Showing 3001 words to 6000 words out of 105161 words
dauraye masa
kaifa da gasara in baiji wlh gobe wajen su Zainaba zanje na siya,
To karki isheni kamar wacce ta bani million,cewar Umma,wucewa Amana tayi wajen kakarsu
Ille tace karbi tsohuwa bani kosan 10 bana bukatar raini shi yasa kikaga ni komai siya nake da
kudina,ba a min kallon banza saboda ni da kudina nake gadarata,iya kudinka iya shagalinka,ille
dai shuru tayi tare da zubawa Amana kosanta tace ga gyaran biyu nan nayi miki,Amanace tace
kwashe abinki zuciyata bata mutu ba bare ki fadawa danki kin ci dani,na girmi tallafinki,babu
Wanda yake ci dani a gidan nan, Ille ce ta kwashe kosanta guda biyu jeki matsiyaciyar
yarinya,shegiya wulakantacciya.
Ae naji gwara ni ummata bata haifi me bin mata ba,kin haifo Baba kin jawo mana bamuyi
dacen iyaye ba,duk mun lalace,wa yasan me kikayi lokacin kuruciyarki,shi yasa Baba ya
gadoki,kisa ya kori waccen yan fulanin daya kawo gidan nan,wlh idan na kara kama Baba dasu
suna iskanci a dakinsa sai na dagargaza musu kai,
Ille ce ta fashe da kuka kowanne yaro yazo yaci mata mutunci akan ta haifi Sulemanu Harka.
AsmaBaffa
Comments dinku shine jin dadina fans tnx a lot.
✳CIRANIN AMANA✳
5-10
By
AsmaBaffa
Haka Sulemanu Harka ya shigo ya riski mahaifiyarsa tana kuka,lafiya Iya?gata nan
Amanace tsinaniya taci min mutunci,cike da takaici Baba ya kwantarwa da Iya hankali ya mike
ya nufi wajen Amana a fusace,Amana tana shan kokonta da kosai,ya fado dakin,Gani yayi
fuskar Amana ba rahma nan take ya tsorata yace haba Yar Amanata a dinga salalawa Iya
mana,a hankali fuska a daure tace an gama Baba,amma ka fada mata bana so a dinga
taimakamin a gidan nan,tunda an San baza a iya tsinana mana komai ba to a daina yi min
rangwami da sauki ko arahar abinci bana bukata,da kudina nake Harkata,shi yasa nima nake
bearing da Amana Suleiman Harka a schl,
To Amanata a dinga hakuri kinji,sai Baba kar kaji komai,Baba jiya ma fa na kamaka wlh da
wata yangwadaddiyar tsohuwa,saura kadan na fasa muku kai,kawai dan Kaine Baba,dan Allah
Baba idan iskancin nan zakuyi ka dinga tafiya inda baza mu ganka ba,Amana zamu bata fa
dama leke kike min a zaure na?to ka daina mana?cewar Amana,
Kaci sa'a wlh na tuna kai Babane da tuni na Tara ma mutane,wai Baba baka jin kunya ka tsufa
haka,kasan bala'in da kake dorawa kanka kuwa,?uwaki Amana kiyi min Addua nima ina so na
daina na kasa,ban San dalili ba,wlh na gaji da bata lokacina ina ma Addua Baba bazan iya
ba,yanzu kai dadi kakeji da muka zama haka,kalli yaranka fa yanda kowa yake babu na gari,
Ni kadai ce bana iban Harka nan irin taka,kana yawa fa Baba idan na gaji nima na kusa, zan
kwace kawai nima nabi sahu,Haba Amana me kike fada haka cewar Baba eh wlh Allah kawai
nima fuskewa zanyi na amsa sunan Amana Harka.
Wlh Baba duk randa na kamaka tsanarka nakeyi,bana son ganin ka,jeka kawai Baba za
kasa na kasa shan koko na Wanda ba wani ne ya sai min ba da kudina nake harkata.
