko karaya a fuskar ta, ɗan rintse ido kawai tayi alamar bata son shouting, ta buɗe idon ta ta kalleshi, ta langaɓar da kai tace
"please Yayana nifa ƙanwarka ce why are you shouting at me? Allah bazan takura maka ba"
Ta miƙo masa tanfatsetsiyar wayar ta, ganin Mufeeda na neman ɓata masa lokaci, kuma ci gaba da tsayuwar su haka zata jefa shi yanayin da ze sha wuya, ya karɓi wayar a gaggauce yasa mata lambar sa ya miƙa mata wayar ta.
Karɓar wayar tayi tare da yin murmushi tace "Nagode Yaya na, Allah ya baka ladan zumunci ka gaida su Mama"
Ta matsa daga jikin Napep ɗin ya kunna yayi gaba yana mamakin hali irin na Mufeeda.
Ta juya zata shiga gida, ɗan Autan su Umman ta ya kira ta, ƙarasawa inda yake tayi, ya kalleta yace
"Mufeeda waye wancan?"
"Yaya nane"
"kamar ya Yayan ki?" ɗan tura baki tayi tace "dan Allah Uncle karka tsanan ta bincike mene ne?"
Girgiza kai yayi yace "tun ɗazu Yaya ke nemanki, tace ta baki Abinci ki kaiwa ƙannen baban ku, Amma babu ke babu saƙon"
Se yanzu ta tuna dire tray ɗin tayi ta tafi gurin Ammar, taɓdijan ashe zata kaɗe a gurin Mama
"Uncle zomu koma gefe tambayar ka zanyi"
Ba musu ya bita suka samu guri suka zauna tace
"uncle dan Allah me yake sa kaji kana tunanin mutum? Ko ka dinga son ganin sa ko yawan mafarkin sa"
Murmushi yayi yace "Autar Baba kenan, Soyayya ke kawo haka"
Murmushi tayi ta miƙe tace "nagode uncle" tayi gaba abun ta.
Mama a ƙule take da Mufeeda, Amma saboda taro bata bi ta kan ta ba ta ƙyaleta se an gama biki.
Aka gama biki dare yayi za'a kai yayar Mufeeda ɗakin ta, aka kaita gurin Baban su yai mata nasiha sosai, se kuka take kowa ya shigo se yayi wa Amina nasiha akan Aure wannan nayi wancan nayi.
Amina ta rungume Mufeeda tana kukan zata rabu da 'yar uwata dan sun shaƙu sosai.
Mufeeda idon ta ƙyar babu alamar hawaye tace "haba Yaya dan Allah kidena kukan nan, haba se kanki yayi ciwo? Ai ni yakamata inyi kuka bake ba, dan kina tafiya zan shiga uku da aiki a gidan nan, dan Mama ba zata bari in huta ba, dan ta tsani taga ina hutawa, wallahi ina candy zanyi Aure in bar mata gidan "
Wasu nawa Mufeeda dariya wasu na mamakin fitsarar ta.
Wata ƙanwar kakar su ce na ƙauye suka shigo da 'yan uwan su, suka fara yiwa Amina Nasiha akan aure, buɗar bakin mufeeda se cewa tayi
"Dan girman Allah ku kyale ta haka Inna haba tunda kuka zo ake abu ɗaya kuke maimaitawa ai ta haddace, abu ɗaya kuke nana tawa yi nayi bari na bari, wannan ai tun zamanin ku aka dena wannan yi nayi bari na barin,"
"Ubanki Mufeeda kinji ko?" ta jiyo muryar Mama, sam bata san Mama ta shigo ɗakin ba.
Jan bakin ta tayi tai shiru, Mama tace
"inna Ladidi ga motocin can sunzo, kuje a raka ta, Amina na Allah ya bada sa'a"
Ƙara fashewa da kuka Amina tayi, Mufeeda tace
"Mama dan Allah su Inna Ladidi su hau wata motar, ya za'ayi a haɗa ta da tsofaffi su ƙara samin ita kuka, mota ɗaya zamu hau nida ita in rakata"
Mafici Mama ta ɗauka ta jefi Mufeeda amma ta kauce Mama tace
"Babu gidan uban da zaki, kina nan dama a ƙule nake dake, zaki gamu dani ne, fitsararriya"
Seda Mufeeda taga da gaske Amina tafiya za tayi sannan tasa kuka, ita kanta Mama dakewa kawai take yi, Mufeeda kam kuka sosai seda aka kaita gurin Baba shi ya dinga aikin rarrashi, dan in aka ƙyaleta Mama seta zane mata jikin ta.
