Showing 12001 words to 15000 words out of 105161 words
ba da yawa ba,yatsunsa kansu abin kallo ne da
birgewa,namiji ne na gaske ko ina Alim ya shiga sai ya haske wajen,Amana idan ta tsaya kusa
dashi duk da cewar itama yar farace amma sai ta tashi a chocolate me hasken gaske lol,
Alim mutumin kirki ne na gari ga hakuri da kawaici,me kyauta,ba ruwansa da duniya,baya
magana sai da dalili,idan zakuyi 1wk tare da Alim indai ba muhimmin abu bane to baza kaji
maganarsa ba,ko a cikin danginsa iya gaisuwa ke hadasu sai su kwana 2 basu ji yace ko hi
ba,yafi yin magana da hannu,ido,etc amma bakinsa baya magana sosai,shi yasa Wanda basu
sanshi ba sai suce kurma ne,haka frnds dinsa sai su yini tare amma daga gaisuwa baya kara
cewa komai,
Best Frnd dinsa Mubaraq shima wani hadaddan handsome chocolate ne yaso ya canja halin
rashin magana na Alim amma ya kasa.Mubaraq dan gidan wani minister ne a Nigeria,kuma shi
lawyer ne,sosai Alim yake kaunar Mubaraq, shima Mubaraq haka.
Halin Mum fatima kuwa abin yafi yawa a kan Alim domin kuwa sai da ta tursasa Alim Auren
mata har guda biyar tana sawa ya sakesu dole,
Matarsa ta farko da mum dinsa ta aura masa Salma ce baya sonta yana kyautata mata,ganin
haka Mum ta ce dole ya saketa ko ta tsine masa,haka ya saketa yanzu haka Salma ta auri wani
mijin tana zamanta lfy, Ramlat Mum ta kara aurawa Alim itama baya sonta,amma tana
hutawa,nan ma Mum ta koreta, Sakeena ma hakan take,sai Maryam itama tasa aka saketa, ta
biyar itace Nusaiba itace wacce Alim ya dan fara Sonta har yayi saduwar aure da ita ta samu
ciki,itace Alim ya hada dabara sai suka dinga nunawa Sam Alim azaba yake nuna mata,shi
yasa Mum ta kyaleta tare da Alim,har cikinta ya isa Haihuwa ta haifi zankadeden yaronta me
sunan Abba Usman suna ce masa Aabid,satinta biyu da haihuwa Allah yayi mata rasuwa,
Alim yayi bakin ciki duk da cewar ba wani sonta yakeyi ba Nusaiba yarinyar kirkice, shekarar
Nusaiba daya da rasuwa Mum ta koma Ethiopia kasarta ta samowa Alim wata yar Uwarta
Sageera,amma Sam Abban Alim yace wlh bazai aura ba,ya gaji da Halinta,tana sa dansa auri
saki ganin Alim me hakuri ne,Abba yace idan ta sa Alim ya auri wata matukar bashi ya nemo da
Kansa ba to taje ya saketa,shike nan Alim ya samu lafiya,
Sai dai Mum ta kulle a ranta baza ta bari wata ta kwace mata danta ba,haka kawai wata tazo
ta cinye mata dukiyar yaro ba,
Yayinda take burin Asiya yarinyar kirki yarta ta auri miji na gari me sonta kajifa son kai.Aabid
dan Alim a wajen Mum yake zama shi yasa Sam Aabid bashi da tarbiyya,saboda yanda take
kaunar jikanta bata yi masa fada,
Ko kukansa taji ta dinga zage zage za a kashe mata jikanta,ko makaranta idan yace baya so
to baza ta bari yaje ba,
Aabid ya gama lalacewa tun yana karami ya iya zagi da cin mutunci iri iri,shima baya son
talaka wajen kakarsa Mum duk ya koya,Alim abin da ya dameshi wajen Mum yaje yace ta bashi
Alim su zauna tare sabo da ya samu abokin zama a gidansa so bored yake.
