Showing 87001 words to 90000 words out of 105124 words
Chapter 30 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt
korar kare"
Shiru Umma tayi tace "Ammar ɗin ne yayi miki haka?"
"Wallahi haka yayi min, ranar ma munje da daddare amma baki ga korar karen da yayi min ba, tunda Mufeeda ta nuna bata sona yake min wulaƙanci"
Shiru Umma tayi sannan tace "Amma basu kyauta ba, kiyi haƙuri Insha Allah zan musu magana, Amma Mufeeda mutuniyar kirki ce"
"Hmm kudai take wa kirki ni ban san me nayi mata ba, kuma goyon bayan ta yake, yafi sonta akan mu 'yan uwansa"
Umma tace "Haka naji Jidda tana ƙorafi akai, Amma ni dai ba tayi min nagani ba, Amma Insha Allah zan masa magana, kiyi haƙuri"
"bakomai Umma na dai gaya miki ne dan kisan me' ake ciki"
Haka Fa'iza ta ci gaba da ɓata Mufeeda a gurin Umman Ammar, Sannan tai mata sallama ta tafi.
Ammar yana ta sauri ya koma gida, se kuma yayi tunanin bari yaje gida ko ze samu Umma tayi tuwo ta bashi ya kaiwa Mufeeda.
Sedai yana zuwa ya tarar kamar ran Umma a ɓace, Umma tace
"Yawwa Ammar naji daɗin zuwan ka, dama ina son ganin ka"
Ammar yace "to Umma Allah yasa lafiya"
"Ammar ɗazun nan Fa'iza ta bar gidan nan, ta kawomin ƙararka akan abunda kayi mata, tazo gidan ka amma kaƙi bari ta shiga gidan ka, wannan wane irin haline? Bekamata ka dinga fifita Matar ka akan 'yan uwanka ba, bance karkaso Matar ka ba amma dai ka kula da' yan uwan ka"
Ammar yaso yayi ƙoƙarin kare kansa, Amma wani abu daya koya a gurin Mufeeda shine, muddin lokacin da babba yake maka magana kayi ƙoƙarin yin magana da niyyar kare kanka, to hakan na iya tunzira mutum, dan haka Ammar yayi shiru Umma ta gama faɗan ta, sannan ya ɗago kai yace
"to Umma Allah ya baki haƙuri, Insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba"
Umma tace "Yawwa ina Mufeedan tana lafiya?"
Ammar yace "lafiya ƙalau tana gaishe ki, bari in koma in Abba yazo kice ina gaishe shi"
"to tsaya ina da gyaɗa me gishiri da aka kawomin bari in baka ka kai mata, sannan ka gaya mata akuyar ta ta haifi yara uku"
Bece komai ba se shiru da yayi zuciyar sa na tafasa, yana tunanin wane hukunci zeyiwa Fa'iza ya huce
Ɓacin ran da Ammar ya tarar ya hana shi gayawa Umma batun tuwo da rashin lafiyar Saima ba, ya karɓi gyaɗa harda tsintsiyar laushi ya tafi.
Ransa a ɓace sosai ya fito daga gidan ze tafi, Halima ce ta dawo daga Islamiyya taga Ammar yana ƙoƙarin tafiya
"Yaya Ammar Ashe kazo? Ina Anty Mufeeda?"
"tana lafiya" Ammar ya bata amsa ya shige A daidaita sahunsa ya tafi. Halima tayi mamakin ganin Ammar ya fito daga gida ransa a haɗe haka, ta ƙarasa ta shiga gidan.
