Showing 75001 words to 78000 words out of 105161 words
kawayensu da wasu manyan ma da zasu dinna,Hamza ma yana da Mota
yanzu zai tafi da kb,Isa da Haladu, Alim ne yace dole sai sunje dinner har dinkin dinner ya
musu.
To fa Badriyya da kawayenta da sauran yan Uwa yan mata suna cikin kano gidan su ango
Huzaifa,suna part dinsu maman Su Huzaifa rakanas ta dauko musu me lalle da kwalliya,dama
Amare sun kashewa jikinsu kudi sunyi gyara sosai,Amana ta rasa me zata siyawa Amare gudun
mawa kawai ta je gidan Me gari aka bata Saniyarta ta gado ta sa aka girba saniya da wuka,aka
gyarata ta karbi motar Hamza aka zuba nama a buhun huna,ta figi motar Hamza sai cikin birnin
kano,wani waje da akeyin kwangilar hada take away takai tace ayi dambun nama lafiyye a zuba
a abin take away unique color na alfarma,
Zoben Gold na Alim da ya taba bata ta cire ta ba dashi jingina hhhh jinginar zobe huuu
Amana aka bata kudin da niyar idan ta samu kudi zata basu su bata zobenta zoben Alim ne
baza ta iya siyarwa ba,baza ta iya rabuwa dashi ba,haka ta karbe kudi ta biya masu dambun
nama,computer Laptop dinta ta Nemo ta siyar da ita nan ta kara figar kyakyawar motar Hamza
ta tafi Saloon da lalle cikin city,
Sai dare aka gama mata,a daren sabo da rashin tsoron Amana ta koma garinsu Wudil,
Amana fa ta fara daukan haske shining kawai takeyi,ga lalle ga gashi yasha gyara,washe gari
Badriyya sai waya take radowa Amana tayi sauri tazo a fara kwalliya da ita,Amana kuwa
kwalliya ta cancada kai kace yaune party, Hamzane yace kiyi amfani da matata Amana kije da
ita kawai ni zamu yi Amfani da ta friend dina tafi tawa girma sosai kinga muna da yawa kuma
zan kai su little Zaliha ma.
Tnx Bro cewar Amana.
Akwatinta guda tasa a bayan Mota,t a cokala takalmi me shegen tsini cikin kayan da akace
na Huzaifa ne a cikinsu tasa wata arniyar atamfa baka da green,dinkin riga da skert yayi mugun
da Meta fam,da kyar take mitsi a ciki,ga takalmi da gyale siriri na daukan magana malam,ta sha
kyau kamar a sace ta kamar wata yar shugaban kasa, Dama ga tafiyar Amana tun asalin ta takama da gadara ce,
Sai zuba kamshi takeyi gashin ta glass a fuskarta brown yayi mugun mata kyau gashi sake a
gadon baya.
Wajen masu take away ta nufa tuni an gama mata komai nata na take away yayi kyau shi
kanshi plastic da marfinsa da aka zuba dambun naman a ciki abin kallo ne,Bare ledar da aka sa
plastic din a ciki wai wai,buhunan take away ta zuba a Mota,sannan ta sa kati a wayarta,sai
canjin kudi sababbi dal dal yan dari dari da ta canja rapa biyu,ta zuba a pose din dake hannunta Direct gidan su Huzaifa ta nufa da motarta,
Yan mata da samari sai sintiri sukeyi a gidan,wasu tsakanin mata da mazan ma har sun saba
da juna sai shagali akeyi tare,musamman aka dauki dj aka sa a tsakar gida zai dinga kida
kwana da yini har a gama biki,Alim duk wacce ta shige sai ya kalleta ko Amana ce ,amma
Amana shuru,ko yaushe yana tsakar gida ko zai ga tazo amma shuru,Shine ya kutsa wajen
Badriyya wai lallai sai ta kira Amana tayi sauri tazo ayi mata kwalliya,Badriyya shine fa take ta
faman kiran Amana,
A waya.
