Showing 30001 words to 33000 words out of 105124 words

Chapter 11 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16346

da mahaifin ta yana jiran isowar Ammar.


Suna ganin mahaifin Mufeeda suka nutsu suka dena wannan rawar kan da suke, suka nemi guri suka zauna, Ammar da Mufeeda na gaban Baba, Baba yai musu addu'a da nasihohi irin na dattawa, ya kama hannun Ammar yasa na Mufeeda a ciki yace


"Ammar ga Amanar Auta na nan, ayi haƙuri da halin ta yarinya ce ƙarama, tana da tarbiyya daidai gwargwado amma akwai yarin ta, Mufeeda ga Mijin ki nan ki kula da amanar Auren ki banda rashin ji, kinji Autar Baba"


Jinjina masa kai tayi tana goge Hawaye.
Baba yace "Allah ya baku zaman lafiya"


Yana gama faɗin haka ya miƙe ze tafi, yana jiyo kukan auta amma yayi waje, yana jin babu daɗi a ransa yana jin rabuwa da autarsa har cikin ransa.






Aminu yace "haba Mufeeda burinki ya cika Yaya Ammar ɗinki ya zama naki, meye na kuka kuma?"


Faruk yace


" ai da alama wannan Amaryar shagwaɓaɓɓiya ce, Ammar zaka sha daru fa"


Jabir ya katse hirar ta hanyar yi musu fatan Alkhairi suka miƙe zasu tafi, Ammar yayi musu rakiya suka yi sallama Faruk yace


"To Oga Ammar abita a sannu dai Yarinya ce ƙarama"


Haushi ya fara kama Ammar akan wannan zaƙewar da Faruk yake, amma ya basar suka yi sallama suka tafi, Yayin da Ammar ya rufe ƙofa ya dawo, tana nan zaune inda ya barta, tana ta goge Hawaye, tsayawa Ammar yayi yana Kallon Mufeeda dan besan ta inda ze fara ba, kaman shi a ce wannan 'yar yarinyar ce matar sa, wannan sunan yayi aure ne kawai amma shida wanda beba duk ɗaya.


"Ke wai bakya gajiya da wannan kukan ne? Se kanki yayi ciwo"


Shiru tayi masa ta ci gaba da goge Hawayen ta hada sheshsheƙa.


Tsaki yayi yace


"sekiyi tayi ai, in kin gaji ko kin gama ga leda nan ki ɗauka kaza ce a ciki"


Yana gama faɗin haka. ya wuce ɗaya daga ɗaku nan dake cikin falon, yaje ya rage kayan dake jikin sa ya watsa ruwa ya canza wasu kayan.


Fitowa falo yayi da niyyar ya kashe fitilar falon, kawai ya tarar da Mufeeda inda ya barta bacci ya ɗauke ta, girgiza kai yayi tare da jan tsaki




"ita wannan yarinyar banda yarin ta ma hadda taurin kai na damun ta"


Ya ƙarasa inda take yace "Ke, ke!" amma sam bata san me yake yi ba, hannu yasa ya bubbugi jikin kujerar da take jiki, amma bata motsa ba sema ajiyar zuciya data sauke alamar baccin ta yayi nisa.


Hannu yasa ya ɗago ta amma baccin ta take, bashi da zaɓi illa ya ɗauke ta zuwa ɗaya ɗakin da yake gado biyu akayi mata, yasa hannu ya ɗauke ta kaman wata 'yar shila se wani irin ƙamshin turare take zubawa.


Yana zuwa ya shimfiɗe ta akan gadon ya tsaya ya ɗan zuba mata ido, fuskarta harta kumbura saboda kuka, ya zare mata mayafin jikin ta, tare da gyara mata kwanciya, idonsa ya sauka akan zara zaran yatsunta da suka sha adon lalle ja da baƙi, zuba mata ido yayi na wani ɗan lokaci yana saƙaa abubuwa daban daban a ransa sannan ya miƙe ya kashe mata fitila ya tafi ɗayan ɗakin.