"Umma wai me kikayiwa Uncle ne? Na ganshi da zan shigo kamar ransa a ɓace"
"me kuwa zanyi masa? Na dai yi masa faɗa ne Fa'iza da Jidda suna yawan kawo ƙorafi akan yana fifita matarsa akan 'yan uwansa, kin san duk abunda Baki yayi yawa, ɗazuma
Fa' iza tazo ta kawomin ƙarar sa shine na ɗan Ja masa kunne dai shine yake fushi"
"Umma kenan kuma a ce duk yawan Family ɗin mu su biyu kawai yakewa haka? Sudai suna da wata manufa a ransu amma wallahi Yaya Ammar baya nuna banbanci, kuma ita Anty Jidda ina itama nata mijin se abunda take so yake yiwa 'yan uwan sa"
Umma tace "to nidai ban zaɓi ɓangare ba kawai dai nayi masa magana ne"
****************
Fa' iza seda ta gama gantalin gidan ƙawaye sannan ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da motar Faruk a ƙofar gidan su, tsaki tayi zata shiga gida Faruk ya fito da sauri yace
"Ke kina ganina amma kika wani basar zaki wuce, lambar yarinyar nan fa ta dena shiga idan na na kira dole ki samo mana wata"
A fusace Fa'iza tace "toni ina ruwana? Ba na gaya maka kowa yayi ta kansa ba, na gaji da shirirtar da kake babu wani kyakkyawan result, dan haka kowa yayi ta kansa"
"Ke kin isa mu fara abu tare yanzu ki zame, ai ta inda aka hau ta nan ake sauka, Yadda muka fara tare haka zamu ci gaba"
"Baza'a sauka ta inda aka hau ɗinba, dalla ja jiki ka bani guri in wuce, niko uban me ya kaini ma haɗa kai da kai tun farko oho"
Faruk yace "Hmm wallahi baki isa ki zame ba, in ba haka ba in watsa komai"
"inka fasa shege ne kai, ka tsaya ka jira in nayi nasara na fidda ita daga gidan kaje ta ƙare muku can, Amma a yanzu kowa yayi ta kansa"
"Ni kike gayawa haka?"
"An gayamaka waye kai? Banda banza wofi"
Tas, Faruk ya ɗauke ta da mari, kallon sa tayi idonta fal Hawaye tace "Nika mara?"
"Na mareki ɗin, kin isa ki cemin banza wofi in ƙyale ki"
"Wallahi baka isa ba, zaka gane baka da wayo sena ɗaura maka sharrin da baka isa ka kwance ba, bunsuru me bin matan mutane kawai"
"inkin Fasa min sharrin keba 'yar halak bace, munafuka koma meye dawa mu keyi inba tare ba"
Hankalin mutane ne ya dawo kansu, mutane suka fara taruwa.
Fuuu Fa'iza ta shige cikin gida tana kuka, tana zuwa ba tayi tunanin komai ba ta gayawa Mahaifiyar ta cewar wani ne ya mareta a waje.
"Mari kuma? Waye ya marekin?"
"wani Faruk ne abokin Yaya Ammar"
Se kuma da ta faɗa tayi wani tunani.
Mahaifiyar ta tace "lallai to ke me kika yi masa daze mareki akan me? To wallahi baze yuwu ba, bari Yayanki yazo gurin 'yan sanda zan kai ƙarar sa, ko kuma shi Ammar ɗin in nemeshi ya gayamin dalilin da yasa Abokin sa ya mareki"
Fa'iza tace "A' a Umma ki ƙyaleshi kawai nasan matakin da zan ɗauka"
Umma tace "Saboda me zan ƙyale shi, baze yuwu ba"
**************
Ammar a zuciye ya koma gida, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Mufeeda tana ta jira Ammar ya dawo taji ya jikin Saima, Amma yanayin sa ya nuna mata ransa a ɓace yake.
Ya dire mata gyaɗa da tsintsiyar laushi, murmushi tayi tace "da gani ba tambaya wannan saƙon Umma ne, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"
Shiru yayi be amsa ba se ƙara haɗe rai da yake yi
"Mijina ya na ganka a hakane? Kodai Jikin Anty Saiman ne?"
"A'a jikin ta da sauƙi"
"to kowani abun aka kuma cewa nayi?"
Kallon ta yayi kamar ya gaya mata kawai ya fasa yace "A'a bakomai"
Ƙyaleshi Mufeeda tayi ta zubo masa Abinci, ya kalle ta yace "A haka kika yi girkin?"
"Naji zan iyane shiyasa na girka maka"
Ammar yace "ke kuma me kikaci?"
"bakomai amma ga Gyaɗa nan da Umma ta bani se inci, amma Allah yau da baka karɓo min tuwo ba seda nayi kuka"
Hararta yayi yace "kawai se in ɗau kwano in tafi maƙota roƙon Abinci kamar Almajiri"
"Allah ya baka haƙuri, ci Abincin ka"
Haka ya maze ya ci Abincin sa, Amma ransa babu daɗi.