Baba jikinsa yayi sanyi Amma bazai iya daina halinsa ba,ya rasa dalili,
Amana duk tafi bashi matsala a gidan sabo da tana masa nasiha amma bazai iya dauka
ba,gwara kawai ya turata Neman kudi kudu ya huta da halinta,kuma da alama zata nemo kudi
sabo da Amana tafi kowa a gidan zafin nema,ga juriya da kwazo.ga karfi ga bala'i dole za a
buga da ita, Amana ita kadai tafi duk yayansa Amfani a gidan,gata me tsananin kyau da diri.
Zama Baba ya gyara kusa da Amana,tare da riko hannunta,kwace hannunta Amana tayi tare
da cewa Baba ni ka daina rikeni kar nima ka mai dani irin watsatsun matan da kake Harka
dasu,haba Amanata nifa Babanki ne duk abinda zanyi bazanyi da yarana ba,to naji Baba mene
ne,yawwa Amanata so nake kema na turaki Lagos Neman kudi,kije Cirani kiyi Sana'a ki dinga
samomana kudi,watakil ma Allah ya baki miji me kudin gaske a can ko? Dariya Amana tayi cike
da jin dadi zata bar jarabar gidansu,tace Allah barmin Baba,wlh sai Baba,shi yasa watarana
kake birgeni idan kayi tsiya ta wani wajen sai kayi dadi ta nan,Allah dai ya biya.
Dadi Baba yaji yanda zai dinga tsula tsiyarsa Amana bata gidan bare ta dameshi da wa'azi.
Kallonta yayi yace yawwa ta wajena,kudi zan baki masu yawa Wanda zasu isheki amfani a
can Lagos kafin ki fara Sana'a.
Sa'a dai sa'adai Baba cewar Amana tana murmushi.
Nan da sati biyu zaki tafi Amana,akwai abokina zan masa waya shi zai kaiki wajen
kwana,amma Baba ba irinka bane ko ?ai shi Amana daban yake yawwa yanzu naji batu Allah
kaimu sati biyun cewar Amana, Baba yace kinga duk manyan maza na suna jahohin kudi
cirani,amma basa tsinana min komai sai lalacewa da suka kara yi,
Duk cikinsu babu Wanda yaje lagos suna cross river wasu suna Abuja,wasu Enugu,jibi
Hamaza na turashi nassarawa lafiya amma jibi da yazo gida doya kawai ya kawo min,sai 3qurtr
da ya zo dasu,dariya Amana tayi tace Baba rannan saura kadan na masge Hamza bashi da
mutunci har ni zai zaga,shi din banza,Baba ne yayi dan turancinsa daya koya a garin Tafa kusa
da Abuja,yace control control Amanata,
Cike da farin ciki Baba ya fito,
Amana shirin Makaranta tayi ta fito tare da yin ball da wani pow da ta gani a kofar dakinsu,tayi
gaba zuwa schl.
Sabon Malami ta tarar a jinsu har an shiga,cike da gadara tana budawa ta shiga class
din,Malamin ta gani a kan wata kujera da ba Wanda yake hawanta a ajin sai ita,
Wajen malamin ta karasa tare da cewa daga wannan kujerar,mamaki ne ya kama sabon
malamin,yace ke dan uwarki ni zaki fadawa haka,sa'an ki ne ni? Kujerar daga gidan ubanka
kazo da ita,ko ta ubanka ce cewar Amana,bude baki malam yayi,yan class kowa yayi luf,
Ke wlh sai na koreki daga schl din nan bari na fadawa p.c hannu Amana ta tura a aljihu tace
uwar principal zaka fadawa,p.c yaci uwarsa ka fada masa ni Amana na fada uban p.c yaci Uban
sa,
Kujerar ta janye malamin na kai ta zame kujerar da karfi ya fadi kasa ta matsa gefe ta zauna
tare da harde kafa daya kan daya.malamin mikewa yayi tare da karkade rigarsa ya fice fuuu
wajen p.c,
Wajen principal yaje ya fada masa komai,principal dai ya gaji da halin Amana,nan take aka
karkada kararrawa aka tara Assembly duka makarantar,
Guri yayi tsit PC yace ina Amana Suleiman Harka?da sauri tace yes gani nan,nasan a kaina
akayi taro, ko bakace ba zan fito gani,
Ta fito ta tsaya gaban dandazon mutane hannayenta biyu cikin Aljihu tana kallon kowa dai
