Showing 66001 words to 69000 words out of 105161 words
Alim ya gujeta ba a lokacin da take bukatarsa.
Baba yace Ku kuma matana wacce taga zatayi aure to tayi aurenta amma ta barwa yayana
a cikin yan uwansu ban yarda a rabamin kan yayana ba su zauna tare su so junansu
zumincinsu yayi karfi,
Kuci gaba da min addua ko Allah zai karbi tubana ya yafe min,na barku da alheri.
Nan Baba tari ya turnukeshi yana ta murkususu Bai kara minti biyu ba yace Amana ki tallafi
zuri'ata tayi kyau,ta gyara,abinda banyi ba kiyi musu kiyi iya kokarinki ki bar sauran ga Allah,
Gaba dayanku Maza da mata Manyan Ku tallafawa Amanata Ku Kula da kan....k...luf Baba ya
cika Allah ya karbi rayuwarsa cikin wannan dare,
Sunyi kuka sunyi Addua mutane sun girgiza da wannan mutuwa,
A daren aka hada gawa akayi komai,washe gari Aka fito da gawa akayi mata sallah aka
dauka akayi hanyar Makabarta a hankali akaji kamar makara na motsi, a tsaya a tsaya a kace
Makarafa na motsi dubban jama'a suka fara guduwa sun firgita,
Liman da wasu tsirarine suka karasa kan makara tare da yayan Sulemanu suka duba Gawa
sai akaga Baba ne yake motsi yana magana Badai asibiti zaku kaini ba a mai Dani gida ko na
tsine muku,yana makyarkyata yace ina Amanata iceko tana Kula da Iyalina,ina su Hamza kai
...kuna tallafa mata kuwa,matana fa sunyi aure?karfa su auri kowa ina son matana ina kishinsu,
idan sukayi aure to nima za a bani Hurulein
Ina littafin da dukiyata take ciki ne Ku raba kuwa?na bawa Haladu buhun masarata
Biyar,Amana a bata sabon injin murzar taliya dana siyo rannan hhh
Ai su Hamza murna da gudu suka suri Baba suka koma gida ana Bai mutu ba Bai mutu
ba,gawa taki rami gawa taki rami Allah wlh sai Baba.
Suna dawowa karfe Biyun rana Baba ya kara margayawa wannan mutuwar gaske ce domin
Har doctor suka dauko ya auna ya tabbatar musu ya rasu, haka suka kara sabon kuka da komai
aka kai gawar Sulemu Harka aka binne.
Amana kuka kamar ranta zai fita sauran kuwa har sun fara Hakura,Amma Amana itakam ba
iya kukan mutuwa take ba,kukan rabuwa da masoyinta takeyi,ga nauyin da Baba ya daura
mata,ga kuma ko secondary bata gama ba,bare ace tayi karatu tunda ba miji ta nemi aiki ta
cikawa Baba Burinsa,
Ga cikin dake jikinta gashi Alim baima yarda nasa bane,ga bakin cikin sharrin da aka mata
ga mutuwar uba duk ita kadai,shi yasa gaba daya ta kusa zarewa,yan uwa duk sun hadu da
aluma masu zaman makoki ana ta yiwa Amana nasiha an zata kukan mutuce kawai,mutane sai
ace Allah sarki Amana duk tafi shiga damuwa ai sun shaku da Babanta duk yafi sonta dole tayi
kuka mutuwar tafi taba ta,
Tun Amana na kuka ita kadai a daki har ta fito waje ta kalli bishiyar da Baba ke Zama sanda
tana Budurwa tazo ta wuce tana bouncing tace ai sai Baba Allah bar mana tsoho,yanda Baba
ke ji da ita komai Amanansa,
Alim dinta ta tuno ta tabbatar da suna tare da tuni ya lallasheta ya sata nishadi da tuni ya
zame mata gurbin uba,amma yanzu Babu me lallashinta,ya tarairayeta ya bata farin ciki ya
tallafi danginta da iyayenta,shine gatanta,iyaye kuma duk lalacewarsu katanga ne,nan take
Amana ta kurma ihu a kofar gidan ga maza masu zaman makoki su Hamza suna ciki,Amana ta
fadi a kasa ta fara burbuwa tare da cewa wayyo Allah Bango ya fadi katanga ta rushe,gatana ya
kare,gatana wayyo gatana,duniya kin juyamin Baya,kin juya min up side down,wayyo uwata
wayyo Ubana...mijina...mijina shikenan nima.