Sallar isha'i ma a gida yayi, Mufeeda tana lura dashi, ya kwanta a falo yayi shiru abubuwa da yawa suna damun sa a rai.
Mufeeda tazo ta zauna a kusa dashi, ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa tace
"Abun so na, dukda nasan nayi yarinta daka gaya min abunda ke damunka amma ganin ka a wannan mood ɗin yana sani a damuwa"
Shafa gashin kanta yayi yace "Waye yace miki ina cikin damuwa?"
"Hmm ai kallo ɗaya nake maka in san a wani yanayi kake, farinciki baƙin ciki ko makamancin hakan duk ina iya ganewa"
Ɗan murmushi yayi yace "kinmin wayo da yawa, ya akayi na bari duk kika gane ni haka?"
"Yaya Ammar gobe in Allah ya kaimu zaka kaini inga jikin Anty Saiman?"
"Ai ko kinje ba zaki ganta ba, likitoci ne kawai suke shiga inda take, amma insha Allah sunce gobe in Allah ya kaimu zuwa jibi idan jinin ta ya sauka za'a cire mata abunda ke cikin nata"
"to Allah ya raba su lafiya, Amma fa harna tsorata da haihuwa"
"Ai komai na Allah ne, kuma Insha Allah ina ta Addu'a ki rabu da cikin nan lafiya"
Ƙasa ya kuma yi da muryar sa yace "kefa Jaruma ce, tsoro ba naki bane tunda 'yar Jaririya dake kike ɗauke da Jaririn Ammar a jikin ki" yai maganar ya shafa cikin nata da kaikace ko kayan ciki babu a ciki.
"Kaga cikani inje in kwanta inajin Bacci ne"
"zomuje ɗakina mu kwana a can, kinji ƙwailata"
Zaro ido tayi kaman zata yi kuka tace "taɓ gaskiya ni A'a wallahi"
"meyasa ba zaki ba?"
"Nifa Yarinya ce dan Allah ka ƙyaleni wallahi hanani bacci ka keyi"
Sosai ta bawa Ammar dariya,
"you are ready for it, that's why you choose marriage"
Zumɓura baki tayi tace "ba wani ni kawai dan ina sonka ne"
ɗaga ta yayi yana dariya tafi da ita ɗakin nasa.
***************
Da sassafe Ammar yana ta shirin fita Maman Fa'iza ta kira shi a waya, ya ɗauka itama mitar zata yi masa, dan haka ya amsa cike da basarwa bayan sun gaisa tace
"Ammar a cikin abokan ka wani ya mari Fa'iza waishi Faruk, yanzu hakan na kai maganar gurin 'yan sanda, dan Allah in ba zaka damu ba ƙarfe goma kaje police station ɗin ayi maganar"
Ammar yace "gaskiya Anty kiyi haƙuri, kinga ina da aiki da yawa, ita tasan meya haɗo su kuje can ku warware abun a station ɗin" Ya katse wayarsa ya fice.
****************
Rana tayi sosai Mufeeda tana tsaka da wani bacci me daɗin gaske, dan kwanan nan Mufeeda tana fama da kasala da yawan bacci, tana cikin baccin taji ana hayaniya a waje kamar ana yaƙi a gigice ta miƙe ta saka hijjabi ta leƙa ƙofar gida, tana leƙawa taga su maman Nur ne suke ta Masifa suna faɗa a bakin layi, Maman Sadiq taje ta gayawa maman Amir cewar Mijin ta na soyayya da ƙanwar maman Nur, nan suka dinga tonewa juna Asiri, dambe ne ya kaure a tsakiyar layi aka yagawa Maman Nur riga ko vest babu a jikin ta aka danna kanta a kwata.
Da sauri Mufeeda ta mayar da ƙofarta ta rufe, ta koma cikin gida dan ita abun kunya ne a gareta a zo wucewa ace anganta tana kallo ana dambe a layi, gaba ɗaya matan layin nan suka firfito suka dinga tonawa juna asiri kuma wani abun in aka gangaro daga gurin Sa'idu me kayan miya magana ta fito.