dai,PC yace kinwa sabon malami rashin tarbiya da cin mutunci gaban aji?yes nayi masa kuma
ko gobe ya kara zan sakeyi masa komai naga dama,
PC ne ya daka mata tsawa ke yar matsiyata,yar gidan Sule tantiri me Neman mata bafa
tsoronki akeyi ba,wlh yau sai kowa ya zaneki a malaman schl din nan cewar pc,
karya kake Saminu PC,gaka nan bakin kwarto dan iska,wlh akan ka zagi iyayena ko ku dakeni
gwara na bar makarantar,babu Wanda ya isa ya taba iyayena ya kwana lfy,makarantar ku din
banza shegu gaba dayanku,PC ne ya cakumo Amana da niyar dukanta nan Amana ta riko
makwallaton wuyan PC kamar zata zareshi daga wuyan,ba shiri PC ya saketa,amma Amana
zagi takeyi iri iri sai da ta gaji ta kada kai ta kalli PC tare da cewar Wanda ya kirkiro boko ma
yaci uwatas,uban uban uwar Bokon an daina bokon dan uwarsa.ta kada kai ta bar schl din,tazo
bakin gate zata fita ta tsaya ta zubawa me gadi rankwashi kwas,sannan tayi gaba,
bagazan bagazan ta shiga gidansu,ba Wanda ta kula ta cire uniform dinta ta tattarosu waje ta
hada da jakar schl din da littafan a tsakar gida ta zuba musu kananzir ta cinna musu wuta,bal
bal suna ci har suka kone kurmus,sannan ta kwashe tokar ta watsar a waje tana bin iska tace
bye bye Boko ni da zan tafi Cirani Lagos garin turancin da Bokon gaba daya, Wani Nishadi taji ya mamayeta da ta tuna zata tafi lagos,
Wanka tayi ta sa wani wandon jean kato Tsoho tukuf gwiwar duk ta yage,tasa rigar Atamfa
katuwa ta kai cinyarta,p cap ta sa wata kalar tsohuwa tukuf da ita,ta fita,wani Namijine ya ce sai
Amana ya garin ne,kallonsa tayi easy T.j easy dai,ya kk?lfy Amana ,kwana 2,wlh tj wai schl ne
zasuyi min iya shege tuni na kwancewa PC number 8 dinsa,dariya tj yayi yace bakya farke
shege ko ki kiramu muzo da yaranmu a yi maganinsa haba Amana ya kike masu sauki
ne,kyalesu nayi kawai sabo da Lagos zan je Baba,
Iyye kice kin kusa fasowa gari gaskiya Dad dinku yana birgeni,murmushi me kyau Amana tayi
ina zuwa tj ku zama cikin shiri zan muku hanya kuma kuzo, sai Amana cewar tj ya zaro 200 ya
bawa Amana ga wannan kya danyi eh yane,godiya nake tj,haba share kawai aike tamuce,jiyafa
Majalisa ta cika ana ta jiranki baki zo,ai ina nan zuwa yau,sai mun ganki.
Rabuwa sukayi da tj,wasu yan matane sukazo wucewa sunci kwalliya yan makarantar k.u.t
wudil ne,sai yanga sukeyi suna yiwa Amana kallon banza,bata kula su ba.har wani turanci
sukeyi su a dole yan University suna degree,tafiya Amana tayi tana kwobarewa tare da takama
tana wani budawa,
Shekewa sukayi da dariya suka tafa,wata a ciki tace oh budurwa har budurwa kyau iya kyau
amma jibi ta kashe kanta,
Amana dai bata kulasu ba,sai wata tace inye kaga maza fa,wannan da gani shaye shaye
takeyi,ko ciwon hauka ya kamata,
A fusace Amana taci birki tare da juyowa,ganin yanda amana ta canja lokaci daya yasa yan
matan nan suka tsorata,zasu yi gudu gashi sun sa takalmi me tsini da damammen skert,
Daya Amana ta cakumo ta hau dukanta sai da ta karya mata hannu daya,sauran su biyun
sun fara gudu Amana ta damkosu saida ta sumar dasu sannan tayi gaba abinta ko juyowa
batayi ba,
Ran Amana ya baci ta fasa zuwa inda tayi niyya ta koma gida,Ummanta ta gani tana yin
Alalar siyarwa ta Rana,can gefe Amarya tana Awarar siyarwa,Goggo shinkafa da miya,Hajiya
shinkafa da wake duk na siyarwa.
