Showing 84001 words to 87000 words out of 105124 words

Chapter 29 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

16343

haihuwar ce se kimin waya"


Shiru tayi tana binsa da ido ya ɗau mukullin motar sa ya fice, duhu ta ci gaba da gani a idon ta dan haka ta nemi guri ta kwanta akan kujera


******************


Mufeeda taƙi yadda Ammar ya maida ita Asibiti tace ita likita yace se cikin ta yayi wata huɗu sannan zata fara zuwa Awo haka ya haƙura ya ƙyale ta.


Bayan fitar Ammar sega su Maman Amir sun shigo mata.
Fuska ba yabo ba fallasa Mufeeda ta karɓe su,
Maman Amir tace "Mufeeda ashe baki da lafiya kina gida? Hankalin mu ya tashi kwana biyu bama ganin ki, shine muka tambayi mijin ki yace mana kina gida babu lafiya"


Mufeeda tace "Eh banji daɗi bane ba"


Maman Sadiq tace "Allah sarki sannu, munso muje gidan naku duba ki ai, to kin san halin Mijin naki bashi da fuska shiyasa bamu tambaye shi ba"


Mufeeda tace "Ai na warware ma Alhamdilillah"


Maman Amir tace "Aikam dai mijin ki bashi da fuska, ai Sa'idu me kayan miya ne ya gaya mana a gaban sa kika wuce kika hau A daidaita sahu kaman ba kya hayyacin ki, kina ta kuka bayan fitar shi mijin naki, shine hankalin mu ya tashi muka ce bari mu biyo muga ko lafiya, shine ya gaya mana ai baki da lafiya kina gida "


Mufeeda tace " Sa'idu me kayan miya kuma? "


Maman Amir tace " Eh wallahi munje cefane yake ga yamana "


Jinjina kai Mufeeda tayi ba tace komai ba, suka ƙaraci soki burutsun su, ciki hadda yi da Maman Nur wadda ta kasance a cikin su, Mufeeda ba tace musu komai ba, ganin Mufeeda bata da niyyar kulasu yasa su kayi mata sallama suka fita.


Ta biyo su tana ƙoƙarin rufe gate ɗinta taga ɗan gidan Maman Nur ya zubara mata da ƙanzo a ƙofar gida, kanta tsaye babu fargabar komai a gaba su Maman Amir, dukda tasan zasu gayawa uwassa tace seya kwashe, idan ya kuma zuba mata ƙanzo a ƙofar gida seta zane shi, haka yaron ya durƙusa ya kwashe yana kumbura fuska yace
"nifa ba barmu ce tace inzo in zubar anan"
Mufeeda tace "ka koma ka gaya mata ƙofar gidana ba bola bace, ta dinga zubarwa a ƙofar nata gidan da yafi kama da bola akan nawa, idan na kuma ganin ka zuba min ƙanzo a ƙofar gida sena mareka"
Mufeeda tana sane ta faɗi wannan maganganun dan tasan se sun gayawa Maman Nur, tana shirin rufe gate ɗinta sega wata mata, za tayi shekaru Ashirin da bakwai ta kalli Mufeeda tace
"Baiwar Allah, kece Matar gidan nan dan Allah?"
Mufeeda tace "Eh nice"
Matar tace "Yawwa dama nice na tare a nan kusa da gidan ki, nazo mu gaisa bakya nan suna na Hajara"
Mufeeda tayi murmushi tai mata maraba suka shiga cikin gidan, suka zauna a falo, suka ɗan taɓa hirar rayuwa da hirar gida, Matar tace "Amma sam banji daɗin zuwa na unguwar nan ba wallahi"
Mufeeda tace "Saboda me?"
Hajara tace "kwata2 matan layin nan kaman Awaki haka suke, naga basu da kintsi sam, tunda nazo suke ƙoƙarin shigemin nagane duk take taken su, idan basu yi wasa ba se nawa mace shegen duka da taɓarya"


"Subhanallah haba Anty Hajara, ai baza akai ga haka ba, maganin abun kawai ki fita sabgar su"


Mufeeda tayi ƙoƙari ta karkatar da hirar tasu, a yanayin maganar Hajara zaka san tayi gwagwarmaya rayuwa, bata da tsoro kuma a tsaye take, Mufeeda ta lallaɓa suka yi sallama.


