Showing 33001 words to 36000 words out of 117506 words

Chapter 12 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8456

"lafiya, don Allah aiki nake nema ko da baku da mai muku
shara ko wanke wanke ko kuma girki ki taimaka don Allah"...............
Matsa mata matan tayi tare da cewa "bismillah" shiga tayi a d'arare ta samu kasan carpet ta
zauna matar ta karasa ciki na mintuna kan ta fito da tire madaidaici a hannunta ta ajiye gaban
khairin tana sakar mata murmushi tace "bismillah ci abinci kiyi sallah se muyi magana" d'an
shiru khairi tayi tana tunani seda matar tace "ni musulma ce er uwarki wallahi bazan cuce ki ba"
tukun khairi ta fara ci....................

Bata wani ci sossai ba ta ajiye matar ta nuna mata bayi dake parlorn taje tayi alwala a parlon
tayi sallah tana idarwa matar tace "baiwar Allah kiyi hakuri kinji? Na san kina bukatar aikin nan
hakan yasa bazan iya ce miki babu kai tsaye ba, ni ni kad'aice se mijina ni nake komai nawa
bana bukatar me aiki kiyi hakuri ga wannan ki hau machine" ta bata five hundred a ladabce
khairi ta kar'ba tana yabon kirkin matar har ranta taji daadi ba wadda yayi mata irin wannan
karamcin, kin kar'ban kud'in tayi da kyar matar ta sata ta kar'ba kan ta fice....................

Haka tayi ta bi gida gida amma bata samu ba wulakanci kuwa ba irin wadda bata gani ba har ta
yardar wa kanta matar Chan ne kawai me karamci a gabad'aya estate d'in, se yamma likis
sannan khairi ta shige gidan karshe shi kam irin me fence d'in nan ne tana tura karamin get d'in
kare ya biyota a 360 ta fito se kuma tayi wawancin barin kofan a bud'e kare kam ya fito dama ta
wuce wasu biyu a gefen bolan gidan a take suka rufa mata baya................

Khairi tayi gudun da bata ta'ba yin irinshi ba a rayuwanta bata dena gudu ba har seda taga ta
fita daga get d'in estate din tukun ta tsaya haki a lokaci d'aya ta fashe da kuka, ita ba gudun
bane ya sata kuka se wasu matasa dake zazzaune saman mota a kofar gidan matan nan me
mutunci su uku suka fara fashewa da dariya kan d'aya daga cikinsu dake danna waya ya d'ago
duk da be fashe da dariya ba amma tana juyowa don kallon karnukan suka had'a ido inda ya
sake wani shu'umin murmushi da ya fi kona ranta akan dariyan da sauran suke harda rike
ciki..................

Seda tayi kukanta ta koshi tukun ta fara tafiya don ganin magrib ya gabato, harara ta bankawa
securities din dake gadin gate din kan ta wuce, se kace su suka kar zomon��踫�� bata wani jima ba
ta samu napep ta hau ta wuce haki kam har lokacin bata dena ba, ga kishi ga ko sallan la'asar
bata yi ba...................
*******

Zaune ta ke a bakin gadon d'akin tana kallon wata kyakyawar mata da zasuyi sa'anni chocolate
color ce daga ganinta er gayu ce kaman momman fatar ta kad'ai In ka kalla ka san kud'i sun

zauna, less d'in jikinta kawai abun kallo ne bare gwalagawaln da suka fi komai d'auke hankali
akanta, "ban san yadda zanyi da musharraf ba hajiya rukayyah rashin auren shi na mugun
damu na".................

Wacce aka kira da hajiya rukayyah tace "hajiya Fatima ban ga ta yadda rashin auren yaron nan
ze d'aga miki hankali ba, tunda ba neman mata yakeyi ba hasali ma Ko kallo mace bata ishe shi
ba ko kin manta aure lokaci ne? Idan lokacin yin na biyun yayi ba se kin mishi magana ba,
sannan idan kika mishi na dolen ma kina da tabbacin xe riqe? Baze rike ba sbd be so, wacce
yake son ma kinga abinda ya faru".................