Ko wacce ranar girkinta ita zata ci da Sulemanu Harka da sana'ar da takeyi.kowacce tana ci
da kanta da yaranta,Amana kuwa ummanta bata bata sai dai ta siya,sabo da bata da saurayi.
Wajen Amarya Amana ta nufa tare da mika mata kudi Bani ta Naira Dari nama biyu zakisa
min kuma Manya,harara Amarya ta watsa mata,ubanki ne ya bani kudin?ko bashi ya baki ba
wlh in bakisa 2meat ba sai na tankadar da tukunyar miyar baki dayanta,ba shiri Amarya ta zuba
mata shinkafa da Nama biyu manya harda gyaran guda,karba tayi tare da cewa cire
gyaranki,na fada muku ku daina yi min mutunci a kan na siyi abunku,bana son a dinga taimaka
min,
Gyaran da Amarya ta sa mata ta cire tace jeki yar Iskar banza.
2weeks ta cika Amana ta gama shirin tafiya Lagos,fitowa tayi sanye da wani 3qtr jean Wanda
wandon kaninta ne Yusuf ta yanke da Almakashi ya dawo gajere,wata falkekiyar t-shirt din
Hamza ta sa ja ta gama kodewa da jemewa,siririn gyale ta daura a kanta,da wata
kwarababbiyar Jakarta karama tasa yan tsummokin kayanta ciki,
Umman Amana sai murna takeyi zasuyi kudi,yarta ta tafi Lagos,yan gidan suma dadi sukeji
masifaffiya zata tafi su Shana,Babane ya kalli Amana sai da dariya ta kusa kwace masa irin
wankan lagos da tayi,Babane yace Amanata ki canja kaya jibarki kamar inyamura haka zaki je
lagos?Yo Baba so kake nayi yawa,Lagos ce fa gwara na saje dasu.
Har tasha Baba ya kaita ya biya mata kudin mota sannan ya bata dubu Hamsin saboda kafin
ta fara aiki,sosai Amana ta Adana kudinta,gashi irin katuwar mota ta hau lexs,
Amana anyi kicin kicin cikin Arna,motarsu ta tashi sai washe baki takeyi tana yin guntun
turancinta,sun kwashe tafiya me nisa cikin duhun dare,har sun wuce rabi sun kusa zuwa,kitttt
driver ya gangare kasa yana ihu yan fashi,ai kuwa sai karar bindiga ce ke tashi,Amana ko a
jikinta,nan yan fashi suka fito da kowa waje,motoci suka gani birjik an taresu,ga wasu motoci
daban na Alfarma sun kai wajen 10 a Jere,daga gani na wani me kudin ne,Amana motocin me
kudin kawai take kallo ta manta a gaban yan fashi take,
Wani daga cikinsu ne ya bugawa Amana tsawa amma ko tsoro baiga taji ba,su Kansu yan
fashi dariyar shigar Amana sukeyi,wani azababben gaye me tsananin kyau da kowa yake
tunanin Bature,kyau kamar Aljani,da ganin yanda yake tafiya Naira ta ratsashi,sai kallonsa akeyi
kowa,yan fashi ne suka nuna shi da bindiga tare da nuna masa wata tsohuwa sukace kayi sex
da wannan maza ko yanzu mu aikaka lahira,
Wani takaici da bakin ciki ya mamayeshi,sai hawaye a idon wannan hadadden saurayi suke
zuba sharrrrr,tsohuwa da kamar kakarsa ce,gata Arniyace,kuma shi da bai taba zina ba ko da
budurwa sai wannan tsohuwar,cikin matsanancin tashin hankali ya riska,tare da dana sanin
zuwa Kano a mota,bai bi flight ba,
Amana ita kanta sai taji saurayin ya bata tausayi,taya zata iya cetoshi,sai kallo take kare
masa,gashi kamar Aljani sabo da kyau,a ranta tace wannan da gani bature ne Allah sarki ko
Hausa ma naga Alama baya ji.