Kowa ya watse ana ta aikin gyara kayan da'aka ɓata na biki, Amma Mufeeda ta maƙale a gurin Baban ta.
Mufeeda ta shiga ɗakin Mama dan ta canza kaya, Yayyen ta wasu basu tafi ba, se Washegari in an gama gyara gida za su tafi, Mama ta kalli Mufeeda tace
"zan gauraya dake Mufeeda, saboda wulaƙanci na aike ki da kaya ki kaiwa su faruku aka neme ki aka rasa bake babu kayan, kinzo da baƙo daga cewa ki bashi kayan biki kika ciko uwar viva kika bashi se kace ke kika saimin, har aka yi taron nan aka gama magana kike sani, zaki shigo hannu na zakiyi bayani uwar wauta "
Mufeeda ta tura baki tace "Haba Mama, Amma lokacin su Anty Murja in suka zo da saurayin su ai ba haka kike musu ba, ke kike cika musu ledoji fa, Amma ni dama bakya sona shiyasa zaki ce na miki wauta"
Anty Murja ce tace "Wait ƙanwa ta, ki kace me a daidaita sahu ne saurayin ki, wanda kika shigo da shi ɗazu fa? Shi kuma waye?"
Murmushi Mufeeda tayi cikin shagwaba tace "To ai shi ne fa, Shine sirikin Maman, Amma take min mita dan na bashi abu, ranar fa da ta hanani kuɗin mota kyauta ya kawoni gida, na manta kayana ya kawomin, na gayyace shi biki yazo, ai yana da kirki ko Yaya fadila"
Wata irin dariya da shewa Yaya Murja da kuma Fadila suka yi, ita kam Mama baki ta saki tana kallon wauta.
Fadila tace "kan bala'i indai wanda kuka shigo ɗazu ne me ash ɗin yadi, wallahi mufeeda yarinta da ƙuruciya ke ɗawainiya da kanki, kai! kofa ƙirjinsa baki kai ba, inaga da kaɗan kika wuce cikin sa a tsaye, kina ganin namiji a murɗe gashi ko fara'a bayayi"
Cikin tsiwa tace "Wallahi Ammar yafi mijin ki kyau, kuma ina ruwana da girman sa aiba goya shi zan dinga yi ba"
Yaya murja tace "Mufeeda in ma Auren ne ki samo dai dai ke kinji professior Auta, waima ba cewa kikayi se kinyi degree ba, zakiyi Aure?"
"ba wani professor Aure zanyi, kuma Yaya Ammar nake so"
Tofa
More Comments More Typing
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨
( *Sai Mata* )
Page 3
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*_A SHORT LOVE STORY_*
*Story and written by*
'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''
Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba
Watpad @ Ayshercool7724
What's app 07063065680
Gmail Www.ayshertadam@gmail.com
Ammar ne yayi sallama ya shiga gida ɗauke da leda a hannun sa ya tarar da halima na tsakar gida tana wa Umman sa kitso, mahaifinsa kuma na gefe akan dadduma yana sauraren radio.
Amsa masa Sallamar suka yi gaba ɗaya, ya samu guri ya zauna a gefen tabarmar da Umman sa ke zaune yace
"Abba sannu da gida"
"Yawwa Ammar ya aikin?"
Ammar yace "Alhamdilillah" sannan ya miƙawa maman sa ledar vivan da ya shigo da ita.
Baban Ammar yace "Ammar ka rage wannan ɗawainiyar da kake mana a cikin gidan nan mungode, ni abunda nafi damuwa da shi ka adana ƙudinka ka tara ƙuɗin aure"
Dafe kai Ammar yayi yace "Abba ba wani abune na siyo ba kayan ɗaurin aure ne da naje aka bani"
"haka dai se aukin yawon zuwa auren wasu amma kai sai jin kan da fushi"
Ammar yayi shiru bece komai ba.
Halima ta ɗakko faranti aka juye kayan akai, Umma ta jinjina kai tace "kai kam Ammar ɗaurin auren waye haka aka baka wannan kayan kaman kaine angon?"
Halima tai farat tace "Wallahi umma wata ce ta gayyace shi, da na zata baze je ba amma.....
Uwar harar da Ammar yai mata ne ya tilasta ta yin shiru.
Abba yace
"me tayi maka kake mata wannan mugun kallon? Ke Halima gayamin ina jinki"
Cikin kame2 Halima tace "Amm.. Dama.. Dama katin ɗaurin Auren na gani a ɗakin sa yace min wata ce ta bashi na bikin yayarta ne"
Abba ya kalli Ammar yace "A ina take kuma 'yar waye? Meye haɗin ka da ita har da zata baka wannan kayan haka?"