Cikin nazari momma tace "na san In har na mishi auren ze riqe amma har yanzu ban samu
macen da ta kwanta min da shi ba amma Ina ci gaba da dubawa In har na samu dole in mishi
don sam hankali na be kwantawa da ganinshi hakan wlh" ajiyar zuciya hajiya rukayyah ta sauke
tukun tace "Toh Allah ya za'ba mana abinda ya fi alkhairi" momma tace "Ameen"................
Hirarrakinsu suka ci gaba dayi na kawaye har suka gangaro kan auren da me aikin su momma
zatayi inda take fad'a mata tana neman wata ma bata san ko zata samu nan kusa ba. Suna
cikin hiran aka kira sallahn la'asar suka mike suka gabatar kan momma ta fara shirin tafiya
dama tun 12 ta zo, har wurin mota hajiya rukayyah ta rakata inda sukayi sallama driver ya ja
mota suka fice Ina ta aikin mamakin yawan securities na gidan..................

*****

Ana kiran magrib tana sallama a kofan gidan da gudu nabeel ya zo ya rungumeta cikin
muryarshi ta yaranta yace "Adda hato a dilli a acci amin nabeela wuli ha jungo tun nane o d'o
woka"(Adda Ina kika tafi kika barmu gashi nabeela ta kone tun d'azu take ta kuka)................

zaro ido khairi tayi tare da kama hannunshi cikin sauri suka karasa ciki Ai kuwa kuka ta samu
nabeela nayi rike da hannunta dada na mata fifita...................

Karasawa gabanta tayi ta rike hannunta hawaye na cika idonta tace "garin yaya nabeela?"
Dada tace "wai fa cewa nayi ta hura wuta ta d'aura mana d'umamen nan ban san yadda akayi
ba naji suna musu da nabeel akan yadda ake sa itace bayan wutan ya ruru kan nayi magana
naji ihun nabeelan nan ma ya sa'be don Maman hamdeeya ta sa mata kamu a wurin"...............
Juyawa khairi tayi tana kallon nabeel tace "kona er uwarka kayi?" Zaro ido yayi yana girgiza kai
wani hawayen na zuba mishi don haka suke in d'aya na kuka to fa dole d'ayan ma ze yi kuka
"A'a Adda kawai na sa hannu Ina kokarin gyara mata itacen se kawai tayi saurin fisgewa shine
bata sani ba ya d'alli hannunta d'ayan" had'e rai khairi tayi tace "me ya kai ka bakin murhun tun
farko, ko yari ma jaulero mivi?"(me ya kai ka kitchen din nace).................

Cikin muryan tausayi yace "wad'u munyal Adda mi metata nastugo"(kiyi hakuri Adda bazan kara
shiga ba) khairi tace "good" tana mikewa tace "Dada ha mi jula mi yaramo chemist"( bari inyi

sallah In kaita chemists) da Toh Dada ta amsa. Seda sukayi sallah tukun khairi ta kama hannun
nabeelan suka fice inda suka bar dada da nabeel.............

Magani aka shafamata a wurin suka kuma bata na sha don ta konu ba laifi,�� suna hanyar
dawowa khairi ta tsaya ta saya musu taliya leda d'aya suna da d'an kayan miya se ta tafasa
musu, suna shiga kuwa himar kawai ta cire ta nufi kitchen in less than 40mins ta gama musu
jollof na taliya seda sukayi sallahn isha tukun suka ci anan dada ke tambayarta ya aikinfa an
samu? Da a'a kawai khairi ta amsa sam bata fad'a mata komai akan tafiyanta ba.....................