Su Hamzane cikin hawaye suka riketa tare da danne kirjinta saitin zuciyarta domin wani
numfashi yakeyi zuciyarta zata buga,
Da kyar aka samu numfashinta ya dawo normal,magana ta fara Ya Hamza a haka rami nima
a binneni,nima dan girman Allah ku harbeni,zuciyarta ta nuna tace ku fasa min nan da Bullet,
Haladu dauko wuka a samu wani ya yankani dan Allah masifar danake ciki tafi karfina,
Kb da Isa ta kamo tace dan Allah ku farke min ciki mene Amfanina,kuka ta kara fashewa
dashi,haka suka shigar da ita gida Amana ta fita daga hayyacinta,
Zazzabi tayi sosai sai hakuri ake bata,yau Kwana hudu da rasuwar Baba,Amana ta dan
gana ta daina Kukan rashin Baba sai na Kukan rashin Alim,amma duk da haka idan taga
abokan Baba da wani abu daya shafi Baba sai kuka mutuwar ta dawo mata sabuwa.
Kamar yau Huzaifa Badriyya ta fada masa rasuwar babansu dole ya taso Abbansa da
kanwarsa Saddiqa suka taho ta'aziya,bayan sunyiwa su Hamza sai suka jera Baban su Huzaifa
a gaba,Huzaifa da kanwarsa Saddiqa suna baya haka suka shiga har cikin gida domin Yiwa
mata ta'aziyya,Amana tana ganinsu haka mutuwar Baba ta dawo mata sabuwa ta dora hannu
aka tare da kwallawa da karfi wayyo wasu suna da Uba mu bamu dashi wayyo Ubanmu...ga
wasu yan gata da Ubansu nan ma da kyar aka lallasheta,sai kuma tashin Alim ya fado
shima,ganin Huzaifa suna yanayi da Alim sai ta fara Hawaye, Tana ta kallon su Huzaifa kamar bata sansu ba,
Huzaifa bai sai me ya faru ba,yace Madam sai hakuri na sanarwa mutuminki yace min yaji kin
yayanki ya fada masa dashi Akayi ta'aziyya zuwansa ukku ma,
Cak Amana ta tsaya da Kukan wato har ta'aziyya yazo ko nemanta baiyi ba da gaske ya
hakura da ita,nan hawaye masu zafi suka zubo mata,
Ta kara wajen Haladu tace wai Alim yazo ta'aziyya?
Haladu yace dashi aka raka Baba har makabarta a mutuwarsa ta karshe, dashi akayi sadakar
Uku,cewa yayi kar mu fada miki bai son ganin kukanki,
Amana a ranta tasan dan kar ya ganta ne ya tsaneta,
Amma kuma taji wani irin dadi da farin ciki tare da da ran Allah sa ya dawo gareta
watarana,nan kuma tayi dariya hadi da hawaye,Amana bamu sanki da kuka ba ko ya kukace
readers?
Huzaifa ne ya fito zasu tafi Su Abbansu na Mota da kanwarsa shi kuma Huzaifa sun tsaya a
soro suna ta hira da Badriyya cike da so yana lallashin Badriyya,Amana ta hangosu a cikin
mutane a fili ta furta ni bani da masoyi babu me lallashina sai kuka tare da tuna yanda Alim ke ji
da ita.Ummanta ne suka fara mata fada sosai,kamar akanki aka fara mutuwa Allah ya hana
Yiwa mamaci kuka haka,idan ma ganinki wani abu to ki sani Baba ba dawowa zaiyi ba kukanki
ba gata bane a wajensa,masifa kike kara masa,daki Amana ta fada taita Kukanta.
