Showing 57001 words to 60000 words out of 117506 words

Chapter 20 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8457


gama mamaye fuskanshi ba iyakacinta gefen baki wadda yasa dimple d'inshi na dama lotsawa,
a matukar kunyace ta zame ta zauna akan plastic chair tana boye fuskanta da hijabin jikinta,
wayancewa yayi ya wani basar kaman ba shi ba tare da fara cin abincinshi.....................








#vote
#share
#comment








'Yar mutan Adamawa

��潤����潤����潤����潤����潤��

IGIYAR RAYUWA��踫葉






��潤����潤����潤����潤����潤��

Story and written by: fateemah Muhammad gurin

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

Page��∴��5儭����5儭������塚��5儭����6儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Da kyar khairi ta sake bayan wasu lokuta amma ta kasa cin abinci sbd wani fitinanniyar
kunyarshi da take ji abinka da fulani, shi kam ko a jikinshi se ma yawan satan kallonta da yake,
da ya gaji ma kwanciya yayi abinshi yana facing inda take zaune tare da lumshe ido, a jikinta
take jin ana kallonta amma ta rasa waye ne ta kalleshi yafi sau abinda yafi se taga idonshi a
lumshe....................

Tana cikin sake saken yadda zata tambayi momma labarin rayuwanta da kuma kaddaran
musharraf taji an turo kofan, murmushi me kyau ta saki tana mikewa tace "sannu da zuwa
mamie" mamien haidar ce tazo tana matukar ganin daraja da girman matan, mamie ma na
murmushi tace "yauwa sannu ummulkhairi" gaisawa sukayi cikin mutumci, su Amrah ma suka
gaisheta ta amsa musu tana tambayansu school, kusa da momma taje ta zauna suka fara irin
gaisuwarsu ta kawaye..................

Nuri ce ta shigo da sallama ganin mamie yasa ta duka har kasa ta gaida ta, amsawa tayi fuska
d'auke da fara'a tace "ya service?" Nuri tace "Alhamdulillah mamie mun kusa kammalawa"
mamie tace "toh Allah ya bada sa'a daughter" tace "Ameen" tana kallon momma tace "momma
inaga ni kam zan koma gida" momma tace "Ohk ku tafi da khairi ma sbd abincin dare" khairi na
mikewa tace "toh momma, se kun dawo Allah ya kara sauki" momma tace "Ameen" sallama
tayiwa mamie.....................

Suka fice tana satan kallon gadon har lokacin idonshi a lumshe yake, bayan nuri ta bi tana mishi
adu'ar samun lafiya, yinin ranan gabad'aya haka tayishi cikin wani yanayi da bata san na
menene ba, a chan asibiti kuma bayan fitansu khairi momma ta mike tana cewa hajiya ruqayya

"zo muyi wani magana" mikewa hajjiya ruqayyah tayi ta bita..............

Mota suka je bayan sun zauna hajjiya ruqayyah tace "menene aminiya da baza ki bari mu koma
gida ba?" Momma tace "hmm Ina so inga komai ya tafi yadda nake so ne ruqayyah, matsalolin
musharraf kara yawa suke bazan ta'ba iya barinshi ya kara wattani uku zuwa hud'u nan gaba ba
mata ba sbd lafiyanshi" hajjiya ruqayyah tace "me ya faru?" Nan momma ta bata labarin duk
abinda doctor ya fad'a, seda ta sauke ajiyar zuciya tukun tace "Ina mishi sha'awar auren
ummulkhairi"........................

