Showing 69001 words to 72000 words out of 105124 words

Chapter 24 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16360

fito da sauri tana kiran sunan sa, be saurare ta ba yayi gaba, cikin sauri ta bishi amma ta bige goshin ta da ƙofa da sauri ya tsaya ya juyo, ƙarar da ƙofar tayi zesa kasan ta bugu sosai ya kalle ta yace


"ke komai ba zakiyi a hankali ba, da kinjiwa kanki ciwo fa?"


Bata kula da me yake cewa ba tayi kneeldown akan gwiwowin ta, ta riƙe rigar sa tana kuka tace
"ba dan hali na ba dan girman Allah kayi haƙuri, Insha Allah bazan sake wulaƙanta maka Abinci ba ko in bari wani ya wulaƙanta maka ba, kayi haƙuri dan Allah mijina ka dena fushi dani komai ya denamin daɗi saboda kana fushi dani, kayi haƙuri dan Allah"


Jin kukan nata yayi har cikin zuciyar sa, ya kalleta yace
"shikenan get up"
"A'a dan Allah kace ka haƙura se in tashi"
"Ninace ya wuce ai"
"ka haƙura?" tai maganar wasu hawayen na bin fuskarta, ya jinjina mata kai alamar eh.
Ya juya ze fice tai sauri tace "dan Allah Yaya Ammar, ka tsaya in dafa Abinci kaci ba dan ni ba dan Allah"
"Shikenan muje"
Har Mufeeda ta kammala girkin kuka take, ta kawo ta ajiye masa tana ƙoƙarin haɗa masa ya kalleta yace "Kukan be isa haka ba? Se kanki yayi ciwo?"
Ai kaman ya tunzura ta, ta sake fashewa da kuka hadda sheshsheƙa.


"Idan kuka za kiyi zan fasa cin Abincin"


Kasa denawa tayi tasa hannun ta, ta toshe bakin ta tana ci gaba da kukan, zubawa sarautar Allah ido yayi, seda tayi me isar ta sannan ta koma gefe ta dinga sauke Ajiyar zuciya, bece mata komai ba ya shiga cin Abincin sa ya nayi yana kallon ta, har ya kammala ya fita, tunani ya dingayi a ransa anya ba wani abu ne yake damun Mufeeda ba, ace dan yana fushi da ita ne zesa taita wannan kukan? Ba yadda zeyi ya zama dole idan tayi ba daidai ba ya hukunta ta.


Kamar Yadda Ammar ya gaya mata be ƙara siyo duk wani abu da ya saba siyowa domin ita, ya dena ajiye mata kaman Madara, Milo tarkacen buscuit da lemo da yake ajiyewa duk ya dena sedai yayi cefanen abunda zaa'a ci kawai, Sam bata nuna masa ta damu da hukuncin ba, Sedai har yanzu sama sama yake da ita ko sakar mata fuska ba yayi, haka take gaba ɗaya a takure sedai idan ta bashi Abinci ze ci, idan ta gaishe shi ze amsa mata.


Tana son shiga maƙota tayi wa Maman Nur ya jiki taji ance ta dawo dan haka tun kafin ya fita ta tambayeshi yace seta dawo.


Seda rana tayi sanyi bayan la'asar sannan ta saka hijjabin ta ta rufe gida ta shiga gidan Maman Nur, duk maƙotan nan na layin su wanda ta sani da wanda bata sani ba sun cika gidan suna ta shewa, Mufeeda tai Sallama ta shiga ta samu guri ta zauna suka gaisa, tace musu
"ina me jegon ne?"
Banza suka yi mata, Wannan Yayar Maman Nur ɗin ce Anty hauwa tace mata "ta shiga wanka amma yanzu zata fito"
Mufeeda ta zauna zaman jiran Maman Nur ta fito, Yayin da Maman Amir se wani binta take da kallon banza.
Su Maman Sadiq na gefen ta taji suna ƙusƙus da wata maƙociyar su, Maman Sadiq tace
"Kin san wani abu Hafsa jira nake inga Yadda maman Nur zatayi ranar suna, ta ishi mutane hadda fidda anko wai za'ayi shagali ta dinga tatsar mijin ta kuɗi tana hana yaranta Abincin kirki tana tara kuɗin cefane dasu fa dama zata yi taron sunan, to yanzu ta haihu kuɗin data ƙulle za ta birge 'yan unguwa su ta ɗakko akayi mata magani, Mijin ta yace bashi da kuɗi "