Sabo da son da Mum kewa Alim ta yarda da kyar ta bashi Dansa Aabid,watan Aabid Uku
kenan tare da Alim suna rayuwa tare,yau da suka hadu da Amana yaune birthday na Aabid ya
cika 4yrs da haihuwa,yaune kuma Amana tayi maganin rashin kunyar Aabid,
Har ga Allah Alim yaji haushin Amana irin dukan da tayiwa dansa amma sabo da hakuri da
kawaici irin nasa bai nuna ko ransa ya baci ba,kuma dama rashin kunyar Aabid ta dameshi ya
rasa ya zaiyi dashi,amma gashi ya hadu da Amana ta koya masa hankali.
Ci gaban labari
Asibiti suka nufa da Aabid nan doctor ya dinga masifa taya za ayiwa yaro irin wannan
dukan,amma Alim shuru yayi bai ce komai ba,bayan sun dawo da dare gidansu ya tafi wajen
Mum tare da Aabid,Mum tana ganin Aabid baki da fuska a kumbure ta gigice tana lfy me ya
sami jikana?Alim ne yayi Sauri yace Mum wata yayiwa rashin kunya ta zaneshi,
Aifa Mum tuni ta fara zagi tana wacce shegiyace yar matsiyata ka nuna min ita wlh sai na
batar da ita, a hankali Alim yace calm down Mum shi fa ya zageta,dan uwarta ita wacece da
baza a zageta ba,ai da nasan gidansu har iyayenta sai sunyi nadamar haihuwarta,Aabid ne
yace Mum ki kyayeta ina conta ta au dani keke,ta ciya min sweet, Rufe min baki sai na kwato ma yancinka,kai dama Alim na lura ba son yaron nan kake ba,idan
baka so ka dawo min da jikana aikin banza na gaji da shirmenka,
Kai a dole me hakuri ko kana gani za a kashe bawan Allah,nan fa Mum ta fara lilita Aabid tana
Lallabashi tare da cewa bazai koma wajenka ba sai yayi 1wk a wajena ya huta,ba yanda Alim
ya iya haka ya mata sallama ya koma gidansa.
AsmaBaffa
Tnx alot readers.
✳CIRANIN AMANA✳
25-30
AsmaBaffa
Mum din Alim ce ta dauki Aabid sai lallabashi takeyi ta rasa inda zata sa kanta,haka ga
bacin ran yau birthday na Aabid amma ko dan party ba a shirya masa ba,part din Abba ta nufa
da Aabid dauke a kafadarta,ko sallama kasa yi tayi ta shiga zuruf tare da cewa kalli yanzu dan
Allah Abban Alim abinda yaron nan yakeyi ya dace,jiba yanda yana gani wata Jaka ta Zane min
jika,Abin haushi ma Alim ya kasa hadawa yaron nan ko dan birthday party,
Kallonta Abba yayi da mamaki tare da cewa party addini ne ko dole ne,wannan dabi'ar
yahudawa ce da mutanenmu suka daukarwa Kansu da shirme,da ka hada birthday party gwara
ka yini kana karatun Qurani,ko tasbihi,ko azumi kana yiwa kanka addua sosai a wannan rana
yafi ka kunna kida.
Tabe baki Mum tayi tana yo dama ai haka zakace,ni dai kawai Allah ya hadani da miji ba
wayayye ba,kana da kudi,ka zaga duniya,kana shiga mutane amma ka kasa wayewa,na
tabbatar duk yarana halinka na gidadanci suka dauko, fuuu tayi waje dauke da Aabid ranar
kusan kwana tayi a zaune tana jinyar Aabid dinta. Alim ne kwance bisa lallausan royal bed dinsa Wanda ya kai karshe wajen haduwa,tunani
yakeyi yanda zai samo me kula da Aabid wacce zata bashi tarbiyar da ta dace uwa ta ba
danta,kafin Allah ya kawo masa wacce yake so ya aura,
Arniyar Wayarsa ya jawo tare da kiran Mubaraq best Frnd dinsa,yana dagawa a hankali Alim
ya fara magana sai ka saurara sosai zaka ji me yake cewa,bakinsa da kyar yake motsawa Frnd
maganar da ka bani shawara kan na nemo me kula da Aabid kafin na samu nayi aure,so ya
kake ganin za samu?
