Showing 51001 words to 54000 words out of 105161 words

Chapter 18 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

8474

Saida Badriyya ta yiwa Amana gashi da ruwa har sau Biyar tana zubarwa tana sake
sabo,wata Ni'imace da karfin dadi suka dinga ratsa Amana.
Amana tace sis wlh kin iya wa ya koya miki?Badriyya tace wajen kawarmu Bilkisa ta gidan
Baba Tsoho,itace take mana lecture akan aure idan mukaje wasa gidanta,har kawata Maimuna
ni na gashe shegiya minjinta ya mata daga daga.

Allah shiryeki cewar Amana, Badriyya tace rufe min baki ba gashi kin amfana ba,yanzu zauna
cikin Bahon na miki wankan sabulu kuma kafin na bude idona.
Ba musu Amana ta zauna aka cudeta tana Badriyya kiyi a hankali mana zaki cire min fata,
Da Allah uwar kwailo duk karfinki kina badani.

Dai dai kirjin Amana tazo Ba ruwan Badriyya ta dirjesu da soso sosai,kara Badriyya ta saki
kutmar....shege Alim dole yayi mukus a bed munafuki... Ashe rashana yake kwasa,fusge soson
Amana tayi fita zan karasa kina tabawa Alim sirrinsa, wlh saina karasa ko na fama miki
ciwonki,da sauri Amana ta bata soson mayya kawai ungo. Tas Badriyya ta wanke Amana tare da daura mata towel sai lokacin Badriyya ta bude idonta.
Har daki ta kawo Amana ta bata mai da nightwear sannan itama tayi,Alwala sukayi suka jero
nafeela da karatun Qurani da sauransu sannan sukayi ta jera adduoi wa komai da ya damesu
na duniya Dana Lahira. Yau bed daya suka kwanta suna hirar zuminci,sai tausa Badriyya kewa Amana tana kwantar
mata da hankali.

Asiya kanwar Alim tayiwa Abbanta waya cewar ta fitar da miji Sadiq yayan Huzaifa kenan dan
kanin Abban Alim dake kano,shima kanin su Alim auta dake karatu a Cairo ya kammala
karatunsa gaf yake da dawowa shima tace ya samu matar aure yar Adamawa state ce Zahra
tare sukayi karatu amma Mum tayi tsalle ta dire tace wlh bai isa ba ita zata zabar masa mata. Itama Asiya tace bata yards da zabin Asiya ba domin Saddiq ma'aikacin Gomnatine bashi da
gadon arziki da Gomnati ya dogara ita kuma tace dole itama Aliya ta auri zabinta wato Sageer
dan gidan Gomnan Kebbi tubabben Bayarabe ne,
Kuma baya da haka ma Mum bata kaunar dangin mijinta.

Babu magiyar da Aliya da Auta basuyi ba Amma Mum ta kekasa kasa taki abinda ya tashi
hankalin dan autanta da kuma Aliya,Aliya tana can kano taki dawowa sai kuka takeyi,dan Uwan
Abba kuwa sai tausarta yake yace addua itace mafita sabida idan aka matsa to Mum zata
tsinewa yaranta wanda hakan barazana ce ga rayuwarsu.



AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳



125-130



By
AsmaBaffa




Ina matukar godiya fans duk naga sakonninku na Kuma Ji yanda kuka nemeni na gode da
nuna kaunarku. Kuyi hakuri ba kuji ni ba,ina kaunarku sosai ina jinjina muku.





Page din nan naki ne MARCYCOOL my sweet and lovely sis.




Basu zarce ko ina ba sai gidan Alim direct Amana Jan Badriyya tayi har cikin Palon part
dinsa nan take Badriyya ta sukukuce wajen kallon asalin haduwa, Badriyya batayi kasa a gwiwa
ba tace Amana yanzu wanna kata'in gidan ne gidan mijinki, anan kike zama?ina Kallon gidan
Mum Alim hadadde Ashe akurkin(cage)kazane ban sani ba,Amana dariya Kawai tayi yanda
Badriyya ke zuba kauyancinta, Badriyya taci gaba Amma Mum ta cuce ni da tuni anan aka
saukeni ko?