Gaba ɗaya batun wai Sa'idu me kayan miya ne yake yamaɗiɗin ya ganta ta bar gidan ta tana kuka shine ya tsaya mata a zuciya, ina ruwan sa da ita daze mata haka, zuciyar ta ji take kaman taje taci uban sa, amma seta ga hakan ba mutuncinta bane a matsayin ta na matar Aure, da tana budurwa ne ba uban daze hana tayi masa tijara, da se tayi watsi da kayan miyar nan da cinikin da yayi sedai a kwao ƙarar ta Baba ya biya.


*****************
Tun daga tsakar gida Jabir yake Sallama amma Saima bata amsa ba, hakan yasa ya harzuƙa ya shiga falon da niyyar ya zazzaga mata rashin mutunci, amma me yana shiga ya tarar da Saima a ruf da ciki a ƙasa.


"ke Saima baki da hankali, wannan wace irin kwanciya ce haka? Sekin kashe min ɗa"
Shiru bata amsa masa ba, dubawa yayi se yaga Jini face face a ƙasan ƙafar ta da sauri ya ƙarasa ya ɗago ta, gaba ɗaya bakin ta ya karkace bakin ta duk bushashiyar kumfa tare da jini da ta daddatse harshen ta da alama jijjiga tayi babu alamar rai Sam a tare da ita.
"Na shiga uku SAIMA!!!"


****************


Mufeeda tayi deciding ko tayi wa Ammar maganar Sa'idu me kayan miya, fasawa tayi dan ta san halin Ammar ba haƙuri amma abun ya dame ta, ina ruwansa da ita? Ita ba shiga sabgarsa take ba amma har ya iya gayawa mutane ga a halin da ya ganta, dana sanin fita ta shiga yi a wannan yanayin daya ganta.


Haka Ammar ya dawo ya same ta, ya takura ta da tambaya akan meke damun ta, amma taƙi gaya masa.
Tana zaune a kusa da shi, yana cin Abinci ita kuma tana cin Aya danba ƙaramin daɗi Ayar take mata ba.


Ƙwace ledar Ayar yayi yace "Mufeeda wai ba zaki Abinci ba se wannan tarkacen? Ni bana son wannan kayan shiritar da kike ci me zasu ƙara miki?"
Ya janyo ta jikim sa ya dinga ɗura mata Abinci ta naci tana kuka dan sam bata jim daɗin Abincin, aikuwa yana gama bata Abincin ta amayar dashi gaba ɗaya, Ammar shiru yayi ya rasa abunyi shi be taɓa zaton haka mata ke shan wahalar ciki ba, haka ya zage ya wanke kayan da tayi aman a jiki ya bata wasu ta canza.


Mufeeda ta kalle shi tace "Yaya Ammar ko in koma gida ne kaima ka ɗan huta, idan na samu sauƙi se in dawo kana wajan dayawa"


"Na nuna miki na gaji ne? Lokacin dana Aure ki ai ba'a haka aka auramin ke ba, da lafiyar ki na Aure ki, ni yakamata in kula dake ba 'yan gidan Kuba, nifa Impact bana son kowa yasan da cikin nan, nafi so in kin haihu a gani"


Da sauri ta kalle shi tace "Amma me yasa?


"Au meyasa ma kike tambaya? Haba ai da kunya a ganki da cikin nan, and am responsible for it, se aganni wani iri"


Kallon sa tayi da tana so ta gaya masa magana amma ta fasa, ya kalle ta yace "Ya dai?"
"bakomai ta bashi amsa"


Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga yayi sallama, Aminu ne cikin tashin hankali yace
"Ammar, Jabir ya kashe Saima"
A firgice Ammar yace "Kamar ya ya kashe Saima?"
Aminu yace "toni mema zance maka ne? Ya fita ya barta taita jijjiga a gida ba kowa se ita kaɗai, ya kirani yanzu muna Asibiti, da naje gidan ko motsi ba tayi, a Yanzu babu me tabbacin tana raye"


Da ƙarfi Mufeeda tace
"Innalillahi wa innalillahi raji'un"


Ammar yayi jifa da wayar yace "Mufeeda ki kwantar da hankalin ki bata mutu ba ai, likitoci na duba ta"






AYI HAƘURI NAYI DOGON PAGE AMMA BANYI EDITING BA.