Wadda aka kira Hafsa tace
" Dama abun nata duk burga ce da ƙaryar banza, gani take kamar duk layin nan mijin ta yafi kowa kuɗi "


" Dalla duk ƙarya ce, shegen ƙaryace da ita ga roƙe roƙen tsiya ita kuma ga rowa "


Mufeeda dai na jinsu ba tace komai ba, Maman Nur ce ta shigo ta fito daga wanka, dama Mufeeda duk ta gaji da zaman, a tsakanin su da suke tare ma suna zagin juna ina ga ita da ba sayi da ita.


Mufeeda tace " Maman Nur ya jiki? " se lokacin Maman Nur ta lura da Mufeeda ya tsine fuska tayi tace
"Naji sauƙi da ba kije dubani bama na warware"
"Nima ba haka naso ba, lokacin da suka biyo min muzo duba ki baya nan ban tambaye shi ba, kuma ni ba wani sanin kan uguwanni nayi ba, baya barina in fita nika ɗai"


Wata uwar shewa suka saki, Maman Nur tace "Allahu Akbar masu miji kaga masuyi dan Allah"
Maman Sadiq tace "Taɓ kaga matar so, dama ina ze bari kifi ta ke kaɗai duniya ba yadda"
Mufeeda ta basar da su tace
"A bani Babyn in ganshi"
Har za'a miƙa mata Jaririn Maman Nur tace "gaskiya Anty hauwa karki bata ɗana"
Anty hauwa tace "saboda me?"


"Haka kurum, daga zuwa gidan ta, in kai mata ankon suna se cewa tayi inyi fatan in haihu lafiya ba rabon anko ba, ƙarshe na haihu lafiya amma seda na dangana da Asibiti"


Anty hauwa tace "to ai gaskiya ta gaya miki, yanzu kingama rabon anko amma kin ƙarke babu lafiya"


Mufeeda ta miƙe tsaye tace "Bakomai, Allah ya baki lafiya, ya raya abunda aka haifa"


"Bana buƙatar Addu'ar ki, inkina da gaskiya ai bekamata da nayi wannan zancen ki tashi kice zaki tafi ba, Yarinya se girman kan banza, ga sana'ar Mijin ta yafi na kowa lalacewa a tsukin nan"


Har Mufeeda zata fita daga ɗakin ta tsaya ta kalli maman Nur tace "Allah sarki matar mangal, se gashi kina aike gidan direban a daidaita sahu atemaka miki da abunda attajirin mijin naki ba ya iya ajiye miki, ashe ma dai wani kuɗin ƙaryar banza ce, kuma karki ƙara sa kamin mijina a shirmen ki Jahila 'yar ƙauye kawai"


Maman Nur ce ta antayo wata zazzafar Ashar "Ke kin isa kizo gidanta ki zage ta"


"Na zage ta ɗin uwata ce? Tun da nazo layin nan nake baku girman ku Amma bakwa ganewa, wallahi babu matar da zata min in ƙyaleta, kuji da kanku ku ƙyaleni inyi rayuwa ta"


Anty hauwa ce ke ƙoƙarin sasanta abun amma ina suka haɗe kai suka dinga zagin Mufeeda.


Mufeeda tace "Anty kwantar da hankalin ki yanzu zan tafi, Amma duk wadda ta zageni ta zagi iyayen da suka kawo ta duniya, kuma wallahi kaf cikin mazan su babu me karamci da girman mijina, kar wadda ta sake zagar mana sana'a babu wadda nazo gidan ta yin barar abunda zamu ci "


Maman Amir tace
" Dalla rufe mana baki karki ƙara haɗa faƙirin mijin ki da mazajen mu"


"Aini banga alamar kuɗin mazajen naku a jikin ku ba, dan da mijin naki kuɗin nasa na Arziki ne da be barki da wannan koɗaɗɗen zanin da rigar ta ɓarke daga hammata ba"


Ai Mufeeda na faɗar haka kowa ya kalli Maman Amir, aikuwa sega riga a ɓarke ta hammata aikuwa aka ƙyalƙyale mata da dariya.
Mufeeda tai ficewarta a hasale tana jin zafin yadda ake cin zarafin sana'ar mijin ta.