Dama in baku manta ba Amana tasan gidan su Huzaifa,Alim yana zaune a farar kujera a
tsakar gida gindin bishiya ga dj na tashi wasu na rawa wasu na hira,wasu matam gulmar Alim
sukeyi ga wani me kyau ga haduwa kamar bature,wasu suce dan india ne,musamman kawayen
su Asiya da kannen su Huzaifa yan iyayin tsiya yan kwalliya da daukan wanka,har fada sukeyi
wai ina marar mutunci matar yaya Alim ne,gwarzuwa me tuko Mota from lagos to kano,sun ga
Alim ba fara"a yanzu shi yasa basa tambayarsa Amana,wasu yan matan kuwa cewa suke
mutum baya kula kowa sai ya dinga fitowa yana wayon kallon yan mata,
Wasu sukace munafukin banza ba fara'a baya kallon ko wacce da mutunci kamar yaga kashi
to uban waye ya sa ya fito waje.
Amana ce ta danna uban Horn a kofar gidan,me gadi ya wangale kofa,ta shararo motar cikin
gidan da Alim tayi tozali.
Sorry masu karatu bakuwa nayi yau shi yasa ban gama typing da wuri ba,n asan kun
jirani,gashi ku karba na wullo muku.........
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
165-170
Official
By
AsmaBaffa
INA GAISHE KU MAKARANTA CIRANIN AMANA.
Da Alim tayi tozali ya harde a kujera ya tsirawa gate ido,tuni gaban Amana yayi mummunan
faduwa,da kyar ta iya parking din motar sannan tasa hannu a saitin kirjinta ta dafe tana maida
numfashi ga mugun sabon Son Alim da ya taso mata,tunani ta shiga na abinda ya faru a baya,
Hawaye ke neman kwace mata a hankali ta maida kukanta tare da furta ah...Oh God ....bazanyi
kuka ba...karki yi kuka Amana ke me dauriyace,amma duk da haka saida hawaye kadan ya fito
tasa yatsa tare da dauke hawayen,sai da ta daidaita kanta sannan ta bude kofa tare da zuro
kafarta daya waje,bata ma son ta kalli bangaren da Alim yake bare ya mata wani wulakancin
tunda yace duk hanyar da zata hadasu kar ta sake ta bi ta wajen,sannan yace mata ya
tsaneta,amma kuma dole sai ta wuce ta gaban su Alim sannan ta shiga cikin gidan part din
Amare,
Alim kuwa kalle kalle yakeyi yanda Amana zata bullo bai kawo itace a Mota ba domin bata da
Mota amma sai kallon motar yakeyi yana tuna inda ya san motar,
Alim a ransa yace wannan kamar motar Hamza,gashi wata kyakyawar kafar mace ya hango
kamar ta yar India,takalmin kawai ya gani ya gane takalmin da yasiyo ne a London ya kaiwa
Badriyya ta bawa Amana,wannan kenan Amana ce tazo da motar Hamza tunda dama yasan
Amana ta iya driving,yes itace Alhmdllh cewar Alim.