MASHA ALLAH, INA ME FARINCIKIN MIƘA SAƘON BARKA DA SALLA GA ƊAUKA AL'UMMAR I NA DUNIYA, FATAN ALLAH YA MAIMAITA MANA.


WANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKA TURAMIN SAƘON BARKA DA SALLA NA GANI INA GODIYA, ALLAH YA BAR ƘAUNA


In an karanta a tayani share please


Don't forget to
Follow
Vote and Comment


Ayshercool
07063065680✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com


Please follow me on Wattpad, vote and Comment


ELEGANT ONLINE WRITER'S


NOT EDITED


Page 26


Ƙoƙarin ci gaba da kwantarwa da Mufeeda hankali Ammar ya cigaba dayi, Amma kuka take Sosai tana nanata "Innalillahi wa and raji'un"


Ammar yace "Mufeeda, Saima fa ba mutuwa tayi ba, likitoci suna ƙoƙarin ceto ranta ne, ki dena kukan nan"


"da kunne na fa naji ance Jabir ya kashe ta"


"Ai bashi ya kashe ta ba, bata da lafiya ne kawai, ki bari gobe Insha Allah zanje Asibitin in ga abunda yake faruwa"


Da ƙyar ya dinga rarrashin ta, ya samu ta sassauta kukan da take yi, bacci ne ya fara ɗaukan ta, ba zato ba tsammani suka ji ana buga ƙofar falo da ƙarfi ana masifa, se yanzu Ammar ya tuna ne rufe ƙofar gida ba, da sauri ya miƙe yaje yaga wani mara hankalin ne yake musu wannan bugun?
Yana buɗewa yaga Maman Nur tana bala'i
"Waye uban ta a garin nan da har za tace zata dakarmin ɗa? Ita ta haifa min shi ko tare muka haife shi, wallahi in yarinyar nan ba tayi wasa ba sena mata dukan tsiya a layin nan"


Kallon da Ammar yayi mata ne yasa ta nutsu tana kame kame, cikin ɓacin rai Ammar yace
"tinkiyar inace ke zaki shigo min gida ƙarfe goma na dare kina zaki daki mata ta? Me tayi miki?"
"Am... Ammm... Dama yarona tace zata daka nazo inji ba'asin me yayi mata zata dakarmin ɗa"
"shine za kizo kinamin hayaniya kamar tashin duniya bama ta daki ɗan naki ba zaki zo kina ɗagawa mutane murya kamar ba matar Aure ba, Wallahi na kuma ganin ki a gidana sena ɓata miki rai, fice ki barmin gida mahaukaciya kawai"
Yanayin Yadda Ammar yake maganar ne ya tabattarwa da Maman Nur ya ƙulu matuƙa dan haka sum sum ta fice.
Ɗakin Mufeeda ya koma, ya tarar da ita a zaune, bugun ƙofar da'akayi yasa ta tashi, ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace
"wai dan Allah meye haɗin ki da matar nan ne?"
Mufeeda tace "wallahi babu wani abu tsakanina da ita, kawai ta tsane ni ne, tun ranar da tace in bata Madara na hana ta, ta sakani gaba a layin nan wallahi badan darajar Aure na ba, wallahi da sena koya mata hankali, bana son biye mata ne kawai, sabon Aurena shine mutunci na, da zarar na biye mata mun raba abun faɗa mutunci na da naka ze zube a idon mutane "


Mufeeda kenan dukda tarin ƙuruciyar ta akwai kaifin tunani.


Ammar yace " Shikenan, ki cigaba da haƙuri ba ruwan ki da ita, duk abunda tayi miki na ba dai dai ba ki gayamin, idan ba tayi wasa ba sena kaita gurin 'yan sanda, mahaukaciyar banza kawai "


" A' a Yaya Ammar base ka kaita gurin 'yan sanda ba, aishi maƙoci haƙuri ake dashi, Allah ya shirya ta kawai, ni yanzu hankali na yana kan Anty Saima"


"Ki kwantar da hankalin ki, Insha Allah zata warware".


