Showing 30001 words to 33000 words out of 105161 words
cewar Huzaifa
Wai wanne ne cikinku saurayin Amana?cewar Badariya,Huzaifa bai San me zai ce ba
kawai sai ya nuna Alim yace gashi,harara Alim ya makawa Huzaifa,
Cikin gida Badariya ta koma dakin Babansu ta dauko manyan tabarmi sababbi dal dal guda
uku musamman Baba ya siya sabo da bakinsa.
Inuwar mangoro me sanyi dake kofar gidan ta shindidawa Alim da Huzaifa,suka ce ta mayar
da sauran saboda guards basa bukata suna can jikin motoci,
Baba ne ya karaso wajen Su Alim a mutunce suka gaisa aka kawo musu ruwa pure water
leda uku me sanyi,
Amana kuwa tana cikin gidan ana ta labarin duniya,dan ma Amana bata fiye surutu
ba,Badariya duk ta fesa cewar Alim ne saurayin Amana sai kallonsa akeyu.
Suna zaune Amana ta fito tana kuyi hakuri Na barku kuzo muje ciki Ku gaisa dasu
Umma,Aabid yana makale jikin Alim suka shiga suka gaisa dasu Umma,Alim a hankali ya cewa
Amana wace Ummanki? Nan Amana ta nunana musu Ummanta wata fara kwal kamar
kwara,suna kama da Amana,gashi yan gidan gaba daya ba laifi suna da kyau sosai Amana ce
ta fisu gaba daya,
Alim zai tafi matan manya kowacce dubu hamsim,Umman Amana dubu Dari,Baba ma dubu
Dari,sai kayan tsarabarsu yace Na Amana ne ta siyo musu,su doya,manja,dankali,etc harda
wayar Haladu,Apple,banana da lemo,su guava, duk abinda suke fada a waya Alim ya siyawa
Amana ta basu,gida da makwafta an rude,
Alim sunyi Sallama da Amana cewar jibi za a zo a dauketa zasu koma lagos,Amana tace to
ka tafi ni idan nayi 3wks sai Na dawo lagos din,Aabid dinfa? Alim ya furta,baki ta turo gaba to
shike nan ka turo jibin a daukeni, Kudi ya bata yace ga salary dinki,
Kin karba tayi to wannan kyautar da kayi a gidanmu ai yafi karfin salary kawai ka barshi,ban
son iyayi karba malama kina bata mana lokaci,Karba tayi tare da godiya,baku ci komai ba,tabe
baki Alim yayi mungode zamuci a gida, Aabid tayiwa bye bye tare da cewa dama nasan ba ci
zakuyi ba Ku yan gayune,Huzaifa yace no ba haka bane Baby Amana, wuce gida tayi aka ci
gaba da labarin duniya. Alim sai wurin dare suka koma can gidan su Kaka.
Amana kuwa bata basu labarin halin da ta Shiga a lagos ba,bata fada musu irin rayuwar da
tayi a lagos ba,kawai labarin duniya ta basu,haka frnds dinta maza ta ba wasu Dari biyar,wasu
1k,tunda Amana taje take yiwa yan gidansu hudubar Ilmi,cikin kwana daya duk kannenta saida
ta sa su a makaranta, Har alkwari tayi musu indai sunyi karatu to zata sai musu motar hawa,sai murna sukeyi suka
sami kwarin gwiwar zuwa Islamiyya da boko,suma yayyen nata sun shiga islamiyyar Matan aure
suna jira Amana ta sai musu motoci,mazan kuwa Amana tayi musu alkawarin jari,suma har sun
fara nutsuwa, Iyayensu kuwa tace Makkah zata kaisu suma wannan dalilin yasa ba shiri suka shige
islamiyyar matan aure,sunga fa lallai Amana da gaske take,
Baba halinsa yana nan Na banza sai Wanda ya karu a kai,har matan aure bi yakeyi,shi yasa
kudin da Alim ya bashi Amana tayi masa wayo ta kwashe kudin ta bar masa iya 20k,sauran
kuwa duk ta biya family schl,
Baba yaso yayiwa Amana dukan tsiya kan ta karbi kudinsa amma sai ya tuna alkawarirrikan
da tayi masa sai yayi shuru da bakinsa, yaune ranar da Amana zata bar garinsu,kananan
kayanta duk ta rabawa su Badariya,su Umma ma sun samu T-shirt dai dai,Aabid ya dami Alim
rigimar a kaishi wajen Antynsa ba shiri Alim ya turo driver guda daya da mota da safe da wuri
yazo daukan Amana,sai kumburi Amana takeyi sai wajen 5pm sannan ta dauko akwatinta tabi
driver suka taho cikin kano city.karfe takwas Na dare suka karaso gidan.