Amana kuwa kasa fitowa tayi saboda da gudun kar tayi kuka,amma haka tayi shahada ta fito
gaba daya da kyar saboda yanda dinkin ya tamke mata ko ina cip cip,tuwon mazaunan nan
gasu sunyi dam sosai,
Ko mayafi bata yafa ba yana hannunta saboda taga cikin gidane kuma tayi ne Sabo da Alim
yaga fa ba ta tashi takeyi ba wai irin ta manta dashi ma wanka take dauka shiga takeyi yanda
taga dama,bayan kwalliyar duk dan shi akayi,shi kuwa Alim yaga duk kayan da ya siya matane
a matsayin na Huzaifa,sai farin ciki ya lullubeshi,ga wani kyau na ban mamaki da Amana ta
karo,da gogewa tare da zama hamshakiyar wata yar budurwa,
Ka rantse bata taba aure ba,
Nan take kishi ya tasowa Alim za a kalli Amana ga maza,to wai ma ina cikin dake jikinta
tambayar Alim,ko ta zubar dashi lallai ma yarinyar nan zanyi maganinta,
Yana ta magana a zuci ji yake kamar yaje da gudu ya rungumeta,yama rasa inda zaisa
kansa,Amana kuwa juyawa tayi tana fito da buhun hunan take away,da akwatinta,mayafinta na
rike a hannunta tana ta tunanin Alim,ji take kamar taje itama ta rungumeshi yanda taga ya kara
kyau da haduwa yar ramace kadan jikinsa ita ma sai kayi masa farin sani za kace ya dan ragu
kadan,Amana a ranta tace uhmm dan gayu wannan uban daukan wanka da yayi haka kamar
zaije dinner,
Ya wani zo ya zauna cikin mata sai kallonsa akeyi,awai dan a kalleshi an fada masa kowa
ce zata soshi dan yana da kudi da kyau ya wani zo sai tallar kansa yakeyi,salon wai ace ana
sonsa tsaki taja a hankali,kaji fa Amana to ina ruwanki.
Buhu buyu ta dauka tana tafiya das das kowa mata da Maza sai kallonta akeyi,Alim kuwa
dafe kai yayi yana hadiyar yawu,yace lallai yarinyarnan kalli yanda take wani bawa mutane
show kalli Maza sai kallonta akeyi lallai zan gyara mata zama wannan ai tangal tangal ne da
aure kaji Alim to ina ruwanka da ita kaida ka tsaneta,
Garemu matan Aure,zawarawa,yan mata,karki bari mijin ki ya dinga dawowa yana ganinki
bakya daukan wanka kamar zaki party,bazawara da budurwa ko kun rabu da mijinki ko saurayi
ki sani bafa mantawa yayi dake ba ko ya daina sonki yana nan yana sa miki ido yana bibiyar
halin da kike ciki,kinci gaba ne ko kin lalace,namiji yana bakin ciki yaga sun rabu da mace taci
gaba,tafi da haduwa kyau da komai da komai,yafi so yaji ance ai naga wance rannan baka
ganta ba ta lalace ta rame ta fige,duk kwalliyar wance tab ai kasa ganeta nayi a hanya,ta dawo
abar tausayi,ko kuma shi wanda kuka rabu ya ganki da kansa,kin lalace murna zaiyi ba zai
damu ba,cewa zaiyi ma wa ya gaya mata,da tana jin dadi a gidana tayi min kaza na kori
shegiya gwara haka gashi ai yanzu ta dawo abar tausayi,ai Baza ta samu kamata ba,tayiwa
kanta,yanzu ni aka bani wannan me zanyi da ita,ai gidansu wuya suke sha etc.idan kuwa ya
ganki kinci gaba,idan yana sonki sai yayi dana sani tayu ma ya dawo yayi ta naci ki koma,ya
rude a kanki zaman da kukayi tare ya dawo masa,ko labari yaji saiya nemi ya ganki face to face
ya ganewa idonsa,idan budurwace sai yaji takaici ko bai aure ki ba,idan matar aure ce zai kara
dinga kaunarki,dan karamin neman aure sai kiji ya fasa,ko ya auro ma yasan kin fita,kowa yana