Mama kam kasa bacci tayi tana ta tunanin koya ya zata kaya wa autar ta? Wani hali take ciki? Kasancewar wannan ce ranar ta ta farko a gidan miji? (🙄🙄 bafa abunda ya faru mama ki kwantar da hankalin ki) Gaba ɗaya ta kasa sukuni bacci kam se ɓarawo ne ya ɗauke ta




Kiraye kirayen salla ne yasa Mufeeda farkawa, tana tunanin koya akai ta dawo nan oho ita dai tasan a falo take tana bacci


Ammar ya je da niyyar ya tashe ta salla ya ji motsin ta a toilet alamun ta tashi dan haka ya fice masallaci.


Tunda Mufeeda ta koma bacci bayan Asuba bata farka ba se bayan ƙarfe tara, ta farka da wani irin ciwon kai saboda kukan da tayi.


A hankali ta miƙe ta dudduba cikin kayan ta ta ɗako brush da toothpaste tayi brush, toilet ɗinta da famfon ruwa dan haka tayi wanka ta saka wasu kayan, Yunwa take ji sosai ga kanta yana ciwo haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito, Ammar ta hanga zaune akan three seater yana danna wayar sa.


A hankali ta fara takowa inda yake, ya ɗan ɗaga kai ya kalle ta, ta ɗan rame ga idon ta a kumbure saboda kukan da tayi, ta ƙaraso inda yake ta zauna a kusa da ƙafafuwan sa tace
"Yaya Ammar ina kwana?"


"lafiya ƙalau uwar kuka" ya amsa mata yana dannan wayar, ɗan ɗaga kai tayi ta kalle shi ta sauke kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta.


Shiru ne ya ratsa na wani ɗan lokaci cikin shagwaba tace
"nifa Yunwa nake ji"


Ammar Yace "ai na ɗauka ba kya ci, je kitchen ki duba"


Ta miƙe ta tafi kitchen, Tana zuwa ta tarar da kayan tea har ruwan zafi ya dafa, ba tayi wata2 ba ta haɗo tea ta dawo falo, ta zauna tana yin breakfast ɗin ta.


Ta kalli Ammar tace "yaya Ammar ɗina kayi breakfast kuwa?"


Kallon ta yayi yace "ke kici naki mana ina ruwan ki dani?"


Tace "to Allah ya bada haƙuri" ta cigaba da cin Abincin ta.


Daga nan shiru ya ƙara ratsawa tsakanin su, Ammar ya maida hankalinsa sosai akan wayar sa.


Tana cikin cin Abincin, aka kira Ammar a waya bata san waye ba se ji tayi yace
"A'a base kunzo ba bacci take yi, kuyi zaman ku kawai"


Buɗe baki tayi za tayi magana, ya galla mata harara taja bakin ta tai shiru ya kashe wayar sa ya ci gaba da danna waya.


Cikin shagwaɓa tace "Wai su waye za su zo kace kar suzo?"


Shiru yayi mata yaƙi kula ta, ta ture kayan Abincin tana tura baki.


"ni ka wani zauna kaƙi kulani ance za'azo kace baza suzo ba ni gaskiya kace suzo dan Allah"


Wata uwar harara yai mata wanda ya tilasta mata yin shiru.


Ta miƙe ta kai kwanukan data karya kitchen ta ajiye, ta dawo ta zauna ta zubawa Ammar ido.


Har yanzu kanta yana mata ciwo, Ammar ya maida kai sosai akan wayarsa yana game.


Kallon sa take yi yayi mata kyau sosai, inama ze kulata suyi hira a ranta tace "a sannu zan sauke wannan halin naka in dai nice"


Fashewa tayi da kuka, Ammar ya ɗago da sauri yace "Ke lafiya? Meye haka?"


Ta lanƙwasa "Nifa kaina ne yakemin ciwo"






Ammar yace "shine zakimin kuka? Wannan koke koken da kike yi ba dole kanki yayi ciwo ba, kiyi min shiru ni in duba magani in baki"


Yai maganar yana miƙewa, yana tafiya tayi murmushi, bayan tafiyar sa ɗaki tayi kwanciyar ta akan kujerar da ya tashi, ya dawo da magani a hannun sa da ruwa ya miƙa mata


"ni gaskiya bana son magani ka ƙyaleni ze dena"


Haɗe rai yayi yace "kika kuma Yimin kuka sena ɓata miki rai tashi ki karɓa"


Ta tashi zaune tasa hannu ta karɓa, ta ɓalli ɗaya zata ƙara ɓalla yace
"ke baki da hankali, maganin har nawa zaki sha?"