Da kyar ta samu ta taimakawa su nabeel da wajibul manzeel d'insu (assignment) tsabar gajiya
da bacci suna ganawa, tayi alwala ta shiga ta kwanta, sede me!!! tana rufe ido fuskanshi ya
fad'o mata yana wannan shu'umin murmushin da sauri ta bud'e ido tana ambaton sunan Allah,
lokaci d'aya ta ajiye a ranta don haushin da ya bata ne yasa fuskanshi ke dawo mata amma
tana mamakin irin kyaun da Allah ya zuba mishi juye juye tayi tayi da kyar ta samu baccin ya
d'auketa.................










#share
#vote
#comment






'Yar mutan Adamawa


��潤����潤����潤����潤����潤��

�� �� �� �� �� ���� IGIYAR RAYUWA��踫葉







�� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� ��潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

�� �� �� ���� 'Yar mutan Adamawa

Page��∴��3儭����4儭������塚��3儭����5儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Yau kwana biyu kenan khairi na fita tana aikin neman aikatau amma bata samu ba wulakanci
kam ba wadda bata gani ba amma da yake ta sawa zuciyarta neman aikin ya zama wajibi a
kanta hakan be dameta ba, babban damuwanta ma kayan abincinsu da suke barazanar karewa
don be wuce ya musu kwana biyu ba.................
Tare da su nabeel suke fita ta ajiyesu islamiyya ta wuce kasancewar basu shiga boko ba ta roka
su dinga zuwa da safe ma ko ran makaranta ne kan su shiga bokon dayake yara ne masu shiga
rai har sun saba da islamiyyar kamar sun shekara cikinta, hannun nabeela ya sabe sossai sede
be warke ba, daga randa nabeela ta kone kullum kan ta fita se tayi musu abincin rana take fita,
tana kuma iyakar kokarinta don ganin batayi magrib a waje ba....................

Yau ma kaman kullum bayan ta gama shiri tayiwa dada sallama suka fito hannunta rike da su
nabeel se da suka shiga gidan Maman hamdeeya fishaa kan suka fito suka wuce kasancewar
kwana d'aya kenan basu had'u ba, bayan ta ajiye su nabeel ta tari napep ta shige kud'in
hannunta saura 300 duk ranta a jagule tana tunanin In bata samu aiki yau ba bata san da wani
kud'in zata fita gobe ba, amma bata cire rai ba Allah na nan...............

Cikin mintuna kad'an suka isa low cost cikin d'ari d'ari ta sauka sbd duk cikin unguwannin da
take zuwa ba wadda gidajen suka tsoratata kaman waennan ga ko wanni gida da securities,
wani gate ta fara knocking gateman din ya fito sanye da uniform yake tambayarta lafiya? Tace
"don Allah matar gidan nake son gani" ta san in tace zata dinga fad'awa gate-mans abinda yake
tafe da ita zasu dinga mata bukulu ne..................

Kallon sama da kasa ya mata kan ya bata hanya ta shige duk da ya san madam dinshi bata
harka da talaka aiko khairi na shiga tana fad'an abinda ya kawo ta matar ta mata korar kare ta
had'a harda gateman d'in ta zage tas, a tsorace khairi ta shiga gida na biyu nan ma wulakanci
aka mata haka ta dinga yawo duk gidan da ta shiga koranta ake, wasu kam ma har cewa suke
ko an aiko ta spying ne, wasu harda barazanar rufe ta a police station sukeyi.......................

A haka har akayi azahar ta samu panpom gefen wani gida tayi alwala tare da komawa gefe ta
shimfid'a d'ankwalinta dukda bata san gabas anan ba amma haka tayi sallanta, bayan ta idar ta
jima sossai zaune a wurin duk damuwanta na kan rashin samun aikin nan ga kud'in hannunta
sun kare ga kayan abincinsu na hanyan karewa, babban damuwanta school tana mugun son su
koma makaranta ko shedan gama secondary d'inta ta samu...............