Kaf saida Amana ta zagaye gidan Tana nunawa Badriyya komai na gidan har sukaje part din

Ma'aikatan gidan mata sai gulma Sukeyi Ashe oga Amana ya aura, Badriyya har yanga take
musu ita ga kanwar matar gidan,
Sama suka hau a part din me gida Alim Sautin kidane ke tashi a manyan speakers dake girke
a Palon Alim,Huzaifa zaune yana chat Alim yana latsa computer system,Badriyya kamar idonta
zasu zubo tsabar kallon tsaruwa, volume suka rage a nutse suka karasa suka gaisa da Juna
suka zauna,Alim kamar zai cinye Amana saboda Kallo,Huzaifa ma rudewa yaya ganin su
Badriyya an dau wanka,

Alim ne ya radawa Amana baby kinyi kyau,wani yarrrr... Amana taji a cikin jininta sakamakon
irin salon da Alim yayi wajen mata
Magana cikin kunne, nan take ta lumshe Ido,kasala ta sakko Mata,ba abinda takeso kamar
tajita rungume jikin Alim musamman yanda kamshinsa ya cika mata hanci me dadin gaske,

Bari mu shirya Cewar Alim,kai kawai ta gyada,Huzaifa ma ya mike ya nufi shiryawa yana bin
Badriyya da mayen Kallo.
Amana taja Badriyya zo muje kiga Saude yanda na kulleta,me gadi ne ya bude musu Dakin
da Saude take suka shiga,Saude Tana ganin Amana ta fara lailayo manyan zagi Tana watso
musu,
Haushi Badriyya taji tace kinji ko Amana, Saude tace tsinannu gadon tsiya, bakar haihuwa,
haihuwar gefen kwalta, haihuwar tsakar Rana,wacce da Rana ubanki yayi cikinki,wlh nice
ajalinki Dan ubanki Tare da Danno ashar lafiyayya.

Amana ta harzuka tace ki daina zagin iyayena nasan darajarsu,Saude tace Ubanki Ma yaci
Uwatas, Uban Uwarki na fada yan tsinannu.
Amana tace Baba me gadi dauko min sandar nan me kamar kulkin yan sanda,aifa Baba da
gudu ya kawo ya bar wajen,Amana ta mikawa Badriyya sanda jibgi rabonki Sis,Badriyya tace
yanzu naji manana wannan shine aha...
Shiga Tayi ta Fara lugudar Saude,Amana kuwa kofar ta rufe musi Tana jin yanda Badriyya ke
tafkar Saude,Saude kuwa bata fasa zagin da take ba.saida Amana taga lallai Badriyya zatayi
kisan Kai sannan ta koma ciki Badriyya wai wanne hauka ne haka ki kyaleta haka ai dukan yayi
yawa kina ganifa ko magana Saude ta Kasa,
Badriyya tace yo ni ina ruwana idan zata yini to wlh zan kwana akan zagin iyayenmu, Amana
tace banason musu fa ke halina dake banza ce baki san kadan ba,Badriyya ta kalli Amana wlh
kin lalace Amana, wai ke kikewa wani fada akan dukan wani.
Naji muje Kawai komai Ai sai ana hangen nesa
Sandar ta kwace ta kira me gadi ta bashi kudi da yawa sannan tace ya bata abinci da ruwa
yaci gaba da tsare Saude.

Saude wacce ta gama jikata bayan su Amana sun tafi tace shegu ammafa wannan kanwar ta
Amana har tafi Amana mugunta, saidai dukan Amana yafi zafi Domin duka daya na Amana
shine goman na Badriyya.
Suna komawa Ciki Alim ya fito cikin shiri ya dau wanka na kece raini cikin pencil jean brown

da riga Sea blue irin color na kayan Amana.
Yasha kyau suma taci Kudi sai shining yakeyi hade da kamshI.
Wani agogon Gucci ne me tsadar gaske a hannunsa,

Huzaifa ma ya hade cikin kanan kayansa black nd white,Alim ya kalli Amana wacce ta ke
satar kallonsa domin ya mata kyau. Kamar dazu ina wanka naji ihu a gidan nan cewar Alim
Huzaifa ma yace nima haka wlh naji kuma na Mace,Amana sun san ihun Saude Ne Amma
sai tace munje ai masu aiki matane wai sunga ga kadangare shine suke ta ihu amma an fitar
dashi.

Huzaifa yace kai mata kenan Alim yace lets go zamuyi Missing flight,akwatunan guards Suka
zuba musu a mota nan Suka wuce sai Airport dake Lagos.