********************


Da Safe Ammar ya shirya yace zeje Asibiti yaga halin da Saima take ciki, Mufeeda tace seta bishi, yayi yayi ta zauna a gida tace ba zata iya zama ba binsa zata yi,
"Kinga kiyi haƙuri bekamata in tafi dake ba yanzu, ki bari inje inga halin da take ciki se inzo muje ki duba ta kinji Jaririya ta"
"Shikenan Allah yasa tana raye ya bata lafiya, muje in raka ka"
Ammar ya wuce gaba tana binsa a baya, suna fitowa tsakar gida ta shaƙi ƙamshin ɗumamen miyar kuka, ta kalli Ammar tace "Yaya Ammar ba kaji ƙamshin miya ba?"
"Naji mana, meyafaru?"
"Kaman daga gidan Anty Hajara nake jin ƙamshin"
Ammar yace "Maybe"
Marairaice Fuska tayi tace "dan Allah Yaya Ammar in baka kwano kace ta sanmin ko loma biyu ne?"
Wani irin kallo Ammar yayi mata yace "Idan tuwon kike so ki dafa mana, kawai se inje da kwano ince a baki tuwo se kace bana baki Abinci, naga ma dai ba shiri kike da maƙotan nan ba, kawai se inje in fara roƙon Abinci"
"Dan Allah Yaya Ammar, ita wannan da zaka karɓo min a gurin ta ba irin su bace, niko loma ɗaya ta bani"
Ammar ya fara ƙuluwa, haushi ya cika shi yaja babur ɗinsa yai waje ya barta a gurin, ɗaki Mufeeda ta koma tana kuka ji take kamar taci babu, ji take inba tuwon nan ba ba zata iya cin komai ba.


*****************


Ammar yana tashi gidan Aminu ya fara zuwa suka tafi Asibitin tare, bayan sun gaisa Ammar yace "Aminu wai dan Allah meyafaru ne? Jiya hankali na ya tashi sosai da abunda ka faɗa, kuma Mufeeda taji gaba ɗaya ta birki cemin da koke koke"


Aminu yace "Hmm Ammar ni nama rasa ta inda zan fara, wallahi duk Faɗan da muka yi wa Jabir sam baya ji, Jinin ta ne ya hau taita Jijjiga. jiya dai har na baro Asibitin likitocin basu ce komai ba, yanzu da Safen nan kuma na kira shi bata shiga"


Ammar yace "Allah ya kyauta, bari muje muji"


Koda suka je Asibiti suka tarar da Jabir a zaune a reception duk yayi wani iri, suka gaisa suka yi masa yame jiki?.


Ammar yace "Jabir wai ya akayi haka ta faru meyasa meta ne?"


Jabir yace "Wallahi da zan fita ne ta cemin kanta na ciwo, na ɗauka kawai rakine irin nata shiyasa ban kula ba na fita, kawai ina komawa gida na tara da duk jikin ta jini"


Wata Nurse dake reception ɗin tana cike files ta ɗago ta kalle su tace "Eh ai da yake ba 'yarka bace dole kace haka mana, kudinga girmama larurar mace me ciki koda kuwa tana da raki, da yake cikin ba' a jikinka ba yake ba dole kace tana da raki ai, ai gashi nan ta kusa rasa ranta, ko Awo bata zuwa ga jinin ta yayi mummunan hawa, bata shan magunguna da'ake rubutawa masu ciki, dan Allah ku dinga girmama larurar mata masu juna biyu komai ƙanƙantar ta ko kuma buƙatun su"


Aminu yace "Ayi haƙuri ranki ya daɗe yanzu wani hali take ciki?"


Nurse ɗin tace "ku jira likitan safe yazo tukuna, Amma tana ICU kuma a rubutun da likitoci suka yi a file ɗin ta, Jinin ta ya hau batasan ma waye a akanta ba sakamakon jijjigar da tayi, an rubuta muku hoton ƙwaƙwalwa zakuje ku biya, masu kula da ɓangaren zasu zo suyi mata, sannan likitoci zasu ranar daza'ayi mata aiki, dan ba zata iya haihuwa da kanta ba"


Aminu yace "Jabir kayi wauta wallahi, bekamata ace haka ta faru da Saima saboda kai ba"


Ajiyar zuciya Jabir yayi ya kasa cewa komai, haka suka dinga sintiri zuwa wajen biyan kuɗaɗe da'aka nema, 'yan dubiya suka dinga zuwa amma babu damar ganin Saima saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman.