Mubaraq ne yayi Dariya yace bari zanwa Mama na maganar a samo wata ka barmin komai a
hannuna,alright Frnd cewar Alim.
Bayan sati daya tsakani Mubaraq ya kawo wata dattijuwa gidan Alim,Alim shi bai da damuwa
nan ya karbeta yana zaune a luntsumemiyar kujera kafa daya kan daya yana latsa waya,ko a
bai cewa Rakiya dattijuwa ba,tunda tazo ko da ta gaisheshi ma hannu kawai ya daga mata
kamar wani sarki,a.c ce kawai ke ratsa Rakiya har karkarwa takeyi,
Wani remote ya dauka tare da dannawa minti daya sai ga wani me aiki ya shigo da
sauri,Umarni ya masa kan ya tafi da Rakiya yayi Abinda ya dace,suna fita ya tura Driver ya
dauko masa Aabid wajen Mum,
Sai da Mum ta zage driver tas sannan ta yarda Aabid ya bishi,
Rakiya aka kaiwa Aabid Nan fa yaro ya canja fuska yana yatsina tare da toshe hanci kamar
yaga kashi,
Da dare ko da Rakiya tazo shiryashi sai da ya zageta sosai sannan ya tafi part din Daddy
sa,Alim duk abinda zakayi zai wahala ya ma magana bare ya hanaka,dan haka tun Rakiya na
hakuri da Halin Aabid har ta fara dukansa, kuma Alim bai taba ce mata ta daina ba,
Yana kallonsu watarana Alim na zaginta ita kuma rakiya tana zaneshi amma Alim bai ce
musu komai,har Rakiya ta kwashe 2mnths tana kula da Aabid,yauma kamar ko yaushe Suna
palon Alim suna kallon film sabo da Alim shi ba ruwansa da kar a shiga inda yake matukar baza
ka takurashi ba ,Alim yana ta aiki a system Rakiya tana canja Chanel taga wata tasha suna haska BF ta bar
tashar Abinta Suna ta kallon,Alim ne yaji nishi kamar ana Sex da sauri ya kalli TV yaga abinda
yake faruwa,Aabid yana ni ki kaimin cartoon Chanel amma ko kallonsa Rakiya taki yi,da Sauri
Alim ya dauki remote ya kashe TV gaba daya,ba tare da yace komai ba ya ebo kudi ya mikawa
Rakiya yace take this na gaji da Halayenki maza na Sallameki,zama tayi zata fara bashi
hakuri,securities ya kira sukayi waje da Rakiya.
Sosai Alim ya shiga matsanancin bacin rai,Mubaraq ya shaidawa matsalar,3days aka kawo
wata budurwa ita kuma,nan ta fara kula da Aabid,Aabid kuwa ya tsani wannan budurwa sabo
da tsawar da take daka masa,
1mnth ltr budurwar nan ta kamu da son Alim kullum sai ta dinga zuwa tana zama a kusa
dashi,yau ma yana nutse kan wata chair 2 seater yar budurwa ta fito tana karairaya tana zuwa
kusa da Alim ta zauna kafadarta na gugan tasa,mikewa yayi har ya daga hannu zai mareta ko
me ya tuna sai ya fasa,itama kudinta ya bata ya koreta,
Basu gaji ba suka kara kawo wata tsohuwa Yakumbo,nan ma Ya kumbo ta dinga yiwa Alim
sibare tana satar masa kudi,ba shiri ya sallameta itama,haka Mubaraq ya dinga kawowa Alim
masu kula da Aabid amma basuyi dace ba,sai ma kara lalata Aabid da sukayi,ko wacce halin
tsiyarta daban. Gashi Aabid kullum zancen new Antynsa yakeyi shi ita yake so a kaishi wajenta ta hau dashi
keke,Aabid da Alim basa wata hira a tsakaninsu bare wasa,saboda Alim bai son Surutu.shi
yasa in ka shiga wajensu sai kagansu shuru kowa harkar gabansa yakeyi kamar basu San juna
ba,ko da Aabid yazo yana so suyi wasa da Alim sai kaga Alim yayi murmushi ya bashi hakuri
cewar yaje yayi shi kadai,
Watarana yayi kuka haka har ya saba,babu wata shakuwa tsakanin Uban Alim da dan Aabid.