Suna cikin Airport kafin a fara musu screening wata kyakyawa yar gayu bahaushiya suka
hango ta taho tana yanga tana taku dai dai hade da juya mazaunai irin na yan duniya.
Alim ta kafe da kallo wanda shi bai ma san da ita ba domin Amana yake ta faman Kallo yana
lallabata ta sha fresh milk tunda ba wata lafiya ce da ita ba.
Amana kuwa da Badriyya kallon wannan matar sukeyi Badriyya ta kama kunnen Amana ta
mata Rada yanda ba wanda zaiji,Kalli wannan Amana wlh mijinki take kallo zatayi miki
snatching,Amana itama ta yiwa Badriyya rada bar shegiya zanyi maganinta, Badriyya a basu
show... A basu show Sis,
a dauko manana yar Sulemanu Harka
CIRANIN AMANA




130-135



Official


By
AsmaBaffa





QUEEN MERMU WANNAN PAGE NAKINE,HAFCYCY DA SUBBY GODIYA

GAREKU,OGA ASY BAN MANTA DA KE BA,INA TA WAJENA MAMAN WALEEDA ALLAH YA
BAR KAUNA.
SAURAN READERS MA NA GODE





Har cikin garinsu kauyensu Badriyya ta kaisu, hamdala sukayi Allah ya kawosu lfy, a
gurguje suka kwashi kayansu Amana ta sallami taxi Man ya tafi,kafin kace me anyi dandazo
ana kallon yan gayu su Amana,kamar bakin larabawa ko indiyawa
Cikin sauri da zafin nama suka fada cikin dan gidansu me kyau,duk yan gidan tasowa sukayi
ana tururuwar rungume su Amana,Amana hannu ta bawa yayyenta mata da maza manya da
yara suna tafawa tas tas tare da share hawayenta,a tsakar gida bisa katuwar tabarma babba
suka yada zango, Cike da mutunci suka gaisar da iyayensu da kakarsu Iyya babar Sulemanu Harka wato
Iyya.
Tambaya sukayi Ina Baba?Umman Amana tace suna asibiti daga nan zasu biya gidan me dori
na Hausa,
Iyya tana sharar kwalla tace ai abokansa me Unguwa da Iliya su suke ta dawainiya dashi sun
hana kowa zuwa sun dauki nauyi anjima zuwa dare zasu dawo daga asibiti.
Gwaggo tace ai wlh wannan tsinanannun yan Daba ne,
Iyya tace jarabar duniya asara ai basu da imani ko kadan,addua tsinuwa na dinga tsine
musu kenan har ranar da mala'ikan mutuwa zai zare numfashi na

Gwaggo tace ohhhh Allah ya rufa mana asiri da ta kare akan Sulemanu shi kadai maganinsa
kenan ishara ce Allah ya nuna masa tunda yaki tuba.
Umman Amana tace wlh kuwa in banda kwala min touch light da sukayi a ka ba abinda suka
min,daya matar Sulemanu tace hhhhh ai ni dadi ma naji da suka masa haka yanzu kinga yayi
karatun tanutsu ba kwartanci,
Matar cikon ta hudu n itama dariya ta kyalkyale da ita tace wai kunga wani mari da suka fesa
min na zata Wlh duniyar ce ta kife kif,Sakina karamar kanwar su Amana tace ta saki dariya tace
gwaggo kinga abinda ya bani dariya wai katon cikinsu zaiwa Iyya fyade wai Iyya wacce ta
rigada ta yi expired, Dariya gaba daya aka sheke da ita,Hamza ya zubawa Sakina rankwashi yace Iyya ai
sweet zatayi kika sani ko danta ita ya gado

Iyya ce ta fashe da kuka sosai tace Allah ya isa tsakinina daku,kuma wanda ya kara min
turanci to ubansa yaci uwatas tsinannu uwarku kuka zaga,kuma dana Sulemanu ba abinda Zai
sameshi aniyarku ta biku
Iyayen ne wato matan Harka su 4 suka ce heeeeeee can ga su gada, dan naki wanne
zalince ne Bai mana ba ai hakkinmu ne ya kamashi,

Amana tace ya isa haka pls ice ko dai Baba jikin da sauki,duk suka ce Alhmdllh Badriyya
tace good,iyayen sukace kai Ku dinga turancinku can mu me muka sani

Hamza yan crossriver gaba daya pidgin English suka koma da su Amana,kb wanda ke bin
Hamza yace you girls are chilling woo,u dey enjoy oooo,Hamza yace I swear come see
enjoyment no be small thing Sis,

Isa ne ya shigo yana budawa tare da yin doro yana kobarewa yayi hugging din Badriyya
yace ahhhh...this girl I know u no dey carry last look at ur skin.
Kallon Amana yayi yace easy easy Baba cutie u r still shining wooo,Amana tace stop this
nonsense joooo...a done big now,a be house wife, no joke abeg that useless thing has past
Man,
Badriyya ce tayi katsalandan tace wait guys just gist me how things goes, abeg stay quite
stingy girl cewar Hamza, dariya sukayi gaba daya Badriyya tace I have a story for u guys, kowa
saurarenta yakeyi sannan tace am in love ,tafi suka dauka gaba dayansu yan ciranin gidan da
sauran yara wanda suke schl suna tsintar turancin Isa yace a bamu musha ya hadu, Amana ce ta fara magana,gaskiya a tsaya a tsaya shuru
kowa yayi har iyayensu dake zagaye dasu a hankali ta furta tunanin mijina nakeyi u knw am a
married woman ,heeeeeee suka fara ihu,Hamza yace shegiya u done fall