"to manya ba guda biyu suke sha ba?" ta faɗa kaman za tayi kuka


Hararta yayi yace "suwaye manyan?"


Yasa hannu ya karɓe na hannun ta data ɓallo ya raba biyu ya miƙa mata rabi yace
"ungo" tsayawa tayi tana kallon sa tace "rabi fa ka bani"


"eh rabin, baki kai ki sha guda ba, ƙarama dake zaki sha magani har biyu saboda shirme, da masu chemist sun fito yanzu da na ruwa zan siyo miki" yai maganar in very serious tone yana wani haɗe rai.


Wata uwar dariya ce ta kama Mufeeda, Ammar yayi mugun raina mata hankali itace ya kamata tasha magani na ruwa sekace jaririya ta gimtse dariyar ta a ranta tace


"lallai Yaya Ammar muje a haka, ka shirya ganin ƙuruciya samfur samfur da yarinta zaka gane kacemin yarinya kuma ƙwaila dani kake zancen, zan maka aikin yara kala kala" .








Masu Comment da addua ina godiya Allah ya bar ƙauna
Domin shawara, gyara ko kuma sharhi
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )








*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com





ELEGANT ONLINE WRITER'S



**Daddy, Baba, Abba, Appa, papa, Yaya, Abee, babi, father, Abbu ❤️❤️❤️*
*I want tell you that we love you 😍😍😍*


*HAPPY FATHER'S DAY*


_Baba kuɗin mota, school fees, nepa bills, saloon, rapper everything father, father, father_


_we rest in your shoulders in every moment,_
__every day is yours but today is special day for you, i will use this opportunity to tell you that we all loves you endlessly our dads we really appreciate your efforts toward us especially in this very period of hardship, on behalf of every female daughter we wish you a very happy moment, we wish you a very long healthy life, more strength, joy happiness and halal money in your account. May Allah_ _subhanahu wata'ala crown your efforts towards us with countless rewards_
_Your female daughter's really loves you 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃_
_
_For those that thier father's pass away, we pray for them Allah's Rahma and Janna, may their gentle souls rest in perfect peace may Allah subhanahu wata'ala gives them a highest rank in jannatul fiddausi
Ameen
_
_I dedicated this page to all fathers all over the world thank you 😍 😍 😍 for your love*_


*Your female daughters really loves you* ❤️❤️







Page 11




Haka Ammar ya kwanta yana mamakin Mufeeda.
Da gari waye Ammar be tashi da wuri ba, bacci yake har kusan takwas na safe.


Mufeeda ta shiga kitchen ta dafa tea tun dare Ammar ya shigo da bread, tayi amfani da ƙwan nan da albasa da kuma naman jiya da suka kasa ci ta sarrafa bredin nan ta gasa, har ta gama Ammar be tashi daga bacci ba.


Ɗakin ta tafi domin tayi wanka kafin ya tashi, amma harta fito ta kintsa jikin ta bacci yake, ɗakin sa ta tafi, tana zuwa ta tarar yana ta baccin sa.


Kan gadon ta hau ta ɗan tsura masa ido a fili tai murmushi tace


"Masha Allah mijina yafi na kowa kyau"


Ta ɗan daki fulon da yake kai, tana faɗin "Mijin So, ka tashi haka baccin ya isa fa"


A hankali yake buɗe idon sa har ya buɗe su duka ya sauke akan Ƙwailarsa, bakin ta raɗau da jan Jambaki, tayi ɗare ɗare akan gadon sa, ƙura mata ido yayi ba tare da yace komai ba ga ƙamshin turaren ta me daɗi yana ratsashi, se sake lumshe ido yake.


Murmushi tayi tace "good morning Baby, na dafa ruwan wanka, in kayi seka fito mu karya"


Yadda ta fita daga ɗakin sa a zuciye daren jiya beyi zaton zata kulashi ba, wani ƙarin mamakin wai har tasan ta dafa masa ruwan wanka.