Waro ido hajja tayi tace "'yar aikin da na turamiki?" Momma tace "ita fa ko kina ga tana da wani
aibu?" Hajjiya ruqayyah tace "a'a sam se hankali da tarbiyya da na lura tana da shi kawai de
gani nake kaman musharraf be so mace me wayewa ba taya za'a yi yaso wadda ko primary
bata dashi, dukda tana kyau da diri kam".................
Murmushi momma tayi tana tuna abinda ta gani d'azu tace "ze so ta ne, tana da hankalin da
nake tunani ita ce kad'ai zata iya fiddashi daga halin da yake ciki gabad'aya, sannan tayi karatu
zuwa ss2 In kinji turancinta ma zaki rantse private school tayi" hajjiya ruqayyah zatayi magana
kenan momma ta fara bata labarin khairi tun daga na iyayenta har ita kanta, wlh se da hajjiya
ruqayyah tayi hawaye.................

Cikin tausayawa tace "khaih duniya!! Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode da ni'imarka
garemu" don wallahi labarin khairi imani ya kara mata, cikin tausayawa tace "ai ko na sami 'ya
aminiya, na d'aukewa mahaifiyarta nauyin duk abinda uwa zatayiwa erta a bukin, sannan me ze
hana In an tashi biyawa Amrah kud'in waec da zatayi nan da two weeks musharraf ya biyamata,
don kin san yanzu karatu shine gatan kowa a duniyan nan"..................

Momma na murmushi tace "mun kuwa gode kuma zan fad'a mata, eh nima nayi tunanin haka In
yaso bayan auren ta ci gaba da karatunta ko a wajen aikinshi ne, sannan Ina tunani su dawo
gida gabad'ayansu mu zauna tare a matsayin en uwa" hajjiya ruqayyah tace "masha Allah,
Allah ya tabbatar da alkhairi, ya batun Nuriyyah kuma?" Momma tace "dazu mukayi maganan
da su yaya Nasir yace yana so asa bukin kawai nan da wata biyu tunda next month zatayi
passing out, kinga se a had'a da nasu khairin don zuwa lokacin itama ta gama WAEC
d'in"..................

Sun kara tattaunawa kad'an kan suka fito jin har an shiga sallan la'asar d'akin suka koma hajja
ruqayyah tayiwa musharraf sannu da jiki tana zolayanshi wato sai abokinshi na nan yake zuwa
gidan ta ko, murmushi kawai yayi bata jira tayi sallan la'asar ba ta wuce...............

Washegari

Da safe ya matsa aka sallameshi suka tattaro suka dawo gida, direct site dinshi ya nufa yayi
wanka da ruwan d'umi yana jin daadin jikinshi, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya
nufi parlorn momma don Allah ya gani yanzu be son kad'aicewa sbd tunanin dake cika mishi

zuciya da kwakwalwa and he hate that..................

A parlor ya kwanta abinshi don ba kowa kasa, yana nan kwance yaji ana gudu a hankali ya
d'aga kai se yaga little ce da wasu kyawawan yara guda biyu mace da miji masu tsananin kama
da juna ga kyau da Allah ya zuba musu daga ganinsu kuma ya ba zuciyarshi kannen yarinyar
nan ne don kamansu, wurinshi sukayo da gudu little ta fad'a jikinshi yayin da su kuma suka jaaa
birki...........

Murmushi ya musu a tare sukace "Ina kwana uncle?" Baki little ta turo tace "he's not uncle he is
paapi, paapi ga nabeel da nabeela cuties siblings" mikewa yayi zaune yana saukar da little kasa
yace "morning twins, ya Dada?" Sukace a tare "tana lafiya, she said we should behave kuma
mu gaisheku, and we thank yhu for everything" murmushi musharraf yayi yace "duka mu
kad'ai?" Nabeel yace "yes paapi"................