Aabid yana jin sallamar Amana ya fanfaro da gudun tsiya ya dafalfaleta,mutan gidan duk suna
Palo banda Alim Wanda sun fita gari da Frnd dinsa khaleed,
Gaishesu Amana tayi ta tafi wajen Kaka can ta ya da zango sai hira sukeyi da Kaka,har tayi
wanka Kaka ta kawo mata abinci sukaci tare da Aabid,
Alim kuwa tun safe yake jiran dawowar su Amana amma shuru har khaleed yazo suka
fita.Amana har tsarabar Goro ta kawowa Kaka,sai murna Kaka takeyi Goro lafiyayye me yawan
gaske,Matar Abba Ishaq kuwa da Haj Sameera kayan miya irinsu su kuka,kubewa
bushashiya,gyada danya etc duk Amana ta kawo musu da yawa.
AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳
65-70
By
AsmaBaffa
Tunda Alim ya dawo yaga ba Aabid yasan Amana ta dawo,washe gari da safe ma Amana
bata fito ba a dakin Kaka taci abincinta,
Har yamma lis Huzaifa yaje yasa Amana tayi shiri sosai cikin wata arniyar shadda sky
blue,suka fito sai kyalli sukeyi,khaleed da Alim suka gani a compound,
Da fara'a tace Daddy barka da yamma,ta kalli khaleed kadan tace ina yini tayi gaba abinta ba
tare da ta jira amsarsu ba, Alim a ransa yace lallai ma yarinyar nan,
Khaleed yace wannan kyakyawarfa?yar uwarku ce? A Ina ka zama Daddy dinta?
Tabe baki Alim yayi tare da cewa Nanny din Aabid ce fa,Aabid yana ce min Daddy shine itama
take fadamin,lallai ka iya zaben Nanny cewar khaleed,sai wurin 9pm Amana ta shigo ita da
Huzaifa,yayi mata siyayya sosai,Alim suka gani shi kadai a Palo,ko me yake jira oho,
Yana ganin Amana ya sauke Ajiyar zuciya me karfi hade da mikewa ya bar palon,washe gari
6am escorts dinsa suka kwashi motoci suka dauki hanyar lagos, da Aabid jirgin karfe 5na
yamma suka bi,Amana sai murna akeyi ana zare ido an hau jirgi,
Mintuna kadan suka sauka a Lagos wani Frnd din Alim Kamal yazo ya daukesu a airport,ya
kaisu har gidan Alim ya wuce abinsa.
Gidan neat kal kal suka samu ko ina kasancewar yan aiki sunayin gyaransu,
Tunda Amana ta dawo ta shige dakinta suka sha bacci da Aabid washe gari ma haka Alim bai
ganinsu Sam,
Kwanansu Uku da dawowa amma Amana bata kara sa wani atamfa ko lace ba damunta
sukeyi,kayanta ta koma sawa,yau shirin wanka sukayi Amana sanye da Wando legins tight iya
gwiwa da rigar ta tshirt armless irin doguwar nan ta kai Rabin cinyarta
Aabid kuwa dan pant ta sa masa ta jashi sukayi bangaren sweeming pool din gidan,
Alim suka gani zaune a kujera daga shi sai short ko Riga babu,yana karanta jarida yana kora
lemo,towel dinsu Amana ta ajiye gefe,da fruits salad da ta hada musu,Aabid ta Goya ta shige
cikin ruwan nan ba tare da suncewa Alim ci kanka ba,
Tunanin Alim Amana bata iya ruwa ba kawai sai ya hangota ta Goya Aabid tana iyo a ruwa
kamar wata kifi,a ransa yace ita wannan komai ta iya kenan.