Kwanjin Isa Amana ta buga da sauri ya dafe wajen yace wlh har yau karfin ki na nan
wai,Haladu da shigowarsa kenan dauke da danyen kifi headphone makale kunnensa yana
Shan Sauti ai ganin Amana yasan dole kudi yazo kawai sai ya fara casa rawa yana slizing
kamar wani Michael Jackson,dariya sukeyi Badriyya tace u too funny.
Alim kwance yana numfarfashi na zazzabi ya fita daga hayyacinsa,10pm wayarsa ta shiga
ruri ba tare da ya duba me kiran ba ya jawo ya daga tare da karawa a kunne Jin Muryar Amana
yasashi Jin sanyi a ransa,cike da karkarwar sanyi yace hello,nan take Amana ta rude Jin
Muryar jariminta ba lafiya, Cike da kulawa tayi kasa da Muryar tare da shagwabe murya tace dear ya najika haka are u
ok,kara narke mata yayi Baby pls come to me i need u badly,
A rude Amana tace sweet Alim me ya sameka pls,a hankali yace kawai ni kizo Baby fever
na damuna I missed u,missed u much more dear amma ya kamata ka Kira doctor kaji,
Uhm no Amana zan warke
Kara lankwashe murya tayi kamar zatayi kuka tace oh dear pls bana son rigima kawai ka kira
doctor kaji,to baby Allura fa za a min kuma bakya kusa bare ki rikeni ki lailayamin,
Uhm kaji rigimarka ko mine,

Kaci abinci?no bazan iya ci ba I am missing u Amana
Rokonsa Amana ta fara dan Allah kaci ka taimaka min kaci abinci Dan darajar Allah kaji,ka
tausaya min Babyna kaji,wani shauki ne ya kara shigar Alim ya kara narke mata zanci kadan to,
cikin wani salon Muryar da bata San tana dashi ba tace tnx oya tashi kuma kar kashe Ina ji zaka
ci sannan ka kira doctor,pls ki kyale doctor ban son Allura fa kamar zaiyi kuka ya furta,

OK to shike nan tunda bara ka kira doctor ba mun bata na daina kulaka ma,
Uhmmmmmm kamar zaiyi kuka yace am sorry Baby,
Ban hakura sai kayi abinda nace oya get up,Babyna bakya tausayina ko?I will kill u just do as
I said ok
Tana jinsa sai shagwaba yake zuba mata tana lallabashi har yaje wajen Mum ta bashi Abinci
yace doctor ya kawo masa magani yasha yayi wanka ya kwanta sannan Amana ta kyaleshi tace
goodnight My Alim muuuuuuuuuahhhhhhh ta watsa masa kiss ta waya sunfi 10,
Alim yace ohhhhhhh u are killing me honey I wish u r here with me hmmm da sai na kwana
ina wasan kwallo,wani dariya Amana tayi me Jan hankali ta fara shagwaba uhmmmm....banda
rigimafa Mine night sweet dreams,pls kiwa Baba sannu da jiki ina nan zanzo kinji ko?to ba
matsala Allah kawoka,haka sukayi sallama.
Washe gari Alim waras ya warke shiri yayi sosai tare da daukan wanka na gaske domin
zuwa Airport dauko Nura da Matarsa.
Mum,Alim,da Abba ne suka tafi dauko Nura,Asiya ma tazo daga Kano domin taron babban
yayansu,
Wani kyakyawa chocolate ne da matarsa black beauty tare da yarsu yar kimanin 3yrs suka
karaso jikin motocin su Alim,
Nan suka dinga Murna da gaisawa,Mum sai hararar matar Nura takeyi da kyar ma ta amsa
gaisuwarta,hakanma dan taga idon Abba ne,
Nura dan wanka mota suka shiga sai gida inda suka ci suka Sha ana ta fira,Asiya sai surutu
akeyi,
Washe gari Autan Mum ma ya sauka shima ya gama schl kyakyawa kamar dan India dan
yafi Nura haske amma Bai kai Alim ba,gida ya kacame ana ta murna da hira,
Bayan Mum da Abba sun tashi suka fara tattauna Matsalar uwarsu
Dan Auta yace Wlh ni bazan yarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login