Hajara ce ta fito itama jin Hayaniya tayi yawa, taje tana ƙoƙarin rabawa.
Maman Amir ta juyo kanta zata daka, Hajara tace "Wallahi kika taɓani sena karya ki gida biyar na bawa karnuka, nafiki rashin mutunci"
Maman Amir tace "Aikin banza keda a gurin sa'idu me kayan miya ake bada labarin baki da miji zaman kanki kikeyi, karuwa kawai"
Hajara tace "Yawwa dama irin wannan ranar nake jira da zaku taɓoni, zan nuna muku wace Hajara yau 'yan unguwar nan babu me rintsawa wallahi, zaku ga tsiya
Tofa!!!
Share please
Domin sharhi gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680.✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨
( *Sai Mata* )
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*_A SHORT LOVE STORY_*
*Story and written by*
'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''
Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba
Watpad @ Ayshercool7724
What's app 07063065680
Gmail Www.ayshertadam@gmail.com
Please follow me on Wattpad, vote and Comment
ELEGANT ONLINE WRITER'S
NOT EDITED
Page 27
Sun ɗauka Hajara ƙarya take, Maman Amir tace
"ke ɗin banza ki hanamu bacci, uwarmu ce ke? Ko kuma halittar mu kikayi?"
Maman Nur kam gida ta shiga ta sako wasu kayan ta nufi gurin Sa'idu me kayan miya tana ruwan Ashar, Hajara tace "tunda kuka ce zaman kaina nake wallahi sena nuna muku zaman kaina nake, A bariki aka haifeni kuma a bariki na girma"
Gurin Sa'idu me kayan miya Hajara ta fara tafiya, tana zuwa ta tarar da wasu matan daya haɗawa munafunci suna ta zagin sa, ko a jikinsa yana siyarwa da wasu kayan miya ya maida su kamar wasu banzaye.
Hajara na zuwa tafara fatali da kayan miyar nasa, ya kalleta a fusace yace "ke mahaukaciyar ina ce meye haka?"
"Mahaukaciyar gidan ubanka ce, kai ni zakayiwa munafunci, kace ina zaman kaina, baka da aiki se tara matan mutane suma jakuna su biye maka, kaita haɗa gulma kuna zagin mutane daga yau in ance ka sake ba zaka kuma ba"
Ta cigaba da fatali da kayan Sa'idau, nan aka saka wawa, har ɗan cinikin nasa na ranar, wannan matar tace yace kaza waccan ma haka guri ya hargitse da hayaniya.
Mufeeda kam Amai ne hana ta sakat, gashi cikin ta ba komai ga amai se taso mata yake, jin layin nasu yayi tsit ne yasa ta ɗauka sun watse dan haka tasa hijjabin ta, tafi ta ko guava ta samu ta siya.
Aikuwa tana fitowa bakin layi inda Sa'idu me kayan miya ke siyar da kayan miya ta tarar da mata sunyi dandazo a gurin, ga wasu kayan miyan na iyo a kwata, wasu an tattake.
mata sun sashi a tsakiya suna zagin sa tare da tsine masa har zata wuce Maman Nur tace
"Yawwa Mufeeda gara da Allah ya kawo ki, ga munafukin da yaje yana yamaɗiɗi a unguwa wai ya ganki kina zance da wani, har mijin ki aka tara aka gayawa, lokacin da kika tafi gida ba lafiya yace auren ki ne ya mutu"
Mufeeda tace "to ni ina ruwana? Me kike so ince ko zan manta yadda ni kika sani a gaba da sharri da cin mutunci a layin nan, a fakaice har maita kika ɗoramin yanzu da ta kwaɓe muku zaki dinga gayamin, kuje Allah ne ya kama ku"
Mufeeda tai wucewarta ta tafi gurin me guava, tana tsaye tana cinikin guava, sega Alhaji Idris yayi parking a motar sa, Sam Mufeeda bata ganshi ba seda me guava yace mata "Hajiya ana magana" tana juyawa Alhaji Idris yace "me guava zubawa babyn nan ko ta nawa take so in biya"
Banza tayi masa tace
"me guava ban ta iya kuɗina"
Me guava Ya zuba mata kamar yadda tace ya bata ta nufi hanyar gida, aikuwa Alhaji Idris ya biyo ta, ta ratse tabi ta lunguna dan ta guje masa, Amma yayi parking ɗin motar sa ya bita.