Murmushi ya kumayi yana d'aukan nabeela sama yace "lets go" little ta fara diddira kafa tana
turo baki tace "paapiii" Da sauri yace "shhhhhhh, oya wuce muje yawo" tsalle ta fara cikin jin
daad'i ta bi shi don har ya riga yayi gaba rike da hannun nabeel, mota ya d'auka suka fice daga
gidan..................
Da misalin karfe goma sha d'aya na Safe momma ta sauko kasa zuwa d'akin Khairi a bakin
gado ta same ta zaune da sauri khairi ta zame kasa, tace "sannu da fitowa momma" momma
tace "yauwa khairi kin gama aikinki kenan?" Khairi tace "Eh na gama momma" momma tace
"Toh khairi bari na baki labarin rayuwarmu inda zaki ji daad'in yanke shawaran da ranki ke so,
ba zan miki dole ba khairi don wallahi kaman 'ya na d'aukeki, Ina so in na gama baki labarinnan
ki yanke hukunci zuwa gobe.....................

Sbd Ina son musharraf yayi aure as soon as possible, kin de ji abinda likita yace a asibiti" Kai
khairi ta d'aga momma zata fara bata labari daga asalin tushensu khairi tace "Amrah ta fad'amin
a yayin da take min bayanin waenda na gani a d'akin asibiti jiya" momma tace "Ohk bari na fara
baki daga auren da aka yi min, Tunda aka kaini gidan mijina dake Abuja en uwa ko wa ya koma
muhallinshi a lokacin na gama NCE d'ina, dama tun kafin auren mamaji ya sa hamma
mahmoud d'in samamin aikin koyarwa a wani secondary school.........................

Na yi good two weeks ban sa hamma mahmoud a idona ba, sam ban wani damu ba damuwa
na d'aya zaman kad'aicin da nakeyi duk girman gidan ba kowa se ni kad'ai a part d'ina, daga
waje kuma daga mai bawa flowers ruwa, drivers, se gateman, tunda na shiga gidan ko kofan
part d'ina ban fito ba................
Abun ya isheni hakan yasa kawai na shirya a wata ranar Monday na fito dayake ina da Lettern
makarantan a hannuna hakan yasa na san sunan makarantan Ina fita driver ya zo da gudu ya
tambayeni Ina zan je na fad'a mishi sunan makarantan aiko be yi kasa a gwiwa ba ya d'aukeni
se makarantan nayi reporting...................

Na fara aiki da kwana biyu ina zaune a parlor naji an banko kofa an shigo da sauri na mike Ina
kallonshi ban hankara ba naji saukan mari hagu da dama a tsorace nake kallonshi yayinda shi
kuma cikin zafi yace "Ke!! Ballagaza, wa ya baki izinin fita aiki? In ba jahilci da rashin tarbiyya
ba taya za'a yi ki fara zuwa aiki ba tare da izini na ba" a tsorace nace "kayi hakuri zaman shirun
ne ya isheni shi yasa nayi tunanin fara aikin kuma naga kai ka ne......" "dakata, ban miki
gargad'in aurena ba Kika nace? Wato kinga mai kud'i shine zaki makale mai ko? Toh bari kiji In
fad'a miki kin shigo kabarinki ne wai har kina da bakin ce mini zaman kad'aici ya
isheki."..................

Shiru nayi kaina a kasa, kafa yasa ya shure ni har seda na kai kasa, nyau ya tofa min kan ya
juya ya fice ajiyar zuciya na sauke, hawaye na silalo min kuka nayi sossai na share hawayena,
ba yabon kai ba amma Allah yayi ni me tsananin hakuri da juriya ga zurfin ciki hakan yasa ba
wadda na fad'awa kuma ba wadda nake da niyan fad'awa, bayan kwana biyu dadda(Aslamiyya
mahaifiyar Mahmoud) ta kirani bayan mun gaisa take tambayata ya aiki? Ban so fad'a ba sam
amma se ta matsa jin na fara kame kame, kuma kaman uwa take a gareni don diddi
na(mamanmu shuwa) haihuwana kawai tayi.................

Wahalana da reno na duk dadda ce, cikin rashin makama nace "hamma mahmoud ya hanani
Dan Allah dadda ki rokamin mamaji ya roka min shi zaman gidan ba daad'i" dadda tace "hanaki
yayi?" Nace "eh" tace "Toh shikenan se anjima" bata jira cewana ba ta kashe wayan se lokacin
naji na shiga hali na tsoro, karfa dadda tayi mishi abinda ze zo ya min abinda yafi
jiya.....................