*******************


Rashin samun tuwon nan ba ƙaramin ɓatawa Mufeeda rai yayi ba dan seda tayi kuka tukuna, kuma taƙi cin komai ita kanta wannan abubuwan suna damun ta sosai, ga tunanin ko wane hali Saima take ciki daya dame ta, waya ta ɗakko ta kira layin Ammar, kafin ta tsinke ya ɗaga yasa a kunnen sa
"Yaya Ammar ya jikin Anty Saiman"
Ammar yace "Jikin ta da sauƙi Alhamdilillah, dan yanzu haka ma bacci take"
Ajiyar zuciya Mufeeda tayi tace "Masha Allah, Allah ya bata lafiya"
"Ameen, nima yanzu nake sa ran in taho, me zan taho miki dashi"
Zumɓura baki tayi kamar yana kallon ta tace "Ni bana san komai, dama dana samu tuwon nan ne da se inci, tunda ban samu ba na sha ruwa kawai"


"Ke wato tunda na fito baki ci Abinci bako? Keba kya tausayin kanki"


"Nima ban san me yasa nake haka ba, Amma ni wallahi tuwon nan nake so"


"to ni karkiyi min kuka, ko tea ki haɗa Kisha, zan san yadda za'ayi kafin in dawo"


Ammar ya dage yana rarrashi a waya, gaba ɗaya ya manta da Aminu a gurin, Aminu yace
"Kaga mijin ƙwaila an dage ana rarrashi da alama an gamu kenan?"
"Aka gamu dame?"
"Ban sani ba, gaskiya wannan ƙwailar she deserves to be saluted, Kai Ammar ka wani kwantar da murya kana rarrashi, kai da kace raino zakayi ya akai ka haɗa ta da raino kuma?"


Ɗan Murmushi Ammar yayi yace
"ba zaka gane ba that girl is so funny and romantic, ban san yadda akai komai ya canza ba"
Dariya Sosai Aminu yake yana tsonakanarsa.
Suka ƙara yiwa Jabir jaje suka bar Asibitin.


******************


Maman Nur suna zaune suna tafe ita da Maman Amir suna hira suka je gurin Sa'idu me kayan miya, nan suka tsaya suna munafuncin nasu da suka saba, Munafuncin Maman Sadiq suke yi, wai mijin maman Sadiq ke son ƙanwar Maman Nur, ita maman Sadiw ɗin bata sani ba, ya saiwa ƙanwar Maman Nur wayar dubu tamanin ya bar maman Sadiq da wayar dubu uku me fasashshen screen, Nan Maman Nur ta dinga zuba tana faɗar irin hidimar da yake musu, Sa'idu se zigata yake, suna cikin hirar Hajara tazo yin cefane, ko kallon su ba tayi ba ta gama cefanen tayi gaba. Tana tafiya Sa'idu yace
"Wai ita wannan 'yar waye girman kai kamar matar me A daidaita sahu, kuma kamar ita kaɗai take zaune a gidan"


Maman Nur tace "Nifa banga alamar tana da miji ba, kamar zaman kanta take"


Sa' idu yace "zaman kanta take to se ku killace yaran ku, dan kar ƙarti su fara muku sintiri a layi"


Nan suka yi ta gulmace gulmacen su sannan suka tafi.


*****************


Fa'iza ta shirya ta tafi gidan su Ammar, tayi sa'a kuwa Umman tana nan, Umma na ganin tace
"Fa'iza yau kece a gari haka?"
"wallahi kuwa Umma, ina Halima ne?"
Umma tace "Halima ta tafi Makaranta"
Fa'iza tace
"Umma naje gidan Yaya Ammar fa"
"Allah sarki ya kika baro su? Mufeeda har ta gaji da mitar banje ba, ina jin kunyar zuwa gidan Ammar, bana son ka dinga zarya a gidan yara, karka takura musu"
Kwaɓe baki Fa'iza tayi tace "Nifa Umma ƙara na kawo miki"
"to ƙarar wa kuma?"
"Ranar da naje gidan Yaya Ammar wallahi a waje ya barni wai Mufeeda tana bacci bazan shiga a tashe ta ba, wallahi a waje yaimin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login