Kwanan Baba Bakwai da rasuwa yau Alim yasa Abbansa,da Nura tare da dan autansu suka
je sukayiwa yan gidan su Amana ta'aziyya,
Lokacin Amana ta kule a daki tana ta zazzabi da kuka,sai jin labari tayi Alim ne ya hana a
tasota,wai zai dawo.
Ga abinci sun kawo musu Mota guda da kudi masu yawa sannan suka tafi,
Haladu ya ce Amana kai mijinki na sonki kinga yanda yake barka kuka kamar mace ke kyace
babansa ne ya mutu,kb yace ai wannan Kukan Uba bai cancanci ayi masa ba sai dai Uwa,Isa
yace kutmar Uba guy nan mace ne,kb yace a macen ma ta gaske,Hamza yace mamakin danayi
mutum kai ba ubanka ba amma kafi yayan cikinsa kuka, Haladu yace kai Burauba naga kuka wajen yaron nan kasan yaran masu kudi yayan Hutu ne
inda kaga mace haka suke basu saba da gwagwamarya ba,wai guy nan daga cewa Amana ta
suma tana kuka ta rame tayi duhu kawai ya barke da kuka shima yo ko uwatace ai bazanyi
kuka ba bare mata,akan wata mace ka kama kuka, Hamza yayi dariya yace ai kabewa ne,Isa yace ai mugun tumatir ne wlh.ammafa yana son
Amana da ka ambaci sunanta za kaga ya kafe ka da ido ya shiga wani hali sai kwalla kuma
kwal kwal,
Kb yace ai da ace ban san Amana ba da cewa zanyi asiri tayiwa guy nan,Hamza yace
gaskiya Uwarsa ta haifawa Amana da Allah ya tsare ta haifawa Wata da,
Suna tsaye suka ga Amana yif tayi kasa ta sume saboda tsananin tunanin Alim,surarta
sukayi Sai asibiti.
Kwananta uku aka sallameta tare da garga din Likita cewar a kiyaye damuwa zata mata illa
kwanan nan,
Suna dawowa gida aka rufarwa Amana da nasiha cikin kuka tana share ido tace ku nutsu na
baku labarin mece damuwata,
Kaf Amana ta kwashe ta fada musu tun farkon Haduwarta da Alim da irin zaman auren da
sukeyi da soyayyarsu,da Mum Alim abinda take mata,da kuma gidan da ta zauna tare da Alim a
garin,da sharrin da aka mata,sai rasuwar Baba,mata har Amana suka taya kuka,sun san Baza
ta aikata haka ba,Hamzane yayi magana Lallai ko waye aka masa haka dole ya yarda kar kuga
laifin Alim,
Da gani har yanzu yana sonki sai yanzu muka gane dalilin da yake barka kuka,
Zamu tayaki da addua Allah ya bayyana gaskiya,Haladu yace Insha'allah zai dawo da kansa
wajenki ki raini cikinki Allah raba lfy,Umma tace shi yasa kike ta kuka haka,gwaggo tace Allah
ya shige gaba,sauran matan sukace Ameen,Amana sai hawayene ke sintiri a fuskarta,ana ta
mata Nasiha,Badriyya tace wlh ko Saude ko Mum ne zasu kala miki wannan sharri na sani
Allah zai saka miki.
Alim kuwa kwana yakeyi ba barci saboda tunanin Amanarsa tsananin sonta,da abinda kuma
ya gani wai kwarto fasiki Amana taci Amanarsa,shima yayi kuka yayi bakin ciki yana wani Hali
ya rasa inda zaisa kansa,shike nan cikin zazzabi,baya cin abinci,duk ya rame sosai,kamar yau
yana kwance a gidansa domin tunda ya dawo gida bai taba ko kwana a gidansu wajen Mum
ba,yauma kwance yake zaman bed zazzabi ya rufeshi a hankali ya furta I missed u me yasa
zaki zalunceni,bayan ina sonki zaki ha'inceni?why Amana.haka yayi ta sambatu,
Mum tayi farin cikin ganin Alim dinta gashi ya dawo shi kadai ba tare da tsinanniya Amana ba.
cewar Mum
Abba da su Nura sun tambayi Alim ina matarsa sai yace ya dan barta a gidansu ta huta Sabo
da rasuwar Babansu zai dinga zuwa can yana da gida a garin nasu a ciki ya sata.