"Abba wallahi bakomai a tsakanin mu, kawai na ɗauke ta ne ta bar kayan ta a Napep ɗina, shine na kaima ta, ta bani katin ɗaurin aure, yau da naje shine ta bani wannan kayan" ya ƙarasa maganar yana ɗan ɓata rai.
Abba yace "Ammar ka gayamin gaskiya, ba ina maka haka ne dan in ɓata maka rai ba ina gaya maka gaskiya ne, idan kuna son juna ne in shige gaba in tambayar maka, Ammar ya kamata ka ajiye iyali, ba seka tsofe a titi ba"
Da sauri Ammar ya kalli Abban sa yace "Abba yarinya ce fa ƙarama, Halima ta girmeta sosai, da shekaru na in auri 'yar mitsitsiyar yarinya ko fa secondary bata gama ba zaman Aure zanyi ko kuma raino?"
"Rufemin baki, meye a ciki zaman aure ba' a shekaru bane, kaiwa kanka faɗa dai wallahi"
Se yanzu maman Ammar tace "Malam dan Allah kayi haƙuri, shi Aure lokaci ne"
"kullum haka kike cewa shiyasa yake ƙin auren yake ƙara sangarcewa"
********************
Sosai Mufeeda take kewar yayarta Amina, gefe guda ga son Ammar dake ƙara mamaye zuciyar ta ba tare da sanin ta ba, da farko dai niyyar rainawa Ammar hankali tayi amma tunda ta tambayi uncle ɗin ta ya tabattar mata da alamomin da take ji game da Ammar alamomi ne na soyayya, duk wanda yace yana son Mufeeda daga lokacin zata dena ganin mutuncin sa ta tsane shi, Amma yanzu soyayya ta mata mugun kamu.
Dukda tana da lambar wayarsa amma tana fargabar kiran sa, dan da alama baya son raini, ɗan haɗuwar da suka yi bata taɓa ganin dariyar sa ba, tana tsoron karta kira ya yarfata, wanda babban abunda ta tsana a rayuwar ta be wuce a dizgata ba.
Tunani duk yabi ya addabe ta, ta ɗanfi jin daɗi idan taje makaranta amma da zarar ta dawo duk se walwalarta ta ɗauke, da Mamanta ta zata kewar Yayarta ne yake damun ta kafin daga bisani taga damuwar tata kaman ƙara yawa take.
****************
Kamar kullum Mufeeda taje makaranta amma abun mamaki yau babu sunan ta a 'yan surutu, babu' yan makara tsit kaman bata ajin, kusan kowa yasan ta a makarantar nan mussman saboda laƙanin ta na professor, ga rashin ji duk wani laifi da ita a ciki, wani lokacin ko laifi akayi aka rasa su waye se asaka sunan ta, wasu malaman kance professor marasa jin magana.
Aka tashi daga makaranta zasu tafi gida ita da fati da yake hanyar su ɗaya, Fati tace
"Mufeeda wai me yake damun ki ne? Ko baki da lafiya ne?"
Girgiza kai Mufeeda tayi tare da ajiyar zuciya tace
"Fati ni abunda ke damuna ba zaki iya maganta min ba"
"to gayamin inji meke damun naki?"
Taja Fati suka tsaya jikin wata bishiya sannan ta kalle ta
"Fatee ina missing ɗin Yaya Ammar sosai, tun ranar da yazo ɗaurin Auren Yaya ban kuma saka shi a idona ba, wallahi duk inda na zauna tunanin sa nake"
Wani dogon tsaki Fati ta ja tace "ke kam anyi wahalalliya, daga haɗuwa da mutum a titi shikenan se kuma ki dinga tunanin sa, to me kike nufi da hakan?"
Mufeeda tai murmushi tace "tabbas son Yaya Ammar nake kaman yanda alamomi suka nuna"
"Taɓɗijan amma kinci kai wallahi, tashi mu tafi ni rana ta nayi"
"Fati idan har baza ki tsaya ni neman mafita ba karki ƙara tambaya ta meke damuna, kuma ki yi tafiyar ki dan sena gama tunani zan tafi"
Tausayin Mufeeda ne ya kamata dan iya sanin ta da ita idan mutum yace yana son ta shikenan ta samu abokin gaba, Amma yau da kanta take furta ta faɗa soyayya in dai hakane to tabbas dagaske take.