son gyara,tsafta,kwalliya etc duk da cewa suma mazan suna da matsala,amma mata shine ur
eye woooo a kara dagewa a daure a cire kyuya da son jiki kiyi iya yinki,
Amarya Sakina ce ta fito ita da ango Ishaq wai yazo kawo mata abinci ta kasa cin abinci
shine yazo da take away sai da ya tabbatar taci ta koshi ta rakoshi zai tafi kafin zuwa after
magrib dinner party,
Da Amana suka ci karo,dariya Sakina tayi oyoyo Anty muna ta jiranki ba dadi ba kya nan,to
banza take away na tsaya daukowa laaaaa hado mana kikayi? Yeah cewar Amana,Nan Sakina
ta dinga godiya Suka gaisa da Ango shima harda godiya,
Sakina ce tayi magana to ki mayar cikin motar kinga ko an kai ciki sai an kara fitowa fa dasu
dole ga mutane,Amana tace af hakanefa na manta kinsan ni ba kawaye ne mata dani
ba,sannan bikina ban samu gatan haka ba ban san ya abin yake ba,bari na maida,ango dai tuni
ya hau mota ya tafi,Sakina ta dauka bari na tayaki...Amana tace commot abeg Amaryace ke ba
aiki ai,matsa ko na makeki,Sakina ce ta radawa Amana ga mijinki can kamar zai cinyeki da
kallo,kinga kalli yadda yake ta muzurai,kamar kishi yakeyi fa,Amana tace zan mareki Sakina
ban son shirme na fasa kaiwa motar ebi ki kai ki zuba,
Kai Amana saurin zuciya da fushi yana nan dai,kyaleta Amana tayi ta koma ta kai kayan cikin
Mota da kanta ta dauko trolley dinta ta juyo kenan taga Alim a bayan yana huci kamar zai
daketa har ta tsorata sai ta tsinci muryarsa yace gyara parking din motarki zan fita da
tawa,Amana itama a fusace tace duk filin nan bai Isa ka dauki Mota ba sai na gyara
parking?Alhmdllh Alim ya furta a ransa saboda dadi hade da sanyi da yaji a ransa Amana tayi
magana yaji muryarta,
Cike da masifa ya kara cewa ko bazaki janye bane?Amana shuru tayi don taga kamar zai
daketa yanzu kuma bata fada,kawai sai ta shiga motar ta janye ta can lungu ta fito a fusace
fuuuuuuu ta ja akwati ta wuceshi.
Badriyya sai murna takeyi Amana tazo Sakina har ta fesa mata Labarin Alim da take away na
Amana da ta musu,
Bayan Amana ta huta saiga Asiya kanwar Alim tazo tana cewa Badriyya wai ina matar Ya
Alim ne?
Da sauri Badriyya ta nuna Amana dake kwance saman gado tana faman tunanin Alim,
Anty Amana ina yini cewar Asiya Amana ta amsa cikin fara'a da sakin fuska,Asiya suna kama
da Alim sai take ganinta kamar Alim,kallon Asiya takeyi tana ta murmushi tana jin sanyi a
ranta,sai suka fara hira, har muryar Asiya kamar ta Alim,Amana sai hira take kakalowa,Asiya
tace muje wajen su Abban Huzaifa da Mama ku gaisa da sauran dangi,Amana ba musu ta yafa
mayafinta tare da kara gyarawa suka wuce,da dan Auta Kanin su Alim suka ci karo Asiya tace
Bro kaga matarfa ya Alim na san baka santa ba lokacin kana schl,Amana a ranta tace wannan
yama fi kama da Alim dina,gaisawa sukayi sosai yana ta tsokanar Amana ashe matas ce
ma,gaskiya na iya zaben me kyau,suna tsaye saiga Nura ma Babban yayansu shida matarsa
da yarsa sun dawo daga shopoing,Asiya tayi sauri ta nuna musu Amana suka gaisa harda hira
sosai da sosai saboda Nura akwai nutsuwa, Amana a ranta ta ce lallai ai wannan Nuran ma
sunfi kama sak da Alim. matarsa ma sai jan Amana take da barkwanci,tambaya Amana tayi wai
ina dana ne Aabid?