Aabid kuwa yana gidan Nura sunyiwa Mum wayo sun daukeshi.
Amana ta gargadi Badriyya kar ta fadawa Huzaifa komai tsakaninta da mijinta.
Kwana biyu laulayi Amana ta fara sosai zazzabi,kwadayi ga yawan sha'awa da takeji kuma
sha'awa r Alim kadai take ji,s ai ciye ciye kullum na kwadayi yan uwanta Maza da mata su suke
kula da ita sosai,kafin tace tana son abu sunyi mata,sai abinda take so suke kawo mata,kowa
lallabata yakeyi dan hankalinta ya kwanta,ta rame sosai sai fari data kara kwal kwal da ita, Yanzu bata da matsalar komai sai ta rashin Alim,sha'awarsa,sai nauyin da Abba ya dora
mata har yau bata sauke ko daya ba,
Sati Uku da rasuwar Baba sai kuma wata sabuwa Umman Amanace ta bijiro da wata tsiya
rigima sabuwa fil ta baro.
AsmaBaffa
Readers a dinga Afwa idan anga mistake,ba lallai Allah ya hada komai abinda kake so ba,idan
kunga abinda bai muku ba kuyi hakuri story a haka yazo,kuma ku dinga nutsuwa a ko wanne
acting da akayi a wannan novel ko wanne page akwai sakon dayake isarwa a dinga gane
abinda ake rubutawa ana masa kyakyawar fahimta ta gaske.na gode kwarai ✳CIRANIN AMANA✳
155-160
Official
By
AsmaBaffa
ANTY SUMEE INA GAISUWA WANNAN PAGE NAKINE.MARAICIN SO FANS INA GODIYA
KWARAI.
Umman Amana ta tsiro da wata tsiya Inda kwata kwata take ta jin haushin Amana saboda
taga yanzu bata da kudi,bata Auren me kudi komai sai dai su Hamza suyi mata,yan kudin da
take dasu duk ta karar dasu a gidan tana yo musu cefane idan mazan basa gida gashi ta biya
sauran yara kudin makaranta,gashi mutane da yawa sunzo wai suna bin Sulemanu Harka kudi
kafin ya mutu ya ranta,sabo da haka kudin bashin da ake bin Mamaci dubu dari tara akayi
lissafi,
Gashi sauran mazan gaba daya sana'arsu batayi karfi ba ga kula da gida,
Gashi wanda sukayi aure ma ko wacce rurowa sukeyi a gidan ake tallafa musu,ga yara
masu tasowa cincirundo,shawara suka hadu iya manyan gidan babu kudin da za a biya Bashin
mamaci kuma ya zama dole,Amanace ta bada takaddun gidan da suka zauna da Alim aka siyar
dashi aka biya bashi, Sauran canji akayi bukatun gida,bayan kwana biyar wani yazo yace shima yana bin bashin
dubu dari biyu Amana ta bada sarkar Gold dinta har guda Hudu da Alim ya siya mata nan ma
aka siyar aka biya,bayan sati biyu wasu suka kara zuwa wannan yace dubu hamsin,wani ashirin
wani talatin,haka mutane suka dinga zuwa su Hamza suka nemo sukayi karo karo aka gama
biyan bashin Baba kaf,kowa na gidan a gida tattalin arzikinsa yayi kasa basu da wani
karfi,gwara ma su Hamza ba laifi,dole suka jinginar da maganar aurensu.
Kullum Umman Amana haushin Amana takeji wai ta kwashe kudinta ta biya bashin Baba ita
kadai arzikinta duk ya kare ita bata bata ko kwandala ba,kuma Amana yanzu da su Hamza take
shawara har meeting sukeyi,
Amana ga halin da take ciki ga kuma Umma kullum cikin hantararta da zaginta takeyi tana
jifanta da muggan kalamai,idan readers baku manta ba Umman Amana ko koko safe a da bata
bawa Amana sai dai ta siya,ganin Amana Allah ya buda mata ta samu kudi tana auren me kudi
shine Umma ta sakko take kula da Amana,yanzu Amana Babu ba mutunci,dama ita Umma me
bata shine nata,idan kana bata to a cikin yayanta kiri kiri zata dinga nuna banbanci.