Kanta ne yake wata irin sarawa kusan kwana uku kenan, ta miƙe layin su domin zuwa ta siyo ko paracetamol ne ta sha, amma kafin ta kai ƙarshen layin sega wannan mutumin da ya biyo ta rannan, basarwa tayi zata wuce yace
"'haba adon gari, ina murna yau kayana ya tsinke a gindin kaba na sake tozali da wannan zuƙeƙiyar halittar amma zaki basar dani ki wuce "


"Wai dan Allah malam kai baka tsoron Allah, baka tsoron kaima wani yayi maka abunda kakewa wani?"


"Na gane ke matar Aure ce, dan har gidan ki nasani, rannan ta ƙofar gida na kuka wuce keda mijin ki, Amma fa kinga a wannan zamanin kowa samawa kansa mafita yake, ki ƙyale wannan faƙirin mijin naki, kizo mu jone zan sakar miki kuɗi kiyi yadda kike so, dukda ina da mata huɗu zan saki ko dukan sune idan kina so dan in Aure ki "


" Auzubillah talakan mijina ya fiye min wawan dattijon banza irin ka, gara talauci sau dubu da Arziƙin daya fito daga hannun Asararre irin ka dukiyar taja da in akabi diddigi ta Haramce"


"Haka kika ce?"


"Na faɗa ko zaka yi wani abu akai?"


"shikenan bari mu gani, zan tabattar miki da talauci masifa ne"


Mufeeda fasa zuwa siyan maganin tayi ta koma gida tana tunanin meyasa wannan masifun suke bibiyar ta haka?.




Ammar na zaune yana kallo da daddare Mufeeda na zaune a ƙasa, itama idon ta akan talabijin yake amma tunanin ta sam baya tare da ita, tayi nisa a tunani, ƙwanƙwasa gate ɗin da aka yi ne yasa Ammar ya tafi ya buɗe.


Mijin maman Nur ne, suka gaisa da Ammar,
"dama zuwa nayi dan Allah ka jawa matarka kunne, daga sallamo mata ta dsga Asibiti ta shiga ta tayar min da hayaniya a gida dan Allah a jama ta kunne karta sake"


Wani banzan kallo Ammar yai masa yace "Gaskiya bana tunanin mata tace, idanma itace wani abun suka yi mata dan sam bata da neman rigima"


"A'a sufa matan nan na yanzu ba shedarsu ake ba, be kamata in kawo maka ƙara ka goyi bayan ta ba"


"Naji amma ni nafi kowa sanin halin ta, idan ba wani abun suka yi mata ba haka kurum ba zata je gidan ka tana hayaniya ba, Amma hakan ba zata sake faruwa ba, Allah ya bata lafiya"


(wato Ammar yace Allah ya bada haƙuri ne baze iya ba)


motsin shigowar sane yasa Mufeeda ta buɗe idon ta.


Ammar ya samu guri ya zauna ya zuba mata ido, seda gaban ta yai mummunar faɗuwa kallon da yake mata dan na tuhuma ne.


"Ina kika ce min zaki ɗazu?"


"maƙota na shiga yin barka"


"Da kin cemin zaki barka kika ɓuge da neman rigima a gidan mutane ko? Yanzu wanne wanda yayi Sallama dani maƙocinmu ne yace daga sallamo matarsa daga Asibiti kin shiga kin tayar musu da rigima, wai matar dama ance jinin ta ya hau, ke wai dama haka kike ne?"


Shiru Mufeeda tayi ta sunkuyar da kanta, Ammar yai faɗansa iya son ransa Ya gama sannan ta ɗaga kai ta kalle shi tace
"Allah ya baka haƙuri bazan kuma ba"
Wasu lokutan wannan halin na Mufeeda ba ƙaramin haushi yake Bashi ba duk laifin da zece tayi bazata taɓa musa masa ba, sedai taita bashi haƙuri ko kuma taita kuka.