Aabid kuwa dariya yake ta bangalawa yau ya shiga ruwa,dama bai taba shiga ba,sun Dade
ciki sannan ta fito zasu huta su koma,gaba daya bata sa bra ba rigarta duk ta manne a jikinta.
Alim gaba daya ya rude ya shiga wani yanayi ganinta a haka,kafe kirjinta yayi da
kallo,yanda ko ya tayi motsi kadawa sukeyi,ji yake kamar ya cafkosu ya shafa,gasu shape dinsu
gwanin birgewa,Amana fruits dinsu suke sha bata San me Alim yakeyi ba,Alim gani yayi Amana
zata koma cikin ruwa kallonsa zai kare,kiranta yayi da sauri, Amana! Wani iri Amana taji a jikinta babu abinda ke birgeta a rayuwarta irin taji Alim ya kira
sunanta,sai taji kamar ta shide,cikin tafiyarta ta gadara da zafin nama ta karasa wajen Alim,shi
kuwa Alim kallonsa yake ta sha yanda Na shanunta suke juyawa,
Ya kwashi wajen 10mnt baice mata komai ba,ita kuwa sabo da tasan yanayinsa baya
magana a kan lokaci sai bata damu ba ta tsaya tana juransa,shi kuwa ba haka bane kallon
kirjinta yakeyi a hankali saboda ya daga jarida nufinsa ita yake karantawa Ashe wayo ya hada
kawai idonsa Na kan Amana ta saman jaridar.
Mikewa yayi daf da Amana kamar zai shige jikinta a zuwan shi tafiya zaiyi,Amana ganin
kyaykyawar surar Alim yana kyalli yasa ta jin wani dummmmmm a kwakwalwarta,ta rasa gane
mene domin bata taba jin hakan ba,
Alim yana sani yayi luuuu ya tafi zai fadi tare da dafe kansa yace ouch...da sauri Amana ta
taroshi ya fado jikinta ragwajaf tare da sakar mata nauyinsa ai kuwa yafi karfin Amana nan take
suka fada cikin ruwan gaba daya,
Sai lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa sai ya fara tamke fuska yana cin magani tare da tsaki
ya fice daga pool din,yana ta faman masifa,aikin banza daga kiranki sai ki jefani cikin
ruwa,komai bakyayi A hankali kamar wata sakarai yaja tsaki tare da barin wajen cike da kunya.
Amana kuwa bata kawo komai ba tace masifaffan mutum,shuru shuru dashi sai masifa,Aabid
ne yace Antyna Daddy baya masifa fa,to naji muje muyi wankanmu,komawa ruwan sukayi suna
ta wankansu har suka gama,
Yau sati biyu kenan hutun makarantar su Amana ya kare sun koma schl,Mum Alim tun safe
take damun Alim kan yazo fa akan maganarsu,haka ya hakura yaje har dakin Abbansa,
Bayan sun gaisa Abba yace Alim wata magana nake jin cewar wai ka tsayar da mata za a je
Neman aure,kallon Mum Alim yayi,Mum kuwa ta daka masa harara ba shiri yace yeah
Abba,amma a kano take shike nan Alim ka turo min driver ka jibi za muje nemo maka
aurenta,cike da takaici Alim yace to Abba ya musu sallama ya bar gidan kamar ya kashe kansa
tsabar bakin ciki,
Kwana tsakani Abba ya shirya tare da Amininsa da Mum Alim,sai driver dan rakiya,flight suka
bi har kano suka dauki Alhaji Ishaq sukaje can garin da za a nemowa Alim aure,
Suka nemowa Alim aure kuma an basu yarinya tare da sa ranar aure nan da 1mnth domin
Mum tace bata so a day lokaci sabo da shedan,
Mum Alim koda sukaje Neman auren mutuniyar kirki ta zama tare da kaunar talaka haka ta
nuna,gidan Amarya sai yabon halinta sukeyi,basu San Mum tana da dalilinta,akwai abinda ta
boye a kasa.su kuwa Allah sarki sai murna sukeyi gida ya rude sabo da jin dadi zasu shiga
gidan Naira.