Sosai Mufeeda tasa gudu yana binta yana ta tsaya taji, da ƙyar ta kai gida tana zuwa ta buɗe ta shige ta rufe ƙofar ta, a tsakar gida ta zube tana ta haki, ya daɗe a gurin yana buga gate ɗinta wai ta fito suyi magana ko nawa take so ze bata, hawaye ne ya fara bin idon ta, wannan wace irin masifa ce daga yin Auren ta zuwa yanzu ta haɗu da ƙalubale daban daban wanda bata san iyakar sa bama, wani irin zamanine wannan ace dattijo kamar Alhaji Idris yana bin yarinyar da yayi jika da ita kuma yasan matar Aure ce.
Tana cikin wannan tunanin taji ƙarar harbin bindiga, ai da gudu ta shige ɗaki ta ƙule a gado jikin ta na cigaba da tsuma.
Hajara ce tayi waya ta kira sojoji, Ashe baban ta babban General ne na Sojoji, mijin ta ma babban soja ne tunda aka haife ta a barrack take, aka turo mijin ta aiki kano tace ta gaji da zaman barrack tana so yakama mata gida ta zauna a wajen barrack, suna shirye2 dawowa kanon aka tura shi yaƙi Maiduguri, dan haka se yasa abokin sa ya kama mata gidan ta dawo ta zauna, dan haka tai waya aka zo hadda Sojoji mata aka tattare mata su Sa'idu da su Maman Nur da suka yi wa juna jina jina saboda duka, dan har jaririn da Maman Nur take goyo aka fasawa kai saboda dambe.
*********************
Maman Fa'iza taji hasuhin abunda Ammar yayi matuƙa da yace babu ruwan sa akan lamarin, ita kanta Fa'iza taji daɗi da yace ba ruwan sa dan tana tsoron Asirin su ya tonu.
Faruk yana gurin aikin sa 'yan sanda sukazo suka tafi da shi, Yayan Fa' iza Abubakar shi ya kai ƙarar sa gurin 'yan sanda akan marin da yayi wa Fa' iza.
Maman Fa'iza ta kira Maman Ammar a waya ta gaya mata abunda ya faru da yadda suka yi da Ammar, Umma ta bata haƙuri tace za tayi masa magana
Umma ta kama mita tana "Nikam na rasa wannan hali irin na Ammar, meye a ciki dan yaje ya taimakawa 'yar uwarsa, kawai yaje station aji
ba' asin meyasa ya mareta ayi musu tsakani tunda Abokin sane shine baze iya ba, kai Allah ya shirya Ammar.
Abba yace " Banga laifin sa ba, tunda bashi yayi marin ba kuma ba shi yace ayi ba, da alaƙar kirki ce tsakanin ta da Shi Farukun da baze mareta ba, babu yarinyar da zata kama kanta wani ya mare ta a banza"
Umma tace "dukda haka dai, tunda har Maifiyar Fa'iza ce ta nemi yaje ai se yaje, inda mutunci ai itama uwarsa ce"
Abba yace "hakane"
Umma ta kira Ammar a waya, yana tsaka da tuƙi sega kiran umma, Yayi parking ya ɗaga wayar, bayan ya gaishe ta umma tace
"Ammar kai duk maganar da za'a gaya maka sedai ta shiga ta dama ta fita ta hagu ko? Yanzu abunda kayiwa Maman Fa'iza ya dace? Meye laifi dan kaje police station anji ba'asin da yasa ze mareta? Aiba raguwa zakayi ba"
"Umma kenan, Allah ya baki haƙuri, amma ni dai nasan Faruk abokina ne, Amma bansan wace irin Alƙace a tsakanin su da har yasa ya mareta ba"
Umma tace "koma dai wace iri ce, kaje kaji kodan Mahaifiyar ta"
"shikenan zani Insha Allah"
"Ai ba zaka ba kaje yanzu suna police station ɗin unguwar su Fa'iza na nan babban titi"
"to Umma"
Ya katse wayar,