Ta miƙe a hankali jiri na ɗibar ta ta tafi ɗaki, ƙirjinta yai mata nauyi se kokawa take da numfashi, tana shiga ɗaki ta samu guri ta kwanta ta rintse idon ta tana maimaita Innalillahi wa inna ialaihi raji'un.


Se ƙarfe goma Ammar ya miƙe ze tafi ɗakin sa yaga wayar Mufeeda akan kujera tana vibrating.








Masoyan Mufeeda ayimin afuwa labarin ne yazo a haka, ban fara rubuta shiba seda na kammala tsarashi, ayi haƙuri a bini a sannu dan ganin yadda zata kaya.


Bana son wannan stickers ɗin ko kuma thanks kawai Comments nake so dan Allah


Dan Allah in kin/ka karanta atemaka a dinga tayani sharing saboda masu bina pvt suna tambaya ta wasu pages ɗin abubuwa sunmin yawa.


Masu bina private suna sanar dani ƙorafi su ko shawara ina godiya daku da masu Comment


Fansa ɗina na watpad don't forget to vote


Har yanzu ƙofa ta a buɗe take domin gyara, sharhi ko kuma shawara
Ayshercool
07063065680
[16/07, 10:00 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com


Please follow me on Wattpad, vote and Comment


https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP




__Happy marriage life to my lovely friend_, __MARYAM MUSA ƁAIDU_I WISH YOU A VERY HAPPY MARRIAGE LIFE DEAR_


ELEGANT ONLINE WRITER'S




Page 22




Har Ammar ze share wayar ya tafi ɗakin sa se kuma ya ɗau wayar ya nufi ɗakin Mufeeda.


Yana zuwa ya tarar har tayi bacci ta dunƙule a guri ɗaya ko kayan jikin ta bata canza ba da alama dai baccin ba shiri ya ɗauke ta, fuskarta duk hawaye se ajiyar zuciya take.
Ɗan girgiza kai Ammar yayi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya cire mata hijjabin jikin ta, a wasu lokutan Mufeeda na da nauyin bacci sosai dan haka ya rage mata kayan jikin ta data kwanta da su, ya ƙura mata ido ta ɗan rame sosai, Amma tubarkallah tana da kyau dai dai gwargwado, musamman idan tana bacci se yaga ƙuruciyar ta ta ƙara fitowa, iya goshin ta ya ɗau zafi sosai yayin da sauran jikin ta yayi sanyi saboda kuka.


Ammar ya daɗe yana kallon ta yana jin wani abu na masa yawo a jikin sa ba tare da ya tabattar dame hakan ke nufi ba, a hankali ya janyo pillow ya kwantar da ita a kai yana cigaba da kallon fuskarta, sosai yake jin tausayinta be kamata ya cigaba da yi mata faɗa any how ba, hakan yana sata a cikin damuwa sosai, gefe guda wayar Mufeeda na ci gaba da vibrating, har ya miƙe ze bar ɗakin yaga vibration ɗin wayar ze iya tashin ta dan haka ya dawo ya sunkuya ya ɗau wayar, baƙuwar lamba ce babu suna ya danna alamar amsawa ya kai kunnen sa zeyi magana, shiru yayi yana sauraren abunda me wayar yake faɗa, kunnuwan Ammar ba zasu iya jure jin abunda wannan la'anannen dabe san darajar Aure yake faɗa ba, Idan kunnuwan sa ba ƙarya suka jiye masa ba to tabbas kalaman soyayya ne wanda ya kiratan yake faɗa


"tun ɗazu nake kiran ki saboda inji daddaɗar muryar ki ko da zagina kiyi in samu inyi bacci cikin kwanciyar hankali, Amma kinƙi ɗaga waya ta, kice wani abu mana mufeeda, Shikenan tunda ba zaki magana ba ɗaga wayar da kika yi ma ya tabbatar min kina lafiya, Ina son ki fiye da yadda wannan mijin naki me girman kai da baki da tabbacin yana sonki"


A hankali Ammar ya ajiye wayar, zuciyar sa tana wani irin bugu da ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjin sa ta fito, gashin jikin sa duk ya mimmiƙe saboda ɓacin rai, ya kalli inda Mufeeda take kwance tana bacci, se faman sauke ajiyar zuciya take she's looking so innocent.