A ranta tace dole na taimaki me kyan nan,Amana ce ta buda tare da kwobarewa da 3qutr
tanta,tace easy sir easy dai,wa yace daku ba ku ba,ai wlh ba mazaje sai ku,duk wajen nan
Matane,Allah dai ya biya ogoginmu,sai Mazaje,irinku kuna birgeni Allah wlh ba a shiga dawa
dan karya, haka Amana taci gaba da yi musu kirari sosai,murmushi ogan yayi na jin dadin
yanda Amana take kodasu,
wani yace Yan mata ina kudi,dubu hamsim din da Baba ya bata ta mika musu ai Mazaje ko
Baku tambaya ba dole na Baku,ai nakune dama,ko wiwi kwa danyi eh yane,murmushi Oga yayi
tare da cewa sai yan mata me kikeso yanzu ayi miki sabo da ke ta wajen mu ce.Amana taga ma
kallai yan fashin nan masu saukin kai ne,kuma basu fiye zalinci ba.nan ta fara magana Allah taimaki Oga waccan me kyan nake so a bani shi ya kaini har lagos a motocinsa,Allah
bar mana oga kar ya taba tsohuwar can,kawai ni a barni dashi,yarinya mun baki shi,kema kina
son ki dan dandanashi ko,ai Oganmu tunda na ganshi nake kwadayinsa a dan bani shi nayi
masa Eh yane ka gane,
Oganne ya dakawa handsome tsawa kai mike tsaye, Allah ya taimakeka ka godewa wannan
yarinyar,ka kuma tabbatar ka kaita inda take so.shi kam wannan me kyau ya cika da mamakin
wannan yarinya marar tarbiyya me 3qtr.abin ya bashi matukar mamaki,lallai tafiya mabudin Ilmi
ce.
Sauran mutane kowa kallon Amana yake har Wanda basa jin Hausa ma.
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
10-15
by
AsmaBaffa
Wannan saurayi tunda Amana ta fara magana yake kallonta yanda take acting kamar a
film,gashi a kankanin time ta canja musu ra'ayi,wani farin ciki ne ya mamayeshi,yarinyar nan ta
taimakeshi a rayuwa babu abinda zai mata sai addua,
Kudinta ogan yan fashin ya mika mata karbi yan mata kuje,haba Oga ai nakune idan na
karba nayi fariya,nifa sabo daku na taho dasu,an gaisheki yan mata kuje abinku,daya ne a ciki
ya bugawa handsome tsawa maza kuje a kaita inda take so,Amana ce tace wa me kyau hey
guy basu rabonsu su samu suma,nan take kuwa ya rubuta musu check na 5 hundred
thousand,sukace tayi kadan ya kara musu 1million,sukace tayi kadan,Amana ce tayi magana ai
sai Oga ayi masa afwa haka,angama yar Oga kuje kawai cewar wani daga cikin yan fashin,
Wannan jerin motocin suka nufa da handsome da Amana wata dalleliya da tafi ko wacce kyau
a tsakiya ita wani guard ya budewa Amana ta shiga,saurayin bai so kazama ta shigar masa
mota ba amma ganin Yan fashin zasu iya canja ra'ayi yasa yayi shuru ya shiga shima,su biyu a
bayan motar,shi da Amana,kana yawa master wlh kayi sauri ka bawa guards dinka dama suja
motocin muyi gaba,zasu iya canja mind yan fashi basu da tabbas,ya kana abu kamar baka son
lafiyarka Baba cewar Amana,harara ya watsa mata,easy man ya kake yawane eh,sabo da kai
fa na taimakawa wlh ganin za a hadaka da tsohuwa,nasan duk da Allah bazai kama ka da laifi
ba amma tsohuwa tukuf