Shi yasa Aabid ya cewa Alim Daddy ka kawo min new Anty ta nafi sonta,shareshi Alim yayi
a ransa yana tab wannan yarinyar marar tarbiya me yin abun maza,Amma tunda Aabid ya
dameshi zai kai Aabid wajenta Saturday ya yini a wajenta yaga me zai faru.
Haka Alim ya kulla shawararsa.
Gidan baki kuwa can wudil kauyen su Amana Baba yaji Amana shuru tunda ta tafi Amana sau
Uku ta kirasu a waya suka gaisa da yan gidan gaba daya,shi kuwa Baba sau daya ya taba
kiranta yajita Lfy shike nan bai kara ba,itama Umman Amana ko ta kan Amana bata bi bare
tasan halin da take ciki,su kuwa sauran kanne da yayye dadi ma sukeji jaraba ta bar musu
gidan zasu Shana,yayinda manyan mazan suke kudu suma cirani suka tafi suna can suna
sheke ayarsu.
Wani abokin Baban Amana dake jigawa state ne ya aiko da yarsa yar 16yrs domin Baban
Amana ya taimaka ya kaita makarantar Boarding dake garin kacako kasancewar kusa suke da
garin,haka sulemanu harka ya karbi Amanar yarinyar nan hannu bibbiyu zai kaita schl ranar
Monday,yarinya dai Mariya tana nan dakin Uwar gidan Sulemanu harka kafin a kaita
schl,Sulemanu sai kallonta yake yi duk inda ta gifta,akan haka ma ya rage fita wajen aikin
yayinda ya gama danawa Mariya tarko.matansa suna hankalce dashi sunga take takensa,sabo
da haka suka kara kafawa suka tsare kan a samu a tseratar da yarinya daga tarkon mijinsu
fasiki.
Yau Saturday 10am motocin Alim suka parker a bakin wajen suya nasu Amana,manager
guard yayi wa magana,few seconds sai ga manager,yau Alim magana yayi da kansa,pls I need
to see that Girl dake aiki anan she look like a Boy,nan manager yace oh Amana Hausa
Girl.yeah cewar Alim
Cikin harshen turanci Manager yace tana gida sai yamma take zuwa aiki,Alim yace bani
Address nata idan ka sani,da sauri manager ya bawa Alim Address na Amana,
Juya motocinsu sukayi har gidan Dan Uzuri,Alim yasha mamakin ragargajewar gidan,yanzu
wannan yarinyar anan take zama Amma kayan da take sawa bai dace ace anan take zama ba,
Gashi gaba daya yaga unguwar tantiran yan iska yan bariki take zama,layin su Amana kuwa a
unguwar ma na daban ne sai ka shahara a iya shege sannan zaka iya zama ciki.
Sosai Alim yake mamaki tare da cewa no wonder yarinyar take karshe wajen rashin
kunya.dole ma Amana baza ta taba zama ta gari ba cewar Alim,Dan Uzuri ne ya karaso jikin
motocin Alim a gigice,
Guard ne ya masa magana tare da kwatanta masa yarinyar da suke nema.
Da Sauri yace Amana yanzu baza a sameta a gida ba tana majalisarsu.