Bayan ta gama sake sakenta ta mike ta ci gaba da tafiya a sad'ad'e har ta samu wani shop
sadakarwa tayi ta karasa ta sayi pure bliss da pure water d'aya ta samu wuri ta zauna taci ta
sha ruwan kan ta ci gaba da roaming har gab magriba la'asar ma a wani gindin bishiya tayi,
ganin magrib ya gabato yasa ta fara neman napep don komawa gida amma ko d'aya bata gani
ba ga hadari da ya had'u lokaci d'aya...................

A mugun tsorace take kalle kalle ko gilmawan mutum d'aya babu securities da suke kofan
gidaje dayawa ma babu duk sun koma daga ciki tafiya ta fara sauri sauri tana aduar Allah ya sa
ta samu ko machine ne, duk hankalinta ya tashi akwai wani gidan da ta wuce d'azu da ko
marmarin shiganshi batayi ba sbd yawan securities din da ta gani kofan gidan akwai kaman
rumfah haka wurin taje ta tsaya amma ko minti biyu batayi da tsayuwa ba wani katon security
ya fito ya koreta..............

Hawaye ta fara ganin iskan ruwa ya taso gadan gadan kana ji ma ruwan na zuwa, ci gaba da
sauri tayi batayi aune ba taji an 'barke da ruwa kam kaman da bakin kwarya ci gaba da tafiya a
haka tayi ruwan na dukanta, daga nesa Chan ta hangi wasu matasa su kusan biyar suna zuwa
zuban ruwan be damesu ba sam se ma wani irin tafiya da sukeyi na kasaita da ji da kud'i dukda
In ka zuba musu ido ka lura sossai zaka san a buge suke................

Ci gaba da tafiya khairi tayi kanta a kasa har ta iso kusa da su batayi aune ba taji an chabke
hannunta a razane take kallon wadda ya riketan zagayeta sukayi suna sheka dariya d'ayan
yace "are yhu seeing this chick komai yaji yau akwai morewa" kokarin fisge hannunta takeyi
amma ba rikon wasa ya mata ba a take suka cire mata khimar suka yasar kokuwa suka fara da
su amma Ina sun mata yawa kuma aka ce sarkin yawa sun fi sarkin karfi......................

********

"Ni wallahi sam ban so zuwa dukkun nan ba, duk momma ta bi ta matsamin da en uwan
mutumin nan" inji fad'ar musharraf kenan yayinda yake driving da motar momma kwanansu biyu
dukku wadda momma ce ta sashi dole zuwa duk rabin en uwanta a achan suke kuma en

uwantan de sune en uwan mahaifinshi don cousins suke, harara haidar ya sake mishi inda
yace.................

"Ko min lalacewan masa de tafi kashin shanu" "mtseww could yhu imagine ni da bana karya ba
na son me yinta amma ni ne da karya a office yau Tuesday amma ban koma ba, na fake da
wani wai banda lafiya" shiru haidar yayi yana kallon hanya kallonshi musharraf yayi na seconds
tukun ya juya kan tukinshi a fili yayi kwafa yana cewa "In miskilanci ne kaima ka san na dame
ka na shanye don ma kaine yasa nake maganan".................

Cikin dariya haidar yace "toh musharraf me kake so in ce maka? Na riga da na saba jin wannan
mitan a duk sadda na raka ka dukku har muje mu dawo kana mita abinda ban sanka da shi ba"
Shiru musharraf ya mishi nan haidar ya dinga magana amma ko ci kanka musharraf ya ki cewa,
ganin musharraf d'in ya d'auki hanyar GRA yasa haidar cewa "Kai gidanmu fah zaka kaini In
d'auki matata don nayi kewarta".................