Bayan sun dawo Abba ya sanarwa Alim komai tare da yabon dangin Amarya,Abba yace son
sai watarana kafin biki ka kawo min sirikata Na ganta,domin Mum dinka tace kana sonta
sosai,Asiya kanwarku ma naji yanda take yabon halinta,haka Nura da Auta Sadiq ma naji sunce
sun Santa yarinyar kirkice. Alim dai cike da mamakin makircin uwarsu yace Hmm kawai,shi kuwa Abba ya zata kunya Ce
kawai.
Amana kuwa harkar gabanta takeyi kawai daga schl sai karatu,zama da kawarta Rufaida
yar gayu yasa Amana ta fara dan canja halinta ba laifi,
Mum tace baza ayi biki ba kawai aure za a daura amarya ta tare,
Biki ya matso Amana a bakin yan aiki taji ogafa zaiyi aure, wannan matar yana sonta ba
zabin Mum dinsa bace,nan Amana taji tarihin Alim har auri saki da Mum ke sashi yi saboda bata
so wata ta ci arzikinsa sai ita uwarsa da ta haifi abinta,
Ko yan uwansa Na jini bata kauna Alim ya musu kyauta sai ta dinga nuna kyashi da bakin
ciki,
Bare Abbansa bata so ko hira taga sunayi da Alim saboda kar ya bashi wani abu,Abban Alim
kuwa shima me arzikine, hassada ce tayiwa Mum yawa,shi yasa bata taba yarda Alim ya auri
wacce yake so,shi yasa duk wacce tasan Alim bazai taba kauna ba har a bada to ita zata nemo
ta aura masa.
Amana tana gama jin labarin taji wani bakin ciki da bata San Na mene ba ya taru ya cushe
mata a zuciya,hankalinta ya tashi ta nemi farin cikinta ta rasa,a ranta saida ta tsinewa Mum Alim
yafi dubu kan wanne dalili zatayiwa Daddy aure, bakin cikin Amana kenan.
Amana tana shiga Palo bata kula da Alim ba ta jefar da Jakarta a palon ta cire takalminta ta
watsar cike da tsananin bakin ciki ta ja tsaki,nan ta fara zagaya Palon,da karfi tace a'a...wai
mene haka ne eh....ina ruwana ma aikin banza aikin wofi,
Minti kadan ta buga kafafu tare da miko hannu kamar damisa zata damki nama tace saina
ehhhhhhhhhh......shake tsohuwar nan.....can wani lokaci ta dakko ruwa ta kafa kai
kwat...kwat...ta shanye tare da jefar da robar tace sai naci uwar tsohuwa
wlh...tambadaddiya.....kodaddiyya.....sokayayya....me suffar hanjin ligidi.... Tayi dakinta da sauri
ta fada bed dinta,Aabid ne ya shigo daga baya shi kam yaga Daddynsa wajensa ya nufa.
Ihun Amana su Alim sukaji sai karaji takeyi a dakinta,da sauri Alim ya bude dakin nata a kan
bed ya ganta kawai wutsil wutsil takeyi tana karajinta tare da tsine tsine,Allah ya baki lfy cewar
Alim yayi waje abinsa.Aabid yana a kafadarsa,
Ranar Amana da kyar ta iya yin wanka haka ta kwana ba bacci,sai asuba ta samu
bacci,Aabid sai driver ne ya kaishi schl,amma Amana tace Sam ita bata da lfy.haka Amana ta
yini da zazzabi,ga period tanayi,harda su amai tsabar bacin ran za a yiwa Daddynsu aure.