Cikin kulawa fati tace "Mufeeda bazan iya barinki cikin damuwa ba, Amma ta yaya zaki cigaba da son mutumin da kuka haɗu a titi, ke kike sonshi ba shi ke sonki ba"
"waya gaya miki baya sona? Ke nifa harna faɗa a gidan mu shi nake so"
Ɗan zaro ido fati tayi tace "to shi yace yana sonki ne?"
"oho masa inma baya sona ni dai ina sonshi, tashi mu tafi gida kar Mama taimin faɗan nata akan na daɗe"
Suka tafi ba tare da Mufeeda fa kuma cewa komai ba.
Yanzu ma a kwance Mufeeda take tana jujjuya wayar ta, tana kallon Lambar Ammar da ta rubuta Yaya Ammar ɗina, ta rasa ta inda zata fara, ita dai bata taɓa soyayya ba, bata san ya take ba amma tana ganin wasu sunayi a lissafin ta yau sati uku rabon ta da Ammar, Amma kullum ta rufe ido shi take gani.
Zuciyar ta ta dinga bata shawarar ta kira lambarsa taji ko yana lafiya?
Danna lambar tasa tayi taita ringing be ɗauka ba, ta sake gwada kiran wannan karon ya ɗaga cikin muryar sa me kama da ta me Izza yace "Asslam Alaikum, a kira anjima zanyi salla ne"
Lumshe ido tayi jin muryar sa tasa ta sakin murmushi, ba tare da tace komai ba ya yanke wayar.
Miƙewa itama tayi ta gabatar da sallar isha'i ta nemi Abincin dare taci seda ta gama abunda take ta hau kan gadon ta ta kuma kiran Ammar, seda ta kusa yanke wa sannan ya ɗauka tare da yin sallama.
Se Ajiyar Zuciya take amma ta kasa cewa komai
"ina ji wake magana"
"Yaya Ammar nice" tana magana gaban sa ya faɗi, yaji ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi, shi yama manta da yarinyar nan amma ya ƙara tsuke fuska yace
"Ke wa?"
"Ƙanwar ka ce Mufeeda"
"Ya a kayi?"
"Na kira in gaishe ka ne, ka manta dani"
"to Nagode ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, Zuciya ce ta ɗibi Mufeeda saura ƙiris ta yi jifa da wayar ta amma ta fasa, ta ji haushin abunda Ammar yayi mata sosai tunanin mene mafita ta shiga yi ta nawa kanta tambayar
"dama haka soyayyar take? Wahala da ɓacin rai, ji yadda raina ya ɓaci a banza, da ina zamana lafiya nikaɗai Amma tunda na haɗu da kai na rasa nutsuwa ta, kai kuma kana can kana hutawar ka, kalli yadda ya amsa min waya, na kira shi dan inji sassauci amma ya watsan ƙasa a ido, aikam baka isa ba dani kake zancen bazan sha wannan wahalar nika ɗai baZan nuna maka WATA KISSAR... (SAI MATA) "
haka ta ci gaba da surutu kamar taɓaɓɓiya har Mama ta shigo ɗakin tace
"ke Mufeeda surutun uban me kike ne haka?"
"bakomai Mama"
Ƙarasowa Mama tayi gefen gadon Mufeeda ta zauna tace
"Mufeeda ki gayamin meke damunki ne? Tun bayan bikin Amina na lura kin zama wata iri, gayamin mene ne?"
Ai kaman Mama ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi ba fargaba kanta tsaye tace
"Mama Yaya Ammar ne"
"Waye kuma hakan?" Mama ta tambaya
"Mama me A daidaita sahun da ya kawomin kaya na"
Ɗan ƙara nutsuwa Mama tayi tace "Me yayi miki?"
"Mama tun ran bikin Yaya ban kuma ganin sa ba fa"
A fusace Mama ta kalleta tace "idan kika bari na tashi sena samo Madoki nazo na casaki a gurin nan, jimin Shashar yarinya, yarinya ƙarama dake kike wani zancen kina son wani ƙwaya nawa kike? Ki maida hankali akan karatun ki ki bar zancen wannan yaron in ba haka ba ni da kene"
Cikin shagwaɓa tace
"Mhmm Wallahi Mama ina son Yaya Ammar ɗina ni ba wani karatu da zan iya idan wata ta rigani Auren sa fa? dan Allah Mama ina candy ni Aure zanyi na ci gaba idan nayi Auren"
Riƙe haɓa Mama tayi tace
"Mufeeda rashin kunyar taki har ya kai ki kalli tsabar idona kice min ke ba zakiyi karatu ba Aure zaki yi, to yanzu