Nura yace yana wajen Maman Huzaifa yana ta bacci,ok kawai Amana tace taja Asiya suka
wuce cikin part din su Huzaifa,Da sallama suka shiga palo da Alim suka fara hada ido yana
saman kujera yana cin snacks da Icecream a gefe,
Huzaifa Ango yana gefensa,mama tana zaune tana jira lallenta ya bushe,ga sauran yan Uwa
mata nan gaba daya cike dam a palon amma Alim yana ciki yana cin abu sunki
tashi,,tsugunawa Amana tayi har kasa ta gaishe dasu kaf cikin mutunci,Mama da fara'a ta
tarbeta tana yata sai yau kika zo muna ta jiranki,dariya Amana tayi,Alim a ransa yace wayyo ta
kasheni da murmushinta,
Tambaya Amana tayi ina Abba da yar tsohuwa kaka kenan idan masu karatu baku manta
ba,Tace tsohuwa tana daki da bakin ta har danki Aabid yana wajenta,Abba kuma yana sama ke
Asiya rakata ta gaida kowa,
Sun mike sunje ko ina sun gaisa da kowa cikin mutunci sun dan dade suna hira da kaka
tsohuwa Aabid bacci yakeyi,kowa na dangi sai da aka nuna masa Amana suka gaisa
Fitowa sukayi amma still Alim yana palon kusa da Mama,Huzaifa kuwa ya koma jikinta ya
nanike ya kwanta a cinyarta,kowa ya shigo sai anyi dariya Ango kamar Amarya me jimamin
rabuwa da gida,
Mamace ta kalli Amana dake shirin fita tace zo yata,dawowa Amana tayi tare da tsugunawa
har kasa,duk wanda yasan Amana a da sai yayi mamakin canjawar halinta yanzu har
Alim,Mama tace zaki dawo dakina da kwana ne? Da sauri Amana tace a a zan zauna wajen
frnds,Haushi Alim yaji a ransa yace da kin dawo nan ai nafi ganinki,Huzaifa yace Anty tafi son
cikin yan mata,hararar wasa Amana ta cilla masa,
Yana dariya yace to mene na harara,kowa yayi mamaki ana cewa matar Alim ce amma anga
basuyi magana da juna ba sai kallo da yake binta dashi kamar maye yana shan Icecream,
Mama ta fuskanci kamar da matsala tsakaninsu Amma sai kowa ya share tunda ba wanda
yasan komai akai,Mama tace to ga dakin mijinki ko can zaki zauna dan iyayi dakinsa shikadai
ne ko angon ma su biyu ne amman wannan marar kunyar Mama taja kunnen Alim tace dakinsa
daban kullum yana cikinmu,yaki bari mu sake,dariya akayi banda Alim da Amana, Umma duk
bata sani ba Alim ne ya tura Asiya ta kawo Amana su gaisa da danginsa shi yasa ya dawo
palon ya zauna Sabo da ya kara ganinta,
Mama tace zauna yata,Amana kallon dakin tayi kaf ba space kujera 2seater ce kawai ta rage
me dama dama,itama Alim ne a kai ya wani kwanta,Mama tace zauna kusa da wannan
kwadayayyen Alim kenan,Amana bata son tayi musu,gashi bata so a gane halin da suke ciki da
Alim tunda shima ya boye,Mama tace gyara musu su zauna mana, Asiyace taje ta fara Zama
sannan ta jawo Amana ta fada kujera suka sa Alim a tsakiyarsu,
Tofa an Dade ba a hadu ba.
Jikinsu ne ya gogi juna,wani uban shock ne da faduwar gaba ya shigi masoyan biyu,
Haushi Alim yaji kar ma tace ya damu da ita,itama Amana haka,Alim ya matso jikin Amana ya
bangajeta da kafada tayi gefen kujera haushi taji a ranta tace dan yana Jin haushi na sai ya
bangajeni,gyara Zama tayi,ya kara bangajeta,Amana a ranta tace kai Kai kai da Zafi fa Bai isa
ba saina Rama wlh ina ruwana dashi,Amana ta matso itama sosai ta bangazo Alim Bai zata ba
ai kuwa ya rikita jikin Asiya,
Asiya tana kallonsu tayi murmushi,Alim a ransa yace halinta Ashe yana nan,nan ya samu ya
kara turota tare da kara hade rai,Amana ta kyaleshi ganin mutane kara bangazota yayi,Ai kuwa
ta samu ta sa hannunta iya karfinta ta turashi jikin Asiya tana nishi