Yanayin kallon da yake mata ne yasa ta tsarguwa, dan haka Ta juya ta sauka ta bar ɗakin, ta koma falo tana jiran sa, koda ya fito falon ƙamshi ne daban daban yake dukan hancin sa, ya samu guri ya zauna harta jere komai na breakfast ɗin.


Ta kalle shi a shagwaɓe tace "Nagaishe ka amma kaƙi amsawa ko"


"to sannu, lafiya ƙalau" ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin janyo flask ɗin shayi.


"No tsaya in zuba maka"


Ta haɗa masa tea, gurin zuba Madara tana zuba spoon ɗaya yace "Ya isa haka"


"taɓ spoon ɗaya, gaskiya ni spoon ɗaya yayi min kaɗan" shiru yayi ya fara shan tea ɗin sa ya kalle ta yace "Ina bredin ne?"


Plate ta miƙo masa ɗauke da bredin da ta sarrafa, ya kalli bredin yace "meye Wannan?"


"kaci kaji mana"


"bredin kika wulaƙanta ya koma haka?"


"ni ban wulaƙanta ba, kaci kaji da daɗi"


Girgiza mata kai yayi yace "bazan ci ba"


Hannu tasa ta ɗakko bredin ta matsa kusa da Ammar ta kwantar da muryar ta sosai tace


"dan Allah Yaya Ammar kaci, na yadda idan babu daɗi na wulaƙanta maka Abinci kamin duk hukuncin daya dace dani, dan Allah"


Yadda tai maganar ne cikin sanyin murya yasa ta bashi tausayi, hannu yasa ze karɓa, ta ɗan girgiza masa kai ta miƙa masa bakin sa, ya buɗe baki ta saka masa.


Ai ba ƙarya bredin nan ba ƙaramin kaiwa Ammar yayi ba, dan yayi test sosai a bakin sa, Mufeeda tasan idan tayi magana ze iya mazewa ya fasa ci dan haka ba tace komai ba ta ƙara miƙa masa wani, ba kunya ya amshe abun sa ya taune ba tare da yace komai ba.


Zata kuma gutsurowa yace "banni inci da kaina, zuba naki kici"


Murmushi kawai Mufeeda tayi tace "Shikenan zanci, gama cin naka"


Ammar yaci bredin nan sosai dan ba ƙaramin daɗi yayi ba, se yaji da'aka sarrafa bredin zuwa wani abun daban yafi bredin daɗi ma, amma be iya buɗe baki yace yayi daɗi ba.


Ya kammala ci ta miƙa masa tissue ya goge hannun sa da bakin sa, har ze tashi ta kalle shi cikin salon kashe murya tace


"Mijin baby ba kace komai ba, yayi daɗi kuwa?"


Ɗan kallon ta yayi ya maze tare da ɗan tsuke fuska yace "ba wani daɗi na dai cine kawai maganin Yunwa"


Murmushi tayi tace "Tunda dai har ya wuce cikin ka ba kayi amai ba ai shikenan" tai maganar tana murmushi, ta tattare Kwanukan taje kitchen ta wanke.


Ta dawo ta tarar da shi a zaune a falon be tashi ba "Yaya Ammar ya haka ba zaka fita bane?"


"Se an jima zan fita" ya bata amsa


"shikenan Allah ya kaimu anjiman, ai gara ka zauna in ta kallon abuna ko?" tai maganar tana kashe masa ido ɗaya.


Hararar ta yayi ya kauda kansa daga kallon ta, tai murmushi ta zauna tana facing ɗinsa, lokaci lokaci suna haɗa ido se yayi sauri ya kau da kansa.


Ta tattara attention ɗin ta tana ƙoƙarin gano meya hana shi fita yau da wuri, kullum yana gama karyawa yake fi cewa, Amma yau yaƙi fita kuma yana zaune a falo, abun mamakin kuma se satar kallon ta yake, sake ɗaga ido yayi suka haɗa ido, ya ɗan maze yace


"lafiya kike min wannan kallon ƙurillan?"