Alim kuwa tun yana damuwa har ma ya gaji gudun kar ciwo ya shigeshi a banza,frnds dinsa
ma sun jajanta masa, sun tabbatar auren babu inda zaije.
Yau daurin aure saura 1wk Amana duk ta rame ita kanta bata San dalili ba,Alim kuwa ko a
kwalar rigarsa indai irin wannan aure ne ya rigada ya saba dashi.
Mum kuwa burinta ya kusa cika,
Kwanaki fa suna ta ja gobe Saturday gobe daurin Auren Alim,dole ya gayyaci abokansa
sosai,Amana kuwa tana Palo tana jira taga wankan auren Alim,itama ta shirya cikin shadda
dark brown tayi kyau kamar itace Amaryar Aabid kuwa ya tafi weekend wajen Mum Alim,
Wani gigitaccen kamshi Amana taji ya daketa,Alim ya sakko cikin hadaddiyar shigar wata
tsadaddar shadda yar gaske fara kwal,yayi Kyan da bai taba yi ba a duniya,ita kanta Amana
gigicewa tayi,
Da Sauri ta mike tsaye tana wani kyafta ido sannan ta fara magana,dan Allah Dan Annabi
dan Darajar Allah dan girman Allah kaje dani daurin auren naka kaji,
Pls Daddy kaje dani sosai ta damu Alim sai yaje da ita,je kiyi shiri kwana yini daya zamuyi
tunda ma hakane sai Na tsaya mu taho da Amaryata.cikin tawagar angwaye dake flight harda
Amana,
Amana burinta idan sunje kano taje gidansu su gaisa da yan uwanta.
Gidan Amarya kuwa an cika makil ana jiran angwaye,Abba da yan uwansa duk Suna
can,Mum ma ta tura Aminiyarta Haj Talatuwa da Haj sameera kanwar Abba da matar Alhj Ishaq
Aisha. Duk suna gidan Amarya ana jira a daura aure.
Angwaye sun sauka a kano sun kara haduwa a manyan motoci Na alfarma tare da frnds na
kano an tafi gidan Amarya daurin aure,Amana tana kusa da Alim,sai tsokanarsu akeyi cewar
tayiwa Amarya wayo,Amana dai tayi shuru ita da Alim a bayan mota Khaleed ne driver,ana ta
zankada tafiya,zuciyar Amana cike da kunci,shi kam Alim ya rasa dalili jin wannan auren yakeyi
daban da sauran da Mum tayi masa,baya jin wani kunci,ya danganta hakan da sabo.
Amana bata kaunar ganin garin Amaryar ma sabo da haka ta kwantar da kanta a jikin kujera
tare da lumshe ido,khaleed kuwa sai tsokanar ango yakeyi yaki yin shuru,sauran motocin
abokan ango suna binsu a baya,
Garin Amarya aka shigo har unguwarsu da layin gidan su amarya wani dandasheshe gida
da duk unguwar babu kamarsa shi aka tsaya da motoci,mutane damkam cikin masallaci da
wajensa,dangin ango duk gasu nan,har su Huzaifa, Amana bude lumsassun idanuwanta tayi
don kallon unguwar Amarya,ai da sauri ta kara damke idonta ganin wani tsantsararren gida me
kyau,gida Na fita kunya,ga mutane sunsha wanka,kamshi Na tashi kowanne cikin shigar
alfarma,
Amana sai zare ido takeyi da mamaki tana kara bude idonta sai kallon dangin Amarya
takeyi cikin suturu Na gaske,da gani sun samu harka,mamaki cike da zuciyar Amana,sai murza
ido Amana takeyi.
Kallo Amana take tayi tana murje ido,ga kwalla ta cika idonta har hawaye ya fara zubar mata
ta rasa meke mata yawo a zuciyarta.
AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