Bayan na gama tunanuka na na tashi na shiga kitchen na d'aura ruwan zafi don yin girki, tunda
nazo gidan da d'an sauran kayan miyan da kawayena suka sayo na kafa murhu, nake anfani
Allah ya taimake ni ma a rayuwana na fi son mai da yaji akan komai, kuma dadda babban roba
guda na yaji ta had'ani da shi a cikin gara na, toh a ranan kayan miyan yake karewa d'an wanda
ya sauran nake gyarawa...................

Wani banko kofan da akayi se da na tsorata, a matukar razane nake kallonshi ganinshi da belt a
hannu yana gyarawa kan inyi wani yunkuri ya rufeni da duka na fitan hankali yana yi yana
maganganu a ciki yana cewa "wato had'ani da iyayena kika fara tun ba'a je ko Ina ba ko? Toh
bari inyi miki me tushe yadda zaki ji daad'in kai gulma" yana cikin duka na garin kaucewa
hannuna ya buge tukunyar da na d'aura se jikina Allah yasa be yi zafi sossai ba amma azabar
wurin kad'ai ya isheni musamman hannun da na buge da shi d'in ganin haka yasa ya kyaleni
yana huci yace "for your own information daga yau In kayan gararki suka kare ki nemi abinda
zaki ci wa cikinki, tunda kince se kinyi aiki ko biyar na bazan kara kashe miki ba, wawiya
jaka"..................

A ranan nayi kukan da ban ta'ba irinshi ba a rayuwana duk da haka ban fad'awa kowa ba nayi
jinyar kaina na koma bakin aikina, In takaice miki khairi a haka muka shafe kusan wata biyu
lokacin ni nake zuwa da kaina in sayi kayan abincin da zan ci kuma In biya kud'in mota da kaina
sbd ya hana drivern shi tukani kwata kwata ma ya hana In ta'ba mishi ko mota ne, kullum In zan

fita zuwa makaranta haka zan ganshi da mata kala kala ba randa na ta'ba ganinshi da mace
d'aya hakan yasa nake ta adu'ar Allah ya rabani da shi da gaggawa In kuma shi ne mijina na
har abada toh Allah ya shiryaminshi......................

Wata ranar laraba da har abada bazan manta ba, bayan na gama d'an girki na na dare kad'an
na ci na sha ruwa, tare da shigewa d'aki shap na manta dawowana ban rufe kofan parlorna
yadda na saba ba, na fito wanka d'aure da zani a kirji naga mutum tsaye a bakin kofan
bayangidan yana ta layi a matukar firgice na juya da niyar komawa se ji nayi an riko ni, irin rikon
da akewa 'barawo In takaice miki a ranan mahmoud yayi min mummunar fyad'e azabar da na
sha Allah ne kawai ya sani.....................

Sati nayi ina jinyar kaina har asibiti naje akayimin d'inki da nurses din suka tambayeni fyad'e
aka min se ce musu nayi eh, sossai suka tsinewa wadda yamin hakan ban tanka su ba har suka
gama aikinsu, nan ma seda na kwana da safe na koma gida Ina iyakar kokari na wajen ganin
ba wadda ya fahimci irin zaman auren da nakeyi, a haka a haka rayuwa ya ci gaba da
gurgurawa duk randa ya shawu ya bugu haka ze zo ya farmin kaman dabba se ya tabbatar ko
numfashi bana iyawa kan yake kyaleni In naki bud'e mishi kofa kuwa duk sadda ya kamani se
yamin dukan da ko tashi bazan iya ba.................