A ranta tace "sekace shiba ni yake kallo ba" amma seta ta taso daga inda take tazo kusa da shi ta zauna ta kalle shi tace


"Kasan menene? So nake in taɓa gemun ka, shike tsolemin ido"


Ɗan buɗe baki yayi yana kallon ta, lallai yarinyar nan ta mugun raina shi, kawai ya ɗauke kansa yace


"tashi daga kusa dani mara kunya"


ƙara narkewa tayi a jikin sa tace
"dan Allah Yaya Ammar sau ɗaya fa zan taɓa dan Allah"


Juyowa yayi yana kallon bakin ta, wanda yayi raɗau da jan baki, se ɗaukar ido yake, dukda kitson kanta ya fara tsufa amma har yanzu yana ɗaukar hankalin Ammar, Yadda take maganar very serious kamar 'yar yarinya.


Ta kuma cewa "in taɓa dan Allah ?"


"Tashi kije kiyi breakfast seki zo ki taɓa"
Murmushi tayi tace "to"


Ta miƙe tana fara' a ta haɗa breakfast ta zauna tana karyawa, ta nayi tana kallon sa tana murmushi, ta kammala ta tattare Kwanukan, tana dawowa ta tarar ya ɗakko mukullin sa ze fita.


Ta ɗan ɓata fuska tace "haba Mijin bebi, haka muka yi da kai? Banfa taɓa ba"


"Ke bana son shiririta, ni fita zanyi Ungo wannan" ya miƙo mata kuɗi ɗari biyar


"Me zanyi da wannan? Naga ka siyo komai na amfani ai"


"Eh baki nayi ko zaki sai wani abun"


"ni babu abunda zan siya"


"Ke ki karɓa meye haka?" ya ɗanyi maganar a hasale.


Durƙusawa tayi tasa hannu biyu ta karɓa tace


"Nagode Allah ya ƙara Arziki, yaja da ran su Umma"


"Ameen"


Suka yi Sallama ya fice.


**********************


Fa'iza ce keta kaiwa tana komowa a ɗakin ta tarasa meke mata daɗi, tana ƙoƙarin tuna menene mafita akan halin da take ciki tabbas tana son Ammar kuma tunda har ya iya Aure ƙaramar yarinya kaman wannan to tabbas itama zata iya jarraba sa'arta akansa amma ta yaya? "


Fitowa tayi falo ta tarar da Maman ta tayi baƙuwa, ba tare da ta kalli inda baƙuwar take ba tace "Mami dan Allah zan fita anguwa, zanje gidan su Nasreen"


"To kiyi sauri karki daɗe, bana son babanku ya dawo yaita min mitar ba kwa nan"


(Nasreen ɗin 'yar ƙanin mahaifiyar Fa' iza ce)


"Ok"


Baƙuwar tace "Ahh Fa'iza ba magana?"


Fa'iza ta ɗan juyo ta kalli matar tace "Ohh sannu" a ƙalla matar tayi sa'ar mahaifiyar Fa'iza, bata kuma bi takan Matar ba ta wuce ɗakin ta.


A gurguje ta watsa ruwa ta shirya ta fice daga gidan, ba ta tsaya ko ina ba seda taje gidan su Nasreen, ta shiga da sallama tayi sa'a Nasreen ɗin tana tsakar gida tana mopping, Nasreen na ganin ta tace "hajiya fa'iza wannan zuwa haka babu waya, anjima nake tunanin in zo gidan ku fa"


"Kinga gurin ki nazo dan Allah ina Umma?"


"ba ta nan tana Islamiyya"


"Muje ɗaki dan Allah ina cikin damuwa"


Ɗaki suka shiga kaman yadda Fa' iza ta buƙata.


"Nasreen wallahi nayi sakacin kasa ga yawa Ammar abunda yake cikin raina, saboda ina ganin baze soni ba, se gashi ance yarinya ƙarama ya aura"


Nasreen tace "Wallahi yarinya ce sosai, ai ke baki je gurin dinner ba, mu munje munga komai wallahi yarinyar nan bata fi shekara sha shida ba, 'yar ƙarama da ita se iyayi in gaya miki tsaf zaki iya goya wannan' yar abar"


"dan Allah ba wannan ba meye abunyi yanzu? Wallahi Nasreen baki ji yadda nake ji a raina ba, ina son Ammar sosai fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login