Harara musharraf ya sake mishi inda ya juya ya nufi Low cost ba tare da ya ce komai ba, a
hankali yake tafiya kaman bayaso sabida karfin ruwan saman dake zuba yana covering view
d'inshi hakan ya sa ya kure hasken lights d'in motar yana shawo kwanan street d'in su haidar
hasken motarshi ya sauka akan shape d'in jikinta doguwar rigan material dake jikinta fitted one
ne hakan ya sa da suka yaga saman rigan be zame ba, runtse idonshi yayi a lokaci d'aya ya
bud'e akan black bra d'in dake jikinta ya kamata har tudun breast dinta ana iya gani daga
nesa.................

Kallon haidar yayi yaga hankalinshi na kan waya be ma san me ke faruwa ba, takaicin matasan
ne ya kamashi me yasa ga mata karuwai dayawa a gari se wacce bata sayar da kanta ba?
Rage hasken motan yayi kan yayi kansu da mugun speed da yasa haidar d'agowa hakan yasa
ya gane me akeyi, su kuma ganin motar tayo kansu yasa suka arci ta kare ita kuma ta du'ka a
wurin tana boye fuskanta a tsakankanin cinyoyinta..................

Wani wawan birki musharraf ya ja a gabanta tare da juya kan motan cikin hanzari shi da haidar
suka sauka sukayi kan yaran wani irin duka suka fara musu da ya bani tsoro don daga ganin
yaran ba su da wani karfi ajeboters ne, duka sossai suka musu kan suka samu suka tsere,
musharraf ya koma mota da sauri yana rawar d'ari don baya shiga ruwa sbd In ya shiga se yayi
zazza'bi me zafi da mura kaman baze yi rai ba............

Heater din motar ya kunna yana kau da kai daga kan yarinyar, haidar ne ya karasa kusa da ita
ya janyo hijab d'inta dake gefe cikin tausayinta yace "baiwar Allah" kuka takeyi sossai inda
jikinta kuma ke tsananin rawa a hankali ta d'ago don ganin waenda suka taimake ta duk da
ruwa ake hakan be hana haske tarwal a unguwan ba kasancewar ko wanni gida sun kunna
kwayayen fitillunsu, had'a ido sukayi da haidar hannunshi rike da hijab d'inta yana mika
mata...................

Kar'ba tayi har yanzu jikinta be bar rawa ba a kuma rud'e take, sa khimar din tayi dukda

wuyanshi ya yage sossai haka ta sa tana chukuikuye shi a kirjinta hannunta ya kama shi ko
damuwa da ruwan be yi ba shi da yake watanni cikinshi ta Ina ze damu, a hankali ta mike ta
bishi don haka kawai taji a jikinta she's safe with them ba abinda ze same ta................

Bayan motar ya bud'e mata ta shiga, ta zauna wani kamshi da dumi da ya buge ta ya sata
sauke ajiyar zuciya motar ya d'auki dumi sossai ita bata ta'ba shiga mota me fidda sanyi bama
balle zafi, d'aga ido tayi don kallon d'ayan se suka had'a ido ta mirror wani d'an banzan hararan
da ya buga mata yasa tayi saurin kau da kanta zuciyarta na bugawa................
Tabbas shine toh me ya kawoshi nan bayan a chan estate ta kalleshi, kau da zancen tayi ta
koma tunanin wani hali dada zata shiga In taga har yanzu bata dawo ba ga ruwa anayi
tunaninta da kukanta ya yanke ne sadda taji me murmushin iskanci da ta sawa suna da haka
wato musharraf na cewa "what are yhu doing? Where are yhu taking her to after the
help"................

Haidar yace "haba musharraf are we leaving her at this rain and that street after all that
happened to her? I'm taking her to Maami she will know what to do with her" su duk a zatonsu
batayi makaranta ba ganin shigan jikinta suna ganin ko tayi ma to irin government dinnan da
basa aikata aikin Chas a boko..............

A zuciyarta take magana "Lallai wato sunanshi musharraf kuma be da kirki be da tausayi,
tsurewa tayi ganin sun nufi gida me rumfa da aka koreta a cikinshi duk da taji yace ze kaita
wurin Maami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login