A haka na samu cikin musharraf, cikin wannan wahalar rayuwan gashi ko nayi niyyan fad'awa
wani se in kasa, don ma makarantan da nake aiki suna min uzuri sbd tausayamin da suke
kullum fuska na a kumbure idona a tare da jini basu ta'ba tambayana wa yake min hakan ba
sede su tausayamin suyi ta min sannu, cikin musharraf me tsananin wahalarwa ne hakan yasa
na kara ramewa nayi baki kirin, har iska na iya d'auke ni In fad'i, ana cikin haka mukayi hutu
yayi daidai da bukin taheer hakan yasa mamaji cewa dole se munje haka muka tattara muka
nufi gombe bayan uban kashedin da nasha a wurin mahmoud kuma naji don sossai na tsorata
da lamarinshi kwata kwata be da tausayi da imani don da cikin ma haka yake duka na yayi ta
naushin cikin hakan ze barni da azaba, ban ta'ba tsammanin musharraf ze zo duniya da rai
ba.........................





*kuyi hakuri plz na jina da kukayi shiru jiya ba lallai gobe ma ku jini ba sbd younger brother na
ba lafiya anyi admitting d'inshi kuma ni ke zama dashi, plz kuyi mishi adu'a bcos he need it*

#vote
#share
#comment




'Yar mutan Adamawa


��潤����潤����潤����潤����潤��







�� �� �� �� �� �� ���� IGIYAR RAYUWA��踫葉







�� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� ���� ��潤����潤����潤����潤����潤��

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo


�� �� �� �� �� �� ���� 'Yar mutan Adamawa

Page��∴��5儭����7儭������塚��5儭����8儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Ba irin tambayar da su dadda basu min ba ganin irin karewar da nayi kaman kud'in guxuri
amma na ki fad'a musu shi ne ma yace musu Ai basu ga yadda nayi jiki ba farkon auren kawai
yanzu cikin nan ne, ba yadda suka iya haka suka bar zancen ba wai don sun yarda ba, har
kunyan shiga mutane nake ji don duk wadda ya ganni se ya tanka..................

A haka aka gama buki muka koma Abuja zama nake na hakuri da juriya har na haifi musharraf
wadda tsananin rabo ne ya ajiye cikin, na shaa wahala sossai lokacin sbd nayi labour ba me
taimakona da kyar na fito tsakar gidan, mai gadi na ganina yaje da gudu ya kira mahmoud seda
ya 'bata lokaci sossai kan ya fito se juyi nake kaman bazan rayu ba, da ya fi to d'inma a kaina
ya tsaya yana min kallon banza ganin zan iya mutuwa su dadda su tuhumeshi yasa ya d'aukeni
ya wurga mota tare da figar motar zuwa asibiti......................

Naquda me wahala nayi kan na haifo shi a lokacin ya kira gida ya sanar musu inda mamaji ya
bashi umarnin maza ya biyamin kud'in flight in koma gida kar ya yarda yace mota zanbi, ba don
ya so ba Se don ba yadda ya iya haka ya biya yazo ya bani ticket a wulakance ko fuskan
musharraf be gani ba, da kanshi ya kaini airport wai baya so inje inyi missing flight in ja mishi
asara, bayan mun isa airport kan na fita a motar nace "baka mishi hud'uba ba" wata uwar
harara ya zabga min a zafafe yace "baki da uba ne? Ke kar ki yarda, don't you dare try me a
airport nan, bayan duk asaran kud'i da nayi da wadda zanyi dole In kun je gida se kin nemi
kakaba min banzan d'ankin nan to wallahi ki kiyayi biyan bashi na".................

A hankali nace "ni de d'ana ba banza bane" waro ido yayi kan yayi wani yunkuri na fita daga
motan da sauri, kwafa yayi tare da juya motarshi ya fice, trolley na naja rungume da d'a na da
tambaya har na gane yadda ake komai a airport se kuma karance karance a haka har na shiga
jirgi na zauna a sit d'ina da karanbani na d'aura belt don ban ta'ba ba................
A jirgin na taune dabinon dake jaka na na saka mishi a baki tare da zuba mishi ruwan zamzam,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login