Yauma gaba daya family na mirgayi Sulemanu sun Hallara a babban palo ana
shawara,banda iyaye a meeting din,
Amana zaune take a tsakiyar Palo ta darararrashe ta sangale kafafu zaman masu ciki sosai ta
rame idan kunga Amana za ku sha mamaki ta rame sosai,kana ganinta sai ka tausaya mata
Sabo da Amana kullum sai tayi Kukan rashin Alim tayi addua tayi ba dare ba rana,
Da addua aka bude taro Hamza yace da Amana sayyada a cika mana da addua kinfi kowa
Ilmi,ai kuwa akayi addua sannan aka kawo littafin wasiyyar Baba daya bari na gadon kowa
gwara a bawa kowa hakkinsa dama Umman Amanace tace wlh sai an dakko an raba gado
domin duk anyi tunanin Sulemanu ya tara dukiya ne a boye shi yasa har yayi littafi guda ya raba
gardamar gado,
Page din farko na littafin aka bude ga abinda aka gani da Babban baki ya sa wani abokinsa ya
rubuta masa domin Harka baiyi boko ba Badriyya ce me karantawa.ga abinda ke rubuce.
AMANATA INA KAUNARKI,Amana na jin an karanta haka ta fashe da Kukan tuna Baba,NI
SULEMANU HARKA BABAN AMANA NA BAWA A CIKIN DUKIYATA DA ALLAH YA MALLAKA
MIN NA BAWA AMANA SANIYATA WACCE NAKE KIWATAWA A GIDAN ABOKINA ME
GARI,SANIYAR BATA HAIHUWA ITA KADAI CE ABINDA NAFI SO A CIKIN DUKIYATA,SABO
DA HAKA SANIYA TA AMANACE KAR TA SIYAR DA ITA TA YANKA TA IDAN ALLAH YA BATA
HAIHUWA TA DAGARGAJI DADINTA.dariya kowa yayi harda Amana me kuka, Page 2. HAMZA NA BAKA TINKIYATA DA RAGO KA YANKAWA AMARYARKA RANAR
BABBAR SALLAH ASHA DABGE,hhhhhh nan ma aka dau shewa da tafi tare da cewa Allah yaji
kan Baba.
Page 3. KABIRU KB DAMIN GERO SHIDDA KA SIYAR KA KASHE KUDIN,
ISA KUMA WAYATA TA CELLULA DA AMANA TA SAI MIN,
HALADU KUWA BUHUM MASARA BIYAR,
BADRIYYA TOLO TOLO GUDA UKU,
SAKINA BARGONSA NA BACCI DA RADIO DA YAKE JIN LABARAI,DUK SUNA GIDAN
ABOKINA ME GARI IDAN BAI BAKU BA KU SHIGAR DA KARA.
MATAN AURE KUWA KO WACCE A BATA RIGARSA DA WANDONSA DAYA DAYA,
SAURAN YARAN GIDAN KUWA KAI KUNCI UWAKU GABA DAYA GA SU AMANA NAN DUK
ZASU KULA DAKU KAR KUCE BAN BAKU KOMAI BA CIKIN KAYAN SAWATA KUMA A RABA
MUKU DAYA DAYA KOMA ME ZAKUYI DASU KUYI.
second to the last page kuwa na matansa ne,
KO WACCE CIKIN MATANA NA BATA KYAUTAR IYA DAKIN DA TAKE CIKI TA ZAUNA HAR
IYA RAYUWARTA,SAURAN GIDAN KUMA KAR WANDA YA SIYAR GABA DAYA NA YAYA
NANE,WACCE TAGA ZATAYI AURE TO BA BATUN SIYAR DA DAKI DOLE SAI DAI CIKIN
YAYAN WATA KO WANI YA SIYA
LAST PAGE KUWA FATAN ALKHAIRI DA ADDUA YA ZAZZAGAWA IYALINSA,
Gaba dayansu sai da sukayi