Suna haka sai Ga Amana sun fito daga wani corner tare da wasu maza su Uku,sai hira
sukeyi.
Alim yana kallonta ta mudubin motarsa a ransa yace lallai wannan ta shahara.
Kafin kiftawar Ido Dan Uzuri ya isa wajen Amana tare da Nuna mata jerin motocin Alim wasu
kalar da bata taba gani ba,Dan Uzuri yace wlh ba ruwana Amana Idan masu kudi kika
tabo,baza ki jawo min bala'i ba,dama nasan rashin mutunci sai yasa kin hadu da ajalinki,gasu
can sai kije wajensu ke suke nema,haka gari banza masu kudi haka baza suzo nemanki ba, Kallon guards din Amana tayi ta gane Me kyau ne mamaki tayi yanda yasan gidan da take
sai ta tuna dasu manager nan tace tabbas manager ne ya basu Address dinta,a fili tace to me
nayi musu kuma hmm bari naje naji,
Da Saudi Dan Uzuri yace ke kika sani wlh kar ki nuna kin sanni,idan sun hallakaki na buga
waya can kauyenku,aikin banza me jaye jayen tsiya,to nafi karfinki li'ilafi kuraysh baza ki jawo
min ba,lakadaja akum a kanki.
Dan Uzuri wani lungu yasha tare da boyewa ciki yana lekowa yaga me zai faru yasan
Amana dai kam sai dai ya bugawa Sulemanu Harka waya ya sheda musu ai Amana ta tsufa a
prison.
Bude mata kofar motar Alim akayi ba tsoro ta shiga,Amana basu saba da gaishe da mutum
ba ko iyayensu basa gaidawa dan haka Sallama kawai tayi ta zauna a cikin motar wani sanyi da
kamshi yana Ratsata,ta lumshe ido wani niima,bugawar zuciya hade da kwarjinin me kyau sun
taru sun mamaye mata zuciya.
Ta rasa dalilin da yasa me kyau yake mata kwarjini,kuma sai ta dinga jin masifar tsoronsa,da
kyar ta iya daga kai ta kalleshi jin shuru baice komai ba,Subhannallah wani azababben kyau
taga ya kara,Wanda ya wuce kwatancen me tunani,gashi sanye cikin wata rantsatsiyar shadda
ta garari milk color,dinkin irin pencil dai dai jikinsa ga kan nan bai sa hula ba sai gashi baki sidik
luf dashi me yawa yash gyaran fuska,ga wani dan Saje da dan gemu das.
A hankali kamar bazai magana ba cike da gadara da izza yana latsa waya ba tare da ya
kalleta ba,ya Umarci Guard ya dauko Aabid a dayar motar,nan da nan matakan tsaro suka
dauko Aabid ai ido hudu Amana tayi da Aabid da karfi ya kwalla kara ta murna da jin dadin
ganin New Antynsa,nan ya karaso da dan gudunsa ya dane jikin Amana sai murna yakeyi,tare
da cewa new Anty zan biki,alright My sweet Boy, I missed u cewar Amana,mic (miss)you too
Aabid ma yace,ta gefen ido Alim ke kallonsu yana jin Dadi a ransa,Aabid dinsa zaiyi farinciki
yau.a hankali Alim yace kuje da Dare after Isha zanzo na daukeshi,Ok Baàbaà sai kuma tace
au Sorry pls.
Daukan Aabid tayi tare da sabashi a kafada nan Aabid ya ce Bye Daddy shima Alim ya daga
masa hannu suka ja motocinsu suka tafi, sun bar Amana cike da Mamaki mutum bai Santa ba
amma ya kawo Mata dansa.Dan Uzuri ne ya fito daga inda ya boye shima yana mamaki a ina
Amana ta samo masu kudi haka har yaronsu suke bata raino.
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
30-35
By
AsmaBaffa
Ina mika Godiyata ga dubban masoyana makaranta wannan novel.
Dan Uzuri a fili ya firta ko ni Dana taso cikin