Da ƙyar Ammar yaja ƙafar sa ya bar ɗakin yana ci gaba da jin Yadda zuciyar sa take bugawa.


Ɗakin sa ya koma ya samu gefen gado ya zauna ya dafe kansa da yake jin tamkar ba nasa ba, yanzu duk iƙrarin Soyayyar da Mufeeda take masa ƙarya take, zata iya cin Amanar sa tayi soyayya da wani a waje da Auren sa a kanta, lallai mata ba abun yarda bane.


Yana wannan tunanin message ya shigo wayar sa
"KA SA IDO AKAN MATARKA TANA AIKATA RASHIN GASKIYA A BAYAN IDON KA"


Wannan shi ne ire iren saƙon da'ake yawan turo masa


"to Amma waye wannan yake turo masa saƙon? Ya akayi me turo saƙon ya samu lambar sa har yasan Matarysa tana aikata rashin gaskiya a bayan idon sa?"
Yadda Ammar ya ga dare haka ya ga rana, bacci ya ƙauracewa idanunsa.


*********************


Ƙarfe biyu da rabi na dare Saima ce kwance tana bacci yayin da gefen ta Jabir ke kwance yana chatting, A hankali ta buɗe ido tana kallon sa ba tare da yasan tana kallon sa ba, voice message ɗin da aka turo masa ya buɗe yana saurarar, amon muryar mace ne ya fara tashi


"My Jabir i can't wait to see you as my husband, na ƙagu lokaci yayi ni kaɗai nasan me make ji akan ka, Amma ni matsala ta ɗaya gaskiya bana son zama da kishiya, bazan iya sharing ɗin ka da wata 'yar talakawa ba, Daddy ze baka gida ya canza maka mota wataƙila ma har muƙami yayi maka a cikin kamfanonin sa, Amma gaskiya ni batun zama da wata ne akwai damuwa"


Jabir yayi ƙasa da muryar sa yace
"My love karki ji komai ni kaina na ƙagu in mallake ki, dan babu wani farinciki da nake tsinta a Auren nan, Mata ta babu abunda ta iya, Ni ban san wani irin tsautsayi ya kaini na Aure ta ba, bayan ga irin ki, yanzu dai so nake ta haihu tukuna kar ace na sake ta da ciki, Amma da zarar ta haihu zan san abun yi"


Ba shiri Saima taji abunda yake cikin ta yayi wata irin juyawa saboda maganganun da Jabir yake yi, A hankali ta miƙe zaune saboda nauyin cikin dake jikin ta, Jabir yana kallon ta haka ta dinga bin bango da ƙyar ta shiga banɗaki, tana shiga ta durƙushe ta dinga zubar da Hawaye tana tuna yadda ta ƙaunaci Jabir, lokacin da take hasashen tayi dacen miji, take tunanin duk cikin mane manta Jabir ne ze riƙe ta ya kula da maraicinta, se gashi Jabir ɗin nata ya sauya komai ya dagule mata, babu wanda zata kaiwa kukan ta se Allah, ba uwa ba Uba, a hannun ƙanin mahaifinta ta girma, cike da tsangwama da bautarwa basu da burim da ya wuce suga ta wulaƙanta dan haka batun ta kai kokenta gidan su be taso ba, ta daɗe a banɗaki tana kuka sannan ta fito, yanzu ma a durƙushe ta dawo ta sa hannu ta ɗau fulo ta kwanta a ƙasa Jabir yana kallon ta amma be ce mata uffan ba ya ci gaba da Chatting ɗin sa.


Bacci ya ƙauracewa idanun Saima, har ƙarfe uku na dare Sannan Jabir ya kwanta, a hankali ta kuma jan jikin ta zuwa banɗaki tayi alwala ta koma ɗaya ɗakin ta shimfiɗa sallaya, nafila tayi ta idar ta ɗaga hannun ta zata yi Addu'a amma ta kasa se kuka me taɓa zuciya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login